BARRISTER SUHAIL

BARRISTER SUHAIL

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----22 

koda Iman ta fito ta daga toilet tayi mamakin ganin abinda Suhail yayi duk wani abinda zata buƙata sai da ya ajiye mata duk da zafin ciwon da take ji bai haka ta yin murmushi ba duk kusanci dake tsakanin da yaya Mubarak da yadda yake kula da ita bai taba yi mata haka ba 

Pad din ta dauka ta koma toilet. Bayan ta gyara jikinta tare da saka rigar da Suhail ya ajiye mata, ta dawo kan gado ta kwanta.”

Suhail ya goge gaba daya stain din dake kan tiles 

ba tare da nuna kyama ko wani abu duk da zai iya cewa wannan ne lokaci na farko da ya taba ganin jinin mutun haka 

yana ajiye mopper wayar ta soma Ringing ganin Sameer yasa ya fita ya buɗe masu kofar Sameer na gaba Maryam na biye dashi a baya har suka karasa cikin falon kan kujera Maryam ta gaida

"laflya qlau Maryam ina nihal"

"tana gidan mama tun jiya ma"

shiru ya biyo baya Sameer ya ce"miya same ta wai"

gira Suhail ya dan ja dan nauyin yi masu ma bayanin yake da kyar ya ce"Tana fama da ciwon mara, daga baya kuma ta fara bleeding .”

maryam ta gane mai yake nufi Sameer ya ce"Malan ka fito ka mata bayani yadda ya kamata ko dai haƙe wa yar mutane kayi har kaji mata ciwo in ba baka ba miya kawo ciwon mara da bleeding kuma kamar wata mai miscarrage"

harara Suhail ya wurga masa dan kunyar Maryam yake ji baiso Sameer yayi Wannan zancen a gaban ta ba

Maryam tayi murmushi ta ce"Abban nihal ba abinda kake tunani bane tun da ya fara maganar nasan inda ya dosa It’s just menstrual cramps 
yawan ci mata idan zasuyi period suna facing wannan ciwon"

Suhail ya ce"ki barsa ai ni bansan Lokacin da ya ajiye aikin Barrister ya koma na likita"

miƙewa Suhail yayi  yayi ya ce"tana ciki "

iman na kwance a kan gado ta rufe idanta amman ba bacci take ba jin an turo kofar yasa ta buɗe idan ta ganin Suhail tare da wata dan taji lokacin daya kirata a waya.

suhail ya ce"nurse zata dubaki"


zama tayi tana kallon Iman a ranta take yaba kyaun ta  ya juya zai fita Marya ta ce"ya suhail akwai maganin da zaka karbo"

"okay kimin text message"

yana fita Ta zauna kusa da iman cike da sakin fuska ta ce"Amaryar mu ya jiki"

kasa tayi da kai ta ce"Alhamdullilah"

suhail na fita ya dauki key din motar sa Sameer ya ce"ina zaka"

"zan amso masu magani a pharmacy"

tare suka fita da Sameer ya dawo magungunan kamar yadda Maryam ta tura masa 

ya kawo mata Iman ganin  Maryam tana ƙoƙarin hada Allura hankali ya fara tashi sai ta gama ta ce"Amaryar zan maki allura"

kai ta girgiza mata alamar a'a "Aunty bana san allura ko a gida ma magani Ammi ke siyomin"

yadda tayi maganar cike da shagwaba Maryam ta ce"ai ita kadai za'a maki ciwon ya tafi gaba daya"

Kuka ta fara kuma taƙi bari ayi mata Maryam ta ajiye allurar ta kalli Suhail ta ce"bari na tafi tunda baza ta bari a yi ba"

suhail ya ce"kiyi haƙuri"

tsawa ya daka mata ya ce"idan baki bari akayi maki ba wallahi sai na kaiki  asibiti kuma ince su dan neki su maki guda goma"

jin Hakan yasa hankalin ta shi ta ce"zan yadda tamin Amman sai ka fita"

dariya Maryam tayi ta ce"to yaya Suhail kaji mi ta ce"

juyawa yayi ya fita yana murmushin mugunta

Iman ta marairace ta kalli Maryam ta ce"Aunty dan allah kimin a hankali , kuma ki tambayi ko ita tasan bansan Allura zafi take min"

naji zan maki a hankali amman sai kim nutsu kar in ji maki ciwo"

Allurar na shiga jikin ta ,ta saki kara a na ganawa ta koma kan gado ta kwanta har lokacin kuka take.

Maryam ta fita wajen su Suhail ta basa ta faɗa masa yadda zata sha sauran magunguna nan

har bakin kofa ya raka su kudi ya dauko a aljihun sa  dashi kansa bai san ko nawa bane ya miƙa mata 

Sameer ya ce"wannan fa kudin minene,ko biyan tane kayi dan tayi wa matar Allura"

murmushi Suhail yayi ya ce"ni dai ban ce ba na bata ne ta siyawa nihal kayan wasa"

Sameer ya ce"kaga malan bama buƙata"

jan hannun Maryam yayi suka tafi 

Suhail ya koma ciki a ransa yana jin haushi  Wannan bakar zuciyar irin ta Sameer.

koda ya shiga dakin Iman a kwance ya iske ta tana bacci ya jima yana kallon cute face dinta da yankan bakin nan da Karami mai kama da na yara.

ya rasa mi zuciyar sa take game da iman tausayi take bashi komai tun Ranar da mami tayi mata wannan wulakanci da kuma sanda yaga hawaye na sauka daga idanun ta yasan tabbas bata ji dadin abin ba 

dubansa ya kai ga agogon dake kulle hannun sa ɗaya saura minti goma key motar ya dauka ya fita a kofar gida yayi sallar Azahar ya shiga mota bakin wani kamarin resturant ya tsaya ya masu order na launch kusan kala ukku dan aci bai san wanene iman zata ci ba 

a falo ya iske ta a kwance kan kujera tana kallo dan ciwon da take ji ya ragu da kusan kashi saba'in 

a gabanta ya ajiye takeaway ya dauki nashi ya wuce zuwa dakin sa har ya gama ci ya fito ya same ta ko kallan su batayi 

gaban ta ya tsaya ya ce"Miyasa baki ci abinci cin ba"

turo baki tayi ta ce"na koshi"

zama yayi kusa da ita ya ce"idan baki ci  ba zan miki irin abin nan na jiya da dare"

ji tayi gaban ya fadi tunawa da Abinda ya faru jiya tsakanin su da kalar matsar Suhail yayi kirjin wanda da safe ma da kyar ta iya wanka kuma har yanzu tana jin ciwon sama sama

dauko leda daya yayi ya bude sakwara ce da miya Agushi an cika ta da naman kaji ya saka mata cokali ya miƙa mata

hannun ta na rawa yasa ta karba ta fara ci yana lura da yadda take ci Kamar bata so 

spoon ukku kadai taci ta kallesa ta ce"idan naci amai zanyi"

amsa yayi ya rufe robar ya ce"okay fadamin mi zaki ci"

"Tea" ta fada cikin sanyin mura

tashi yayi ya ce"give me few minute"

koma wa tayi ta kwanta.

zeenat ce kwance a dakin mahaifiyar tana danna wayar ta yau kwana ukku kenan tana kiran Suhail a waya yana dan na mata rejecting tun tana damuwa har ta daina

wayar dake hannun ta fara kara ganin lambar Yusrah kawar ya sa ta daga 

bayan sun Gaisa yusrah ta ce"ina Suhail kwana biyu ko labarinsa baki min"

ajiyar Zuciya Zeenah ta sauke jin yusrah ta sosa mata inda yake mata kaikayi a halin yanzu ko Sunan Suhail bata so taji wani ya amta

"yana nan lafiya qlau"

Yusrah tayi shiru tana sauraren abinda Zeenah Zata ce ganin batayi magana yasa ta gane kila ma bata san da maganar ba amman ya zama dole ya fada mata abinda suhail ke boƴe mata kullum yana mata karyar zai aure ta sai gaji kuma ya zage chan yayi auren ya tare da matar sa

yusrah ta ce"ki hau whatapps na tura maki wani abu"

zeenah ta shiga ta fara dubawa mi zata gani invitation Suhail ne da kuma hotan da aka dauke shi da abba ranar bikin tayi zooming din hotan ta tabbatar da Suhail.

wayar ta saki ta fasa wani kara take hankalin mahaifinta ya dawo kanta 

da gudu tayo kanta tana tambayar lafiya 

wayar kawai ta iya nuna mata ta ma kasa magana