Sawun Giwa

01

by @ammimalami99

BAUCHI 
ATBU Teaching hospial. 


Dakin asibiti ne madaidaici inda wutar dakin fitilan dake tarr take haske duk wani abu dake cikin dakin. Y’ar windown dakin a bude take labulen da aka mata rufa dashi a janye an tsakale shi tsakanin rodin windown hakanne ya saka iska mai dadi ta wannan safiyar take shigowa ta cikin net din jikin windown zuwa cikin dakin. Marar lafiyar dake kwance saman gadon dakin karamar yarinya ce mai kimanin shekaru sha daya tana baccinta yayinda aka mata rufa da zanin gado fari. Layar drip ce sakale a d’an karamin hannunta ruwan da ake kara mata na diga ahankali suna bin layar zuwa cikin jijiyarta. 
Wata dattijuwar mata na zaune kan kujerar da aka tanadar ma masu ziyara a dakin tana magana da wata mata dake tsaye a gabanta ta jingina jikin y’ar durowar da aka ajiye gefen gadon. Matar bazata wuci shekaru talatin ba tana sanye cikin kayan nurses da babban hijabinta fari. 

“Ai Alhamdulilah ma da suka samu zuwa asibitin da wuri” Nurse dinda ke tsaye take fada. 

“Nake gaya miki arziki Khausar taci Hadiza, yanxu da ace basu samu adaidaita sahun nan ba ai da ba haka ba, likitan ma baki ga yanda ya zage yana yiwa Aishan fada ba”.

Hadizan ta amsa ta “Ai Inna da ba dan kokarin Aisha akan yarinyar nan ba da nace tayi wauta, ai tun lokacinda taga tana habon jinin nan yakamata ace ta kawo ta an duba ta kinga yanxu ga asthma ga sikila ga kuma wannan ai abun yayi yawa” ta karasa tana yarfa hannunta. 

Inna ta girgiza kai “Nima da laifi na ai, dan kinga ranar tashi mukayi ba wasu kudin kirki, gashi Mujitaba ba kiran da bata mai ba ya tura mata koh dubu goma ne ta kawo yarinyar nan asibiti amma dayake yasan kudin zata tambayesa sai yaki dauka. Niko dana ga haka sai nace mata ta barta kawai tunda habon ba mai yawa bane wata kila idan tasha jikon zogale zai daina ashe rabon zatayi wata kwanciyar asibitin ne”. 

Hadiza ta girgiza kai itama cikin tsananin jimami kafin tace
 “Toh wai Inna nikam ina maganar aikin nan da kikace yaron Malam ya samo mata?”

Inna ta dora hannu a habar ta “Inaa Hadiza ai jiyan ne intabiyu din karfe bakwai na safe zuwa sha daya toh kinga iwarhakan ai muna asibiti”.

“Kai subhanallahi, aikin nan rimi rimi ana farin ciki bayan fafutukar da ake tayi amma kaddara tazo ta gifta, toh yanxu kuma bazasu sake bata wata interview din ba”. 

Inna tace “Toh bansani ba, naga dai tanata kiran shi Ahamat din daya samo mata aikin bata samesa ba”. 

Hadiza tace “Toh ubangiji Allah ya kawo mafita ta alkhairi, Allah ya bawa Khausar lafiya” ta karasa tana raba jikinta daga durowar nan.  

“Ameen ya rabbi”. 

“Toh Inna bari ni na wuce dama matron Luba ce take gayamun kuna nan dan jiya ban shigo asibitin ba sam bansan an kwantar da Khausar ba”.   

“Toh shikenan Hadiza, mungode”. 

“Zan dawo in Allah ya so in Aishar ta dawo” ta karasa tana ficewa daga dakin Inna na mata sai anjima. 

Nurse Hadiza bata jima da fita ba wata matashiyar budurwa ta bude kofar dakin ta shigo. Madaidaitan idanuwanta da suka fada ta fara saukewa akan kanwarta Khausar dake kwance saman gadon kafin ta maida su kan Inna data juyo tana kallonta itama. Ta furta sallama cikin gajiyayyar muryarta dan ba karamar jigata tayi ba a cikin kwanaki biyun nan da Khausar ke rashin lafiya. 

“Kin dawo” Inna take tambayarta bayan ta amsa sallamarta. 

Aisha ta tattare hijabinta launin maroon na roba ta baya kafin ta zauna gefen gadon tana daga kanta ahankali. 

“Na dawo Inna, ban samu ganin likitan ba ma. Nurse din dai tace mun za’a sake kara mata wasu ruwan anjima tukunna sai su sallamemu”. 

Inna ta girgiza kanta “Ni Abu, yanxu har wasu karin ruwan zasu sake mata, shima wani kudin ne koh”. 

“Wallahi Inna ki bari kawai, harkar asibiti dama ai sai da kudi”. 

“ai shiyasa nake ce miki da kun wuce da ita nan center can dake Kobi da kudin basu kai haka ba” Inna ke fada. 

Aisha ta lumshe idanuwanta da suka mata wani nauyi har yaji yaji suke mata saboda rashin baccin kirki ga kuma gajiya. 

“Centre nan ba abunda zasu iya mata Inna, ba wasu likitocine a can ba”. 

Ta fadawa Inna dan tun ba yau ba Inna tasha maida magana akan asibitin nan. Dan duk lokacinda rashin lafiyar Khausar zata tashi Aisha bata taba yadda ta kaita wani karamin Healthcare center. Ita kuma babbar asibitin dukda basu kai private tsada ba din sai sun tatse ta tass tukunna wani sa’in ma harda bashi saboda kwantar da Khausar din sukeyi, ga test test, ga tulin magani da suke hadata dashi wanda dole sai an siye su. 

“Toh ai shikenan, Hadiza bata jima da fita ba tazo dubiya”. 

“Okay Allah sarki, zanje mu gaisa in sha Allah”.
Inna ta sake cewa “ Yaya, kin samu Ahamat din”. 

Aisha ta gyada kanta tana sauke idonta kan y’ar karamar wayarta ta Nokia data siya jiyan jiyan nan bayan ta siyar da sabuwar wayarta iphone XS max da saurayinta Mu’azzam ya siya mata saboda biyan kudin asibitin Khausar. 

“Na samesa Inna nayi magana dashi yace zai sake kirana. Toh ba’a jima ba ya sake kira yace ya musu magana sunce inje yau karfe sha daya”. 

“Alhamdulillahi” Inna ta fada cikin farin ciki kafin Aisha ta kara da “Har dubu ashirin ya turo mun a account dina yace a siya maganin Khausar dashi”. 

“Kaii amma Ahamat dinnan anyi d’an albarka. Allah dai ya saka mishi da alkhairi. Kinga kuwa da baiyi aure ba Aisha dana ce Mallam ya hada ku dashi dan ni wannan Mu’azzam din naki banga abunda yake tsinana miki ba. Kinga shi kuma wannan daga almajiranta Allah ya daga darajarsa gashi yanxu har aikin kamfani yakeyi”. 

Aisha ta lumshe idanuwanta tana sauraren mitar Inna kamar ko yaushe. Ba dama taga wani wanda suka taba sani ya samu rufin asiri batace dama zai auri Aishan ba. Ta sani tun ba yau ba mutuwar iyayensu ita da Khausar yazo da wani karin nauyi ne ga Inna harma da Mallam shiyasa tunda ta samu ta karasa karatunta take fadi tashin neman aiki koh zata ragewa su Inna wani nauyin dan rashin lafiyar Khasar dinma kadai wata dawainiyar ce. 

Karfe takwas da rabi tabar asibitin lokacinda Juwaira y’ar Inna tazo da karin kumallonsu. Sai data fara tsayawa suka gaisa da Nurse Hadiza wadda ta kasance wata makociyarsu ce da suke tsananin mutunci da ita kafin ta fita tana tsaida adaidaita sahu. Ya ajiyeta dai dai wajen gidansu inda wani d’an garuwa ke jidar jarkokin ruwansa daga cikin baro yana shiga cikin kofar gidan dasu. Ta bashi kudinsa kafin ta nufi kofar gidan wanda idan ta waje ka kallesa zakayi tsammanin karamin gidane.

Ta daga labulen da aka sa a y’ar karamar kofar wacca kana shiga y’ar karamar varenda ce inda kofar dakin mai gidan wato Mallam take a hannunka na dama. Saida ta tsaya ta kwankwasa kofar dake a bude labulen dakin kuma a sake yace mata ta shigo tukunna kafin ta daga labulen ta shiga. Yana zaune kamar ko yaushe saman dardumarsa dake gefen katifarsa kulolin karin kumallonsa ajiye a gaban dardumar yayinda yake lazumin Al-Qur’anin dake bude agabansa. 

“A’a Aisha yaya naga kin dawo, dazun nan Juwaira tace mun zata kai muku abin kari ai” Mallam yake fada bayan sun gaisa. 

Aisha dake tsugunne bakin kofar tace “Eh Mallam wajen aikin nan zan koma sunce zan iya zuwa Interview din”. 

“Toh Madallah, maza kije ki shirya ki tafi. Allah ubangiji ya bada sa’a”. 

“Ameen Ameen, nagode” Aishan ke fada. 

“Jikin Mamata da sauki dai koh”.

“Alhamdulillah da sauki kam dan sunce ma anjima da yamma zasu sallameta”.

Mallam ya gyada kai “Allah ya kara mata lafiya”. 
Ta amsa da Ameen kafin ta mike tana shigewa cikin gida. 

Cikin gidan fili ne babba da aka shafeshi da siminti yayinda ta kofar hagu kofofi uku ne a jere. Kofar farko toilet ne, sai dayar dake kusa dashi kuma bandakin wanka ne. Gaba dashi kadan anyi wata kofar wadda asali an yita matsayin store ne amma daga baya sai Muktar d’an yayan Mallam ya maidawa Inna shi shago inda take saka abubuwan siyarwarta wanda akasari kayan abinci ne irin su maggi da kayan dandano, man girki dasu tumatirin gwango, shinkafa da garin kwaki sai kayan miya irinsu timatir, tatasai, attaruhu da kuma allayahu. Kofar dake da d’an tazara dashi kadan a dayar bangon kitchen ne. 

A gefen daman gidan dakuna biyu ne wanda suma suke a jere. Dakin farkon na matar Mallam ne ta biyu Fatima wacca ake kira da Maman Nana kasancewar y’ar autarta kuma takwarar Aisha Nana ake ce mata. Katuwar deep freezer ce gaban dakin wacca Muktar ya siyawa Maman Nanar wanda take sana’ar siyarda kankara, zobo da kuma kunun aya dashi. 

Gefe da dakinta dakin yara matan gidan ne. Inna tanada yara maza uku, Murtala, Muhammadu da kuma Mujitafa wanda dukansu sunyi aure sai y’arta daya Juwaira. Maman Nana kuwa yaranta biyu kacal Hindatu wacca itama tayi aure sai Aisha wato Nana. 

A dayan bangon dakin dakuna biyu ne, na farko shine dakin Inna sai gefensa dakin da mazan suke zama a da kafin suyi aure aka maida shi store. Tsakiyar filin gidan kuwa katon tanki ne na ruwa da aka manna a bango kusada kofar kitchen sai wani famfo a kusa dashi da dan dakali da akayi wanda nanne wajen wanke wanke. Gefe dasu kuwa katon drum ne baki da mai garuwa keta sintiri zuwa cikawa sai kuma wasu jarkoki bakake wajen guda goma a ajiye. Bayan haka akwai wani dakalin shima da akayi can kusada store wanda robobi ne da bokiti ajiye samansa da butotcin alwala. Akwai wata kofar da zata fidda kai bayan gidan inda nanne Mallam ke kiwon kaji da kuma ragunansa.

Mallam Usman Bappah yanada Yaya daya Murtala. Allah yayi masa rasuwa da jimawa tun farkon aurensa yanada d’a daya Muktar, mutuwarsa ya saka rikon Mukhtar din ya dawo hannun Inna wanda a lokacin ta haifi Murtala daya ci sunan Yayan Mallam da kuma kaninsa Muhammadu. A lokacin Mallam bai kara aure ba dan suna zaune wani karamin gida ne mai katuwar rumfa a waje inda yake koyarda almajirai dan mallanci gadonsa sukayi shi da yayansa Murtala. Daga baya da zai kara aure ne suka dawo wannan gidan. Duka yara mazan Mallam sunyi karatu saidai cikin ikon Allah Mukhtar ne kadai Allah ya sakawa albarka a karatun ya samu aiki a wata babbar masana’anta. Cikin ikon Allah yayi aurensa har yakeda yara mata biyu Aisha sai kuma kanwarta Khausar wacca a wajen haihuwarta ne mahifiyarsu ta rasu. 

Da farko ma anyi tunanin Khausar bazatayi rai ba dan bakwaini ce kuma sikila dan maman nasu kanta sikilar ce. Sai bayan ta fara girma kuma aka gano tanada asthma abubuwan sukazo suka hade. Mukhtar rayuwa ta mai zafi dan sai rikon yaran duka ya koma hannun Inna kasancewar gidansa bashida wata tazara da gidan Mallam din. Da sassafe zaizo ya kai Aisha makaranta kafin shikuma ya wuce aiki.  Aisha na da shekaru sha uku lokacinda aka mahaifiyarsu ta rasu  kuma sai Allah ya dora mata tsananin kaunar kanwarta khausar. Dan bayan Inna ba wanda kuma yasha wahalar Khausar kamar Aisha. Tana dawowa daga makaranta koh uniform bata cirewa saita duba Khausar tukunna, in batada lafiya kuma kamar itace batada lafiyan kuma wannan abun sosai ya sakawa Mukhtar tsananin tausayi da kuma kaunar Aisha a ransa dan idan ya kalleta ma sak mahaifiyarta yake gani. 

Mutuwar mahaifiyarsu da shekaru biyu Allah yayiwa Mukhtar rasuwa. Irin rasuwar data daki ahalin gabaki daya dan ashe wai hawan jini yakeda shi bai wani maida hankali sosai ba akansa. Tun bayan mutuwar matarsa kuwa sai abun ya kara yawa har ya fara taba organs dinsa yana d’an rashin lafiya kad’an kad’an. Kuma cikin rashin sa’a asibitin da yake zuwa basu maida hankali sosai ba dan basu taba mai scan ba ma. Ana haka kuwa watarana kawai ya fadi ana kaisa asibiti kuwa akace stroke ne barin jikinsa daya ya mutu kuma bai cika kwanaki biyu ba Allah yayi masa rasuwa. 

Wannan rasuwar ta rikitar da Aisha matuka dan lokaci daya k’addara ta maida su marayu tun da kuruciyarsu. Duk lokacinda ta kalli Khausar kuwa wani nauyi ne takeji yana sauka kanta mai girma dan tana tuna yadda kowa idan ya shigo dakin Inna gaisuwa zai kallesu ne su biyu itada Khausar cikin tausayawa, suka koma ababen rauni, kalmar marayu ta zauna a kanta daram saboda yanda kusan kowa sai ya fadi wannan kalmar. Kowa ya kallesu sai ya kirayesu da wannan kalmar. Sun rasa uwa kuma sun rasa uba, wata iriyar jarabawar da wanda Allah ya jarabta da ita kadai zai iya ganewa, wanda yake maraici kadai ne a wannan lokacin zai kalli Aisha yace ya fahimci me takeji. 

Rayuwar gidan Mallam ba mai zafi bace dan ya daukesu tamkar yayansa, Inna kuma ta rikesu da amana kamar yanda ta rike babansu hakan ya saka basu taba kuka dasu ba. Maman Nana ma suna zaune ne lafiya da Inna kuma koh sau daya basu taba samun sabani da ita ba. Nana ce dai wacce suke sa’anni da Aisha suke samun matsala da ita shima kuma ya fara ne tun suna kanana. Tun lokacinda suke zuwa makaranta tare Aishan na fitowa da sakamako mai kyau ita kuma tana cikin wa’enda suke daukar position kusan na karshe. Duk lokacinda hakan ya faru kuwa Mallam zai bada kudi a siyowa Aisha chakulet yayinda ita kuma Nana baza’a siya mata komai ba. Wannan ya haddasa rashin son Aisha a zuciyar Nana matuka. Dan wani lokacin ma kawai sai ta tsiri fada da Aishan batareda ta mata komai ba. A wannan lokacin kuma Maman Nana takan dake Aisha dan Allah yayita da saurin hannu. 

Inna tana daki tanajin komai amma bazata tanka ba dukda tasan cewa Nanan ce batada gaskiya saboda kawaici irin nata, bataso tayi magana Maman Nanan taga kamar tana nuna su Aishan yaran dakinta ne ita kadai. Sai idan Aishan ta dawo daki tana goge hawaye sai ta rarrashe ta tana bata baki akan ta kasance mai hakuri, wani sa’in kuwa idan Nanan ta mata wata muguntar a idon Juwaira ta mammake Nanan suyi fada da yayar Nana Hindatu. 

Haka rayuwar gidan ta cigabar musu da dadi ba dadi har Hindatu tayi aure dan itama ta girmewa su Aisha sosai. Bata jima da aure ba Juwaira itama tayi aure saidai shekara biyu da aurenta kishiya tayi sanadin rabuwar aurenta sai kuma tun daga lokacin bata sake aure ba. 
Lokacinda su Aisha suna SS2 wani malaminsu ya bada shawara a biyawa Aisha ta rubutu jarabar WAEC tareda y’an karshen aji saboda kokarinta. Haka kuwa akayi ta zana jarabawar cikin kuma iko na Allah ta wuce. Nana na ganin haka ta taddawa Maman Nana hankali kan saidai Aishan ta jirata in yaso sai su shiga jam’ian tare. Inna bataso haka ba koh kadan amma dataga Mallam ya yarda da zancen sai batace komai ba dan itama a lokacin tafison ma Aishan tayi aurenta ta huta tunda akan su ne ma Mallam ya fara saka yara matan gidan Jami’a tunda Hindatu da Juwaira duk a sakandiri suka tsaya.

Shekara ta zagayo Nana tayi passing Jamb da kyar, wani d’an yayar Maman Nana Atiku ya karbi takardunsu yace zai nema musu admission a nan Bauchi State University dayake lecturer ne shi a can din. Admission letter ta fito Nana an bata Nursing yayinda ita kuma Aisha suka bata English. Wannan abun ya mugun daure hankalin kowa a gidan barin Aisha data sha kuka kamar me dan dai sunsan cewa Aisha tafi Nana kokari nesa ba kusa ba sannan results din Nana bai kai ace an bata Nursing ba amma sai gashi an batan. Abunda basu sani ba shine a wannan lokacin Nana da ma idonta a bude yake tarin samari ne da ita sunfi a kirga. A cikin samarin nata kuwa hadda shi Atiku d’an yayar Mamanta wanda shi yanada aure ma harda yara biyu. Shi sukayi magana dashi ta fada mishi abunda takeso dan shi da farko ma har yace kawai a bar Aisha ta samu Nursing din nata mana itama Nanar a samo mata kawai tunda kowa yasan shine babban burin Aisha amma tace a’a ya bata course dai daban da bazai amfane ta ba. Abun ya bashi mamaki amma dayake Nanar y’ar gidansa ce sai yayi abunda tace din kuwa. 

Da Uncle Murtala ya tambaye Atiku akan lamarin sai yace wai shima baisan inda matsalar ta fito ba sunsan halin jami’ar gwamnati sai ahankali tsab za’a iya chanja maka takardu da wani hadda karyar zai sake duba al’amarin yagani amma sai gashi har lokacin fara semester yayi ba wani labari. Abun ya taba Aisha sosai ta shiga damuwa ba y’ar kadan ba amma sai Mallam ya zaunar da ita yace mata ta cigaba da addu’a watakila hakanne yafi zamar mata alkhairi dan wani lokacin mutum zai so abu amma ba alkhairi bane sai kaga Allah ya musanya maka. Inna ma tayita bata baki itama kuma ta cigaba da addu’a har Allah yasa taji ahankali English din yana kwanta mata a rai wannan ne dalilin da ya saka ta dage sosai akansa dan dama can tanada kokarinta. Shekaru hudu cif ta gama ta fara aiki a wata Tutorial centre ta WAEC da NECO bayan ta kammala NYSC dinta. 

Ita kuwa Nana sai a lokacin ma taci rabin karatunta dan ba kokari gareta ba, ba kuma karatun takeyi ba. Carry over kam yafi a kirga wanda ta kwasa saida ta fara bin hanyoyi tukunna ta fara wuce aji. A lokacin kuwa idanuwanta sun bude sosai samari gareta manya da kanana, bata kula kowa kuwa sai mai naira a hannunsa. Yau tana motar wancan jibi tana motar wancan. Wannan rayuwar data keyi tana damun Aisha sosai dan ita suke daki daya da ita da daddare tana jinta tana wayoyinta. Islamiyya kam ba’a magana dan dukda kowannensu a wajen Malam suka sauke Al-Qurani da kuma wasu littafai saida ya sake sakasu Islamiyyar dake anguwarsu kasancewar ya daina koyarwa da jimawa saboda tsufa sosai da ya kamasa. A masallacine dai kawai yake koyarda manyan dalibai da suke zuwa koyon ilimin addini. 

Nana rayuwar da taga dama takeyi, yau wannan wayar ce a hannunta jibi watace. Maman Nana tayi fada tayi duka tayi zagi amma komai sai sake gaba yakeyi. Mallam kansa duk yanda yake kokarin yin tsaye akan Nana ta wuce duk inda yake zato. Ranar da Mujitaba ya kamata wani ya sauketa cikin wata mota da daddare saida yamata dukan kare karfi amma dukda haka Nana bata daddara ba. Maman Nana kuwa irin uwayen nan ne da basa iya rike halshensu in suna fada haka zakaji tana kiranta da sunaye wanda a zahiri binta sukeyi saboda bakin uwa kamar yankan wukane akan d’anta. 

A dayan bangaren kuwa Aisha tanada matukar natsuwa da kokari sosai wajen kame mutuncinta. Ita koh irin yawon nan na y’an mata koh tara abokai ba yi takeyi ba shiyasa akowani lokaci Nana ke mata kallon sakarya, bakauyiya wacca bata wayeba. Tasha samun samari wanda zasu zo suna sonta amma suna jin cewa iyayenta sun rasu kuma tana da kanwa sikila zasu gudu dan gani suke kamar Khausar zata zame musu nauyi suma. Shekara bata rufa ba Centre da Aisha ke aiki suka rufe saboda rashin samun dalibai kuma sai tun daga lokacin bata sake samun wani aiki ba. Shekara ta kusa cikewa kullum cikin fadi tashi ake wajen neman aikin nan amma ba’a dace ba. Murtala da Mujitafa suma sun gwada sa’ar su amma Allah bai kawo ba dayake shi Muhammadu a Azare yake zama da matarsa dan can yake aiki.

Mu’azzam ne tsayayyen saurayin da suka rufa wajen shekara daya suna soyayya dashi. A wani bikin kawarta suka hadu dashi yana cikin abokanan ango kuma tun lokacin ya karbi numberta wajen amaryar. Da farko bata baiwa zancensa mahimmanci ba dan haka ya mata kamar irin samarin nan masu karya dan ba laifi Allah ya zubawa Mu’azzam kyau. Fari ne tas dashi mai kyakkyawar fuska ga kuma saje. Irin wa’ennan mazan kuwa mafi akasari ta sha gani a kawayenta mayaudara ne shiyasa bata cika daukar wayarsa ba. Sai daga baya data lura kaman dagaske yakeyi tukunna ta fara kulasa. Shi bai gama karatunsa ba, computer yake karatu yana final year dinsa, ya fada mata kuma da mamarsa ya girma babansa ya rasu yana karami da yake kuma iyayen mahaifiyarsa nada rufin asiri sai suka dauki nauyinsa dan har mota garesa. 

Ahamad kuwa wani tsohon dalibin Mallam ne da yayi almajiranta wanda sati biyu da suka wuce ya kawowa Mallam ziyara bayan shekaru da dama. Ahamad din kasuwanci ya fada inda ya fara aiki da wani kamfani kuma Allah ya sanya masa albarka yakeda rufin asirinsa. Da Mallam yake basa labarin Aisha da kuma neman aikinta sai yake cewa ai kamfanin da yakeyiwa aiki sun buda wani sabon branch nan Yelwa ta kawo takardunta dan sun fara neman ma’aikata in sha Allah zai samo mata aiki. Sati daya chif kuwa ya sake dawowa da albishirin Aisha ta samu aikin zataje interview idan wani satin ya zagayo. Wannan abun ya saka mutanen gidan matukar farin ciki, Mallam yayita yiwa Ahamad godiya. 
Kaddara ta gifta ranar da zataje interview din sai suka tashi Khausar ba lafiya tun bayan asuba. Wannan ne dalilin da ya saka bata samu zuwa interview dinba a ranar sai washe gari bayan sunyi magana da Ahamad ya nema mata uziri a wajensu. 

***