01/2
~~~
Aisha tana taka kafarta cikin gidan kukan ragunan Mallam dake bayan gida suka fara mata sallama. Ta kofar kitchen ta hango Maman Nana tsaye gaban kantar kitchen din tana harhahada robobin zobonta. Aisha tayi sallama cikin siririyar muryarta data saka Maman Nana juyowa tana gyara daurin zaninta a kugunta.
“Wa’alaikumus salaamu Aisha kun dawo ashe, sun sallameku kenan”
Ta girgiza kanta tana karasowa gaban kofar kitchen din “A’a basu sallamemu ba sai anjima da yamma, interview dinnan zanje”.
Kalmar interview tazo da wani sauri ta daki kirjin Maman Nana da wani irin karfi, irin karfin daya saka ta jin kamar ta hadiyi garwashi ne. Allah ya gani tun Aisha na karama babu wata mugunta a ranta gameda ita. Koh sau daya bata taba jin rashin son yaran nan ba koh taji wani abu gameda su sai yanxu. Sai yanxu da girma yazo musu take ganin kamar Aishan na kokarin kama hanya daban da zata kaita ga nasarar rayuwa sabanin hanyar da y’arta ke kai. Halin da Nana ke ciki yana bakanta mata rai, irin bakin ciki da kowaci uwa takeji idan taga d’anta na kokarin fadawa halaka koh kuma kaucewa hanyar ubangiji.
Tun lokacinda Aisha ta samu aiki a Tutorial centre dinnan wannan abun da takeji a zuciyarta ya fara yin dashe a zuciyar. Ta kanyi kokari sosai wajen ganin ta kawar da abun daga ranta dan har lokacinda Aisha tabar aikin aka fara fafutukar neman wani bata sake jin komai a ranta ba sai sati biyu da suka wuce da Ahamad ya diro kafarsa cikin gidansu.
Samo mata aikin nan da yayi ya mugun tabata dan sai take gani dama ace Nana ce, ta gama makaranta har zata samu aiki a asibiti. Nanar ma da akayi tunanin ita takeda chance din samun aiki saboda course dinda takeyi amma sai gashi akace wai zakaran da Allah ya nufa da cara koh ana muzuru ana shaho sai yayi.
Dukda Aishan bata samu aikin ba tukunna amma dai kowa yasan kokarinta, kowa yasan cewa takardunta masu kyau ne duk inda basu dauketa aiki ba kuwa saidai idan wani abun suke nema ba hazaka ba.
Da farko tayi tunanin Aishan ta rasa damarta tunda gashi bataje interview dinba jiya amma sai yanxu data ambaci zata sake zuwa ne ta sake jin wannan abun. Wannan abun data kasa danne sa a zuciyarta lokacinda Ahamad ya kira yace ya samo mata aikin, interview din kawai zataje. Sai taji abun ya kara yawa kamar ya gama dasa kansa a zuciyarta ya kara girma hadda rassai.
“Ba jiya ne interview din ba?” Ta tambayeta tana kokarin hadiye abunda takeji a zuciyarta.
Aisha ta kada kai ahankali tace “Eh toh Yaya Ahamad ya musu magana dai sunce zan iya sake komawa yau”.
Maman Nana ta kada kai kawai kafin ta furta kalmar “Masha Allah”.
Aisha ta karaso kofar kitchen din tana leka murhun da itacensa basu gama mutuwa ba tace “Zan samu ruwan zafin wanka mama”.
Maman Nana data juya tana cigaba da dibar robobinta tace “Ga wa’enda na dama kunu can cikin tukunya sai kin sake dorasu sunyi zafi”.
“Yauwwa mama” Aisha ta fada kafin ta karaso cikin kitchen din wanda bangwayensa sukayi baki kirin tsabar hayakin girki. Ta bude tukunyar taga ruwan ba yawa sai kawai ta fita waje ta dauki bokiti daidai mai garuwan nan yana zubinsa na karshe.
“D’an juye mun sauran ruwan cikin bokitin nan dan Allah Sani”.
Sani yace “toh” kafin ya juyo kan jarkar sa zuwa cikin bokitin nata. Ya juye mata su ta dauki bokitin zuwa kitchen ta zuba kafin ta sake tadda wutar wanda a lokacin har Maman Nana ta hada robobinta ta debe su zuwa kofar dakinta ta zauna tana zuba zobon a ciki.
Daki ta wuce straight inda Nana ke kwance kan katifa tana sharar baccinta dan sarauniyar dama ba yanxu take tashi ba sai can tsakiyar rana tukunna. Dakin nasu ba wani babba bane sosai dan Katuwar katifa ce kasan dakin inda Juwaira da Nana ke kwana sai karamar katifar Aisha dake jingine jikin bango dan tana tashi take nade zanin gadonta ta tayar da ita. Kanta ce a gefe daya inda Nana ta jera kayan kwalliyanta sai wata y’ar karamar kofa wadda nanne yakamata ace shine drawer kayansu amma Nana ta mallake ta dan rufeta ma takeyi tasa mukulli.
Akwai y’ar karamar durowar gefen gadon Maman Nana da aka dora T.V akai ta sony kasusuwa ne jere samanta wanda Nana ke karbowa koh tayi renti. Sai akwati daya gefen sa inda suke sa zannan gadonsu dan duk a dakin Inna kayakkinsu suke yayinda Khausar kuma take kwana a dakin Inna.
Bayan T.V ta leka ta dauki makullin dakin Inna da Juwaira ta ajiye mata kafin ta sake fita taje ta bude ta shiga. Shima dakin girmansa sak kamar nasu saidai shi wannan akwai gado sai wata drawer dake cikin bango babba mai kofuna uku ga kuma kujeru guda biyu sai mirror din gadonta wanda shi zaka kalla kana shigowa cikin dakin.
Ta bude kofar gabaki daya tana sakin labulen kafin ta zame hijabinta.
Ta zauna gefen gadon ta saka hannunta cikin aljihun rigarta y’ar kanti tana fitoda ragowar kudin dake ciki da kuma Nokiarta. Ta tsurawa wayar ido kawai tanajin kewar babbar wayarta dan ba laifi ta saba da ita a y’an watannin nan data fara amfani da ita. Tayi farin ciki sosai lokacinda Mu’azzam ya kawo mata ita dan rabonta da babbar waya tun lokacinda tana 300 level datayi wata Blackberry wayar tazo ta fada ruwa ta daina aiki ana gyara ta sau daya kuwa wayar bata sake komawa dai dai ba. Tun tana lalacewa ana kaiwa gyara har tazo ta mutu gabaki daya, Allah ya taimaketa lokacin Uncle Muhammadu yazo ziyara da matarsa ya siya mata wata Samsung dan dama ta farkon Uncle Murtala ne ya siya mata. Itama kuma daga baya sai siyarda ita tayi saboda kudin maganin Khausar dan kasuwar Inna yanxu ba sosai take ci ba, Mallam ma kuma ragunan nasa duk rashin lafiya sukeyi shiyasa kudin suke wuya toh bataso kuma ta sake tambayarsa wani kudin shiyasa ta siyar da wayar ta siya karama.
Toh bayan Mu’azzam ya siya mata iPhone dinne kuma yanxu Allah yayi itama saita siyar da ita. Tunanin Mu’azzam ya fado ranta a karo na ba adadi. Rabonta dashi kwana uku kenan yanxu duk ta kirasa kuwa wayar bata shiga. Da sukaje asibiti da Khausar ta kira sa dan Mallam ma da sukaje asibitin tare dashi kudin da yazo dasu tun a gadon da za’a bata suka kare. Ga Uncle Mujitafa dama shi tun lokacinda Khausar din ta fara zazzabi zazzabi take kiransa baya dauka. Uncle Murtala shima wayarsa bata shiga ba. Data ga batada mafita sai ta danna mai kira amma ringing din duniya Mu’azzam bai dauki wayarsa ba karshe ma sai cemata akayi wayar a kashe shiyasa kawai ta fice sai kasuwar waya taje ta siyar da ita.
Ta tsurawa numbersa ido waccca tayi saving da M da heart a gefe saidai yanxu kasancewar ta maida sim din a karamar wayar ya saka heart din ya koma wata y’ar alama. Ta danna kira tana sakata a speaker taji wayar a kashe. Sai kawai ta yadda wayar kan gadon ta mike tsaye, inda sabo ta saba da wannan halin nasa tun tana fushi har ta daina tasa masa ido kawai dukda abun yana bakanta mata rai matuka. Excuses kala kala yake bata wanda wasu ma hankali koh dauka bayayi. Ta saka masa ido ne kawai dan duk ranarda yakaita bango zai gan wata fuska tata da bai taba gani ba dan ita a rayuwa ta tsani a raina mata da hankali.
Kudin ta dauka kawai, a ranta tana ayyana adadinsu kafin ta ciro wata jakar rataya a kafada ta y’an makaranta dake rataye cikin drawer kayansu jikin wata kusa da aka buga a bangon. Hindatu ta musu kyautar ta itada Nana lokacinda tana Final year. Jakar kuma dayake tanada kyau sai haryanxu bata lalace ba dan idan ka kalli jakar zakasan ba sabuwa bace amma bazaka aza mata shekarun datayi ba. Ta lalubo purse dinta ta saka kudin a ciki kafin ta mayar da ita ta rufe.
Sanin cewa ruwanta basu tafasa ba yasa ta fito waje bayan ta zame hularta ta gaba kadan gaban gashinta dake cikeda yalwar gashi daya kwanta saboda hular data sa ya samu damar bayyana kansa. Yanda gashin ya kwanta yayi luf gaban kanta sam bazakace kanta akwai kitso ba saidai da kitson dan satinsa daya cif Juwaira ce ma ta mata shi kasancewar ta iya kitso. Kananan gashi gareta a gaban kanta wanda basa kamuwa duk yanda za’a kamasu shiyasa akowani lokaci yake kwance gaban gashinta kamar ba’ayi kitson ba.
Ta janyo wata kujerar zamansu ta katako ta zauna tana taya Maman Nana zuba sobonta. Saida suka juyesa tas ta tayata sake kirga zobon tukunna aka sake tsomasu cikin robar ruwa saboda wanke zobon da ya zuba jikinsu ta fara jera mata su cikin freezer tata.
“Mama kankarar ma narkewa takeyi”
Maman Nana taja tsaki tana mika mata gorar data dauraye cikin katuwar robar dake gabanta tace
“Ai nepa ba sa kyauta min wallahi, tun jiya da safe fitarku asibiti suka kawo wutar kuma koh awa biyu batayi ba suka dauke shikenan kuma har yanxu shiru kikeji”.
Aisha ta karbi gorar tana sawa cikin freezer
“Allah sa dai su kawo wutar ki samu kankarar ta tashi kar azo siya kuma babu”.
“Ameen fa” Maman Nana ta fada.
Saida suka gama taje ta juye ruwan cikin robar wajen wanke wankensu tukunna taje daki ta tube rigarta ta daura zanin wankanta. Saida ta yafe jikinta da wani dankwali tukunna ta fito taje ta debi ruwan ta sirkasu cikin bokiti. Ta dauki bokitin da kwandon wankata ta shiga bandaki.
Bata jima ba ta fito ta shirya cikin wata jalabiya cream da Inna ta siya mata cikin gwanjon wata yarinya da akace wai a America suke zama ita da iyayenta.Toh kayan nata wai sabbabi ne bata wani sasu sosai ba a yanda matar take fada kenan kan cewa ai Inna tasan masu kudi bare wa’enda suke zama kasar waje wani sa’in ma bai wuci sau biyu suke saka kaya ba shikenan bazasu sake waiwayarsu ba. Duk cikin kayan ma da Inna ta daukar mata wannan rigar itace tafi kowacensu kyau itama kuma tana matukar son rigar dan sau kusan hudu kawai ta taba sakata.
Ta shirya cikin rigar kafin ta saka ribbon a shukun dake kanta tana daure gashin dashi ta dora farar hula ta yane kanta da farin mayafin rigar. Sosai kuma rigar ta fito da hasken fatarta mai kyalli sai idanuwanta da suka fada ne kadai dan harta suri jakarta zata fita ta sake komawa ta ja layin kwalli a idanuwan nata aikwa lokaci daya zanen kwallin ya kawata idanuwan bakin gashin idon yana sake fitowa radau. Dama ta shafa Vaseline a labbanta ta fice bayan ta rufe dakin Inna taje ta ajiye mukullin bayan TVn dakinsu.
Tayiwa Maman Nana sallama shima Mallam ta masa yana mata Allah ya bada sa’a.
A hanya ne kafin ta karasa babban titi ta kira Inna tana tambaya ya jikin Khausar har ta bata ma suka gaisa dan ta farka harta ci abinci. Taji wani sanyi a ranta jin muryar kanwar tata da dake matukar kauna kafin ta tari adaidaita.
“Hajiya ina zakije” Mai adaidaita ya tambayeta bayan ya tsaida kekensa.
“Yelwa zaka kaini”
“Muje toh”.
Ta taka kafarta ta shiga da bisimillah tana karanta addu’ar shiga abin hawa kuma har sun fara tafiyar mai keken yace
“Hajiya ina a Yelwa?”
“YK ventures” Ta fada sunan da zuciyarta ta haddace sa tun lokacinda Ahamad ya fadi sunan.
Sunan kamfanin da shine mabudi kuma asalin chanja rayuwar Aisha izuwa wata hanya daban tareda budo wani shafi na rayuwa wanda bata taba hango wa kanta shi ba.Sunan da kuma zai kasance shine mabudin wannan littafin gabaki daya.
Ma’abota karatu, hajiyoyina, yayyena da kuma kannena ina fatan kun shirya.
Ina fatan kun shirya tafiya cikin rayuwar Aisha dan fuskantar abunda YK ventures ya tanadar mana a tare. Ku shirya saboda wannan labarin zai taba zuciyarku, zai girgiza ku ya karya muku zuciya ya kuma sake gyara muku ita da yayyafin ruwan sanyin da aka jika furanni masu kamshi a cikinsu. Wannan alkawarin alkalami na ne!
Nice taku