1. Waye shi?
Alhaji Muhammad sadiq wani attajiri ne da yake cikin garin Abuja dake unguwar Maitama. Yana ɗaya daga cikin hamshaƙan masu kuɗin Nigeria. Dalilin hakan yasa ya zama sanennen mutum a duk faɗin ƙasar.
Ya mallaki gidajen mai bila adadin sannan yanada companies dayawa da ake sarrafa kayan abinci masu inganci, ga kuma tafka tafkan gidan gonakai.
ʼYar sa ɗaya tak a duniya. Sanadiyyar haihuwarta Allah yayi wa matarsa Maryama rasuwa shekaru goma sha tara da suka wuce. Bayan rasuwarta ne aka mayar da sunan ta zuwa ga yar data haifa. Alhaji Muhammad sadiq ya sake aure bayan shekaru huɗu.
Ya auri Hajiya zainab wadda ake ƙira da Umma. Hajiya Zainab bata taɓa haihuwa ba domin ita ba mace mai haihuwa bace. Dalilin mutuwar auren ta na farko kenan kafin Alhaji Muhammad sadiq ya aure ta.
Hajiya Zainab ta ɗauki son duniya ta ɗaura wa Maryama tamkar 'yar cikin ta. Tana matuƙar kula da ita sannan tana mata duk wani abin da uwa zatayi ma ʼyarta.
Hajiya Zainab ta shiga ɗakin Maryama tare da yin sallama. "Haa, dama baki gama shirin ba? Wannan Ai sai ku makara a fara banda ku. Duba lokaci," Ta ɗaga kai tare da nuna tafkeken agogo mai zanen ɗawisu dake manne a bango. "Tara da rabi fa, kuma naga a katin invitation ance za'a fara dinner ƙarfe goma. To yaushe kika gama shiri har kuka isa?"
Maryama ta ɗago kai itama ta dubi agogon cikin fargaba a lokacin da ta zaro dara daran idanun ta da suka sha eye makeup.
"Umma wallahi duk makeup ɗinnan ne yasa na makara. Gashi nace wa Hauwee tazo 9:30 dai dai..."
Bata rufe baki ba suka hango hasken fitilar mota daga window. Tayi maza ta je bakin window da yake hawa na biyu ta ɗaga curtain ta hango Hauwa na fitowa a mota daga kasa.
"Waiyyoh Umma ki tayani saka kayannan dan Allah. Yanzu zata hauro ta balbale ni da faɗa ban gama shiri da wuri ba."
Hajiya Zainab tayi dariya, "To matso na tayaki."
Maryama ta matsa kusa sannan ta tayata saka kayan yadda bazai ɓata mata kwalliya ba.
Babbar super ce mai muguwar kyau, kalar peach mai ritsin baki. Ancon dinner ɗin da zasu kenan na gefen ango. Angon ya kasance uncle ɗin ƙawarta Hauwa.
Ana cikin zuge mata zip suka ji sallamar Hauwa. "Eh! ai dama nasan baki gama ba sarkin ƙalula." Ta faɗa tare da zuwa kusa da Maryama tana galla mata harara cikin wasa. Itama nata ɗinkin ya mugun mata kyau sosai ta fito wata sarauniyar kanta.
"Umma ina wuni," ta ɗan duƙa ta gaida Hajiya Zainab.
"Lafiya ƙalau Hauwa. Kin bar gida lafia?"
"Kowa lafiya ƙalau Umma. Mama tace na gaishe ki."
Hajiya Zainab ta murmusa. "Ina amsawa. Idan kinje gida anjima nima kya miƙamin nawa gaisuwar."
Itama cikin murmushi tace, "Inn shaa Allahu zata ji." Hajiya Zainab ta fice ta barsu.
Hauwa ta sake galla wa Maryama harara. "Yanzu ko kinsan ƙarfe nawa? Ni kiyi sauri ki ɗauko ɗankwalin ki na ɗaura miki."
Maryama tayi dariya. "To Hauwee ai dole na." Tayi maza ta dauko dankwalin akan tafkeken gadonta ta miƙa mata. Nan da nan Hauwa ta naɗa mata haɗeɗɗen ɗauri. Hauwa gwana ce idan aka zo ta fannin irin waɗannan abubuwan.
Sunyi kyau sosai. Dukkan su kyawawa ne, kowacce nada madaidaicin fuska dake ɗauke da madaidaitan hanci da baki. Idanun su ba'a magana don kyau, gashi sun sha kwalli kamar a India. Dukkan su farare ne amma Hauwa tafi Maryama haske.
Su ba guntaye bane sanan ba dogaye ba. Tsawon su daidai yeke da average height na mata da dama. Su ba sirara bane sannan ba masu ƙiba ba, sai dai Maryama ta ɗanfi Hauwa da cika kaɗan.
Hauwa ta ɗauko hand bag ɗinta data jefa shi kan gado da zuwanta, ta fito da wayarta ƙirar iPhone latest design.
"Matso kusa na haska mu." Maryama ta Matso daf da ita cikin style irin na 'yan gayu sannan Hauwa ta ɗauke su selfie.
"Munyi kyau sosai. Bari kiga nayi posting a instagram page ina yanzu zakiga comments da likes buhu buhu." Hauwa ta faɗa a lokacin da take faman lallatsa wayar ta.
Maryama tayi dariya tace, "To Hauwee muje dai kar driver ya gaji da jira. Kinsan haka wancan karan ma da muka je Park a sallah yayi fishi yace mun shanya shi."
Suka fice a ɗakin tare da sanarwa Hajiya Zainab sun tafi. Tayi musu gargaɗin cewa su kula da kansu kuma su dawo da an gama dinner.
****
Sun isa gurin dinner ƙarfe goma da kusan rabi. Sun ɗan kwashi mintoci masu yawa kafin isowar amarya da ango. Tafi da ihu ne ya cika Hall ɗin a lokacin da amarya da ango suka nuna kansu. Kyau wurin amarya ba'a magana don kuwa ta haɗu ta haɗe har ta gaji.
Kayan da ke jikin ta ma kawai abin kallo ne bare kuma uwa uba fuska. Ango ma yasha kyau ga ƙamshi. Dukkan su kamar wanda aka tsamo daga randar turare. Sai hasken flash na waya da camera man ake gani ta ko ina don ɗaukar su hoto da video.
Muryar Ali jita ne ta fara tashi cikin hall ɗin har izuwa lokacin da suka isa gurin zaman su. Bayan wassu yan mintuna aka bude fili da addu'a sannan abokan ango da amarya sukayi speech tare da shan rawa. Hauwa ta tashi tsaye taja hannun Maryama.
"Tashi muje muyi rawa," Maryama tayi jim tana kallon ta.
"Bazaki tashi ba? Ke kullum haka kike dama sai kace wadda aka saki dole kizo." Maryama tayi fuskar zolaya ta miƙe tare da ɗaukan clutch bag ɗinta sannan suka nufi wajen rawa suka fantsama ciki. Hauwa juyi take yi kamar ba gobe tana dansewa. Ita ma dai Maryama tayi ƙoƙari ba laifi.
Bayan wassu mintoci masu ɗan yawa Maryama ta taɓo Hauwa ta mata Magana daf da kunnen ta tace mata ta gaji. Hauwa ta gyaɗa mata kai sannan Maryama ta koma inda suka zauna ɗazu.
Ta danyi jim tana kallon shagalin da ake faman sha. Ta kalli Hauwa sai tayi 'yar dariya cikin ranta tace oh su Hauwee iyayen shagali. Ta ɗauko wayarta ƙirar Samsung latest design, ta shiga video tana recording dai dai saitin Hauwa sannan sai ta fara ɗan zagaya wayar tana ɗaukar wassu mutane daban.
Tana cikin yi ta hango wani kyakkyawan mutum ta cikin wayarta. Zaune yake gaban dinner table dake ɗan nesa da inda take. Duk sauran kujerun dake zagaye da table ɗin babu kowa akai sai wanda kyakkyawan mutumin nan ke zaune.
Wani saurayi ne mai ƙwarjini, irin wanda zai cika maka idanu a duk lokacin da kallon ka yayi artabu dashi.
Ji tayi gaban ta ya faɗi ras!
Don kuwa shima inda take zaune yake kallo. Sai ta tsayar da wayarta cak dai dai kanshi bata motsa ba, ta zuba wa cikin wayarta idanu. Bayan sakanni ƙalilan ta farfaɗo daga kallon da take masa, ta tuna cewa ɗaukan shi take yi kuma ya sani.
Tayi maza ta sauƙe hannunta daya sha lalle da warwaro, sannan ta fita a ɗaukar videon. Jakarta ta buɗe sannan ta saka wayar a ciki, ta rufe ta ajiye a kan table.
Ɗago Idanun ta tayi ta kalli inda yake sai taga ya juya fuakar shi gefe bayan yaɗan kalle ta. Ajiyar zuciya tayi tare da ɗaukar bottle water ɗinda ke gabanta a kan table.
Hannu tasa ta buɗe murfin sannan ta tultula ruwa cikin glass cup dake ajiye a gefe. Ta ɗago glass cup ɗin ta shanye ruwan tas amma ji tayi kamar bata sha komai ba.
Ya salam...!
Me yake damu nane haka? Sai kace ban taɓa ganin namiji ba? Ta faɗa cikin zuciyar ta a lokacin da take faman zuba wani ruwan. Nan ta ƙara shanye wannan ma sannan taji alamun tasha ruwa. Ta sake wani ajiyar zuciyan. Tana son ɗaga idanu ta kalli inda yake amma ta gagara.
Kamar daga sama taji ance, "Maryama manyan mata. Wato kowa na shan shagali ke kuma kinzo nan kin zauna abinki."
Maryama ta ɗago kai ta kalli mai mata Magana. Murmushi ne ya baiyyana a fuskar ta.
"Hasina dama ana ganin ki? Rabona dake tun ranar graduation ɗinmu. Allah sarki ya kike?"
"Lafia lau wallahi. I hope it's the same with you. Naga Hauwa ai ana can ana kakkaryawa nace tunda naganta kema zan ganki." Hasina ta faɗa cikin maganar 'yan gayu da class.
Hasina kenan, yar gayu ce sosai. Ga kuma Allah ya mata kyau kamar aljana sannan itama tana ɗaya daga cikin 'yayan manyan Abuja. Magana daya biyu sai a saƙala turancin a ciki. Idan kuma baka iyawa da ita sai kaja gefe kayi kallo.
Maryama ta kalleta cikin sakin fiska. "Seventy percent correct, duk inda kika ga Hauwee zaki ganni. Meye labari?" Hasina ta samu kujera kusa da ita ta zauna tana cewa,
"Just dry dai for now. I'm missing you guys da kuma school life ɗinda mukayi. Yanzu muna nan babu wani abun yi. But soon zan fice Florida, a can nake so nayi karatu da yardar Allah. Ke fa? What's going on with you?"
Maryama ta kai kallon ta inda saurayin nan ke zaune.
Gefen fuskar sa ake hangowa wanda yake ɗauke da cikakken gira, kyawawan idanu da kuma dogon hanci. Tana iya hangowa madaidaitan lebban sa daga inda take.
Yana da 'yar doguwar haɓa mai ɗauke da cikakken gemu amma ba mai tsawo sosai ba, wanda ya samo asali daga doguwar sajen dake shimfide a gefen madaidaicin kunnen sa.
Yasha hula zanna bukar da yake kala ɗaya da tsadadden kayan jikinsa.
Maa shaa Allah,
Maa shaa Allah...,
Ta gangara da kallon ta zuwa ga madaidaicin dogon wuyan sa dake ɗauke da adam's apple, faffadan kafadarsa, ƙirjin sa...
"Maryama...! Maryama...!!"
Cikin rashin shiri Maryama ta dubi Hasina, "Na'am, ina jin ki Hasina, kika ce meye ma?"
"Lafiya kuwa Maryama? Tunanin me kikeyi haka? Like you were so out of space the whole time."
Maryama ta ce, "Sorry dan Allah kiyi hakuri. But ina jinki fa ba wai bana sauraron ki bane. Kika ce zaki tafi Florida batun karatun ki.
So zaki je ki karanci course ɗin da kike so kenan? Medicine. Kin taɓa sanar dani muna shool cewa kina sha'awan karantar likitanci."
Hasina tayi murmushi tace, "Ashe kina sauraro na. Ban gama decision akan course ɗinda zanyi ba tukunna. Amma ina son karantar likitanci gaskiya. I like it.
Ke fa? Meke faruwa dake game da ci gaban studies din ki."
Maryama ta dubeta tace, "Umm, ina jin ni ina Nigeria fa don gaskia bana tunanin Abba da Umma zasu iya haƙuri suga na fita waje nayi nisa dasu. Sunfi so su sani gaba suyi ta ganina. Batun course ɗinda nake so kuma, i think... computer science. I like it." Ta ƙarasa maganarta da murmushi.
Hasina tace, "Eh wannan gaskia ne. Ko ni zan bada shaidar hakan, ba zasu so kiyi nesa dasu ba, you'll leave them lonely. Anyways, zanso nayi introducing ɗinki ma yaya na.
My one and only ya Najib da nake baki labarin sa yana zama a Canada. Just last week ya dawo. Yazo hutu tare da bikin Fatima. Kinsan she's our cousin, groom ɗin kuma childhood friend ɗinshi ne."
Maryama ta gyaɗa mata kyau alamun ta gane bayaninta.
Tabbas Hasina tana ji da yayan ta Najib sosai. Sau tari tasha bawa Maryama labarin sa yadda yake son ta sosai da kuma yadda yake ji da ita duk da cewa bai cika zama a gida ba, wato Nigeria. Komai nata ya Najib ɗina yace zai min kaza, ya Najib ɗina ya bani kaza.
Maryama tace "Oh... Haka. Hauwee ta faɗa min ranan cewa amaryar cousin ɗinki ce. Kinsan mu muna side ɗin ango ne."
"Tabbas kuwa, shiyasa na ganku ke da Hauwa kunsha ancon groom's side. Mu kuma munsha anco ɗin mu na side din bride." Suka yi dariya.
Hasina ta ɗan yi dube dube cikin mutane. "Af, kinga yayan nawa ma har ya ɓace, dama he does that alot, kuna tare dashi amma sai ku rasa shi.
Da nake zuwa nan nafa hango shi zaune ta can. Yanzu haka ya fice waje ne ɗaukar business call."
Maryama ta sake gyaɗa kai alamun ta jadada lallai yayan Hasina busy guy ne. Tayi 'yar ajiyar zuciya tace, "Ba komai ai, akwai next time."
Hasina ta miƙe tsaye ta ɗan taɓo ta a kafaɗa. "To ni bari na koma wajen wanda muke tareda su kada suyi ta nemana. Dama cewa nayi bari na nemo ki nazo mu gaisa, amma kafin na tafi bari muyi selfie,"
Ta faɗa a lokacin da ta buɗe wayarta ta shiga camera. Maryama tayi murmushi tace, "Okay to bari na taso."
Suka yi posing cikin style irin na masu ɗaukar hoton zamani sannan flash ya haska kyawawan fuskokin su. "Thanks Maryama, it was nice seeing you again, call me."
Maryama tace "Okay bye, sai munyi waya."
Hasina ta gyaɗa kai cikin murmushi sannan tayi tafiyar ta.
A hankali murmushin dake fuskar Maryama ya gushe a lokacin da kallon ta ya koma inda ta hango saurayin nan ɗazu.
Baya nan,
Babu kowa kan kujerar,
sannan sauran kujerun ma babu kowa a kansu kamar yadda ta gani ɗazu a lokacin data hango shi. Ta ɗan shiga dube dube ko zata ganshi, amma hakan bai faru ba. Nan da nan taji ta shiga wani yanayi na rashin jin daɗi. A hankali ta zauna kamar ƙwai ya fashe mata a ciki.
To ko Ina yaje?
Ko tafiya yayi?
Zan sake ganin shi? Idan kuma ban sake ganin shi bafa?
Waye shi? Daga ina yake?
Tambayoyin da Maryama ke tambayar kanta kenan cikin ranta. Tana cikin wannan yanayin ta jiyo Hauwa na faɗin,
"To kuma dai, ya naga fuskar ki tana nuna alamar rashin jin daɗi? Yanzu yadda kowa yake having good time, ke kuma a naki yanayin ya sha ban ban da hakan.
Ko kin gaji ne sai mu wuce gida yanzu?"
Ta ɗago kai ta dubi Hauwa ba tare da tace mata komai ba.