2. New catch
Maryama sai faman latsa wayarta take yi sakamakon kasa bacci da tayi. Ta sake duba lokaci a fuskar wayarta, uku saura na dare. Ta ɗan runtse idanunta kamar mai jin ciwon kai sannan ta buɗe su. Cikin wayarta ta shiga videos, ta shiga kallon wanda ta ɗauka a dinner.
Waye shi?
Ta sake tambayar kanta da bata da amsa a lokacin da videon yakai daidai inda wannan saurayin ke kallon ta. Ta katse videon tare da rufe wayar sannan ta ajiye shi kan side drower.
Blanket ɗinta mai laushi ta janyo ta ƙara shigewa ciki a lokacin da ta kwantar da kanta kan pillow. Ta rufe idanunta tana fatan bacci yazo mata lokaci kusa. Jefi jefi takan yi motsi kan tafkeken gadon ta alamun bacci bai zo mata yadda take so ba.
Washe gari ta tashi da ciwon kai. Fararen idanunta sun ɗan yi ja, sannan kasan idanunta sun kumbura sakamakon rashin isasshen bacci. Bayan tayi wanka ta gama shiri ta wuce sashen mahaifinta.
Maryama tayi sallama tare da buɗe kofa, Hajiya Zainab ta amsa mata cikin sakin fiska.
"An tashi lafia Umma? Ya jikin Abba na?"
"Lafiya ƙalau Maryama. Likita yanzu ya bar nan kuwa bayan yayi wassu 'yan test haka. Ya sanar mana cewa Abban ki ya samu sauki sosai."
Farin ciki ya bayyana a fuskar Maryama. "Zan iya shiga na duba shi?"
Hajiya Zainab ta sarkar mata murmushi tace, "Sosai ma kuwa zaki iya shiga ki duba shi har kusha hiran kuma. Zan sanar da Binta ta hauro mana da breakfast sama sai muci tare."
"To Umma, bari na gaida Abba sai na sauƙa kitchen na taya ta kawo wa."
"Allah ya miki albarka Maryama."
"Ameen Umma." Sannan Maryama ta wuce ɗakin mahaifinta duba yanayin jikin nasa.
Sallama tayi ta bude ƙofa sannan ta shige. Kishingiɗe ta same shi akan gadonsa da pillow a baya. Idanunsa sanye suke da prescribed glasses sakamakon ciwon idanu da yake dashi irin na manyance. Hannayensa rike suke da jaridar Daily trust.
"Abba, lallai jiki yayi sauƙi sosai tunda naga har jarida kake dubawa." Maryama ta faɗa a lokacin da ta ƙarasa kusa da mahaifinta.
"Alhamdulillahi, sauƙi ya samu Maryama. Likita bai daɗe da ganina ba, yace na samu sauƙi sosai."
Maryama ta zauna a gefen gado da fuskar farin ciki. "Ai yanzu Umma take faɗa min. Allah ya ƙara maka lafia Abba na.
Jiya dana dawo daga biki naso na duba ka amma lokacin dare yayi kuma nasan kayi bacci. Sannu Abba na."
Alhaji Muhammad ya dubi 'yarsa cikin jin daɗi sannan ya ajiye jaridar a gefensa. "Ai ba komai. Ta ta faɗa min kin damu sosai."
Maryama ta gaishe shi cikin ladabi ya karɓi gaisuwa cikin sakin fuska.
Alhaji Muhammad ya kasance yana da ciwon hawan jini. Lamarin abin sai da addu'a da kuma kulawa sosai.
Ya sake duban 'yarsa da kyau cikin damuwa. "Ya naga idanun ki kamar suna ciwo? Naga kamar yau ɗin kin yi min wani iri Maryama."
Cikin fuska irin ta mai ɓoye damuwa tace, "Abba idanuna basa ciwo. Hidima ce dai irin ta biki to shine yau na tashi da ciwon kai. Kuma ba ma sosai yake damu na ba.
Anjima ƙadan zan daina ji inn shaa Allahu. Ƙila ma yunwa ne." Ta karasa maganar cikin dariya, shima dariyar yayi.
Maryama bata so yasan ta kasa bacci da wuri a daren jiya bare ya kai ga tambayar ta dalilin hakan.
"Abba bari na sauƙa ƙasa zanje kitchen na taya Binta kawo breakfast. Umma tace yau a sashen ka zamu karya."
Alhaji Muhammad ya murmusa sosai domin yaji daɗin hakan. "To maza ayi sauri a kawo don nikam har na fara jin yunwa."
Maryama tayi dariya sannan ta miƙe ta nufi ƙofa tana faɗin "Za muyi sauri mu hauro da komai."
****
"Ke dan Allah? Iyye...," Maryama ce a kan gadonta tana waya da Hauwa. Kwance take ruf da ciki a lokacin da take wasa ta siraran ƙafafunta. Wulla ƙafafun takeyi cikin jin ɗaɗin hirar su.
Hauwa ce take bata labarin an haɗata da wani saurayi ɗan gayu son kowa ƙin wanda ya rasa.
"Ya Habib ne ya haɗamu. Friends ne sosai. Munyi magana ta waya kafin ya dawo Nigeria. Haɗuwar mu a dinner ɗin auren ya Habib shine haɗuwar mu ta farko physically.
Maryama, na faɗa miki... he is insanely handsome!" Ta ƙarasa maganar ta cikin ƙaramar ihu tana murna.
Maryama tayi dariya sosai. "Iyye ƙawata? Maa shaa Allah. Amma dai nayi fushi baki faɗa min da wuri ba sai yau. Ai da kin bani labari da ɗumi ɗumin ta."
Hauwa ta sauƙe guntuwar ajiyar zuciya daga ɗayan layin. "Allah sarki Maryama kiyi haƙuri. Ranar da aka haɗa mu, ranar da mukaje dinner, ina cikin rawa ya Habib yasa aka kira ni.
Lokacin kin yi min nisa kina zaune can wata uwa duniya. Dana dawo gurin ki kuma sai naga alamun kamar bakya cikin good mood, ko meye ya sameki oho ɗinki dai, shiyasa ban sanar dake ba."
Maryama ta juya daga ruf da cikin da tayi ta kwanta a bayanta a lokacin da gashinta mai tsawo ya baje kan bedsheet. "To naji. Malama baki faɗa min sunan shi ba."
Hauwa tayi dariya. "Ai ban gama ba ke kike katse ni dama. Sunan shi Najib."
Maryama tace, "A'a, suna mai daɗi. Gaskia daga ji ma nasan ya haɗu kuma nasan ƙawata bata zuwa kusa da samari sai haɗaɗɗu. I can't wait to see him. Yaushe zaki kawo min shi mu gaisa?"
"Ai dole na kawo miki shi ku gaisa. Amma sai mun saba tukunna don kinsan ba wani sabo a tsakanin mu for now.
Ina ji a jikina cewa nayi masa kamar yadda yayi min. Sanda aka haɗa mu kada kiga yadda shimfiɗar fuskar sa ta kasance cikin fara'a. Sannan ga yanayin shi na cika wa mutum idanu da ƙwarjini, ya wuce tsammanin ki."
Nan Maryama ta shiga duniyar tunanin kyakkyawan saurayin data gani a ranar da suka je dinner. Shima ya wuce tsammani.
Ta sha ganin samari masu kyau da ƙwarjini amma bata taɓa ganin wanda yake da irin nasa ba. Kallo ɗaya tayi masa taji kamar ya fizge wani sashe na tunaninta ya tafi dashi.
Waiyyo ita!
Gashi babu abinda ya haɗa su bare har suyi kusa da juna suyi magana. Kuma nan da nan ya ɓace mata ba tare da tasan ina ya tafi ba.
Ko dai aljani ta gani?
Kai... ba aljani ta gani ba.
Dole yana da budurwa. Kai, wannan sai dai 'yan mata.
Ƙila ma da aurensa.
Anya matan sa basu fi daya ba kuwa? Ƙila ma biyu, koh uku, koh huɗu.
Hmm...,
yaya zatayi?
Meye abin yi?
"Hello Maryama," Hauwa na faman magana a dayan layin. "Kina jina?"
Firgigit! Maryama ta firgito daga kogin tunanin data tsunduma.
Tayi ajiyar zuciya tare da ƙanƙame wayarta kusan kunnen ta. "Sorry Hauwee, ina jinki fa. Kika ce meye ma?"
"Oh, na ɗauka da gangan kika share ni don kinji ina tambayar ki any new catch?" Hauwa ta faɗa cikin tsokana.
Maryama tayi dariya tace, "Kema dai kinsan idan akwai ai ke za'a fara faɗa wa. To kuma meye kike hanzari na baka na zuba?"
New catch?
Eh fa lallai new catch, tunda tunanin ta ya kasa samun hutu cikin kwanakin nan. Wancan saurayin yana yawan faɗo mata a rai alhalin ko waye shi bata sani ba. Daga ina yake ma bata sani ba, balle ta samu wata ƙaramar masaniya a kansa.
Taso ta bawa Hauwa labari amma sai tayi tunanin babu amfanin yin hakan.
"Okay to besty na yarda dake. Anyways jiya naga status ɗin Hasina a whatsapp. Wai sati mai zuwa birthday ɗinta kuma ta turo min message na invitation. Nasan kema tayi inviting ɗinki. So zaki je ko?
Nikam gaskiya bana tunanin zani don a day to her birthday zan tafi Kaduna." Hauwa ta faɗa, tana sauraron me Maryama zata ce.
"Ke dawa zaki Kadunan?"
"Ni da yaya zamuje. Shi zai kaimu ma."
Maryama ta tambayeta ko lafia. "Lafia ƙalau kawai dai zamu je ziyara ne, kinsan kaje kaga 'yan uwa akwai daɗi."
"Haka ne kam. To a gai da mutanen Kaduna. Batun zuwa birthday ɗin Hasina kuma, gaskiya kinsan ban cika fita ba sai dake. Abin zai min wuya... ni ɗaya ba daɗin zuwa"
Hauwa ta fara mata gunaguni. "Haba ke kuwa kije mana? To kije a madadi na. Kinsan Hasina bazata ji daɗi ba. Kuma naga dai kunfi shiri ma da ita. Jinin ku yafi haɗuwa, kinga kuwa idan baki je ba kinsan sauran."
Maryama tayi ajiyar zuciya cikin rashin yarda. "To naji sarkin wayo. Zanje amma saboda kin sani dole."
Hauwa tayi daria tace,"Yauwwa ko ke fa? To ki gaimin da Umma sosai kuma Inn shaa Allahu kafin na wuce Kaduna zan zo."
Itama Maryama tace a miƙa mata nata gaisuwar sannan wayar ta katse.