Rabin Raina

3. Tabbas shi ne

by @inkedbynadeerah


Misalin karfe huɗu saura na yamma driver yayi gidansu Hasina da Maryama. Sam bata jin daɗin zaman motan saboda Hauwa bata kusa. Motar shiru kamar anyi mutuwa banda karar a.c da ake jiyo wa. 


Yau kwana uku kenan rabuwan ta da Hauwa, tazo mata ziyara kafin wayar su jiya akan zata wuce Kaduna da yayanta. 


Takan maida kallonta daga screen ɗin wayarta zuwa window ɗin mota a lokacin da take ganin mutane da gine ginen da suke wucewa. Sun ɗan ɗauki lokaci kafin su isa sakamakon hold up da suka samu a hanya.


Sun zo daf da wani tafkareren baƙin gate security ya danna remote ya buɗe musu motarsu ta shige. Sun kwashi kamar sakan goma kafin suka isa frontage ɗin gidansu Hasina yayinda motarsu ke tafe a hankali kan hanyar dake gyare da kayan lambu, bishiyoyi masu tsawo da kuma furanni da suka sha gyara.


Driver yayi parking motar gaban tafkeken mashigar gidan. Maryama tasa hannu ta buɗe ƙofar bayan motar sannan ta fice. Da fitarta driver yayi hanyar fita daga harabar gidan. 


Maryama ta gyara mayafinta daya zagaye ƙasan wuyanta zuwa 'yan kafaɗunta a lokacin data shige cikin gidan tare dayin sallama. Masu aiki suka amsa tare da mata sannu da isowa. 


Ko ina a cikin gidan yana nuna shaidar kuɗi don haɗuwa. Akwai kayan alatu iri daban daban na zamani da aka zuba. 


Ta isa tsakiyar wangamemen living room ta hau matakalan da zai kaita sama, ɗakin Hasina. 


Ta wuce ɗakuna sun kai bakwai kafin ta iso na Hasina. Tun kafin ta shiga take jiyowa shewarsu tare da kiɗin da yake tashi sama sama. Murmushi tayi don tasan zata sha magana cewar ta sako atamfa bayan tasan girls party zata zo. 


Buɗe ƙofar tayi ta shige a lokacin da kiɗin yake faman shiga kunnenta sosai. Dukkan su suka waiwayo don suga waye. Nan fa wata sabuwar shewa ta tashi, suka yi caa kanta suna rungumar ta na murnanar sake ganin ta. Yawancin su sunyi secondary school tare da Maryama.


"Maryama dama zan sake ganin ki? Gaskiya an daɗe ba'a haɗu ba." Wata kyakkyawa a cikin su da taci top da wando irin na masu zuwa party tayi magana cikin ɗaga murya saboda sautin da yake tashi.


Sauran ma suka tofa albarkacin baki su. Duk cikin su babu wanda bata haɗe ba, ko kuma nace babu wanda kudi baya nunawa a jikin ta. Da ka gansu kasan 'yayan masu akwai ne.


Maryama ta sakar musu da faffaɗan murmushin da ya tabbatar musu cewa itama tayi murnuar haɗuwa dasu. "Naji daɗin sake ganin ku. Rabona daku tun ranar graduation ɗinmu a school. 


Ko ina celebrant ɗin take? Naga na shigo kuma ban ganta a cikin ku ba."


"Ta ɗan shiga bathroom ne. Amma Maryama, unmatchable dressing code... meyasa kika sanya atamfa? It's a party not a wedding event." Wata daga cikin su ta bata amsa tare da mata magana akan atamfar data saka. 


Sauran ma suka fara mata magana akan hakan. Maryama ta fara rarraba idanu irin na marasa gaskiya cikin wasa a lokacin da ta haɗa tafin hannayenta biyu tana musu alamar suyi haƙuri. 


Sukayi dariya da suka gane me take yi. Suna cikin haka suka ji an rage volume ɗin sautin da yake tashi. 


"She looks good in it. Style ɗin atamfar yayi kyau sosai." 


Hankalin su ya koma kan Hasina dake tsaye gefen speaker. Sanye take da wani red da golden gown mai dogon hannu daya bayyanar da surar ta. kwalliyar fuska kuma ba'a magana, dama ga kyau sai kuma aka kara da makeup. 


Kanta babu ɗankwali sai gashinta dake tufke tsakiyar kanta cikin donut bun. Kunnuwan ta kuma sanye suke da wassu dankunnayen barima irin na classic ladies. Tayi kyau matuƙa kamar a sace ta a gudu. 


Hasina ta isa daf da Maryama. "Ai na ɗauka ma bazaki zo ba don nikam har na cire rai. Kuma gashi you came late har an kusa a yanka cake."


"To ai gani na iso. Kuma kinsan yamma yayi yanzu, akwai hold up sosai a hanya shiyasa ban iso da wuri ba." 


Maryama ta ɗago hannunta dake ɗauke da gift bag "Ga gift ɗinki, Happy birthday." sannan ta ajiye inda aka tara tulin kyautuka. 


"Thank you na gode sosai. Kowa yace nayi kyau amma banda ke."


Maryama ta dube ta. "Kinyi kyau sosai, sauran sace ki ya rage." Dukkan su sukayi dariya.


Hasina ta sanar dasu nan da lokaci kadan zasu sauƙa ƙasa su yanka cake, sannan ɗaya daga cikin su taje daf da speaker ta ƙara volume suka ci gaba da rawar su. Suka janyo Maryama cikin su wai itama sai tayi rawa don sunsan halinta sarai zata iya zama tace nata kallo ne. 


****

Kishingiɗe yake kan kujern dake gefen gadon ƙayataccen ɗakinsa. Dogayen ƙafafun sa miƙe suke kan ƙaramin table ɗinda ke gaban shi, faffaɗan bayan shi na manne da pillow mai laushi.


Ya ɗan kwantar da kansa sannan hannayen sa naɗe suke ƙasan ƙirjin shi. Idanun sa rufe suke alamun yana cikin bacci. 


Wayar shi dake ajiye a gefen gado ne ya fara vibrating. Ya buɗe idanun sa a hankali irin na wanda yake cikin bacci ya dubi inda wayar take. Bayan yayi wa wayar kallon wassu sakanni ƙalilan ya rufe idanun sa har wayar ta katse. Call ya sake shigowa a karo na biyu, nan ma bai motsa ba. 


Bayan wassu mintoci masu ɗan yawa, ya miƙe da salati sannan ya kai hannun sa kan wayar ya duba lokaci ba tare da ya duba missed calls ba. Shida saura na yamma ya nuna a screen ɗin wayar. 


Tun da yayi sallar la'asar ya kishingiɗa a kujera ya fara aikin bacci bai masan lokaci yaja haka ba. laptop ya janyo dake ajiye tsakiyar gado, ya kunna don tura email ɗin wassu aiyukan daya ƙarasa dazu wa ma'aikatar sa dake ƙasar Canada. 


Bayan ya gama turawa ya sake duba lokaci yaga magrib ya kusa. Gashi kuma yana jin bacci har a lokacin, sai faman lumshe idanu yake yi. 


Yakan raba dare yana aiki a laptop sakamakon nisa da yayi da ma'aikatar sa, wannan shine dalilin da yasa bacci baya isan shi cikin kwanakin nan.


Ya Sanya takalman sa masu laushi na yawon cikin gida ya fice daga ɗakin. Ya fara sauƙa matakala zuwa ƙasa da niyyar zuwa kitchen ya haɗo fresh coffee. Shine kadai abinda zai kore masa baccin daya mamaye masa idanu. 


Yakan sha coffee mug daya zuwa biyu idan zai raba dare yayi aiki ko kuma idan ya tashi daga baccin sassafe. 


A lokacin da yake sauƙa ƙasa yana iya jiyowa hayaniya daga living room. Girgiza kansa yayi yana jaddadawa lallai ƙanwarsa da ƙawayenta masu hayaniya ne. Yana jiyosu suna ƙirge daga one zuwa three a tare, ya sake jiyowa suna faɗin happy birthday Hasina. 


Bayan nan kuma babu abinda ya biyo baya banda ƙarar ɗaukan hotuna na wayoyin su da kuma hasken flash, sai dariyan jin daɗi da sukeyi.


Asalin shi ba mai son hayaniya bane. Yafi so yaji guri shiru ba tare da unnecessary noise ba. Sauƙowa yayi ya raɓe ta gefe guda inda baza'a hango shi ba sannan ya wuce ƙofar tafkareren kitchen ɗin gidan. Coffee machine ya nufa tare da mug ɗinsa a hannu daya dauko daga mug sets, sannan yayi wassu danne danne a jikin machine ɗin. 


Bayan wani ɗan lokaci coffee ɗinsa mai zafi tare da kamshi ya zubo cikin mug har sai daya kusan cika sannan ya dannan wani button coffee ɗin ya daina zuba. 


Masu aiki dake gurin sai kwasar gaisuwa sukeyi tun yana amsa su har ya gaji yayi ficewar sa ba tare da ya sake kulasu ba. Hanyar daya biya ya sake bi ya hau matakala don ya koma ɗakin sa. 


*****


Maryama ta buɗe jakarta da niyyar ɗaukowa wayarta itama ta ɗauki celebrant hoto, sai taga baya ciki. Sai ta tuna ta barshi cikin ɗakin Hasina bayan sun gama selfies kafin su sauƙo. 


"Hasina na manta wayata a daƙin ki, bari naje na ɗauko don gaskiya duk hotunan dana ɗauka dake bada wayata bane." 


Hasina ta dube ta tace, "Muje tare, nima na manta na ɗauko Cannon camera ta wanda zan ɗauki hotuna da ita." 


Suka haura ɗakin tare. Maryama ta ɗauki wayarta dake kan dressing mirrow ita kuma Hasina tana faman dube dube.


"Maryama ko zaki sauƙa kafin nazo? Kada suji shiru coz naga i'll waste more time kafin na samu cameran nan."


"To shikenan ba komai. Idan baki samu ba kawai ki sauƙo, ina so muyi pictures da wayata."


Maryama sai faman duba screen ɗin wayarta take a lokacin da take tafiya hanya zuwa matakala. Hankalinta na kan hotunan da suka ɗauka tare da Hasina kafin su sauƙa living room yanka cake. 


Tana daf da taka matakalar farko kawai taji tayi karo da wani abu kamar gini. Jinta tayi gefe guda kamar an ture ta a lokacinda wayarta ta faɗa ƙasa kan rug ɗinda ke shimfiɗe a gurin. 


A gafen ta kuma ƙarar fashewar tangaran taji. Cikin kiɗima ta zaro idanu, ta ɗago kai tare da dafe ƙirjinta don ganin dame tayi karo. 


Idanun ta suka sauƙa kan blue shirt. Ƙasan shirt ɗin ya jiƙe da wani abu da yake ƙamshi mai kama da coffee. A hankali ta kai kallon ta sama don ganin mai jiƙaƙƙen rigan.


Ras! 


Gabanta ya faɗi a lokacin data kalli fuskar shi. Maryama taja numfashi cikin mamaki tare da buɗe baki cikin ruɗani, ta ƙara zaro idanu sosai. 


Da gaske ne?


Ko mafarki take yi? 


Domin kuwa fuskar wannan mutumin dake gabanta yana kama da wancan saurayin data gani a dinner ɗin bikin da taje da Hauwa. 


Ya kalli fasasshen mug ɗin daya tarwatse tare da ruwan coffee daya watse ƙasa yana kwalala. 

Ya mayar da kallon sa ƙasan rigarsa daya sha wanka. 


Ya runtse idanunsa alamun zafin ƙunan da yake ji a dai dai inda coffee ɗin ya zuba. 


Idanunsa da yanzu babu nauyin bacci ko kadan ya buɗe, ya kalle ta ba tare daya ce da ita komai ba. 


Itama Maryama idanu ta zuba masa tare da shaidar mamaki karara a fuskar ta. 


Ta kasa furta komai. 


Tabbas shi ne...! 


Shi ne saurayin data gani a dinner ɗin bikin data je tare da Hauwa. 


Kuma shi ne wanda ke cikin video ɗinda ta ɗauka a wayarta rannan.