RAGAYAR DUTSE

PAGE 7

by @nanahaleema11

  *RAGAYAR DUTSE.*


              ©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*

*Page 007.*



A hankali yake cin abincin kamar ba ya so, abincin ma cikin steeze ake cinsa, yana yi yana kaɗa ƙafa. 


Rabin abincin ya ci ya tashi daga kan dining ɗin ya dawo cikin falo ya zauna yana shan ruwa. 


Tunda ya zauna ake kiransa a waya, wata wayar ya ɗauka wata kuma ya share. 


A lokacin Jaafar ya sakko daga sama, ya kalle sa ya ce, "baza ka je aiki bane?." 


Ya ɗaga ido ya kalle sa ya ce, "zan je, sai dare."


Jafar ya ce, "to ka san kana da meeting ko? Kuma ka ba da time." 


Ya ɗan furzar da iska daga bakinsa ya ce, "na sani Jazy, zan san abinda zan yi." 


Jafar zai yi magana aka kira wayar Rehaan, ya duba ya ga video call ne kuma mahaifinsa ne. 


Sai da ya yi connenting da laptop ɗin gabansa sannan ya gyara zama, dan Abba ya fi so ya dinga yi masa magana da fulfulde, a ganin Abba in ba ya yi zai manta da yaren ne.


Rehaan ya ɗauki wayar ya ce, "jam bandu na Abba." (Barka da safiya). 


Abba ya ce, "Jam Noi a woni? Noi kuuɗe?” (Ya ka ke, ya aiki?).


Rehaan ya ce, "Jam Alhamdu lillah." 


Abba ya yi gyaran murya ya ce, "sai na ga ka rame, ina fatan kana lafiya?.." 


ya kalli Jafar ya ce, "Jafar ya yi rashin lafiya ne?." 


Jafar ya cire glasses ɗin idonsa ya ce, "bai yi ba, kawai kwana biyu baya son cin abinci, sai ya ce komai ba ya yi masa daɗi." 


Abba ya ce, "Rehaan yaushe zaka zo Nigeria?." 


Sai da gaban Rehaan ya faɗi, ya daure sannan ya ce, "Abba!." 


Abba ya katse sa ya ce, "kar ka yi musu Rehaan, wannan lokacin zuwan ka ya zama dole, bazan karɓi uzuri ba."


Rehaan ya ce, "Abba akwai aikin da zan je in yi a Jedda, a bari in na kammala sai in dawo nan." 


Abba ya bisa da kallo ya ce, "yaushe zaka je aikin?."


"Nan da four weeks."


"Ka dawo gida ka yi four weeks ɗin, in ya so daga Nigeria sai ka wuce."


Ya yi ajiyar zuciya ya ce, "to Abba, zan shigo in sha Allah." 


Abba ya ce, "yaushe?."


"next week."


"A'a Rehaan, this week nake so ka shigo."


RehAn sauke ido ƙasa bai kalli mahaifinsa ba ya ce, "To Abba, zamu dawo." 


Abba ya ce, "Allah ya kaimu." 


Rehaan ya amsa da amin, Abba ya ce, "Kar ka damu, haka rayuwa ta ke, yau da gobe sai Allah." 


Ya gyaɗa kai ya ce, "in sha Allah." Basu jima suna magana ba suka yi sallama Abba ya kashe wayar. 


Rehaan ya daki kansa yana yamusha gashin kansa ya ce, "bana son zuwa, bana son zuwa gida, bana son Jazy!." 


Jazy ya zauna a kusa dashi ya ce, "Baka so ka ga Mamy, Banisha da Riyya?." 


Ya kalli Jazy da idanunsa da suka fara canja launi ya ce, "ina so, amma bana so in je can. In ina son ganin su zan iya aikawa a ɗauko min su, amma bana son zuwa nigeria."


Jay ya ce, "ka yi haƙuri mu je." 


"Ina ji a jikina kamar akwai abinda zai faru in na je Jazy, Ina ji kamar in na je bazan dawo da rai ba."


"Ka cigaba da addu'a, babu abinda zai same ka in sha Allah." 


Ya sauke numfashi yana gyaɗa kai cikin gamsuwa da maganar Jazy. Ya san addu'a ce kawai maganin damuwarsa. Jafaar ya miƙe ya ce, "zan fita, Chef zai zo, sai ya yi maka abinda ka ke so." Ya sake gyaɗa kai bai ce komai ba Jazy ya fita.


Jazy bai jima da fita ba ya ji ana danna doorbell, kamar bazai miƙe ba sai kuma ya tashi ya buɗe ƙofar suka haɗa ido da Alma a tsaye tana murmushi. 


Kafin ya bata hanya ta shigo ta mayar da ƙofar ta rufe tana kallonsa tana murmushi. Fuskarsa babu murmushi, ya bita da kallo ganinta da jaket abinda bai cika gani ba. Alma ta yi pecking ɗinsa a kumatu tana shafa fuskarsa, wacce take da kwantaccen gashi mai kyau da ɗaukar hankali.


"Where is Jazy?" Ta faɗa tana kallon sa. 


Girgiza mata kai kawai alamun ba ya nan. Sai ta ji daɗi a ranta, ta riƙe hamnunsa suka zauna ta fuskance sa sosai ta ce, "me yake damun ka?." 


Ya ɗan kalle ta kafin ya janye ido ya yana girgiza kai alamun babu.


Alma ta miƙewa tsaye ta cire jaket ɗin jikinta ta juyo da fuskarsa dan ya kalle ta.


Ya kalle ta ɗin ya ganta sanye da riga ƴar ƙarama wacce bata wuce yace mata bra ba, sai ƙarmin wando wanda ko cinyarta bai gama rufewa ba. Ta zubo da gashinta tana sake juya gashin a gabansa. 


Ya ɗauke kai daga kallon ta, ya rasa meyasa ƙirar turawa bata burge sa, gasu dai farare tas, ko ina yana ɗaukar ido, amma sam baya so, bai sani ba ko dan a cikinsu ya tashi ne oho. Shi ko ƴan nigeria farar fata bata cika ɗaukar hankalinsa, farar fata in dai ba Mamy ba, bata wani burgesa.


Rehaan yi tsamani ba ya ji t ta zauna a kan cinyarsa, ya ɗan yi ƙaramin tsaki jin tana kai hannunt fuskarsa tana shafa gashin fuskarsa. 


A hankali ya ce, "Alma please." 


Ta matso da bakin ta kusa da fuskarsa ta ce, "Please Ray, i want to you" ta faɗa tana niyar saka bakinta a cikin nasa. 


Da hanzari ya janye ta daga jikinsa ya miƙe ya ce, "bana son haka, please ki je."


Ta bi sa da kallo tana sake matsowa kusa dashi, ya bita da kallo yana ji kamar kansa yana sarawa ya ce, "Alma ki ƙyale ni." 


Ta marairaice ta ce, "Why?." 


Ya rufe ido ya buɗe ya ce, "just go" ya faɗa yana hawa sama da sauri ya barta a tsaye a wajan. 


Alma ta bi shi kallo cike da takaici da baƙin ciki, ta kalli camera da ta saka a jikin laptop ɗinsa da take kan table, ta cire tana tsaki dan ba haka ta so ba, koda an ɗauki video yadda ya kamata yanayinsa bai yi daidai da yadda take so ba. So take ta yi masa video a yanayin da kowa ya gani ya san baya cikin hankalinsa, kowa ya san ya shiga wani ɓangare da ya zama private a rayuwarsa. 


A lokacin aka yi mata waya, tana ɗauka ta ce, "We fail, next time" ta faɗa tana saka rigar da ta zo da ita, ta ɗauki abinda ta zo dashi ta fita.


Rehaan yana hawa sama ya faɗa kan gado yana sauke numfashi cikin wani irin yanayi. 


Wani irin abu yake ji yana tafiya jikinsa, ya dafe kai cikin wani yanayin da bai san meye ba. 


Ya miƙe ya tsaya a gaban madubi yana kallon kansa, ya saka hannu ya hargitsa gashin kansa yana girgiza kai. 


A hankali ya dinga sauke numfashi, yana jan ajiyar zuciyar, ya diga maimaita Subahanallahi a zuciyarsa, a hankali ya fara jin nutsuwa tana shiga jikinsa. 


Ya buɗe ido a hankali yana kallon kansa, ya zubawa kansa ido yana ƙarewa fuskarsa ido, yana kallon yadda Allah ya yi halita mai kyau a fuskarsa.


Tabbas shi kansa ya san yana da kyau, indai kyau ake zance ya san yana sahun gaba a layin masu kyau. Shi ɗin mai kyau ne, kyau wanda ake kira kyau, kyau na shiga gasar masu kyau.


Bai san meyasa ba, yana jinsa kamar fanko, kamar akwai abinda ya rasa. Ya rasa me ya rasa haka? Meyasa yake jin kanasa a yanayin da yake ciki meyasa?.



         *******


Tunda suka gama haɗa record ɗin ranar suka rabu da Salim sai nufi hanyar gidan marayu da ta tashi a can. Sai sauri take yi sboda kar ta je an kulle gate, dan yamma ta kusa ta san ƙarfe shida ake rufe shiga.


Tun daga gate ta ka gaisawa da mutane cikin raha da wasa da dariya, kowa ya santa, tunda gidan gidansu ne,  a nan ta tashi, ta rayu, ta yi makaranta, da komai da komai. 


Kai tsaye office ɗin wacce suke kira da Mama ta nufa, ta ɗan yi knocking kaɗan aka bata damar shiga ta tura ta shiga da sallama.


Mama ta amsa kafin ta ce, "A'a Islaha, kece tafe?." 


Ta ɗan yi murmushi ta ce, "ni ce. Ina yini?."


"Lafiya lau, ya aiki?."


"Alhamdu lillah."


"Yau ke ce kika shigo?."


"Eh ni ce, na kawo ziyara ne."


Mama ta ce, "kin kyauta kam. Gashi ƴan uwan naki basa nan, sun ɗan fita." 


Da mamaki ta ce, "sun fita kuma Mama, yanzu shida ta kuaa, daman ana kaiwa after six a waje?."


Mama ta ce, "tunda na ce basa nan sai ki yarda ba nan, kin san suna sana'a. Ɗaya tana ƙunshi, ɗaya tana zuwa koyan ɗinki. Na san yanzu za ki gansu."


Islaha ta ɗan girgiza kai ta ce, "shikenan, in sun dawo ina gaishe su" ta faɗa tana ɗaukar handbag ɗinta ta fita.


Mam ta bita da harara ta ce, "sai da na faɗa mata yarinyar nan tana da matsala amma ta ce ita ba haka ba. Mtsw! Ni na san matakin da zan ɗauka a kanta, in ba haka ba akwai damuwa babba. Yarinyar  nan ƴar jarida ce, zata iya aikata komai, dan ba mutunci ta cika ba."


Islaha lokacin da ta fita cikin gidan ta shiga, ma'aikata gidan suna ta gaisawa kafin ta shiga asalin ɗakin da take kwana. 


A guje ƴan mata biyu suka taho wajanta suna faɗin, "Adda Islaha." 


Suka rungumeta itama ta rungume su tana murmushi ta ce, "Ƙanena ya ku ke?." 


Ɗaya daga ciki ta ce, "Lafiya lau muke Adda, jiya na kira ki a waya baki ɗauka ba." 


"Ayya ban gani ba ma, da na gani a guje zan kira ki Hafsy." 


Ta ce, "ku zo mu je daga waje."  


Suka fita suna hira, cikin nishaɗi Hafsy ta ce, "Adda tunda ki ka bar gidan nan ba ya yi mana daɗi wallahi." 


Ta yi dariya ta ce, "ni kaina da tunanin ku nake kwana nake tashi. Yanzu meye labari? Ina su Humaira da Sauda? Ban gansu ba."


Hafsy ta ce, "Hmm!" Ta faɗa tana kallon bayanta alamun bata so ta yi maganar a ji. 


Zainab ta ce, "Adda lamarin Sauda da Humaira sai addu'a kawai, yanzu sai su kwana biyu basa cikin gidan nan." 


Islaha ta gyara tsayuwa ta ce, "ina suke zuwa?."


"Waye ya san inda suke zuwa Adda?."


"Kuma Mama ta san suna fitar?."


Zainab ta ce, "wani lokacin ma tare da ita suke fita da ita." 


Ishala zata yi magana suna ji an ce, "Ke Zainab, Hafsa! Ku koma ciki!. Bakwa ganin yamma ta yi ne?."


Islaha ta kalli Mama sannan ta kalli su Zainab, ta ce, "Ku koma, zamu yi waya." 


Suka gyaɗa kai suka koma. Mama ta ce, "lokacin ziyara ya ƙare, sai wani lokaci." Islaha bata ce komai ba, ta wuce ta fita daga wajen.


Tana fita Mama ta koma office, ta ɗauki waya tana zagaye tana jira a ɗauka. Ana ɗauka ta ce, "Ni fa yarinyar nan Islaha tana bani tsoro, kun san yarinyar nan ƴar jarida ce, abu kaɗan zata yi ta saka a shiga tashin hankali."


"Yanzu nan na tarar da ita ta tsare yara tana yi musu tambayoyi, kun san tana da yawo, kuma jarida aikinta ne, dole mu samu mafita kafin wani abun ya zo ya faru."


Ta yi shiru alamun ana bata amsa sannan ta ce, "ya dai kamata, ya kamata a san abinda za a yi, in ba so ake lamari ya lalace ba." 


Ta sake gyaɗa kai ta ce, "shikenan" ta faɗa tana kashe wayar tare da buɗe window tana kallon islaha a harabar gidan.


Ta girgiza kai ta ce, "tauraruwa mai wutsiya, ganin ki ba alkhairi bane. Kin bar gidan ma baza ki bari mu yi rawar gaban hantsi ba. Ina god…