PAGE 8
*RAGAYAR DUTSE.*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 008.*
Juwairiyya ce take fitowa daga apartment ɗinsu, ta hangi Janan ta dawo daga wajan aiki ta karɓo kunun sadaka da ake yi daga wajen masu aiki.
Juwairriya ta ce, "Janan!." Janan ta tsaya tana kallon ta har ta ƙaraso kusa da ita ta ce, "Riyya ya aka yi?."
Riyya ta ce, "Jibi Hamma zai dawo."
Janan ta buɗe ido da mamaki ta ce, "don Allah?."
Ta yi dariya ta ce, "wallahi da gaske, kin ga key ɗin apartment ɗinsa, zan je in gyara masa."
Janan ta ce, "bara in canja kayana na zo mu je, ina zuwa" ta faɗa nufar part ɗinsu a guje.
Janan da guje ta shiga part ɗinsu, Mama ta bita da kallo ta ce, "ke kuma daga ina haka?."
Cike da zumuɗi ta ce, "Hamma Ray ne zai dawo jibi, zamu gyara apartment ɗinsa ne."
Mama ta bita da kallon takaici ta ce, "shine ki ke zumuɗi haka, kamar wacce aka yiwa albishir? Kuma duk ma'aikatan gidan nan a rasa wanda zai gyara masa sai ke?."
"Bani zan gyara ba fa Mama, ni da Riyya zamu gyara."
Ta taɓe baki ta ce, "sai ki je ai."
Janan ta shige ɗaki ba jimawa ta fito tana sauri, Mama ta tsayar da ita ta ce, "Tsaya Janan."
Ta tsaya tana kallon Mama, Mama ta miƙe ta shiga ɗaki ta ɗauko wani abu ta miƙa mata ta ce, "karɓi."
Ba musu ta karɓa tana jiran ƙarin bayani. Mama ta ce, "maganin tsari ne na karɓo masa, ki ɗaga kafitar da yake kwana ki saka a ciki, kin san yanayin da yake fama in ya zo gidan nan, wannan zai taimaka masa sossi.
Janan ta juya abin a hannunta ta ce, "Amma Mama meye wannan ɗin?."
Mama ta ce, "kamar yanzu na ce miki maganin tsari ne ko?."
Janan ta yi shiru tana kallon abun. Mama ta ce, "kuma in za ki saka, kar ki bari Juwairiyya ta gani."
Janna ta ɗan yi sak kamar bata yarda ba, sai kuma ta gyaɗa kai ta fito daga ɗakin jikinta a sanyaye.
Mama ta yi muemushi ta ce, "dakyau, dake zan dinga amfani Janan, tunda yana cin abin hannunki ai zance ya ƙare. Sai na ga bayan Rehaan wallahi, ba ta hanyar mutuwa ba, ta dankwafar dashi ya daina motsin kirki" ta faɗa tana komawa ta zauna tana kaɗa ƙafa, tana aiyyana irin abubuwan da zata yi masa.
Janan ta wuce apartment ɗinsa da yake kusa da na Abba.
Wajensa ba kamar wajensu Mama yake ba, dan shi sai ka shiga gate ka haɗu da lafiyayyen compound sannan zaka je ƙofar falon.
Compound ɗin yana da girma, ga motarsa nan a ajjiye, dan yawancin motar da yake hawa ba a gida yake barinsu ba, suna hannun Shams babban yaronsa a ɓangaren kula da lafiyarsa.
Ɗawisu yana ta yawo a compoud ɗin, ga flowers masu matuƙar. Ga gazebo guda biyu a compoud ɗin, kamar ba a gidan apartment ɗin yake ba. Kamar gida ne mai zaman kansa, dan girmansa da yadda yake a kammale.
Kaf gidan daga ɓangaren Abba sai nasa ne kaɗai suke da upstairs, amma ko ina babu sama sai wajensa kaɗai.
Janan ta wuce corridor, ƙofar falon ma mai thumb print ce, amma akwai code da ake amfani dan a buɗe, sai kuma card da ake buɗe ƙofar dashi kamar atm card.
Falon babba ne sosai, wanda ake kira sa luxary, irin wanda babu tarkacen banza sai kaya masu amfani. Falon kamar na turawa, komai tsaf dashi cikin tsafta. Ga ƙhamshin turarensa ya gama kama ko ina na apartment. mai girma sosai wanda yake ɗauke da komai da komai a cikinsa, har kitchen akwai da duk kayan amfani.
Ta wucce falon zuwa stairs, ta hau a hankali har ta buɗe ɗakin wani madaidaici falon mai kyau da ɗaukar hankali. Akwai bar a falon daga cen gefe, an yi adon glass cups da kujeru masu kyau. Sai bedrooms guda biyu kacal, sai library da wajen motsa jiki.
Tare suka sakko ƙasan, suka fara gyara main parlour ɗin suna yi suna hira. Suka gama da parlour suka hau sama, nan ma suka gyara shi duk da babu wani dauɗa. Daga ban suka shiga bedroom ɗinsa. hira suna gyarawa duk da babu wata dauɗa sai yar ƙura kaɗan.
Babban ɗaki ne sosai ba kaɗan ba, yanayin girman ɗakin sai kayan ciki suka zama ƴan kaɗan kamar ba a saka komai ba, dan space ɗin da yake ɗakin tsaf za a saka wasu funiture ɗin set biyu kujeru ma.
Bed ɗin yana tsakiyar ɗakin fari tas dashi, hatta bedsheet ɗin da komai na kai fari ne tass.
Sai mirror da yake can gefe a ajjiye, babu wani tarkace a kai sai turaruka masu yawa.
Daga can gefe akwai glass door, cikinsa babban falo ne da tv da komai. Kujerun ciki farare ne suma, kujerun kamar gado kamar kuma kujeru, komai tsaf.
Sai prayer room an yi sa a can gefe kamar masallaci, girmansa mutum biyu ne kacal zasu yi sallah. An yi masa ado mai ɗaukar hankali, ga sallaya masu kyau a ajjiye akan carbinet. Sai alkur'ani da yake ajjiye, sai azkhar da jarbi. Komai na prayer room ɗin fari ne tas, iya kallon wajen ma nutsuwa zai baka balle ka yi sallah a ciki.
Wardrobe ɗin falon ƙatuwa ce sosai, tana gefe a ajjiye kamar babu ita.
Riyya ta ce, "Janan zan shiga bathroon, ki gyara nan."
Janan ta gyaɗa kai ta fara gyara kan gadon, abinda Mama ta bata take juyawa a hannunta tana tunnain ta saka ko kar ta saka, kallon ƙofar banɗakin ta yi ta ga bata hango Riyya, ta yi ajiyar zuciya ta fara ƙoƙarin sakawa ko zata shiga.
Daƙyar ta saka ta daga gefen wajan pillow, ta gyara ɗakin tsaf ta bi bayan Riyya zuwa banɗakin, ta tarar da ita a wajan closet ɗinsa tana gyara masa kayansa. Closet ɗin ma babba ne, komai na sa yana ciki, hatta carbinet na takalma duk suna ajjiye a wajenZ
Sun jima suna gyarawa sannan suka fara goge goge, suna yi suna hira har suka gama suka fita kowa ya wuce wajan babarsa.
Mamy tana ganin shigar Riyya ta ce, "har kin gama?."
Ta ɗaga kai ta ce, "na gama, ni da Janan mu ka yi."
Mamy ta bita da kallo ta ce, "Riyya ba sai da na faɗa miki kar ki je da wani ɗakinsa ba? Sai da na faɗa miki kar ku tafi da wani ki tafi ke kaɗai ko?."
Ta ce, "Mamy gani na yi Janan ce, bata da damuwa, tunda har abincinta yana ci."
"Ni ai ban ce ga wanda zai je ga wanda bazai je ba. Kai tsaye na ce miki ke kaɗai, ke kaɗai za ki je, in baza ki iya ba ki bar ni nayi. Meyasa za ki tafi da Janan?."
Juwairiyya ta ce, "ki yi haƙuri, ban ɗauka zuwa da ita zai ɓata ranki ba."
Mamy ta yi ajiyar zuciya kawai bata ce komai ba, tana tunanin irin yanayin da ɗanta zai kasance in ya dawo gidan.
Janan tana shiga wajan Mama ta tare ta, ta ce, "kin saka?."
Ta ɗaga kai ta ce, "na saka Mama."
"Kin tabbatar kin saka dai ko?."
"Na saka mana Mama."
Mama ta yi dariya ta ce, "Allah ya yi miki albarka; na san kina son Rehaan. Shiyasa na zaɓe ki ki saka masa, na san bakya son komai ya same sa. Je ki ki huta kin dawo daga aiki kin gaji."
Bayan wucewarta Mama ta kalli Sameer ta ce, "mu jira dawowarsa, wanann zuwan na mu ne." Sameer ya ce, "Haka nake so na ji Mama, Allah ya bamu nasara.
*****
Ishala da ta fito ta tarar da babbar yayyar Saheer Adda Sa'ida a zaune. Islaha ta yi murmushin jin daɗi da ta ganta, dan kaf gidan ita kaɗai ce mai sonta, daga ita sai Hamma.
Islaha ta ce, "Adda sannu da zuwa."
Ta yi murmushi ta ce, "Hajiya Islaha, tun ɗazu nazo aka ce baki dawo daga wajan aiki ba. Gashi har ina niyar komawa dare ya yi."
Ta sake yin murmushi ta ce, "ina yini."
"lafiya lau Islaha, ya aikin?."
"Alhamdu lilah. Ina Nabila?."
"Su Nabila suna gida, suna gaishe ki."
Ta yi murmushi ta ce, "ina amsawa" daga haka ta ƙarasa wajan abinci.
A lokacin Saheer ya shigo ya zauna suna hira, ta zubo abinci ta zo zata koma ɗaki.
Adda Sa'ida ta ce, "Islaha ki zo ki zauna a nan mana."
Ta ɗan kalli Mama, ta ga bata harare ta ba sai ta dawo ta zauna, dan tashin hankali ne bata so ita.
Saheer ya ce, "ni mamaki ki ke bani Adda, har nawa Nabilan take da zaki fara tunanin wai bata yi aure ba? Gabaɗaya shekarun ta ashirin fa, har yaushe ta kai matakin yin auren da zaki ɗaga hankalin ki?."
Ta taɓe baki ta ce, "ku dan ba a gidan kishiya ku ke bane, shiyasa baza ku san abinda nake ji ba, wallahi da Mama tana da kishiya da yanzu Labiba da Hannatu sun ɗaga hankalinsu akan aure zasu yi. Ana nan ana yar musu da magana kan sun ƙi aure, musamman in suna da ƴan uwa sun yi sun barsu."
"To a yar mana, duk abinda mutum zai ce ai bai isa ya yi abinda Allah bai yi ba ko? Kuma duk maganar mutum sai dai ya yi ya gama, aure lokaci ne dashi."
Ta kalli Mama ta ce, "Mama Saheer yaro ne, bai san abinda nake ji ba. Tunda aka aurar da yaranta guda buyu sa'anin Nabila, shikenan kullum cikin baƙar magana nake. Nabila ta yi kwantai bata yi aure ba waye waye. Shiyasa nake so Allah ya kawo mata ta yi auren ta huta."
Mama ta ce, "to ina ruwan ki? Dan ayi mata gori sai me? Duk wanda ya yi nata gorin shi ya jiyo, kuma bazai aurar da ita ba."
Saheer ya ce, "abinda na gani kenan, kar garin farantawa kishiya ki aurar da ƴarki ga inda bai kamata ba, ki tsaya ki nutsu ki bawa ƴarki miji na gari. In akasin ne haka duk abinda ya zagaya a kan ki zai ƙare, kishiya sai ta yi miki dariya, babu abinda ya dame ta."
Ta girgiza kai ta ce, "baza ku gane ba" ta faɗa tana cigaba da girgiza kai dan a ganinta basu san yanayin da take ciki ba. Ita ko waye yazo neman auren bashi zata yi dan ta huta da gorin kishiya.
A lokacin Hanan ta shogo falon da sallama, suka amsa duk suka bita da kallo, ta zauna a kusa da Adda ta ce, "wash na gaji wallahi. Adda yaushe ki ka zo?."
Ta harare ta ta ce, "ta ya zaki san nazo kin tafi yawon ta zubar? Tun safe ina gidan nan amma baki dawo ba sai yanzu."
A lokacin Baffa ya shigo falon, ya kalli Hanan ya ce, "ke daga ina ki ke a daren nan?."
Ta turo baki ta ce, "Baffa makaranta na je fa."
"makarantar ce tun safe sai yanzu zaki dawo? Ki faɗa min inda ki ka je."
Ta kalli Mama alamun ta saka baki, sai kuwa Mama ta ce, "Baffa ta faɗa min zata bi ya dubiyar ƴar ajinsu."
Ya dawo da kallon sa ga Mama ya ce, "ta faɗa miki zata bi ya dubiya? Dubiyar ce tun safe sai yanzu za a dawo?."
Mama ta ce, "daga makarnata ta bi ya can fa, dole ta daɗe ai."
Ya gyaɗa kai ya ce, "wa ta duba?."
"Ƴar ajinsu ce ta gamu da tautsayi, ita ta je dubawa."
Baffa ya bi Mama da kallo itama tana kallonsa kafin ta ce, "baka yarda bane ka ke kallona? Ai ka san bazan yi karya ba. Dubiya ta je, kuma gata ta dawo, ba shikenan ba?."
Baffa ya girgiza kai ya ce, "Ki cigaba kin ji Zulaiha, ki cigaba da goya musu baya, wata ran za kiyi danasani."
Mama ta ce, "babu danasanin da zan yi wallahi, me nayi da zan yi danasani? Dan ƴata ta je dubiya sai ya zama zan yi danasani?. Allah ya raba mu da danasani, ban santa ba, kuma bazan santa ba in sha Allah."
Baffa ya bita da kallo, sai ya yi murmushi ya ɗaga kai ya fita daga falon.
Sa'ida ta kalli Mama ta ce, "Amma Mama..."
ta dakatar da ita cikin faɗa ta ce, "na san abinda nake yi, ba hankali da iya magana ki ka fi ni ba. Ni na haifi Hanan da Labiba, duk abinda zan yi musu babu wanda zai kai ni ƙaunarsu. Ya ishe ni, bana son wata magana, in ma a wuta na cilla su suka ƙone ƴaʼyana ne ko?."
Sa'ida da Saheer suka yi shiru basu ce komai ba, Mama ta miƙe ta shiga ɗaki Hanan ma ta shiga.
Sa'ida ta kalli saheer ta ce, "Saheer na wuce, Allah ya kyauta."
Ya gyaɗa kai bai ce komai ba, ta fita shi kuma ya kalli Islaha. A lokacin ta miƙe ta shiga kitchen ya bi bayanta.
Ya same ta a tsaye tana haɗa kayan wanke-wanke zata yi. Ya bita da kallon ƙauna da soyayya, ya jingina da bango yana kallon ta ya ce, "Boddi am."
Ta juyo kalle sa ya ce, "me ya kai ki orphange ɗazu?."
Ta kalle shi da mamakita ce, "Saboda gidanmu ne, na je gidanmu ganin yan uwana da dangina, shine kawai."
Ya girgiza kai ya ce, "Amma ba na ce miki duk lokacin da zaki je ki dinga sanar dani ba? Meyasa ki ka fara tsallake umarnina ne? Bani da daraja ne yanzu ko son da ake yi min ne ya yi ƙasa?."