BARRISTER SUHAIL

CHAPTER 23

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾


Mallakar


KHADIJA WRITES


YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION

(YOTA)



💖 Dedicated To My Mom 💖



بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ


🅿️----23


haka mahaifiyarta ta dauki wayar tana kallon invitation da kyau da kuma hotan Suhail duk da baifi sau biyu suka haɗu ba amman ta gane fuskar sa take fuskar ta sauya


ta kalli zeenah da har ta soma fita daga hayyacinta "waya tura maki wannan"


cikin kuka ta ce"mummy yusrah ce"


Suhail ya cuceni ya ci Amana ashe aure zaiyi shiyasa duk lokacin da na mishi magana sai ya ce busy busy wannan shine busy bazan taɓa yafe masa ba mummy


kamo ta tayi zuwa jikin ta ta ce"kiyi haƙuri Zeenah ki kirasa kiji ta bakin shi Suhail din tukun"


a fusace ta ce"in kirasa fa kika ce mummy haba kinsan tun lokacin da nake kiransa yana kashe min waya"


"duk da hakan ni nace ki kirasa"


wayar ta mika mata 


Suhail na zaune a falo ya hado wa Iman tea ya matsa sai ta shanye wayar sa ta fara Ringing dauka yayi ya fita zuwa valcony 


yana daga wa yaji Murya zeenah cikin kuka ta ce"Suhail You betrayed me,duk soyyayar da na nuna maka wannan shine sakayyar da zaka min kaje ka auri wata chan"


dafa kansa yayi yana sauraren maganar da zeenah ke fada masa sai ya jira ya gama fadar duk Abinda yazo ranta dan Wannan karin yasan shine baida gaskiya kuma ya san rana mai kamar haka zata zo amman bai tsanmace ta da wuri haka ba


sai da ta gama ya ce"Zeenah ki fahimce wallahi is not my fault , Abba ne ya aura min ita amma idan har kin amince, I’m ready to marry you"


murmushi tayi mai cike da takaici "Suhail kenan banyi arhar da zan shigo gidan ka a Matsayin mace ta biyu ba Allah ya hada kowa da Alkairi Amman ka sani bazan taɓa yafe maka ba tsawon lokacin da ka dauka kana batamin mayaudari kawai


katse wayar tayi Suhail ya jima yana maimata kalmar mayaudari a ransa amman yasan ya cancanci ya amsa suna fiye da haka a wajen zeenah


ya jima tsaye a volcony din yana ta tunanin inda zai billo wa al'amarin 


haka ya koma ciki Iman ta bisa da kallon tuhuma yanayin ta gaba daya ya chanza ko kulata baiyi ba ya koma dakin sa


Zeenah na kashe wayar ta kalli mummy ta ce"daddy ya dawo"


"mi zai maki"


"mummy zan faɗa masa ya kira Abbas ya fada masa ya turo mahaifin sa zan aure shi"


maganar a iya baki kawai amman take a zuciyar ta ba haka bane mummy ta kama hannunta ta ce"Zeenah take everthing easy nasan yanzu kina cikin fushin Abinda suhail yayi maki amman ki kara tunani kar ki yanke hukunci dai zai saki a damuwar da tafi wanda kike ciki yanzu"


shiru tayi sai hawayen dake kai koma a kan fuskar ta mummy ta tashi  ta ce"bari na saka precious ta kawo maki lunch idan kinci ki samu natsuwa sossai anjima sai muyi Magana"


kai kawai ta iya daga wa har ranta take jin dadin maganganun da mummy ta yi mata taji hankalin ta ya kwanta


tana nan a Zaune precious ta kawo mata indomie da tea bisa umarnin mahaifiyarta 


Zeenah ta dade zaune tana kallon plate din indomie da Precious ta kawo mata amma ko cokali bata iya dauka ba.


Tun maganar da Suhail ya fada mata ke yawo a kanta 


“If you agree, I’m ready to marry you”


Ajiyar zuciya ta sauke


A da wannan maganar ce mafi girman burinta 


Amma yanzu bayan ya riga ya auri wata, sai ta ji kamar an zuba mata gishiri a ciwo 


Wayarta ta dauka ta shiga gallery


Hotunan Suhail ne suka bayyana


Wani hoto yana sanye da suit, sai wani da suka dauka tare a gurin shakatawa 


a ranta take tunanin Yanzu shikenan ta rasa Suhail har abada dan baza iya jurar ganin Suhail da wata mace in ba ita ba 


Hawaye ya zubo mata


A hankali ta share su


Iman tun da ta lura Suhail ya fita ne dan ya amsa waya taji zuciyatar gaba daya babu dad'i hakan ya sa ta dauko Al'quranin ta fara karantawa dan shi kadai ke zai samar mata natsuwar da take ƙoƙarin rasawa


cikin sanyin murya take sautin karatunta ya mamaye falon gaba ɗaya bama tasan lokacin da Suhail ya fito sanye yake cikin ƙananun kaya gyara murya da yayi yasa ta rufe Alqur'anin da sauri


Ina wuni 


“Lafiya Ya jikin?” ya amsa mata 


“Da sauki”


Kai ya gyada


“Kin sha maganin?”


“Eh.”


Bai ce komai ba amma a ransa ya ji dadi 


A karo na farko da tun bayan aurensu ta masa magana babu Alamun kunya ko tsoro


har ya kai baƙin kofa zai fita ya juyo ya ce"ko Akwai abinda kike buƙata?"


kai ta girgiza masa 


ya fita 


parking yayi Kofar gidan su Zeenah da mamakin ya dannan thumprint dake buɗe masa yaga yaƙi accepting kenan Zeenah ta sa an cire kenan Ganin baida amsar tambayar ya fara knocking


daya daga cikin security ya bude masa kofar ya shiga