BARRISTER SUHAIL

CHAPTER 24

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----24


a compound din gidan ya tsaya yana ta ƙoƙarin kiran layin zeenah switch up daya daga cikin yan aikin gidan ta fito hannun riƙe da kayan wanki kiran ta yayi ya ce ta kira masa Zeenah

"okay wa za'a ce mata"
dan duk Zuwan da yake gidan bata taɓa ganin suhail ba kasancewar ita tana aiki bangaren wanki da guga ne yanzu ma kayan wanki tazo amsa

juyawa tayi ta koma dakin zeenah tana kwance a kan gado ta zuba wa celling din ido cikin wuni guda zeenah ta yi baki ta rame idanun ta har sunyi ciki tabbas so masifa ne 

mercy ta shigo ta risina gaban Zeenah ta ce"Aunty you have a visitor"

kallon Zeenah tayi ta ce"wanene"

"aunty nima ban sani ba"

"i'm coming"

haka mercy ta koma ta isar da sakon Zeenah na gatanan zuwa

ba'a fi minti biyar ba ta fito sanye da abaya white colour shi kansa sai da yayi mamakin Zeenah to kodai tayi rashin lafiya ne ganin ramar tayi yawa

Zeenah na ganin suhail ta juya zata koma ciki da sauri ya sha gaban ta ya ce"Zeenah Please ki saurare ni dan Allah" 


"suhail miya kawo ka gidan mu,oh kazo kaga ko na mutu to ban mutu ba ina nan da raina"

Suhail ya ce"dan Allah ki saurare ni magana nazo muyi"

murmushin yake tayi ta ce"Suhail ba wata magana data rage muyi ni da kai, Suhail ka cuceni Shekara nawa na dauka ina jiranka kullin busy Ashe kai kana chan kana shirin aure dan allah na roke ka ka fita daga Rayuwa kaje chan kai da matar taka allah ya baku zaman lafiya kuma Zan cigaba da rokon sakayya ta dan Allah ka tafi ka barni da ciwon da kawa zuciya ta idan har baka fita ba zan saka security suyi waje da kai "


fashe wa tayi da kuka da gudu ta koma ciki har ga Allah Suhail yaji tausayin Zeenah,ya rasa ta ina zai fara yi mata bayanin abinda ya faru ta gane ba laifin sa bane

haka ya karaci rayuwar sa a wajen ya fita a mota ya jima yana nazari taimakon Sameer kadai yake bukata a wannan lokacin hakan yasa ya nufi gidan sa

a kofar gate yayi parking ya kira ya fito duk yadda Sameer yayi ya shigo ciki ya ƙiya hakan yasa ya shiga front seat duk wanda ya kallin Suhail yasan yana cikin tashin hankali

sameer ya ce"Suhail miya same ka?"

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce"Sameer ina cikin tashin hankali zeenah ta gano da zancen aure na"

sameer ya ce"a ina  taji"

"nima ban sani ba"

"shiyasa Suhail tun farko na so ka fada mata idan taji daga bakin ka zai fi da ace wani ya faɗa maka kuma nasan zata fahimce ka"

Suhail ya ce"yanzu miye solution"

"ai mafita ɗaya kaje ka same ta kuyi magana"

"daga gidan su nake yanzu,infact kora ta ma tayi har tana iƙirarin zata saka security su fitar dani"

Sameer ya dafa ƙafadar ya ce"Yanzu  nasan zuciyarta cike take da tsanarka amman Abu ɗaya zakayi kaje ka sami Abba ka fada masa gaskiyar komai akan Zeenah kuma ka roki alfarma ya je wajen mahaifinta idan har kayi haka zata tabbatar da gaske auren ta zakayi kuma zata rage jin haushin ka"

jinjina kai suhail yayi cike da gamsuwa da shawarar da sameeer ya basa sallama yayi masa ya wuce gidan sa ya koma jin an fara kiran sallar Magariba sai yayi sallah ya shiga gidan

babu kowa a falo sai kamshin turaren wuta dake tashi ta ko ina dakin iman ya shiga fitowar daga wanka kenan daure da towel bata ankare ba taga Suhail tsaye bakin kofa da gudu ta koma ciki 

murmushi Suhail yayi dan ya gano mi take boye masa bakin gado t
ya zauna ya ce"Ashe ko zaki kwana a toilet din nan idan har baki fito ba zan ta zama anan nima"

turo baki tayi ta ce"ni fa ba kaya jikina"

"ki fito ki saka kayan mana ai ba hanaki nayi ba"

kusan minti goma tana tsaye a toilet ganin da gaske ba fitar zaiyi ba ta buɗe kofar a hankali ta fito 

taƙi yarda ko ido su hada fa sauri ta dauki hijabin dake gefen gado ta saka Suhail ya bita da kallo ya ce"ni kike boƴe min a jikin naki bayan babu abinda ban gani ba"
cikin sauri ta dago ido tana kallon sa ganin ko kunyar fada mata wannan maganar ma baiji ba 

tashi yayi zai fita ya ce"kin sha maganin ki"

"Eh" kawai ta fada 

sai da yayi sallar isha'i ya kama hanyar gidan su ganin motar Abba ajiye a parking space yasa ta nufi part din sa knocking yayi Abba dake Zaune a falo yana karanta newspaper ya bada izinin shigowa 

Suhail ya ƙaraso cikin palorn kan lallausan carpet dake shimfiɗe a dakin ya zauna cikin girmamawar da ya saba ya gaishe da Abba ya amsa bayan tambayar ya amarya ya ce tana gida lafiya qlau

shiru ya biyo baya Abba na kallon bakin Suhail yasan akwai magana 

ajiye newspaper din yayi ya ce"Suhail hope everthing is going well naga Kamar kanason cewa wani abu"

ya rasa ta ina zai fara shi kansa ma baisan mi zaice sai Abba ya kara magana a karo na biyu ya daurewa ransa ya ce"Abba aure nake so zan ƙara"

Abba bai san lokacin da ya zare gilashin dake sanye a idanun sa ba tashin hankali ya bayyana ƙarara akan fuskar sa