GADAR TSAUTSAYI 6
by @nusybee143
Page 6
Shiru Haisam ya yi na yan sakwanni, kafin ya ce "nima ina wannan tunanin wasu lokutan,amma kuma wacce iriyar ƙungiya kake gani zata dauki nauyin shigo da miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasar nan?ta daukar fansa ce ko ta ta'addanci zalla?"
Musa ya ce "to yanzu ba na ce ba dai,amma mu cigaba,akwai lokaci, bincike zai nuna"
Haisam ya yi murmushi yana faɗin "Weldon Musa!You tried,but you have to be careful,ya kamata ka iya takunka,don yarinyar nan tana da haɗari sosai
Yanzu abin da za mu mayar da hankali akai shine, menene cikakken sunanta?
A ina take da zama?ko na ce a ina take sauka idan ta shigo Nigeria?
A wacce ƙasa take da zama?don da yiwuwar sai mun bi ta har ƙasar da take!
A wannan wata gudan ina so na samo komai game da ita, saboda alƙawarin da na ɗauka, don haka mu zama ready, yanzu haka tana Nigeria,mu yi ƙoƙari mu san next move action ɗinta,da kuma inda take shirin zuwa nan gaba kaɗan, saboda mu daƙile ta"
Ɗaya daga cikin abokan aikin nashi mai suna Awwal ya ce"Sir!
Wannan lokacin sai mun yi da gaske, zata iya kamuwa, in dai har ba da tsafi take yi ba ,amma abin akwai mamaki yadda mace take dealing ɗinmu a ƙasar nan,macen ma yarinya ƙarama kamar wannan "
Murmushi sosai Haisam ya yi yana kallonsa,a hankali ya ce"ka raina mace ne?
Kana ganin ta gaza ta yi irin wannan aikin?"
Awwal ya girgiza kai ya ce"ko ɗaya Sir!kawai dai na ga ba'a cika samun mai karfin zuciya a cikinsu ba, wadda zata iya aikata irin wannan aikin"
Haisam ya ce"har wadda ta fi ta ma za'a samu
Abin da ke akwai na case ɗinta shine safarar miyagun ƙwayoyi ne sai Yahoo,bata safarar yara ƙanana,bata safarar muggan makamai,bata safarar mata don ta lalata su,kuma har yanzu ba mu samu wani single rahoto da yake bayyana tana kisa ba
Kuma duk waɗannan abubuwan da na lissafa akwai macen da ta haɗa su tana yi,don haka kar ka zauna kana mamakin abin da ta yi,ka yi focusing akan yadda zata shigo hannu kawai"
Awwal ya jinjina kai kawai,tabbas maganar CSO Haisam gaskiya ce,akwai matan da suke aikata waɗancan abubuwan da ya lissafa duka,kuma su ma suna gudanar da rayuwarsu yadda suke so
Sun ɗan juma suna tattauna yadda za su shawo kan matsalar, Haisam yana sake jaddada musu kowa ya kasance a ankare, sannan kuma ya kasance cikin shiri a kowanne lokaci
*ROXY*
Thursday,23rd October,4:00am
Su bakwai ke a cikin ɗakin da ya kasance kamar parlour,haske ko'ina,ga hayaƙi na taba da na shisha da ya bule ɗakin har ba'a iya ganin abin da yake cikin dakin sosai,gefe kuma kiɗa ne yake tashi kaɗan kaɗan daga ƙatuwar home theater ɗin cikin waƙar Go down dey ta shaggy da spice
Su uku ne mata, Roxy da take kan computer tana danne-dannenta,gefenta kuma ƙatuwar tukunyar shisha ce tana bulbulawa cikinta hayaƙi,sai Amra da take zaune a tsakiyar maza biyu, David da Salis Wise,sai Hannah da suke buga wasan karta ita da Jamilu da oga boss, wanda ainihin sunansa shine Rabi'u
Shaye-shayensu kawai suke yi hankali kwance,ga kayan maye kala-kala,ciki har da giya da cocain, waɗanda suke taɓawa lokaci lokaci
Banda Roxy da ta yi focusing akan abin da take yi da shishar da take sha,bayan wani lokaci ta daki table ɗin da yake gabanta tana faɗin "an gama da wannan harkar!"ta ture computer ɗin gabanta ta yi baya ta faɗi ta fashe
Kallonta Jamilu ya yi yana murmushi,ya ce"ya dai our boss?
I hope kin kwashe kuɗin?"
Kaɗa yatsunta biyu ta yi,ƴar manuniya da na kusa da shi,tana yatsina fuska ta ce "ai ba masu yawa bane kuɗin, Just 70m"
"Murmushi suka yi kusan dukkansu, Amra tana murmushi ta ce"wow!
Congratulations!ya Kamata kuɗin nan ki haɗa mana shagali da su"
Hanna ta ce"Yes ma!
Idan da hali ma ba'a ƙasar nan ba,ki bari sai mun koma Ibiza "
Yatsina fuska, wadda ta zamar mata kamar dabi'a ta yi tana kallon Hanna, kafin ta ce"No way!
Ya kamata mu rinka tuna wasu abubuwa idan muna aikata wasu
Ko ba komai za mu rage zunubi "ta mike tsaye tana gyara zaman jacket ɗin da take jikinta ta ce"wani orphanage na samo,ina son na yi donating kudin zuwa can"
Gaba ɗayansu babu wanda fuskarsa ta washe sai Oga boss,ya ce"wow!
Good idea my dear,hakan yana da kyau,i love the way you care for others in life Roxy, I will help you in sha Allah "hannu ta ba shi suka tafa, sannan ta samu waje ta zauna
Wani kallo David ya bi ta da shi,haka zalika Hanna, saboda tsananin mamaki da takaicin maganarta,kafin su yi magana Amra da take watsa mata wani banzan kallo ta ce"okay!
Na gane yanzu,wato orphanage ɗin da kika ja mu last week ita za ki kai kuɗin ko?"
Roxy ta kalle ta cikin kwanciyar hankali ta ce"ina wannan tunanin"
"Tabɗijam! to wallahi ba ki isa ba!
Babu yadda za'a yi ki tsallake mu,mu da muke yi miki amfani dare da rana ki miƙawa wasu matsiyata ƙasƙantattu kuɗi
Kina yin hakan ne don ki siya soyayya a wajen mutanen ƙasar nan?
Ko kina so ki canja ne ki nuna cewa yanzu ke kin zama ta gari?to wallahi ba ki isa ba, I can't take this stupidity,dole dai ku arna sai kun nunawa mutane butulci irin wanda kuka saba
Dama jiya ina ciki da ke,kin kai ni unguwar talakawa na shaƙi wari da ƙarnin talauci sannan kin gasa min maganganu,Ni ba zan biye miki ba, hankalinmu ba iri ɗaya bane shiyasa ban kula ki ba,na ƙyale ki kika yi ta abin da kika ga dama
To shine yanzu za ki fifita waɗancan matsiyatan akan buƙatarmu?to wallahi ba ki isa ba,ba ki kai wannan ba!!!
Wacece ke da za'a zuba miki idanu kina yin abin da kika ga dama?arniyar banza da wofi kawai"
Gaba ɗaya ɗakin zubawa Amra idanu suke yi, wadda take ta masifa ko mayar da numfashi bata yi, banda Roxy da take zaune a kusa da shisha ɗinta tana cigaba da zuƙa tana fitar da hayaƙi, fuskarta babu alamun damuwa ko kaɗan, Oga boss ya dubi Amra cikin jin takaicin wannan abu da ta yi,rai a ɗan ɓace ya ce"wannan abu da kika yi sam bai yi ba Amra!
Ita ce shugabarmu,kin ɗaga mata murya saboda kuɗinta, wanda ta nemo da wahalarta, tana biyan mu albashi wanda ya ishe mu shan sharafinmu,tana ɗaukar nauyin duk wani abu da muke buƙata,ina ganin wannan hayaniyar ba ki yi ta a inda ya dace da wanda ya dace a yiwa ba,hakan butulci ne
Sannan kar ki sake yi mata gorin addini, saboda itama tana da nata addinin,kuma ta yarda da abin da take bautawa"
A fusace Amra ta dube shi ta ce"malam ba da kai nake ba,da uwar ɗakin da kake neman gindin zama a wajenta nake"Oga boss zai sake magana Roxy ta ɗaga masa hannu, har yanzu bata kalli sashen da suke ba, asalima zuƙar hayaƙinta take yi hankali kwance
Miƙewa ta yi tana tafiya kamar mai rangaji, har ta isa gaban Amra, wadda hantar cikinta ta kaɗa ganin yanayin Roxy, Roxy ta yi wani killer smile tana kallonta, kafin ta fara magana cikin izza yadda ta saba
"Me kika ce ma?
Wai.....na kai ki gidan talakawa na wukaƙanta ki na gaya miki magana bla bla bla!
Ina son na tuna miki asali da tushenki ne!
Yes!!!so nake na tuna miki ke ma ba kowan kowa ba ce,ba ƴar kowa ba, face yar gidan malam Namadi mai kayan miya a gefen kasuwa,kuma na san kin tuna da hakan, that's okay for me
Sannan da kike maganar kin yi min aiki,aikin da waccan matar da kike kallo a matsayin ƙasƙantacciya ta yi min aikin da ko makamancinsa ba ki isa ki yi min ba, sannan wannan kuɗi nawa ne,Ni na yi wahala na samo shi,ke ma idan za ki iya go ahead and get yours, best of luck Madam monkey!"ta ƙarashe maganar tana bubbuga kafaɗarta ta dama
Har ta juya ta sake juyowa tana kallon Amra wadda ta ƙame a waje ɗaya, ba tare da damuwa ba ta ce"yawwa sai Maganar addini,ke wanne addinin kike bi tukunna?"
Ba Amra ba,hatta su Oga boss sai da suka razana suna kallonta cikin tsananin mamakin wannan tambayar,da ƙyar Oga boss ya dube ta ya ce"musulma ce mana"
Kallonsa ta yi tana murmushi ta ce"really Oga boss?
To menene shaidarka na addinin nata?sau nawa ka taɓa ganin ta yi Sallah?ka taɓa ganin ta tana azumi?"
Shiru suka yi gaba ɗaya, Roxy ta ce"to bata da addini,kar ta sake yi min gorin addini, otherwise kuma wani abu mara daɗi ya biyo baya, I can't take that nonsense"
Shiru wajen ya ɗauka,don da alamu ran Roxy ya ɓaci, sai da ta ɓata kusan mintuna biyar tana danna waya sannan ta kalli David ta ce"David ya batun aikin da na ba ka?"
David ya numfasa ya ce"ma na gano kusan komai da ya danganci jami'in
Sunansa HAISAM Abdulmalik Madaka,mai riƙe da muƙamin CSO a hukumar DSS,mutum ne mai matuƙar ƙwazo da ƙawazuci a aikinsa,idan ya saka abu a gaba to tabbas sai ya ga bayansa,sai ya yi nasara akansa
Haka tarihinsa ya zo Ma'am "
Jinjina kai ta yi ta ce"uhumm!
Ina jin ka, cigaba mana"
David ya gyara zama ya cigaba"sai batun iyalansa,ya yi aure shekarun baya,amma zaman shekaru uku kawai suka yi da matar sakamakon matsaloli irin na cikin gida,sun rabu yanzu haka, ƴarshi guda ɗaya Rasheeda Haisam makawa, wadda suke kira da Amna tana hannunsa"
Ɗan murmushi ta yi ta ce"wow! that's is very interesting,ina jin ka, cigaba"
"Ba shi da yaya ko ƙani,bashi da uwa,ta rasu,yana rayuwa tare da mahaifinsa Alhaji Abdulmalik Murtala Madaka, wanda ya kasance ɗan kwangila ne,kuma cikakken ɗan kasuwa,amma harkokin kasuwancin nashi sun fi yawa a Abuja da Lagos,da matar babansa hajiya Mariya Madaka,ita kuma babbar likita ce da take riƙe da asibiti nata na kanta"
Roxy ta jinjina kai ta ce"good job David,a ina suke da zama?"
"Suna zaune a Rocky estate ne"ya bata amsa"Roxy ta ɗaga kafaɗa tana taɓe baki tana murmushi ta ce "good,ina phone number ɗin tashi da na ce ka samo min?"
David ya ce "na tura miki ta Whatsapp"babu musu ta miƙe ba tare da ta sake magana ba,ta fito zuwa compound ɗin gidan,tana kallon yadda gari ya fara wayewa,don an ɗan kwashi lokaci da gabatar da Sallar asuba
Kamar mai nazari haka ta fara bin compound ɗin da kallo, kafin kuma ta ɗauke kai ta nufi backyard ɗin gidan kai tsaye
*MALIYA ESTATE, KANO STATE, NIGERIA*
A yau iyalan suna cike da farin ciki da kewa kuma duka a tare, saboda tafiyar su Iman izuwa ƙasashen da za su je karatu,ita dai Ummeey duk da yadda ta zama mujiya a cikin iyayen yaran hakan bai hana ta cigaba da kawo gudunmawa ta ko'ina ba
Kasancewar ta san suna son kayan zaƙi tuni ta saka an shirya musu dubulan da alkaki,sai cake,aka yi packaging ɗinsu a bokitai masu kyau
Da kanta ta yi sallama ɗakin Hajiya Ruƙayya, inda ake ta shirya kayan da za'a tafi da su, Hajiya Sa'adatu da take zaune ita da Saleem suna sake shirya kayan tafiyar ta su ta ɗago kai tana kallon Ummeey gami da amsawa
Tana murmushi ta ajiye bucket ɗaya da take riƙe da shi,itama mai aikinta da ta riko sauran biyun ta ajiye,tana murmushin ta dubi Hajiya Sa'adatu ta ce
"Hajiya ga su nan,na ga yaran namu akwai son kayan zaƙi,shine na saka aka yi musu, Allah ya taimaka ya bayar da abin da ake nema"
Surayya da take fitowa daga ɗaki, kasancewar ta fi kowa raini a cikinsu ta dube ta ta ce"an gode Ummeey,amma da ba ki bayar an yi ba,mun riga mun karbo wanda aka yi mana already, Allah ya saka,amma da kin tafi da shi"
Kallonta Ummeey ta yi, duk da cewa ranta ya sosu amma sai ta yi murmushi, kafin ta kai ga magana Hajiya Sa'adatu ta riga ta
"Amma abin da mamaki Hajiya Zainab,na ga dai lokacin da Shaheeda zata tafi zuwa karatun nata kamar ba kiyi mata wannan hidimar ta kayan zaƙi ba, gashi na kasa yarda cewa kin fi son yaranmu akan yadda kike sonta,don dai babu munafunci mu dai mun fi son yaranmu akanta "
Hajiya Ruƙayya da ta shigo ta dubi Hajiya Sa'adatu da sauri, wadda ta mayar da hankali kan Hajiya Zainab tana kallon reaction ɗinta tana fatan ta tanka, Hajiya Ruƙayya ta ce"kayya!
Ai yadda ta faɗa ɗin ne,ɗa na kowa ne,itama ai ƴaƴanta ne,ita ɗin mai iko da su ce, Hajiya, Allah ya amfana,an gode sosai, Allah ya bayyana Shaheeda "Hajiya Zainab ta yi ɗan murmushin yaƙe ba tare da ta yi magana ba ta juya ta nufi hanyar barin parlourn, ba tare da ta kula da kallon rainin da suka bi ta da shi ba
#Nusy_bee