NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)
CHAPTER 33 (Broken 11).
by @deejasmah
CHAPTER 33 (Broken 11).
Tsura masa fararen idanunta tayi tana mai nazari akan shi, sai kuma ta maida su ta rufe tana sakin ajiyar zuciya. Sai da ya gaji don kan shi kafin ya sauketa har lokacin da murmushin da ko tayi rantsuwa ba zata yi kaffarar cewa ba ta tab'a gani ba a fuskarshi, cheeks d'in ta ya yi pecking yana cewa " thanks wife, Allah yayi miki albarka".
"Uhm" ta amsa tana komawa kan sofar da take zaune shi ko juyawa yayi ya koma d'akin shi in da a can ya kira sahibar ta shi a waya ba shi ya gama ba sai kusan shad'aya yana ajiye wayar wanka yayi ya shirya a pj masu taushi kana ya doshi d'akin nata time d'in ma har ta fara bacci sai bai tashe ta ba duk da kuwa da k'walamar shi ya shigo. Rab'awa kawai yayi ya kwanta sai da asuba ne ma ta san ya shigo da ta tashi sallah, sanda ya dawo masallaci tana cirewa Sairah diapernta da ta b'ata zama yayi yana kallonta. Gaishe shi ta yi ya amsa yana murmushi toilet ta wuce ta yi wa yarinyar wanka sannan ta fito, baby oil kawai ta shafa mata yarinyar ta koma bacci wani diapern ta sanya mata kafin ta ja bargo da niyyar komawa nan shima ya shigo ciki. Ba ta hana shi yin abinda yake so ba sai dai kuma ba ta ba shi yanda yake buk'ata ba, shi yayi koman shi sai da ya samu nutsuwa kafin ya saketa yana mai k'arewa fuskarta da ke hawaye kallo.
"What it is wife, ba kya so ina tab'a ki ne?".
"Ko d'aya".
"Toh me yasa kike kuka in na taɓa ki, besides ba kya maraba da ni ba kamar da ba".
"Ban san me kake magana a kai ba Yaa, ni wanka ma zan yi" ta furta tana sauka daga gadon, rigarta ta ja ta zura kafin ta doshi toilet, idanun da ya rakata da su ya lumshe kafin ya tashi shi ma ya bi ta bayin. A nan ma ya k'ok'arta sai dai ba ta ba shi dama ba, duk da tana jin abinda yake mata a rai da jiki but ta yi blocking duk wata hanyar da zai saka ta ji dad'in da bak'in ciki da damuwa wanda yake da babbar effect ga duk wani sexu@l feelings don ba a had'a abu biyu lokaci d'aya ko dai ta cire damuwar ta karɓe shi ko ta bar damuwar ta cigaba da ƙin shi.
Haka aka yi wankan suka fito riga ta zura kawai ta fara gyaran gidan yayinda shi ma ya wuce room d'in shi shiryawa yayi cikin kayan da ya saba fita da su don yau yana son fita da wuri, za suyi monthly ward round wanda ake yi da kusan duka ma'aikata bai kuma son yin latti kun san soja bai son latti don ma a haka suna mugun d'aga mai k'afa.
Cikin lokaci k'ank'ani ta had'a nigerian chicken nuggets pie wanda ake yi a cikin bowls sai ayi baking sai wings ta kuma dafa apple tea da yaji kayan k'amshi ta jera komai akan table sai ta ajiye pure orange juice, ruwa da fruits. Sai ta cigaba da aikin gyaran gidan da dama ba wai ta gama ba ne tana dai yi tana ajiyewa ne, san da ta gama ne ta sake komawa tayi wanka inda kamar kullum shiryawa ya d'auketa lokaci mai tsayi tana gaban madubi ya shigo d'akin.
Kallonta ya tsaya yi yana cewa " i thought kin gama ne ki zo ki bani abinci".
"Yanzu dai zan gama, na zaci ka wuce ma".
"Nope, ke nake jira".
"Ok 2 mins".
"Uhm" ya amsa yana d'an tab'a wuyanta da ke nan sai shek'i yake yi, gocewa tayi ta mik'e tsaye. Double slitted A-line gown ta sanya wani material mai santsi tumeric color, ya zauna tsaf a jikinta saboda 'yar bud'ewar da tayi gashinta ta gyara ta yi oiling sannan tayi waxing gaban da kyau ba ta shafa hair color ba sai tayi spraying ta nufi parlorn ba tareda ta sanya d'ankwali ba.
Tana fitowa ya tsura mata idanu kamar zai cinyeta, baki ta tura gaba ta fara serving d'in shi a plate ta zuba masa da wings d'in ta had'a ketch up da cream sai d'an pepper kad'an ta tura gabansa. Ta had'a masa tea ta ajiye masa da fruits sannan ta ja kujera ta zauna, kallonta yayi yace "ke ba zaki ci ba?".
"Zan dai sha tea, sai anjima zan ci".
Ok ya amsa sannan yayi bismillah yana kai cup d'in bakinshi idanunshi k'yar a kanta, itama tean ta had'a tana sha tana kawar da idanun ta daga kan shi duk da ko tana jin yanda idanunshi mai kaifi suke zuba wasu guba a jiki da jininta. Silently suka kammala breakfast d'in har ya rigata gamawa saboda saib'inta, mik'ewa yayi daga table d'in bayan ya goge baki da hannunshi da tissuen da ke kan table d'in.
Hannunshi ya kai zuwa ga k'irjinta da ke bud'e janyewa tayi tana tura baki, murmushi ya saki mai k'ara masa kyau yace " kin yi kyau ne sosai, anya zan iya fita ma kuwa". Kallonshi tayi a kaikaice ta watsar kamar ya mata laifi duk da ko yau ne karon farko da ya tab'a faɗa mata haka wanda shi ne ya k'arawa haushinta yawa ne.
Sake cewa yayi " ko d'aya fushin nan bai miki kyau wife, ki daina fushi kin ji?".
"Ni ba fushi nake yi ba, to miye ma abun jin haushin? Absolutely nothing".
"Hmm okay dear, na tafi".
"Allah ya tsare" ta furta tana shan shayinta, ajiyar zuciya ya sauke kawai ya nufi wash hand basin hannunshi ya wanke yayi drying da towel d'in da ke wurin kana ya nufi hanyar fita. Rakashi tayi da ido sannan ta ajiye cup d'in hannunta, gyaran wurin ta yi tsaf ta maida su inda su ke kafin ta wuce ciki.
Shiga tayi ta kwanta a kan gadon kwanciyar rigingine ta tsurawa Popn d'akin idanu kamar mai karanta wani abu, sai dai duk yanda ta so ta gaza shima saboda ba ma ta cikin hayyacinta balle ta samu damar yin tunanin. Tana jin son hutu daga abinda yake faruwa, shi ne dalilin da ya sanya ta so tafiya Abuja but yanzu babu wannan maganar don plans sun rushe. Duk runtsi dai ta san dole ne ta bawa kanta hutu ko da na rana d'aya ne, amma ba ta san ta yaya ba.
Sairah da ta farka ne ta rarrafo jikinta ta kwanta tana cewa " Mimmie" da sauri ta waigo zuwa gareta tana murmushi tace " Princessa!". Washe baki ta yi da hak'wanta guda biyu suka bayyana tana gwalan-gwalan tana tab'a mata k'irjin alamun tana jin yunwa, cewa tayi "Oya come to Mommy".
Zaunar da ita tayi a jikinta ta fara shayar da ita tana shafa gashin kanta, kwanciya tayi a jikinta tana numfashi. Sai da ta tabbatar da ta k'oshi kafin ta zareta ta d'aurata a kafad'a tana patting bayanta sai da tayi gyatsa kafin ta sauka daga gadon da ita, toilet ta shiga ta cire mata diapern jikinta tsarki tayi mata da kyau kafin ta fito. Wani ta saka mata ta shiryata cikin baby dress black color mai yarfin gold, farar socks ta sanya mata da black baby loafers mai kyau. Taje mata gashi tayi ta d'an kama shi sama-sama da ribbons k'ananu wasu short clips ta sassaka a cikin gashin sannan ta d'an sa mata band black. Mayafi babba ta sanya sannan ta k'arasa gaban mirror ta fara musu hotuna masu kyau ita da yarinyar, sai da tayi iya yin ta kafin ta ajiyeta da wayar. Kaya ta canja zuwa more decent Bubu gown na lace ta had'a jakar babyn da nata, fita tayi da kayan ta ajiye a waiting room kafin ta d'auki Sairahn suka fita. Sai lokacin ta samu energyn yin breakfast, tana kammalawa ta kashe komai ta d'auki car key ta rufe koina ta fita waje. A baby carriage ta sanyata ta saka mata seat belt da kyau kafin ta d'auko kayan da ta ajiye a waiting room ta saka a backseat, kana ta shiga motar ta ja zuwa office.
San da yaje CMD bai riga ya iso ba sai kawai ya fara ganin patients, wanda ya d'auke shi d'an time k'alilan kafin ya iso. Ko da ya zo d'in shi ma bai neme su ba sai to-12 kafin aka kira shi, white coat d'in shi ya saka mai d'auke da sunanshi PT. A. Yerwa Burhaan sai kuma ID card d'in shi da ya mak'ala shi ma a jikin pocket d'in shi ya sakaya k'wayar idanunshi da farin glasses ya fita.
Locking office d'in yayi yana fita waje, inda rukunin offices d'in nasu yake ya had'u da Adnan shi ma da white coat. Musabaha suka yi suka jera a tare Adnan yana tsokanar shi da wai kullum sake murjewa yake yi alamun Nadeefah ta iya kiwo, shi dai bai tanka ba a haka har suka k'arasa inda ake jiransu a babbar board room d'in inda kusan kowa ya hallara. Ba su dad'e da zuwa ba CMDn ya k'araso babu b'ata lokaci suka fita zuwa cikin asibitin inda suka fara da A&E wanda a nan ne speciality d'in shi yake wato orthorpaedic duk yawanci soldiers d'in da yak'i ya ritsa da su ne, wasu sun rasa k'afa wasu hannu wasu kuma karaya ne da gocewar k'ashi. Sun jima sosai a ciki kafin suka wuce can general wards ba su suka kammala round d'in ba sai after 2, masjid suka tafi sai da suka yi sallah suka koma ciki. A babban board room suka zauna nan fa aka fara tattauna akan conditions d'in patients d'in da suka duba, Kowa kuma sai da yayi magana akan abinda yayi observing da reasons d'in shi na fad'in haka inda wasu zasu iya supporting d'in ka ko akasin haka ya danganta da kalar views d'inka da kuma matsalar.
3:30 aka tashi daga meeting d'in kowa ya nufi office d'in shi, musulman ciki dai masjid suka nufa sai da suka yi sallah kafin suka koma ciki masu neman abinci suka nema. Shi dai ciki ya koma da niyyar had'a kayanshi tea ya fara had'awa da ya shiga cikin office d'in kana ya zauna a couch d'in da ke daga can gefe, sai kuma ya mik'e tsulum zuwa ga table d'in shi hango wayarshi da ya ajiye tun fitar shi. D'auka yayi ya tarda miss calls kusan 20 a take k'irjin shi ya buga ganin sunan mai kiran " Cherrie🍒🥀" ga messages guda biyu, bud'ewa yayi na farkon cewa tayi ''me yasa ba ka ɗaga min kira?" Na biyun kuma " Thank you".
Murmushi yayi yana imagining darun da zasu yi da ita yayi dialing numberta har ta katse ba ta d'aga ba, kan kujera ya koma ya sake kira shi ma sai da ya kusa katsewa ta d'aga ba ta ce uffan ba.
"Cherrie!" Ya furta cikin kashe murya.
Baki ta tura kamar yana gabanta tace " uhmm".
"Cherrie".
"Ba wani cherrie a nan, bayan ka daina sona".
"In na daina sonki in so waye?".
"Ba ga shi ka k'i d'aga wayata ba? Ina damun ka ko?".
"Oops Cherrie ba na kusa da wayar ne fa, mun je round ne kuma na bar wayar a office".
"Saboda ban da muhimmanci ne ya sa ba zaka iya tafiya da wayar ba".
"Ba a shiga da waya round Hajiyata, ba kuma zan karya dokar ba for you".
"Saboda ba ka so na ko".
"Hey dear ki bi a hankali mana, kar kuma ki had'a kan ki da aikina okay".
"Okay, ya aikin?" Ta amsa tana mai jin k'uncin yanda yake datseta a tsakiya, haka nan jikinta yake mata sanyin kar fa ta shiga ta sha wuya don ta dad'e da sanin a tsaye yake kamar Alu.
"Aiki Alhamdulillah kina ina ne?" Ya tambaya yana duban Adnan da ya shiga da ledan takeaway a hannu, shi ma kallonshi yake yi yana mamakin wannan murmushin fuskar tashi kamar an masa bushara da aljanna don haka sai yayi maza ya k'arasa kusa da shi cike da tsegumin son jin abinda ya sa shi nishad'i ya zauna.
"Ina gida".
"Amma ai ba yanzu kuke closing ba, miya faru?".
"Mai 3-5 d'in ne ba zai zo ba shi ne na wuce by 2".
"Ok".
"Zaka zo ne?".
"Kina son gani na yanzu ne?".
"You know that ina son ganin ka kullum ba kuma zan gajiya da ganinka ba har abada ".
"Me too cherrie, yanzu kuwa zaki ganni in shaa Allah kina son wani abu ne?".
"Yea, burger and fries".
"Na ina?".
"Dominos".
"An gama, Dearest".
"I love you Baby, sai ka zo".
"I also love you sai kin ganni, bye".
"Bye" ta furta tana blowing masa wani mayen kiss, lumshe idanu yayi yana sauraran abinda ta zuba masa a jiki ba tareda ya janye wayar ko ya lura da ta katse ba.
Dariya Adnan ya sanya mai k'arfi cikeda mugunta yana nuna shi, tsaki yayi yana cire wayar daga kunnenshi ya ajiyeta gefe yana kallonshi. Dariyar shi ya sake k'arawa yana cewa " ashe zan ga wannan ranar ya Allah, BAY is this you?".
"Wai wannan wani irin iskanci ne haka zaka wani saka ni a gaba da dariya Aa ba ni ba ne kai ne".
"Ai abun ne da mamaki, Dude me nake gani haka".
"Abinda idanunka ya gane makan dai ne, i'm in love".
Tafa hannu yayi yana sake k'ara k'arfin dariyarshi yace " finally! Finally!! Na daɗe ina jiran ranar nan da zaka yi realising".
"Realising me?".
"That ka daɗe kana son ta mana, ikon rabbi" ya furta yana sake tuntsurewa da dariya.
Tsaki ya saki yace " gaskiya duk wanda ya ci kai ya huta, kai yaushe ka ganni a soyayyar da har zaka min sharri".
"Tun kafin kai ka gane hakan, yanzu dai komai ya daidaita kenan kai dole mu yanka cake".
"Yea komai ya daidaita tunda har an ba ni aurenta, in four months time in shaa Allah tana gidana k'ark'ashin ikona".
"Ban gane aure ba, wani auren kuma zaku yi ko ka saketa ne ban da labari?".
Wayarshi da ya ajiye ya d'auko ya bud'e cikin hotunanshi ya shiga ya nemo pic d'in Fareesahr ya ajiye masa a kan cinya yana cewa " She's Fareesah Mai katifa, ita ce yarinyar da nake so and in shaa Allah zan aura nan da wata hud'u".
"Kan kut......." Ya ja dogon ashariya ba tareda ya shirya ba yana jefa da wayar kamar an ba shi wuta, ya mik'e tsaye kallonshi yayi da mamaki yace " miye haka kake wani ashariya".
"Wata tunkuza ce nake gani haka, kace min you are in love da ita. Ita Nadeefahr fa ina son nata da kake yi?".
"Ni nace maka ina son ta".
"In baka son ta uwar me kake mata".
"Wannan kai za'a tambaya ni yaushe na tab'a ce maka ina son Nadeefah?".
"Ohh really? kai wani irin shameless human ne Burhaan, meyasa baka da wani buri da ya wuce nunawa duniya that Nadeefah ba ta da wani matsayi a gareka sai matar da aka cusa maka? Wannan wani kalar wawanci ne?".
"Ni kake kira haka Adnan......?"
"Ai kafi gaban nan Burhaan, wallahi kai ba mutum ba ne duk soyayya da ladabin da yarinyar nan take nuna maka ba ka gani ka kuma rasa da me zaka saka mata sai da auro mata wata mata class a matsayin kishiya anya ka na da tausayi kuwa?".
"Au dan zan yi aure shi ne laifi? A ina aka hana aure?".
"Babu inda aka hana, yau inda ace auren soyayya kuka yi da Nadeefah don ka ce zaka k'ara aure ba laifi ba ne a kan ace auren had'i ne wanda kowa a family ya san baka son ta".
Nisawa yayi yana kallonshi da kyau ya cigaba da cewa.
"A irin aurenka wanda ta gidanka ba ta k'aruwa da komai sai tozarci da musgunawa ko an gaya maka in su iyayen Fareesah take ko wa suka ji yanda kake mu'amalantar iyalinka zasu baka 'yar su ne?".
"Ita Nadeefahn tace ina cutar da ita? Yaushe kuma na tab'a tozartata ko na musguna mata da har ya zama abinda zai sa a k'i ba ni mata?".
"
"Ka rantse ba ka musguna mata, ko don kaga tana da hak'uri da tolerance?".
"Ka daina halin mata Adnan".
"In dai sanin ya kamata ne halin mata toh ka kirani mace kawai Burhaan, aure ne dai ko kaje kayi tayi amma ina son ka sani daidai da rana d'aya ka cutar da matar ka sai Allah ya saka mata".
Shiru yayi yana sauraran shi kamar irin uba da d'an nan gabad'aya ya rasa amsar da zai ba shi, shi ko a harzuk'e ya cigaba da cewa " ban tab'a sanin ba ka da wayau ba sai yau, Burhaan in ma kana da shi toh ya tashi a banza wallahi"
"Ad....."
"Kar ka sake kirana Malam, ga ka ga Fareesah nan Allah ya baku zaman lafiya da ita mtssw" ya juya ya nufi k'ofa ya fita yana mai banging masa k'ofar, da idanu ya bishi yana mai mamakin yanda Adnan yayi reacting da kalar zagin da yayi masa.
Tsaki ya saki shima ya mik'e tsaye ledar abincin da ya shigo da shi ya d'auka da jakar shi da ya had'a, fita yayi yai locking k'ofar. A parking lot ya had'u da Adnan sai dai ko kallon banza bai ishe shi ba, don yana ganinshi ya ja motar ya bar wurin. Tashi motar ya shiga ya tadata ya bar asibitin a gate ya bawa soldiern dake bakin duty ledar hannunshi ya ja motar ya hau titi da kyau.
Bai tsaya a koina ba sai a dominos d'in da tace sai da yayi mata order har da wainda ba ta ce ba ya ja motar zuwa gidansu, in da ya samu kyakkyawar tarba a can yayi Magrib da ishai sai to 9 ya dawo gida.
*************************
Ba ta dad'e da zama a office d'in nata ba ta jiyo muryar Suleim tana tambayar Fatee ko tana ciki, tana jiyo tana bata amsa sa Eh murmushi tayi tana kallon yarinyarta da ke wasa a keken yara tana wasanninta babu damuwa ko d'aya a fuskarta. Tura k'ofar Suleim tayi ta shigo da sallama, waigowa tayi ta amsa tana fad'ad'a murmushinta.
"Kin kyauta kenan?".
"Me nayi sweetheart ina Afdhal?".
"Au baki san abinda kika yi ba huh Lele? Kin kashe layukan ki jiya wani irin kira ne ban miki ba kika k'i d'aga wayata k'arshe ma kika kashe wayar gabad'aya, na kuma zo har gidan na gama ringing bell baki fito ba balle in sa ran zaki bud'e balle ki bari in shiga ciki".
"Ayyah Sweetheart wallahi jiya bacci nayi sosai ban tashi ba sai yamma".
"Kiran wayar fa, shi ma baki gani ba?".
"Ban gani ba wallah, a dnd take fa shiyasa".
"Kin rufe kan ki a gida ba kya tsoron wani abu ya faru?".
"Ba abinda zai faru in shaa Allah, and ba wai locking kai na nayi ba kawai dai ina son zama ni ɗaya ne ko yanzu ma haka ina son zama ni d'aya''.
"Zama ke d'aya cutar da ke kawai zai yi ba zai taimake ki ba, so ki daina please ".
"Kuma ku daina damuwa, ba abinda ze same ni i'm alright dear".
"Na ji tohm,,,,princess!" Ta juya kan Sairah da ke ta zillo da ganinta, d'aukarta tayi tana ta mata gwalan-gwalan alamun sanayya. Zama tayi suka fara fira ba ta ma dad'e ba ta koma nata office d'in d'auke da Sairah a hannunta ita kuma tayi focusing a kan aikinta da kyau.
Zamanta a office d'in ya sa d'an damuwarta ragewa sosai, hakan ne ma ya sa ta kasa tafiya gida sai to 6. Ba ta bi ta kan Burhaan ba balle ta san ya dawo ko bai dawo ba girkin ta kawai ta yi ta ci tayi wanka ta zauna tana kallon wani series a Show max, wanda sosai ya d'auke mata hankali ko da ma ya dawo har ya ci abincin ba ta sani ba sai da ya shigo cikin d'akin nata. Barka da dawowa tayi masa ta cigaba da kallonta, zama yayi a kan gadon shima yana kallon screen d'in system d'in yana shafa haɓar ta.
"Fareesah na gaisheki".
Kallon ashe ba ka da wayau tayi masa sannan tace " ina amsawa" tana janye idanunta zuwa inda suke.
Shiru mai tsayi ne ya biyo bayan maganar da tayi, bai sake magana ba shima don yana a Islaam d'in shi mara son raini har yanzu duk kuma wani ra-ra-gefe da yake yi don ya samu ta saki jiki ne don bai son yanda take yi kamar ya cuceta.
Gajiya yayi ya zame ya kwanta yana mai rungume da Sairah a jikinshi yana danna waya har bacci ya kwashe shi, ita ko sai after 11 kafin ta zame ta kwanta.
Zaune take a main parlor da shirinta tsaf na fita, sai dai haka nan take jin k'yuiyar fita sai tayi zamanta tana kallon shirin Ae dil hai mushkil duk da ko movie d'in ya kwana biyu but ba gajiya da kallonshi don har k'asar ranta tana admiring kalar soyayyar da Ayan yakewa Alizeh duk da ba ta sani ba bai kuma samu courage d'in gaya mata ba sai a lokacin da komai ya k'ure. Lumshe idanu tayi tana tunani a ranta shin ko dama Burhaan ya dad'e yana son ita Fareesahn ne hakan ya sa ya k'i amsar tata soyayyar? Ajiyar zuciya ta sauke tana mai jin rauni yana baibayeta in dai har ya san Fareesah da daɗewa ya kamata tayi masa adalci, amma kuma ai babu adalci a soyayya kowa kawai biyan muradinshi ya sani in da ko akwai ta toh shi Burhaan ne ya fi kamata ya yi mata adalci ko ba don komai ba ko don irin soyayyar da ita d'in ta nuna masa.
K'arar babbar mota tana honk ne ya katse mata tunaninta da ta tafi, numfashi ta ajiye tana kallon parlorn don da a nata firgicin ta zata tana kan hanya ne. Sai kuma mik'e tana lek'e ta window 'mai ya kawo babbar mota gidan nan?'. Tana nan tsaye sai ga motar ta shigo ciki, Maskawa constructions aka rubuta a gaban motar ta na tsaye taga wasu sun fito. Inda ta ajiye motocinta suka nunawa security da suke tare sai kuma suka ciro meauring tape suka gwada tsayi da faɗi na wurin, ba su jima ba suka gama mai da komai na su suka yi suka ja motar su suka fita daga gida.
Kai ta gyad'a kawai ta koma inda ta ke da farko, system d'in ta kashe ta koma ciki kayanta ta had'o ta fita da su waje. Tana saka kayan a mota Jethro ya taso yana gaisheta, amsawa tayi tana cigaba da abinda take yi d'an gyaran murya yayi yana cewa " Madam constructors d'in sun ce wai za'a kwashe motocin nan though sun yi measuring d'in wurin haka".
"Why?".
"Haka dai suka ce".
"Sai suka ce ka gaya min ko?".
"No, sun..."
"Tunda kace A'a to ya isa, ka gayawa wanda suka aikeka wurinshi okay?".
"Ok Ma".
Juyawa tayi ciki ta d'auko Sairah dake aikin bacci tun safe a carriage d'in ta ta saka ta tasa mata belt, sannan ta shiga ita ma motar ta ja ta bar gidan.
Washegari da asuba tana gyaran d'aki sai ga Islaam da ya tafi masallaci ya shigo, tsayawa yayi ya jingina da mirror yace " ina car keys d'in ki?".
"Me zaa yi da su?".
"Za a kwashe motocin ne akai su garage d'ina, don zaa rushe garage d'in za a had'a da fili a yi ginin part d'in da Fareesah za ta zauna".
"Ginin mene? Ba dai a nan zata zauna ba?".
"A nan mana".
"Gaskiya ba zan iya zama da ita ba".
"Why?".
"Ni dai haka nan, kawai ka raba mana gida".
"Ba zan iya ba, tare zaku zauna da ita".
"Nima ba zan iya zama da ita ba gaskiya".
Tsura mata idanu yayi yana cewa " wannan kuma damuwarki ce, kuma ra'ayinki so maganarki ba damuwa ta bane ki bani key".
"Saboda ni ban da muhimmanci a gidan nan right".
"Ki bani keys Nadeefah ban son magana".
Kallonshi ta tsaya yi hawaye yana cika mata idanu, yayinda sabon rauni yake dad'a kamata cewa yayi " ba zaki ba ni ba ne?".
"In dai har had'a mu zaka yi gaskiya ba zan iya zama ba".
"Ga ki ga hanya nan ai, Allah ya bada sa'a".
Ya k'arashe yana duban madubin drawern ya bud'e nan ya ga keys d'in a ajiye juyawa yayi niyyar yi ya bar d'akin ya jiyota tana cewa.
"Okay then".
"Ok then" ya amsata exiting the room, kasa jurewa tayi ta zauna a kan gadon tana fashewa da wani kuka mai cin rai. Zamansu a gida d'aya is abu ne da ba ta tab'a sawa ranta ba, ta yi tunanin raba musu gida zai yi wanda shi ne kwanciyar hankalinsu baki d'aya don ta tabbatar in suka zauna a tare sai matar ta san bai sonta cusa mai ita aka yi wanda ba komai zai janyo ba face zubewar mutunci da darajar da ba ta da tabbacin ya siya mata a wurin yarinyar.
Tana zaune tana kukan ya dawo d'akin da keys d'in ajiyewa yayi a inda ya d'auka ya juya ya fita, k'ara sautin kukanta tayi. Sai da tayi ma'ishi kafin ta share hawayenta tana murmushi mai ciwo lokaci yayi da zata yi abinda ranta ya dad'e yana sak'a mata ba tafiya zata yi ba amma zata ɗauki hutu.
Tashi tayi ta cigaba da aikinta kamar ba abinda ya faru, sanda ta shiga d'akin na shi yana zauna a kan kujera yana waya ba ta kalleshi ba tayi gyaran ta fita. Kitchen ta koma ta had'a breakfast Salmon wraps tayi sai oven-roasted potato and plantain ta d'anyi peppered sauce kad'an ta dafa mint and lemon tea da ya ji k'ayan k'amshi jera komai tayi a kan dining kafin ta wuce ciki. Wanka tayi tai kwanciyarta tana ta lissafi har barci ya d'auke ta, ba ita ta tashi ba sai after 10.
Wanka ta sake yi tana fitowa Sairah na tashi sai kawai ta koma da ita wanka tayi mata ta shiryata ita ma ta shirya cikin plain silky gown bak'a. Hijabi Sky blue ta d'auka sai takalmi da handbag blacks su ma parlor ta kai ta ajiye ta dawo, baby bag d'in Sairah ta had'a kaya ta d'aukar mata kusan set uku sai baby food d'in ta da milk da komai duk ta had'a, fita tayi zuwa kitchen water flask d'in da ta sa ruwan zafi ta d'auko sai robar da ta sa bananas da apple a ciki. A bag d'in ta jera kafin ta koma cikin d'akin yarinyar ta d'auka ta fita, ba ta ko zauna cin abinci ba don ba ta jin yunwa ko d'aya. Fitar da kayan tayi nan ta ga motocin a garage d'in shi kamar yadda ya fad'i d'in, a baya ta ajiye komai ta koma ta d'auko jakarta kashe kayan wuta tayi ta rufe cikin gidan ta fita.
Yerwa Estate tayi wa tsinke direct gidan Umma ta sauka babu kowa a gidan sai masu aiki da ke kai komo alamun sun fita ne, ba ta kai ga shiga ba ta juya zuwa gidan Hajjah.
A kan dadduma ta tarda ta tana lazumi bayan idar da sallahr duhaa da tayi, zama tayi a gefen daddumar tana kallonta ita ma duban nata take yi tana kai k'arshen lazumin tayi addua ta shafa.
"Barka da safiya Hajjah".
"Me ya sameki?" Ta tambaya cike da kulawa tana d'aukar yarinyar da ke ta zillo zata je wurinta.
"Babu komai".
"Babu komai aina bayan fuskarki ta nuna kin sha kuka sosai menene?".
"Hajjah wai gida d'aya zai had'a mu?".
"Me ya faru da hakan?".
"Hajjah zai fa ta wulak'anta ni a gabanta ne fa".
"Kul da maganar wulak'ancin nan daga bakinki, babu abinda zai faru sai alkhairi in sha Allah".
"Hajjah baki san Ya Islaam ba ne".
"Ba maganar sanin shi ba ne ko rashin hakan rabon gidan naku ma zai iya sakawa ta san komai a kan ku, ina amfanin yana d'oki in zai bar gidanki yaje wurinta ko ya dinga damuwa in zai bar wurinta. K'iri-k'iri ya nuna mata bai son ki sai ita, a ma bar wannan maganar ba ta shi ake yi ba in shaa Allahu ba ma zai yi hakan ba" .
"Ni dai Hajjah ba zan zauna da ita ba kam, ko dai ya raba gida ko in bar mata gidan".
"Au duk maganar da nayi da ke bai miki ba ko? Toh gaki ga hanya nan ki bar gidan ko an gaya miki ita kika yiwa asara? Kan ki zaki yiwa da 'yar ki".
"Hajjah...."
"Ba wani Hajjah idan dai ba zaki ji abinda nace ba, ki cire damuwa a ranki ki zauna da kowa lafiya in shaa Allah komai zai zo k'arshe kuma ko banda rai sai ya gane darajarki a wurinshi".
"Uhmm Hajjah na ji ga Sairah nan ni zan tafi office".
"Ok tohm Allah ya tsare hanya".
Duk'awa tayi tai kissing yarinyar a cheeks tana mai amsawa da Ameen, tayi wucewarta. Direct daga nan office ta wuce ta zauna tana ta tunani, ganin tunanin ba zai k'ara mata komai ba ne sai kawai ta tashi ta fita ba ta d'auki mota ba da k'afa ta fita tana tsallaka titi.
Sai kuma tsayuwar yayi mata wani kala sai yana tuno mata da undergraduate years d'in ta lokacin da take tsayawa a train stations ta shiga trains or subways zuwa school ko zuwa gida lokacin ba ta koma dorm ba.
Murmushi tayi tana kallon keken da ya tsaya a gabanta, shiga tayi ciki ta zauna me keken yace " Hajiya ina zamu je?".
"Mu je dai" ta amsa tana d'aga wayarta wata number ta kira sai da ya kusa katsewa aka d'aga.
"Kun bud'e ne?".
Shiru tayi tana sauraron amsar da aka ba ta sai ta kuma cewa " an yi reserving V.I.P ne?".
''Ok tohm, on my way".
Daga haka ta katse wayar tana gayawa mai keken inda zai kaita.
Zaune yake a eateryn da ya kawo Fareesah zata ci abinci, daga school ya kawota nan don ta gaya masa ba ta ci abinci ba don a yanzu ba su da aiki sai yawon gidan abinci.
Kiran Hajjah ne ya shigo wayar shi bai d'aga ba kamar kullum sai da ya gama ringing sannan ya kirata back.
"Barka da yamma".
"Yawwa, ka kira Lele ko kai kazo ta zo ta d'auki yarinyar nan, yau kuka take tayi".
"Ita Lelen fa?".
"Tun Zuhr nake kiranta bai shiga".
"Bari in kirata".
Dialing number Lelen ya fara yi yana kallon Fareesahn da ta k'ure shi da idanu kamar zata cinye shi, shi ma dai bai shigan ba switch off ake gaya mai.
Sake kira yayi still bai shiga ba, kiran Hajjahn yayi ya shaida mata da yana tafe yanzu.
"Cherrie kin gama ko, mu je in ajiye ki a gida".
Har za ta tambayeshi me yake faruwa sai kuma ta tuna yanda ya tsani bin ƙwaƙƙwafi don haka tace toh ta mik'e don dama sun gama hira suke yi, tashi tayi suka je wurin biya ya biya suka tafi a hanya ma sai gwada number yake yi bai shiga.
Yana ajiye Fareesahr bai ko tsaya ba ya ce mata zai je ya dawo kana ya juya akalar motar zuwa Yerwa ko gidan Umma bai shiga ba ya wuce gidan Hajjah, sanda ya shiga ciki da Yana ya fara cin karo tana goye da Sairahn a baya ita kuma tana jijjiga ta. Gaisheta yayi da girmamawa ta amsa ita ma cikeda girmamawa, lokacin ne Hajjah ta fito hannunta da waya kallonshi tayi tace " ai da fari na zata Lelen ce tazo da na ji mota ta shigo da sai na b'ata mata rai".
"Ai har yanzu number nata bai shiga kuma duka biyun ko dai network ko ta kashe su".
"A dalilin menene mutum da hankalinshi zai kashe waya ba ma d'aya ba har biyu Islaam? Ai ko ni nan da na tsufa ban kashe waya balle ita tana d'iyar mace, ga yarinyar nan sai kuka take ni har tsoro ma na ji na sha ko wani wurin ke mata ciwo sai daga baya na gane rigima ce kawai".
"Yau 'yan rigimar na kusa ne shiyasa".
"Ita fa ba gwanar shi bane sam, yarinyar da take wuni cir a nan gidan har sai an zo d'aukarta amma yau tun fa wurin 12 take kukan nan shi ne ma abinda ya tsorata ni".
"Bari dai mu je mu gani k'ila ma tana hanya".
"Ita ai ta sani, sai anjima tohm Maman kuka zo nan tohm '' Hajjahr ta furta tana kwanceta daga bayan Yana, mik'a mai ita tayi ya amsheta ai ko da sauri ta shige jikinshi ta lafe tana sauke ajiyar zuciya. Dariya yayi yana cewa "yau Hajjahr kike wa k'yuiya Princess".
"Ai ko queen ce ku je kuyi ta fama sai da safe" ta k'arashe tana mai rataya mai baby bag d'insu. Sallama yayi musu ya fita zuwa waje jakar ya fara ajiyewa a front seat kafin ya shiga ya zauna a k'irjinshi ya kwantar da ita ya sa musu belt da kyau kafin ya tada motar a hankali. Yerwa complex ya nufa wurin Lelen don ta san ya d'auki Sairahn ba sai taje gidan Hajjah ba.
A kusa da motarta yayi parking yana ayyana cewa 'tana nan kenan ma da gangan ta kashe wayar' tsaki yayi ya fito rungume da ita ya hau saman nata inda yau ne karon farko da ya tab'a zuwa shagon, maaikata ne suke ta kai-kawo a wurin alamun sun kusa tashi. Wata matashiya ya hango da uniform ta fito daga VIP lounge d'in su inda ake special treatment hannu ya d'aga mata da sauri ko ta k'araso tana masa barka da zuwa a tunaninta shi ne mijin matar da suka gama ma gyaran jiki sai da ta k'araso ta ga ashe mijin madam ne.
Da sauri ta gaishe shi ya amsa a fisge yana tambayar " madam d'in taku fa?".
"Ai ta wuce gida tun d'azu?".
"Gida kuma? Tun yaushe?".
"Tun da rana, don na shiga office d'in ban ganta ba so na zaci ko tana office d'in Madam Suleim ne sai da ta zo nemanta ne da Asr sannan na san ta wuce".
"Kuma ba ta fita da motarta ba?".
"Eh, a nan ta bar shi ban san me yasa ba".
"Ko tana da matsala ne motar?".
"I don't know sir".
"Ok thanks". Ya fad'i yana juyawa ya fita, a daidai stairs ya had'u da Suleim tana rik'e da hannun Afdhal dake tafiya koina, tsayawa tayi tana gaisheshi ya amsa blankly yana cewa "tun yaushe Nadeefah ta tafi gida?".
"Wlh ban sani ba Yaa, kawai na shiga ne ban ganta ba shi ne Fatee take cewa sun zata tana wurina kuma motar ta ma tana nan".
"Ok then goodnight" ya furta yana sauka daga stairs d'in ko Yusairahn dake son zuwa wurinta bai bari ta amsa ba, zaman da suka yi d'azu yayi kafin ya ja motar zuwa gida.
Parking yayi ya fita daga motar ya bud'e k'ofar part d'in shi ya shiga ciki, bai ko zauna ba ya shiga cikin parlor sai dai tsit babu motsin kuwa sai na fan da sanyin Acn da ya cakud'e da k'amshin turaren parlorn. Kallon agogo yayi 17 minutes to 5, kai ya gyad'a ya nufi dining nan ya tarda warmers a ajiye. Lek'a kitchen d'in yayi ba kowa sai ya fito ya nufi d'akin ta shima dai babu kowa har toilet, fitowa yayi ya koma dining d'in ya bud'e warmer guda d'aya nan ya tarda ashe abincin safe ne wanda ya ci ya rage ba sabo aka yi ba.
Ji yayi k'irjinshi ya buga daman yarinyar tana hannunshi sai kawai ya koma waje cikin motar ya shiga ya sake kwantar da ita ya nufi gate. Tsayawa yayi yana tambayar security " yaushe Matata ta fita?".
"Around 10".
"Ba kuma ta dawo ba?".
"Yes sir".
Ok ya furta yana jan motar ya harbata kan titi, ciro wayarshi yayi ya fara dialing number Umma tana shiga bai ko tsaya gaisheta ba ya fara tambayarta ko Lele ta zo no tace masa sai ya katse wayar yana sake kiran hajjah itama dai maganar d'aya ce bata dawo ba. Motar ya ja ya koma Yerwa complex bai shiga ba yake tambayar securityn dake duty ko Nadeefah ta dawo Aa yace, sai ya canja tambayar tun yaushe ta fita? "12:15 ma bata yi ba ta fita".
Ok thanks ya amsa shi har zai ja motar si ga d'ayan securityn yazo wurin gaishe shi yayi ya amsa securityn ne yace " mijin Madam Nadeefah ko?".
"Eh ni ne lafiya dai ko?".
"Eh ta bani ajiyar motarta ne tace min yanzu zata dawo kuma har yanzu bata dawo ba".
"Ka ga fitar ta kenan?".
"Eh yallab'ai".
"Wani mota ka ga ta shiga?".
"Ba ta shiga mota ba napep ta tsallaka ta hau a can wurin" ya furta yana mai nuna inda ta tsaya.
"Ina ka ga keken ya yi da ta hau".
"Can hanyar " ya amsa yana nuna inda ya ga keken ya ja wanda ya rabe kusan gida uku wato "ung rimi, unguwar sarki ko Isa kaita". Godiya ya masa ya ja motar ya bar wurin, a dai dai junction d'in da ta nuna masa ya tsaya rasa ina zai dosa yayi sai ya ciro wayarshi yana duba last location d'in ta Sultan road ya nuna masa jan motar yayi location d'in wurin yana guiding d'in shi yana zuwa dai-dai wajen ya ƙare. Tsayawa yayi a wurin yana kallon yanayin hanyar yayinda wani sabon tsoro ya sake kamashi yana mai tuno kalamanta na safiya " zan tafi in dai had'a mu za'a yi".
Ba dai tafiya tayi ba?
In ma ta tafi ina zata je?.
Me yasa kuma ta bar masa Sairah ba ta tafi da ita ba?.
Muma dai kai zamu tambaya Aleji🌚
Countdown to book 2
9042522373
Moniepoint Khadija Ismail
Evidence ta WhatsApp ***
Deejasmah ✍🏼