NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)

CHAPTER 35 (HIS WIFE).

by @deejasmah

CHAPTER 35 (HIS WIFE).


"With all due respect, Yaa ba zan iya ba ka nemi wata ta had'a maka please".
Ta furta kan ta tsaye babu ko d'arr bare shakka, dubanta yayi yana mai cewa " ban dai isan ba kenan?".
Girgiza kai tayi tana cewa "ka Isa har kayi yawa kawaici dai ba zan iya bane".

" Ba dai zaki yi ba ".

" Ban iya ba ne fa, ban ma san ta ina ake had'awa ba so a bar ma wannan maganar".

"An bar ta Madam, zan nemi wanda zata yi".

" ok " ta furta tana maida hankalinta kacokan ta kallon da suke yi, shi ma bai wani jima ba ya tashi.


Kasancewar jumuah ne ya sanya da ya fita daga masjid direct gidan Umma ya nufa, gaisawa suka yi ta amsa kadaran-kadahan kamar yadda itama take masa tun da maganar auren nan ya shigo. Sai dai bai yi k'asa a guiwa ba ya zauna, yana nan zaune sai ga drivern Hajjah ya kawo sak'on abincin da Nadeefahr ke yi every Friday nan fa Umman ta dinga shi mata albarka ta kuma kirata a waya tana gode mata kamar wacce ta kawo musu duniya.



Kawo abincin bai fi da 5 minutes ba Safwaan ya shigo da sallama ganinshi zauna ya sanya shi fad'ad'a fara'arshi cikeda isgilanci yace " ka ga manyan angwaye na k'asa".


"Ina wasa da kai ko Safwaan".

" Kai Yaya ka fa san wannan sha'anin namu ne , ni naga ma har wani haske kake k'arawa ne. Yanzu bikin saura kwana nawa ne?".

Harara Umma ta b'alla masa yana kallo ko ta kai bai bi ba ya cigaba da shakiyancinshi sai da ta gaji tace " kai Safwaan fitar min a parlor ".



"Haba Ummana ɗa autan ki ne fa, uhmm wai Ya Islam yaushe zaka kawo mana ita  mu gaisa ne".



"Ba za dai ka daina ba ko?" In ji Umma tana sake jifanshi da kallon gargad'i shi ko Burhaan d'in cewa yayi " yawwa Umma ranar Sunday zan kawo miki ita ku gaisa". 

Kai tsaye tace masa " ta sha zamanta na gode".

"Umma....."


"Ka gaida mutanen gidan in kaje".


Tana furta haka ta tsantsame jikinta ta tashi, da idanu ya bita while Safwaan ke ta k'ok'arin suppressing dariyar da ta ciyo shi. Girgiza kai yayi ganin ta wuce ba tareda ta dubi ko gefen da yake ba yana mai mik'ewa tsaye cikeda shak'iyancin da ba wai ya daina ba ne dama yace " Yaa ba wai wucewa zaka yi ba?".


"Yes zan lek'a Mommy ne kafin in tafi".


" Okay then Allah ya tsare, a gaida princes da Lele".


"Uhmm, za su ji".

Hanyar d'akin Umman ya nufa tana kwance kan kujera waya take yi hakan ya sa ya samu waje kan sofarta ya zauna da niyyar jiranta ta kammala, sa dai d'agowa tayi tana mai nuna masa hannu alamun " lafiya kuwa?".

" Da ma zan wuce ne".

"Sai aka yi ya?" ta tambaya bayan ta kawar da wayar gefe, miyau ya d'an had'iye yana mai cewa " nothing, sai anjima ".



" Allah tsare". Ta furta tana cigaba da wayan da alamu da Abba da bai gari take yi, cikin sanyin jiki ya bar d'akin sanda ma ya fita parlorn babu kowa don haka ya fita kawai yana jan motar shi ya bar gidan.



Gidan Mommy ya nufa kan shi tsaye a nan ko ya samu tarba mai kyau irin wacce bai yi tsammani ba duba da yanda suka rabu a waya don har da tayin had'ad'diyar jollof rice ya samu sai dai bai ci ba don ya baro Nadeefah tana girki in kuma akwai abinda ya tsana shi ne missing abincin ta. Ruwan dake gabanshi kawai ya sha yana mai dubanta jin maganar da take yi "D'an albarka har ka kawo kud'in kayan fad'ar kishiyar ne?".


"Ki yi lissafi Mommy duka da kayan lefen nawa zai iya ci?".

"Maganar lefe kai ta shafa ai ni abu d'aya na sani".


"Wai Mommy me yasa ake son maida ni kamar wani mara gata ne a garin nan? A ce duk yawan nan namu an rasa mai had'a min lefe? Ba fa kyauta nace a min ba......"



"Ake son maida kai mara gata ko kai ke k'ok'arin maida kanka? Ai Burhaan mun maka iya gatan da muke ganin zamu maka amma tunda bamu iya ba ai shiyasa kowa ya barka da taka iyawar ga ka ga shi nan Allah ya bada sa'a".



"Mommy.....!".



"Islaam kar ka sake min maganar lefe a gidan nan, in mu nan mun k'i had'awa ai ita yarinyar ba zata k'i zuwa siyo kayan da zata saka a jikinta ba ko. Sai kaje ka d'auketa bakinka alaikum amma in ka sake min batunta sai na b'ata maka rai fiyeda tsammanin ka".



"Amma fa kina saida kayan nan Mommy".


"Eh, kai ne ban ga damar siyarwa ba, ina dai kayana ne?.


"Shikenan, ba komai".


"In ma ba shikenan ba Islaam kazo kayi abinda zaka yi, nace in ma da komai don Allah ka zo kayi mu ga iya naka yin don ubanka".



"Allah ya baki hak'uri".


"Wannan kuma matsalarka ce" ta furta tana mai cigaba da cin abincin da dama shi ya tarda ta tana yi, ganin yanda tayi banza da shi ne ya sanya shi mik'ewa cikin sanyin jiki yace " sai anjima".


"Mu jima da yawa". Ta amsa masa cikeda tsiwa, ajiyar zuciya ya sauke kawai ya fita bai sake zuwa koina ba ya nufi gida. A hanya ko zuciyarshi fal take da tunanin abinda ake masa sai kawai tunani ya fad'o masa a rai, a take yayi na'am da tunanin don ya tabbatar in har su manyan da suke sama da shi sun k'i yi masa toh tabbas na k'asa ba zasu k'i ba. Fiddo wayarshi yayi ya fara kiran number Najwaah in da ringing biyu a na ukun aka d'aga.


"Barka da rana Yaa".

''Yawwa Najwaah, ya gidan da yara?".


"Kowa yana lafiya".


"Kina ina ne haka?".


"Ina gida".


"Yau kina off kenan?".


"Aa dawowata kenan morning na yi".

"Ok, kina jina ko?".


"Eh Yaa".


"Wani aiki zaki d'an min ba mai yawa ba ne ko wahala yana dai da cin lokaci".

"Haba Yaa ai babu komai duk wahalarshi matuƙar bai fi k'arfina ba in shaa Allah zan yi".

"Yawwa, dama lefe ne zaki had'a min".


"Lefe kuma?".


"Eh lefe ai kin san shi, kayakin akwati na amare ba?".


"Eh, amma ai Yaa ni ban iya ba".


"Sai ki samu wanda yake yi ke dai kawai ki zama in charge sai in tura miki kud'in"

Shiru tayi tana mai sauraranshi k'irjinta yana bugawa, don tana tsaka mai wuya ne ba zata iya cewa Yaa Islaam A'a ba duk da ko mugun haushinshi da suke ji kan auren nan. Sai dai ta tabbatar ba zata iya ba don Umma ta musu kashedi mai shiga jiki kan saka hannu akan lamarin da ya shafi auren nan, tace su bar shi yayi kayan shi shi kad'ai ko contributions da ta kawo maganar a had'a masa cewa tayi sai ta sab'a mata kamanni balle yanzu ta ji ta had'a lefe...


"Kina ji na?" Ya katse mata tunanin da ta tafi.

"I'm sorry Yaa ina ta tunanin wanda zan had'a ka da shi ne".


"No need of that ki neme shi kawai in ya fad'i abinda ake buk'ata sai ki yi updating d'ina".


"Ai Yaa ka ga ni ba wai na san kan abun ba ne ka yi magana da Ya Budu don ta fi mu iyawa ko na bikinka da Lele ita Umma suka had'a komai na alada so ba wai na san su sosai bane".


"Ban ce ke zaki ba Najwaah, ke kawai zaki samu wani ne yayi".


"What if ya saka kaya marasa kyau? Ba ma wannan ba ya zancen buk'atun al'ada da ake yi a lefe ka san fa kayan da ake yi ba irin ordinary kaya".


"Wai Najwaah miye kike wani corner-corner ne? Ke baki san kaya masu kyau ba ne toh aina kike samun naki wainda kike sakawa? Kuma maganar al'ada ai ba al'adun mu d'aya da su ba Bahaushiya ce so wanda zamu kai irin na Hausawa ne ba wani abu ba".



"In dai hakan ne ka yi magana da Ya Budu kawai".


"Wai ban san da ita ba ne na kiraki".


"Yaa ka yi hak'uri Allah ban iya ba ne".


"Ba zakiyi ba kema ko?".


"I'm sorry, wlh Yaaa ba daga ni ba ne....."


"Issokay, thanks" ya furta yana datse wayar yana mai jin wani haushi a ran sh, itama ji tayi babu dad'i amma ba za tayi ba tunda Umma ta gama magana bayan nan ma ya zata iya had'a lefen kishiyar Lele? Haba.


Tsaki yayi yana faɗin wasu kalmomi k'asan mak'oshinshi yana mai jinjina abinda ake masa yau, wanda in da sun ga dama zasu da wani vendor wanda ba sai kowa ya ji ba amma ji yanda su ke wahalar da shi. In da ko shima zai sani da ba zai dinga kiransu suna wulak'anshi ba, tad'a motar yayi yana hawa titi don dama parking yayi a gefen hanya gudun samun matsala a kan hanya.






Yana shiga unguwar a titin farko yaci karo da Ya Nazeef zai fita wanda distant cousin d'in su ne but a nan ya rayu har shima ya fara aiki da Yerwa Corporation yayi aure da dad'ewa duk a cikin Yerwa, tsayawa yayi ganin haka sai shi ma ya tsaya. 


" Haji Islaam likita bokan turai, kuma angon gobe" ya fad'i cikeda barkwanci kasantuwarshi mutum mai tsananin barkwanci wanda ko kusa duniya ba ta dame shi ba.


"Kai Yaa Nazeef har da kai?".


"Ai ba zolaya ba ce, don ba k'arya nayi ba Angon Lelen Yerwa ne ita da Amarya". 


"Toh shikenan na amsa kam, Ya iyali?

"Mun gode Allah, ya gidan da Yusairah?


"Kowa lafiya Ya aikin?".


"Alhamdulillah, ba dai wani sauk'i yanzu ma haka meeting nake da shi da wasu bak'i".


"Shi ne na ka tsaya in kayi latti fa Yaa Nazeef".



"Ba za ai lattin nan ba kam in shaa Allah".


"Toh Yaa Nazeef, Allah ya tsare bari mu samu mu k'arasa kai ma kar kayi latti".


"Toh shikenan Islaam ka gaida gidan ".


"Za suji in shaa Allah" ya amsa yana shigewa cikin motarshi.


Ganin Nazeef ne ya tada masa wani k'aimi sai ya fasa wucewa street d'in su, kawai sai ya shiga layin da shi Yaa Nazeef d'in ya fito specifically ma gidan shi yayi wa tsinke. Securityn da ya d'an koma ya zauna kenan bayan bud'e gate ne ya ji k'arar honk, tasowa yayi ya bud'e nan yayi arba da bak'uwar fuska don shi Islaam ba wai yana wani ziyara ba ne sosai. Ko da ma yana yi toh bai zuwa gidan duk da ko kasantuwar matar gidan d'iya ga k'anwar Umma tsakaninsu da ita a family shi ma ba wai raga mata yake yi ba.



Securityn bai yi k'asa a guiwa ba don ya tabbatar da cewa duk wanda ya gani a gidan toh either d'an uwansu ko wani abokin arzik'i amma ba wai wani can wanda ba a buk'ata ba, don tsarin 'yan Yerwa tabbas daban yake da na kowa. Bud'e masa yayi ya shiga ciki ko gaisuwar shi bai amsa ba sai hannu ya d'aga masa kawai ya shiga ciki.



Da sallama a bakinshi ya shiga parlorn wasu yara ne dake zaune suka amsa suna duban mai shigowa, ganin Burhaan ya sa da gudu suka taso suna " oyoyo Uncle". Rungumesu yayi dukansu shima sai da suka d'an dauki time kafin ya zaresu yana zama kan cushion. Zagayeshi suka kuma yi kowa yana son a amsar gaisuwarshi da tambayar Sairah da suke yi, gabad'aya ya amsa musu yana mai cewa "ina mommyn ku?".


Babbar cikinsu mai suna Sanayah ce ta mik'e tana cewa "barin kira ta" da kai ya amsa mata ba ta ma ko lura ba ta shige ciki. After like 2 minutes sai ga ta sun dawo da maman da ba kowa ba ce face Ainah, tana bayanta tana maimaita mata tambayar anya ta san wanda ya zo kuwa?.


"Allah Mommy Uncle Islaam ne".


"Ko dai Safwaan?".

Kafin ta kai ga ba ta amsa sun k'araso cikin parlorn, turus tayi ta tsaya tana mamakin abinda ya kawoshi gidanta sai dai shi bai masan sun fito ba don hankalinshi yana kan last born d'in ta Raihaan da ke bada sallahu wurin princess kamar wata babba.


"Ashe ko Burhaan d'in ne da gaske" ta furta cikin kasa b'oye mamakinta.

Dubanta yayi da kyau yana d'aga mata kai in affirmation yace " ni ne kuwa".

"Allah ya sa ba wani laifin na yi ba, ka san Ainah da laifuka take".

"Wani irin laifi kuma? Abu nake son ki d'an min".


Kallonshi tayi tsaf tana cewa " ni in maka abu? Wani kalan abu ne wannan zan maka ka tsallake jama'ar duniya bayan ni da kai ba wai shiri muke yi ba?".

"Waye yace ni da ke ba ma shiri? Yaushe muka yi rikici da kike fad'in haka?".


"Well ba mu yi rikici ba amma kowa ya san ni da kai ba ma wani jituwa haka nan balle aje ga maganar in maka abu, shi ko wani abu ne haka da ka tsallake kowa ka zo wurina a kaf mutanen Yerwa?".



"You see ko? Kayan lefe nake son ki had'a min".


Washe hak'ora tayi tana mai cewa " ahh ashe ma business ne yazo, waye zai yi aurene haka saboda in san kalar budget d'insu" ta tambaya tsakaninta da Allah don ita ta manta da wani maganar aurenshi.


"Na amaryar da zan aura in the next two months ne".



Fashewa tayi da dariya tana tafa hannaye, tsura mata idanu yayi yana mamakin abinda ya sanyata dariya har haka. Sai da tayi wanda ya isheta kafin tace " shi yasa ka zo gida na, sannu da ƙoƙari! Ikon Allah!".


"Toh miye abun dariya a maganar nan?".


"Ban son yin kuka ne Islaam don in na biyewa yanda zuciyata take toh shakkah babu kuka zan yi, amma yanzu na fahimci dalilin da ya saka ka tsallake dubban mutane ka zo wurina lallai ma".


"Ban gane kuka ba".


"Kuka mana, ashe kallon da kake min kenan ni ban sani ba".


Runtse idanu yayi ya tsani magana a kaikaice, ya fi son komai a yi masa shi kai tsaye hakan yasa yace " Ni fa duk ban son wannan, just go to the point Ainah".


"To ba zan yi ba Burhaan in na ga dama ma sai in kaika k'ara cos ka ci min zarafi wato gani mak'iyiyar Nadeefah ko? Shiyasa ka kwaso k'afa ka zo wurina in had'awa kishiyarta lefe, wannan ma ai zagi na kake yi".


"Waye yace ke mak'iyiyar Nadeefah ne, don kawai ance ki haɗa lefe shine kike cewa na zage ki?".


"Burhaan don Allah ka ce ba wai saboda ka ga ina yawan samun issue da Nadeefah ya sa kazo wurina in had'awa Amaryarka lefe ba? Ko an gaya maka ina mata abunda nake yi saboda na tsane ta ne? Mtsww ba laifinka bane Islaam ni ce na cika magana da shiga abinda bai shafeni ba".


"Ba abinda ya kawo ni nan ba kenan, business ya kawo ni in kika ga dama zaki yi".


"In kuma ban ga dama ba fa?".

"Then..?"

"Toh ba zan yi Islaam".

"Ba zaki yi ba?".


"Ai kaji ni da kyau".


"Ok nagode" ya fad'i yana mik'ewa.


"You are welcome" itama ta furta tana tashi tsaye, a da a baya yana mata kwarjini har bata iya rashin mutuncinta a gabanshi. A yanzu kam haushinshi take ji in tana da hali ma ta kamashi da duka sai ta ga bai motsi kafin ta k'yaleshi, fita yayi daga parlorn ta raka shi da mugun tsaki tana harararshi ciki ta wuce tana mita.



Zama yayi yana mamakin yanda jamaar Yerwa suka d'auki d'umi kan maganar aurenshi kai kace wani laifi gagarumi yake shirin aikatawa, wayarshi ya zaro ba tareda yayi shawara da kowa ba ya shiga bank app d'in shi account number Mommy ya lalubo kud'i masu yawa ya tura mata da description 'Lefe'. Yana turawa yayi murmushi ya ja motar ya bar gidan direct ya nufi na shi gidan don yau yayi yawo ainun.



Tun da ya shiga street d'in ya hango wata mota 206 parke a k'ofar gidanshi bai cika damuwa da abubuwa ba sai dai kuma hakanan ya ji yana son sanin motar waye. Don iya saninshi ba su da mai kalar motar a Yerwa bai kai ga k'arasawa ba wata ta fito daga gidan ta shiga motar, bai gane wacece ba amma tabbas ya san ya santa hakan ya sa ya k'aimi gurin isa inda motar take.




Yana isowa gate d'in motar tana barin wurin da ido kawai ya bi motar har ta juya a daidai gaban gidan Farhaan, ta gabanshi ta wuce ta fita daga layin completely tsaki yayi kawai ya danna honk aka bud'e masa. Yana shiga kiran Mommy na shigowa wayarshi, d'agawa yayi da sallama sai dai maimakon a amsa ya jiyo muryarta tana cewa.


"Burhaan don ubanka ni saar ka ce?".



"Mommy me nayi?''.


"Au me kayi kake tambayata? In gaya maka ba zan yi abu ba shine zaka tura min kud'in ina kuma tambayarka kana tambayata?".


"Mommy kud'in ba zai isa ba ne? ".


"Ni kake son maidawa mahaukaciya ko Burhaan?".


"Ina na isa Sweet Mom".

"Ka tura account numberka in maido maka da kud'inka kafin ranka ya b'aci".


"Mommy ki yi hak'uri ki had'a kayan nan kawai, Allah ya k'ara girma ".


"Islaam".

"Mommy I'm sorry, in akwai abinda bai kai ba ki gaya min".


"Burhaan ni ko? Zaka zo ka sameni ne" ta fa'di tana katse wayar, dariya ya kwashe da shi yana bud'e entrance door d'in ya shiga da sallama.


Amsawa tayi tana duban yanda yake murmushi, lallai ma namiji wato ya had'u da ita a waje shi ne don ya nuna mata shaidan had'uwarsu zai shigo mata gida yana murmushi?. Zama gefenta yayi yana kallonta sosai tayi kyau cikin Embellish atamfar da ta sanya mai ganye a jiki kalar burgundy da cream sai gold d'in jikinta wani kalar d'inki aka mata irin mai lafewar nan a jiki sannan an ci k'irjin da kyau don mole d'in da yake kafad'arta ma ya fito haka k'irjinta da ya tasa saboda shayarwa shima ya fito hannun ma wani irin k'arami aka mata kamar an so yin mara hannun ne gabaɗaya ga tsagun da aka mata a gefe da gefen rigar har kusan cinya ta kashe d'aurin da ake kira ture kaga tsiya. 



Zama yayi yana wasa da k'afar princess da itama an mata gayu cikin wata exclusive silk material kalar hot red, dukan su k'amshi suke yi kamar an bud'e kamfanin turare a wurin. 


Kamar ba ta so tace " barka da dawowa Yaa".

"Uhmm Wife barka da gida, irin wannan cin wanka haka?".

"Uhmm" itama ta amsa tana maida kanta gefe sai ta jiyo muryarshi yana jefa mata tambayar " waye ya zo gidan nan yanzu".


"Wani dama ya zo gidan nan ne?".

"Ba wasu sun zo ba?".

"Ni ma ban sani ba kam" ta amsa tana k'wafa alamun akwai abinda ke ranta.

"Me ya faru wife? Waye kuma ya zo gidan nan?".


"Wacce ka aiko ne tazo Yaa, ta kuma isar da sak'o yanda aka aikota and tace tana gaisheka ".

"Wace ce haka?".

"Yaya don Allah ka barni haka nan, na san ka ganta a waje ko in ce ka san da zuwanta".

"Wai Nadeefah miye kike min haka, ina tambayar ki kina wani irin magana?".


Maimakon ta ba shi amsa sai kawai ta fashe da kukan da take ta rik'ewa tana mai jin d'aci akan harshenta, kukanta ba k'aramin d'aga masa hankali yayi ba da sauri ya tashi daga wurin zamanshi ya zauna kusa da ita. Rarrashinta ya fara yi duk da bai san musabbabin kukan ba jikinshi yana ba shi yana da nasaba da ko wacece ta shiga bak'ar motar da ya gani a waje, juyin duniya yayi da ita kan ta fad'i wacece ta zo amma fafur ta k'iya sai jan hanci take yi. 

Had'e bakinsu yayi wuri d'aya wanda ya tilasta mata yin shiru ba tareda ta shirya ba, sai da yayi ma'ishinsa ya kuma tabbatar da ta natsu kafin ya janye. Idanu ya tsura mata yayinda ita kuma ta kwantar da kanta a kan kafad'arshi tana sauke numfashi a hankali, a kunnenta ya sake tambayarta waye ya zo.

"Ni ma ban santa ba".

"Baki santa ba? Then me ya saki kuka?''.

"Ba komai".

"Ok, ina zuwa" ya furta yana zareta daga jikinshi, mik'ewa yayi ya fita zuwa waje gate ya nufa ya fara kiran securities d'in dake wajen. 



Da sauri suka k'araso gabanshi suna tsayawa a wurin chief securityn ne ya amsa masa da "yes sir".

Dubansu yayi tsaf sannan ya jefo musu tambayar "wacece ta fita daga gidan nan yanzu ?".

"Sir, ba mu san ta ba wannan ne karon farko da ta fara zuwa".


"Karon ta na farko? Kuma ku ka bar ta ta shiga?".

"Tace ka san zata zo".

"Me?".

"Yes sir".

"Ina ta shiga toh?".

"New building sai main house".

"Okay" ya na furta haka ya juya ya koma can new bulding d'in, tardawa yayi maaikatan suna cigaba da ayyukansu da sun ma kusa kammalawa gabad'aya don kings constructions ba dai azama ba wurin aiki ga shi ba algus ko amaja komai na su tsaf ga kuma inganci. Suna ganinshi suka tsaya suna sake gaishe shi, amsawa yayi yana duban kings d'in dake mik'o masa hannu musabiha suka yi da tambayar aiki kana ya d'aura da mak'asudin zuwanshi wurin.

"Wata ta shigo nan bayan fitana?".

"Ohh amarya ba, ta zo ganin wuri".

"Amarya kuma?".

"Eh itafa tace aikinmu yayi kyau amma tace a canja design na wancan wall d'in amma na mata bayanin cewa baya cikin contract".

"Ohhh wow, bayan nan fa me tace?".

"Nothing, ta dai yaba da ayyukan da muke yi".

"Ta gaya muku sunanta ne?".

"Nope".

"Itace wannan?" Ya fad'i yana mik'a masa wayarsa da ya nemo hoton Fareesahr duk da zuciyarshi tana raya mai ba ita ba ce don itace mutum ta ƙarshen da zai yi expecting gani a cikin gidan a wannan lokacin.


"Eh itace kam".

"Okay na gode sosai, sannunku da aiki " daga haka ya juya ya fita, fitar ta shi ko tayi dai-dai da kiran da ya danna zuwa wayar Fareesahn.

Ringing biyu ta d'aga da muryarta na koyaushe da take masa magana tace " Babe..."


Tareta yayi da tambayar da ya firgita ta ainun " me ya kawo ki gidana, me kuma kika gayawa matata?".


"Kamar ya me ya kawoni gidanka? Ni aka ce maka na zo gidanka?".


"Ina tambayarki kina tambayata?".

"Ai ban gane in da tambayar ta dosa ba ne babe, ni me zai kawo ni gidanka?".


"Kar ki raina min wayau mana, yanzun nan fa kika bar gidana ina kuma tambayarki kina min yawo da hankali''.

"Ni aka ce maka na je gidanka? Ni da ko fita yau ban yi ba ban da lafiya ba ma haka ba kai in aka ce maka na zo sai ka yarda ma? Sai kace wacce ta k'osa, tabbas akwai abinda matarka take ƙullawa...."


"Hey! Dakata min kar kuma ki sa matata a maganar nan if not ranki zai b'aci" ya katse ta cikin zafin rai.


Kuka ta sa masa cikin kissa tace cewa " in ba matar ka to wacece zata fad'a maka irin wannan maganar ka yarda, so take ta shiga tsakaninmu da kai ko ta ja min bak'in jini".


"Dama kin daina wannan kukan don ba shi zai saka in yarda da ke ba ko kad'an kuwa, ni ba sakarai ba ne and na san ko wacece matata kuma in baki sani ba yau ki sani don zan aureki ba shi ke nufin ban son matata or ban san darajarta ba infact ban had'ata da kowa a matsayi da komai so, ki tsaya matsayin ki ".



"Ni ce baka son kenan?".

"Duk yanda kika ce, ni dai ina miki kashedin ki tsaya matsayinki kar kuma ki sake gigin zuwa min gida".


"Ina ganin ba forcing d'inka na yi ba ka ce kana sona, in ka daina ma zaka iya sanar min sai a fasa tunda dai kai baka bincike duk abinda aka gaya maka shi kake yarda da".


"Wani bincike zan yi bayan da idanuna na ganki?".

"Ni?" Ta furta cikin sanyin jiki.

Clearly ya amsa mata da " sure, in kuma kina da twin ne sai ki gaya min kina ganina kika shiga wata bak'ar mota. Zan zo har inda kike za kuma ki min bayanin abinda ya kawo ki gidana, ohh na fahimta ma so kike ki watsa min gida tun baki shigo ba ko?".


"Aa ni kawai fa...."


"In na so duk zaki min bayani, dama kina magana akan fasa aure ko? ".


"Ni ba haka nake nufi ba, i'm sorry".


"Kin yi min laifi ne ni? Matata kika ma wa dole ki bata haƙuri yanzu kuma".


"Haƙuri fa?".

"Kar kiyi don Allah kin ji?".

Bai jira cewarta ba ya bud'e k'ofar ya shiga ciki, tana zaune a inda ya barta sai dai sab'anin d'azu yanzu ba kuka take yi ba wayarta take dannawa. Zama yayi gefenta yana cewa Fareesah " ga ta nan ki bata hak'uri ".


Ya k'arashe yana kara mata waya a kunne kafin ta kai ga yin motsi ta jiyo muryarta tana cewa " ki yi hak'uri".


Lumshe idanu a hankali tace " issokay"  ta k'are ta na mai mik'a masa wayarshin da yana amsa kashewa yayi ya ajiye akan table d'in da ke gabanshi ya na mai sake maimaita kalmar " sorry".

"Issokay fa kuma ni ban ce maka tayi min wani abu ba".

"Ai da yake yau na fara saninki da ba zan san in an miki wani abu ba".

"Uhmm" ta furta tana mai jin d'acin maganar Fareesahn yana dawo mata kamar yanzu tayi shi musamman ma kalmar ' matar cushe gandun rashin zuciya' da ta jefeta da shi har da k'arawa da "da fatan kin shirya zama da matar so tunda ke baki da zuciyar tafiya daga gidan da ba a buk'atar ki ".


Dubanta yayi da kyau yana mai nazartar yanayinta wanda ya gama bayyana na abinda ke ranta na mai dad'i ba ne, hannu ya kai bisa nata da ke cinyarta yana matsawa cikin rarrashi. Ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ta mik'e zuwa kitchen biyota yayi a baya har zuwa gaban salad d'in lettuce da take k'ok'arin had'awa Fareesahn ta shigo gidan kuma ko da ta fita kasa k'arasawa tayi don komai nata ya tsaya cak hakan ya sanya ta gaza amma yanzu ta k'ok'arta ta had'a suka fito wurin abincin da tayi dirty rice ta dafa wacce komai nata ya wadatu sosai sai burnt pasta in hot milk sauce sai kuma salad d'in da kuma traditional baobab and apple juice with coconut extract.

Cikin sanyi suka ci abincin yau har yana tayata gyaran wurin da suka gama, tare ma suka yi wanke-wanke suka shirya kayan sai janta yake da hira ita ko ta k'i sakin jikinta yayinda haushinshi yake cikata. Ta kasa gasgata wai shi yake zuwa wurin yarinyar can yake gaya mata bai sonta dole akai masa ya aureta kuma yake zaune da ita, wanda ba k'aramin cin mutunci bane a gareta don ma Allah ya taimaketa bata tanka ba balle har ta fad'i wata maganar da zai bata abinda take so.


Shi ko da bai san me ya faru ba ma duk jikinshi yayi sanyi da yanayinta don ya tabbatar ba k'aramin abu zaa fad'a mata tayi haka ba, sai dai duk yanda ya so sani ba ta ba shi damar haka ba don gani take kamar raina mata wayau yake k'ok'arin yi bayan haka ma ta ya zata dubi idanunshi tace masa wai " Fareesahr tace mata baya sonta ne?" Da wani harshe da wani bakin? Ai yanda ta bar maganar a wurin ta bar shi kenan har abada in shaa Allah ba wai ta manta bane aa akwai randa zata mayar da martanin da zai rama wannan kalma ya kuma gogeshi daga ran ita wacce ta fad'in, da wanda ya fad'in mata da ita da aka sanarwa.



A ranakun sosai suka samu matsala da Fareesahr akan maganar har sai da mahaifiyarta ta shiga ciki kiranshi tayi wai tana mai fad'a akan bincike da bai yi, ai bai kamata komai aka fad'in masa ya yarda ba tare da ya bi kadin maganar ba. Har da d'aurawa da " ka san mata idan zaa k'ara mana abokiyar zama sai a hankali duk kuma wata hanyar da zamu bi don ganin hakan ya watse mu kan bi hakan kuma ba wai laifi ba ne don so ba abinda bai sawa amma in ana nunasshemu da nuna mana hanya sai kaga da an yi komai ya wuce kamar ba a yi ba".



Kallonta yayi yana gyad'a kai wato in ya fahimceta she wants to brainwash him akan matarshi kenan? Murmushi yayi mai sauti kana yace " ni fa Mama matata ba ta gaya min komai kan zuwanta ba, da idanuna na ganta tana fitowa daga gidan. Kuma ni Mata ta ba kalar matan da zasu iya komai don hana mijinsu aure ba ne, ko d'aya babu wannan a ranta maganar fasa aure ita Fareesah ita ta fara maganar don kawai na mata fad'a kuma Mama I'm sorry if magana ta ta ɓata miki rai amma gaskiya ba zan iya auren wacce ba zata ga darajar matata ba. In tana ganin ba zata iya zama da ni da Mata ta yanda ta ganmu ba toh za a iya fasawan kamar yanda tace d'in".



Kasa magana tayi tana kallonshi at the same time ta na mamakin kalar halinshi na yanda zai iya zama gabanta ya na mata zancen rabuwa da d'iyarta kamar bai san ita wacece gareta ba. (Lallai bakiga ma komai a halin Burhaan ba kam, mutumin da ya shaidawa Abbu wai bai son Nadeefah ne zaki ji mamakin don ya gaya miki zai fasa auren 'yarki da yake so?).


"Ai ko bata kyauta ba don ni bata gaya min taje gidanka ba, amma kayi hak'uri hakan ba zai sake faruwa ba. Zan mata fad'a tabbas don bata kyauta ba ba kuma d'abia ba ne sam-sam".



"Ai bata don karɓar laifin ta taje d'in sai pretending take yi wanda shi ke ɓata min rai, tunda dai ta san bata kyauta ba me yasa ba zata amsa laifin ta baɗa haƙuri ba? Secondly ta kuma daina min batun matata don ina ganin girmanta ba kuma zan shirya da duk wanda zai raina ta ba".


"Zata kiyaye in shaa Allah, maganar matar ka kuma tabbas ka cika d'an halak don haka ake son namiji mai tsayawa a gidanshi hakan ne ma zai bamu k'warin guiwar baka ita don mun tabbata hannu na gari zata shiga a dai cigaba da hak'uri".


"Nagode" ya furta yana mik'ewa sallama yayi mata ya ajiye mata hasafi akan table ita ko sai shi masa albarka take ta yi. Bai ko jira fitowarta ba ya ja motarshi zuwa BAY clinic don dama can zai je ta kirashi. Yana shiga a entrance ya had'u da Adnan da tun daga randa suka samu sab'anin nan har yau bai tanka shi da fari shi ma ya d'auki fushin da shi amma a yanzu shike shan wuya don nauyi sun masa yawa yana kuma buƙatar shi a rayuwarshi ko da da shawara zai ba shi kai ko fad'a ne suyi as long as suna shiri toh shi hakan ya isheshi ma wanda shi ma shigowarshi kenan, da sauri yayi parking ya fito daga motar yana k'wala kiran "Buddy".


Tsayawa yayi cak har sai da ya k'araso yana zuwa ya sake kiranshi yana mai dafa kafad'arshi harararshi yayi yana mai cewa " dallacan ka rabu da ni Malam".


"Ba zan daina ba don ubanka".


"Bakinka ne dama ba nawa ba so kayita yi in ka gaji ka daina".

"Sai yau kaga damar zuwa clinic d'in nan kenan?".

"Eh, in kaga ba zaku d'auka ba ka koreni" ya furta yana fara tafiya. 

Shi ma tafiyar ya fara yace " ba inda za a koreka kaje, but ka tuna in boss ɗin ka ne ka daina min magana da gatsali".


"Ok boss, kai don ubanka ba zaa a ce boss d'in ba, kayi abunda zaka yi".


Dariya ya kwashe da shi yana cewa " banza kawai welcome back".


"Uhmm".

"Wai kai wannan d'aurewar ta me cece guy? Duk kabi ka ci kunu ko kyau ma bai maka ba".


"Ya zaa yi ya min kyau tunda ba the great B.A Yerwa ba ne wanda ba a gaya masa gaskiya ya ji".


"Abar wancan maganar guy, yanzu dai ina da buk'atarka ka sani kuma dole in faɗi"


"Kai ne kake buk'atata? Anya kuwa, in ma kana yi bari ma kaji in dai kan wancan shegen auren da zaka yi ne toh gwara ma ka cire ni sabgarka don wallahi ba abinda ya shafe ni".


"Ohh shiyasa ka k'i d'aga kirana kenan, ka kyauta ai".


"In d'aga wayarka in ce maka mene?".


"Ai ba kai zaka ce min ba ni ne zan ce maka, ko ma banda abun gaya maka ya za ai muyi more than 2 months wai ni da kai ba ma kula juna? A 44 kayi blocking duk wata hanyar had'uwarmu nan d'in ma ka d'auke k'afarka d'if sai yau ka zo d'ad'in abun ma baka ɗaga kira na kuma hankalinka a kwance, hakan kai yayi maka dai-dai?".


"Ina ce kai kace a bar maganar nan".


Dubanshi yayi sarai ya san waye Adnan ya kuma san bai fushi amma in yayi ko shi iyayen miskilanci sara masa yake yi, amma abinda bai gane ba shine yanda yake mugun fushi da shi akan zai k'ara aure bayan ko ElSadeeq bai tab'a nuna masa damuwa ko a fuska ba ne.


"Yanzu shi maganar shirin bikin fa".

"Ai wannan kuma kai ta shafa ba mu ba".

"Ba ka saukon ba dai Kenan?".

"Na sauka mana, amma hakan ba shi zai sa in yi abinda har rantsuwa nayi akan shi kuma ma ba wani abu bane mun yi na farko yanzu zaka iya yi da kanka".


"Toh ni na san yanda ake yi ne?".

"Ai koya ake yi, mun maka na farko yanzu kai zaka yi kayanka".

"Why?".

"Haihuwa d'aya horon d'uwawu".


"Me kenan?".

"Ohon maka".

"D'an iska kawai".

"Na ji d'in".


Daga haka kowa ya shige office d'in shi, kamar kuma yanda Adnan yace ya sauko amma fa maganar biki ko da wasa bai yarda ya k'ara masa ba shi ma dama ba ita ba ce a gabanshi don yanda tace in ma fasawa zaa yi a yi toh shima haka take ta side d'in shi don ya rantse zai iya fasawa don babu wata mace da ta isa tace wai zata iya fasa aurenshi har yaji ya damu. Sai da ya jewa Umma da k'orafin auren fatattakarshi tayi tana kuma jaddada masa kar ya sake ma ya fara maganar fasa auren biki ne an yi an gama,haka nan ya hak'ura ya koma wurinta dama ba wai ya hak'ura da ita ba ne completely haushin abinda tayi masa yaji. Kuma ya tabbatar da ta yi laushi don sosai ta ba shi hak'uri ta kuma had'a da kissa wurin ba da hak'urin ya sa ya d'an sauka kad'an bai kuma sake mata kamar da.



Ko Nadeefahr ta lura da rage zuwa tad'in da yayi sai dai ko kusa ba ta kawo maganar zuwanta gidan ne ya kawo musu matsala ba, ta fi bada hakan ga ganin damar shi na in yaga dama yau yayi kaza gobe kuma ya canja. Bata bi ta kai ba ta dai yi amfani da damar wurin tabbatar da matsayinta a gidan da rayuwarshi gabad'aya ta hanyar sake b'ullo da sabbin salo masu tsayawa a rai a zamantakewarsu. Ba kuma irin salon da kan nuna kai tsaye ga abinda take nema ko ya sauyata daga yanda take ba, tana a yanda kowa ya sanya a komai na rayuwa. Gayunta na nan girkinta ga uwa uba sabon ajin da ta k'aro kamar wacce ba ta damu da lamuranshi ba at the same time kuma tana nuna masa kulawa fiyeda k'ima hakan ba k'aramin mamaki ya kan ba shi ba kuma sosai ya sa shi shiga taitayinshi yake ganin girma da kimarta a idanunshi duk da a cewarshi har yanzu bai sonta irin son soyayya kamar yanda yake ji akan Fareesah amma ya na jin wani irin nauyinta da gudun b'ata mata fiyeda yanda yakewa ita Cherrien ta shi. Hakaza ya na masifar son kasancewa tare da ita fiyeda baya, sannan yana sa ta a lamarinshi ta hanyar neman shawaranta a mabanbanta lamura da lokuta kuma har ya kan yi amfani da su su kuma b'ulle masa kuma yana yabawa kulawarta a kan shi yana kuma treating d'in ta irin yanda take masa. A wannan tsukin ita kanta ta gane tana da matsayi a rai da rayuwarshi hakan ya sa ta koma gefe ta kwantar da hankalinta sai k'wank'wadar romon k'auna suke yi.



Da kanshi ya tura mata kud'in kayan fad'ar kishiya a kan ta sai komai yanda suka yi mata wanda ba ta siyo kaya birjik ba wainda take buk'ata kawai ta siya don tana da kayan da bata tab'a amfani da su ba na lefenta ma bata ma gama sanin yaya suke ba. Sai kawai ta bud'e lefen ta zab'o wasu ta kai d'inki, itama Yusairah itama akwati d'aya ta had'o mata duk kud'i ya bata har da na d'inki, gyaran jiki, hair and henna sai kace itace amaryan kai ko da zai bawa amaryan ta shi ma sai da yayi shawara da ita kan nawa zai bada. Ba ta sa mugunta ba a matsayinta na skincare expert ta gaya masa yanda zai bata har kud'in turaren amarya duk da ta san hausawa ba su cika yin turare ba amma kuma in an bada ba laifi ba ne, sai na makeup lalle da kitso da kuma sauran abubuwa na buk'atun amarya.



Ita da kanta ta ware kayan da ya kamata a d'inka mata ta kuma had'a shi da tailor wanda neighborn mai mata d'inki ne don ba ta son damuwa shiyasa ba ta kai wurin natan ba. Ba ma zuwa tayi ba number ta ba shi shikuma ya neme shi tare ma suka je da Fareesahr kamar yanda ta nuna masa, ita ta zab'i style d'in da zaa mata ciki har da shigen wanda ta gani a jikin Lelen randa ta je wanda har yau bata daina girgiza da yanda ta ganta ba. Duk da ta tab'a ganinta a hoto amma ganinta a zahiri ya sa ta gane hoton ba k'aramin rage mata kyau yake yi ba, wato ita d'in mace ce d'aya har da rabi irinsu ne ake kira da hurul'ain a duniya. Kai ita fa tana namiji tana da kamar Nadeefah ba abinda zata yi da wata mace ai sai dai ta yi fatan gamawa da duniya lafiya.



Don har ga Allah Nadeefah ta cika kuma bata da nakasu tun daga kan cikin gidanta, k'amshin gidan da ma fatarta gayunta, k'amshinta da class. Ji fa duk yanda ta so ɓata ranta don ta biye mata ta samu abun fad'i amma ko d'ar bata yi ba, sai ma murmushin da ta dinga yi data kammala ko ce Mata tayi " thanks, yanzu zaki tafi ne ko da saura?". Wato ta yi masifar iya allonta ta kuma wanke shi tsaf ta shanye, ga uban gashin da ta hango a kanta wanda ita ta san babu ta inda zata kai kanta ko gefen takalmin Nadeefah ne sai ga shi zata had'a miji da ita. Wanda shi ma tun farko ta farawa kan ta fad'a akan shi don ko ba a fad'i ba ta san ba ajinta ba ne saboda kyau da tsari irin na shi ta na kuma ganin matarshi jikinta ya k'ara sanyi amma ba zata taɓa karaya ba. 


Ko da ta zab'i dinkin kai tsaye Burhaan yace A'a wai yayi tsiraici da yawa tsayawa tayi tana kallonshi don ita ai matarshi ta saka wacce ta fi haka nuna jiki bai kuma ce bai yi ba sai dai ta shafawa kanta ruwan sanyi ta zab'i wani d'in har ma ta samu ta shigar da wainda ta siya don fitar biki don ta lura ba wasu masu k'wari zata samu daga gidansu ba kuma bata son tab'a kayan lefe da sai daga baya ake gaya mata sai ranar bikinta zaa kawo kayan. Lallab'awa tayi ta samu ya biya duka kud'in suka baro wajen ya kaita gida shi ma ya tafi na shi hidimar.



A hankali ranaku suna shud'ewa har aka shiga satin biki in da amarya take ta gid'imin hidimar da zata yi na biki, tun daga kan kalolin events da za'a yi wanda ake sa ran ango zai saki bakin aljihu shi da abokai kamar yanda suka san cikakken Kanuri ya kan yiwa amarya da k'awayenta anko sai dai ba suji komai ba hakan ne ya sa suka rufawa kansu asiri suna hidimarsu su d'aya. Har events d'in ma dole suka rage su zuwa uku kacal, ladies eve, k'auye day da kuma kamu da suka shirya har da k'aton hash tag d'in su na #the_B&F_love_story da a da sun so saka #becoming_Mrs_BAY ne sai suka ganshi a Instagram wanda page guda aka yi creating na bikinshi da Nadeefah duk da ko yayi shekaru a yanzu haka amma tsarin bikin abu ne da zaa yi shekaru ba'a daina batun shi ba don an kashe kud'i ainun su ko dai a lallab'a ne a yi wanda zaa iya kuma a hakan za su yi yak'i a cikin unguwa kuma zai zama abu da za'a yi ya zancen shi a arewa don shakka babu gidan kud'i zata shiga.



Tun da aka shiga satin ita kanta Nadeefah hidima yayi mata yawa don da farko 'yan familyn babu wanda ya shigo zancen bikin don Suliem har kusan zaginta tayi akan rashin zuciya ita dai bata biye ba ta nace musu da kiraye-kiraye tana sa musu kukan so auke damuwa ya kasheta kafin suka fara zuwa d'in shi ma ba da yawa ba ne. Ko Adnan sai da ta kira shi fin goma kafin ya bar Salmah zuwa bikin. Friends d'in ta ma suna ta zuwa kuma suna kan bata shawarar yanda zaa kammala bikin ba tareda ta samu wani damuwa ba. 



Ta gefen Burhaan ko sosai ya samu support daga wurin matarshi ba ta d'aga masa hankali ba ga kuma tsayuwar daka da tayi wurin tabbatar da an yi komai lafiya, kud'i kawai ya sakin mata ta hanyar ba ta card d'in shi don duk abinda ya taso ta cire kawai ba sai ta kirashi ko an jirashi ba. Da taimakon su Sophia ta samu suka tsara komai sai ya zamana har role d'in da iyayen ango ka d'auke duk ta kwashi wannan a ka, the only go to person a kan sha'anin bikin was Hajjah kullum sai ta kirata taji yanda ake ciki.


5 days to biki aka zo dankin amarya da k'yar da sa bakin Abbu da Baba Tijjani da suka kira 'yan familyn aka had'u a gidan taran masu zuwa, a haraba suka tare su kana sukai directing d'in su zuwa part d'in amaryar da sai ranar ma suka san yanda yake. Gaisawa suka yi a mutunce kana suka ba su abinci da drinks da kayan buk'ata kuma ko a fuska ba su nuna musu ba su son auren ba. Yayar Fareesah mai suna Aunty Aseeyah ce har da cewa wai "ina uwargidan" Ya Budu tace " Tana ciki tana aiki, me ya faru ne?". 


Murmushi tayi tace "babu komai wallahi, Allah dai ya had'a kansu ya kuma kad'e fitina" Ameen duka suka amsa Ainah me bakin magana ko har da cewa " in dai ta Nadeefah ne ai gidan zaman lafiya aka zo don tun daga k'uruciya har yau a kaf family ba ta da abokin musayar yawu ko da na wasa ne kuwa".


"Tabbas, fad'a da damuwa ko d'aya bai cikin halinta so in shaa Allahu ma ba zaa tab'a b'atatta ba".


"Toh Masha Allah muma ta gefenmu haka yake in Allah ya yarda".


"Toh Allah ya yarda, bari mu baku wuri ku kintsa toh ". Suka juya suka fita don sun ga suna k'ok'arin kafa kayanda ba ma su tab'a ba don direct daga company ake kawo kayan maza ne ke kafawa mata kuma direction kawai suke bayarwa wani lokacin ma da plan d'in su suke zuwa wanda tun a online sukan tura catalog a zab'i tsarin da yayi musu su aiwatar. Su ko dangin Fareesah da kan su suka shirya d'akin da kitchen da komai har da labulayya suka saka don daga yau sun gama sai sun kawo amarya kuma, d'akin yayi kyau dai-dai da k'arfinsu da suka kammala kuma suka zauna suka ci abincinsu sai da suka k'oshi tsaf kafin kowa ya fara haramar tafiya.



Saboda gulma irin ta su bayan sun rufe d'akin sun saka key a jaka maimakon su wuce gida sai suka d'auki food flask d'in da plates suka nufi main house da tun farko suka gane gidan tsarin mace guda ne na k'anwar tasu dai kawai an yi ne amma ya fi kama da BQ. Su na tura ƙofar suka tarar da shi a bud'e tsayawa suka yi suna k'arewa waiting room d'in kallo wanda dispenser ne kawai a ciki da cushion sai curtains d'in da ya zagaye duka wurin da TV a girke a gefe wanda yake bango guda d'aya sai AC da humidifier itama babba da ita sai zubar da tiririn k'amshi takeyi. Gyad'a kai suka yi suna cire takalma don daga ganin tsarin parlorn sun san dole a cire takalmi don zagaye yake da rug mai taushi wanda ko ba a fad'a maka ba ka san ya ci kud'i mai yawa ainun.



Tura sliding door d'in wurin suka yi suna shiga cikin main parlorn da ke cike da 'yan suna hirar 'yan uwantaka ka d'auka duka cousins ne a wurin amma har da su Mommy da Mommy Hafsat, dararraku kawai ke tashi suna saurarar Nadeefah da ita ce ke ba su labarin kowa ya natsu don Nadeefah akwai iya bada labari don komai tsaf take bada shi, wanda take bayarwa don kawar da hirar lefen da suka k'i had'awa suke yi. Sallamarsu ya katse musu maganar duka suka d'ago kai suna kallonsu da mamaki suna kuma godiya ga Allah da Lele ta katse wancan hirar da sun tarda su suna yinta ga shi ba su iya magana a hankali ba Mommy ce ta katse shirun da cewa " ahh har kun gama kenan?".


"Wallahi fa mun gama muka ce bari mu kawo kwanuka" inji gwaggon su Fareesah tana kallon parlorn a sace itama akasin sauran da suke yi a bayyane don samun details na d'akin. 


"Ayyah da baku wahalar da kai ba ai, yara zasu zo su d'auka ma".


"Ba komai ai da yake ma tafiya za mu yi ma".


"Toh Masha Allah bari a taka muku kun sha aiki ai, sannunku da k'ok'ari"".


Ita da Mommy Hafsat sai Ainah ne suka rakasu har inda suka ajiye motarsu da ita kad'ai ta fita daban a harabar, shiga suka yi Aunty Aseeyah ce zata yi driving d'in Mommy Hafsat har da ba su kud'i wai su k'ara mai a hanya don ita da Umma suka kai kayan sa-rana ta al'adar malam bahaushe kuma ta ga an basu hasafi kuma ta tab'a raka dankin gidan Gangarida an basu hasafi. Godiya suka yi sosai kana suka ja motarsu suka tafi, suna fita kowa ta fara zazzage abun cikinta na mamakin da suka gani.



Su ko su Mommy komawa ciki suka yi suka cigaba da hirarsu ko ta kan su basu bi ba, ba su suka tafi ba sai kusan 5 na yamma suka bar su Suleim da Zulfaa da Salmah sai Sophia suna cigaba da tsare-tsare sai da Islaam ya dawo shi da Adnan da ya zo d'aukar matarshi kafin suka watse da sunan gobe za su cigaba daga inda suka tsaya. Gidanta ta sake gyarawa ta had'awa Burhaan ruwan wankan da tare suka yi da shi wanda ya ja musu dad'ewa ainun har aka kira magrib don a gabad'aya kwanakin nan sake zama maye yake yi yanda ko d'an irin d'okin kawo masa sabuwar jini d'in nan bai yi, kuma fa ba wai bai jin ɗokin ba ne tsabar ƙwarewaa shariya da nuna abu bai dame shi ba da kuma son kasancewa da Nadeefahr da yake sakawa ya manta wai aure zai k'ara.






Washe gari sai ga sabbin furnitures daga wurin Abbu masu matuk'ar kyau wainda a lokacin da mata maganar cewa tayi bata so don duka kayan musamman kayan gadonta sukayi abu ne da ba kullum ake kwana a kansu ba. So she thought ma ya bar maganar sai ga sets hud'u na kujeru d'aya wanda ya kasance 2 sofas farare for waiting room, 2 sets na main parlor d'ayan kuma na parlornta duka masu kyau ne sosai kuma sabbin yayi. Duk da bata yi expecting ba amma sosai taji daɗin kayan da aka kawo musamman na living room d'in wanda a baya set d'aya ne mai guda takwas so yanzu an yi mixing d'in colors, kwashe tsaffin aka yi aka jera wainda aka kawo suka canja mata curtains zuwa colors d'in da aka kawo masu kyau da aji har da dining. Aka sake fixing chandeliers sabbin fitowa da rugs masu taushi nan fa d'aki ya sake fitowa ras musamman da ta sake gyarawa tayi mopping ta baza k'amshi. Kiran Abbu tayi ta masa godiya sosai ko da Burhaan ya dawo yayi mamakin yanda aka gyara d'akin har yake mata tsiyar k'in bari a yi painting da tayi da yanzu yafi haka haske. Ita dai murmushi tayi kawai tana mai sake bin gidan da kallo don ya burgeta sosai, ba ta kuma yi wani aikin gyara da yawa ba tunda banda cikin bedrooms d'in ta da yanzu ta rasa inda zata sa kanta don aikine zai kusa gamawa da ita musamman na kayan sawanta dake shak'e da closet.



Kawo wainnan kaya shi ya bud'e k'ofar shigowar gudunmawa daga 'yan familyn yanda ka san ita ce zata yi auren alerts ne suke shigowa ta koina daga wannan sai wannan sai dai kawai ta kira wanda ya turo tayi godiya. Da ta nunawa Burhaan ko tayata godiya yayi yana bata shawarar ta tara tayi wani abu da kuɗin tunda dai ba wani abu zata yi da shi ba a yanzu, dama itama shawararta kenan akwai kud'in da take ta ajiya na ribarta daga spa d'in ta. Maida kud'in tayi zuwa savings d'inta, kafin a gama bikin ta ga me zata yi da shi.



Kwana uku bikin a nan shagonta ta yini akai mata face therapy da lips therapy sai toning da tayi da turaren jiki, aka gyara mata kai da lalle, ita ma Yusairah an mata lalle sai dare kafin ta koma gidan in da ta tarar da Burhaan ya kawo sabbin toileteries masu kyau har da manyan humidifiers ta k'akk'ara a parlornta da main parlor da na shi. Fresheners da turaruka na tsinke da rushi hand washs liquids soaps komai dai masu tsada ma ba a magana. Komai dai tsaf sai san barka acan-acan irin na 'yan gayu ajin farko.




A ranar ne kuma su Fareesahr suka fara bikinsu da k'auye day yayi kyau sosai sun yi k'ok'ari sai dai babu ango, haka rana na biyu da suka yi ladies eve amarya tayi kyau ta haska dama ba zuwa zai yi ba sai pics aka tura mai. Ranar ne Nadeefah ta zauna ta masa face therapy da lips therapy na angwaye, har gyaran ƙumba nan ya fito ras kamar ta canja shi abunka da zuciya sai kuma ta ji mugun kishi ya kamata har sai da ya fito a fuskarta.



Rungumeta yayi ya na mai jin jikinshi ya na sake yin sanyi kamar ya fasa yake ji, bai tab'a sanin haka Nadeefahr ke da muhimmanci a wurinshi ba sai yau. Lallashinta ya fara yi har da bata tabbacin ba zai tab'a rainata ko wulak'anta ta kan aurenshi ba ya k'are yana rufe bakinta da wani zazzafan kiss, biye masa tayi don tana neman abinda zai rage mata raɗaɗinabinda take ji kukan Yusairah ne ya katse musu hanzarinsu. Sakin bakin juna suka yi suna nishi a hankali a kunnenta ya rad'a mata magana, ta janye jikinta tana murmushi a kunyance rik'ota yayi yana mai jin wani sabon yanayi da kunyanta ya ke sakashi lashe lips d'in shi yayi ya na mai cewa " Allah I'm serious, ban k'oshi ba mu je ki d'auketa sai a ji da ni". Ya k'arashe yana rik'e hannunta gud'a d'aya tare suka nufi inda take zaune, harshenta ashe ta tauna da hak'oran da suka fito shine take kuka. D'aukarta tayi tana jijjigata ta na me cewa " yau kin ji yanda ake ji kema ko? Haka ai kike saka ni a gaba kiyi ta cizo".



"Dama cizon da zafi ne?".

"Eh mana" ta fad'i tana sa mata nonon a baki ai ko yarinya ta sake ciza da sauri ta zareta tana shishita. Naughtily ta jiyo muryanshi yana cewa " nata ne yake zafi kenan?".


"Na kowa ma ya na da zafi fa".


"But nata kike complaining kad'ai banda nawa".


"Dama kana cizo na ne......." Tsayawa tayi a tsakiyar maganar ta na kallonshi lumshe idanu yayi da wani d'an iskan kallo yana mai cewa " ehen". Rufe idanu tayi tana cewa " Yaya mana" dariya ya kwashe da shi yana cewa " baki tab'a jin cizon nawa ba ko, kan ki ba'a nan yake ba".



Tsingulinshi tayi tana cewa " ni dai ni dai....." Dariya ya fashe dashi yana rik'eta jikinshi itama dariyar tayi ta na b'oye kanta a jikinshi sosai ta na sakin masa rigimar shagwab'a. Ganin suna dariya sai itama Yusairahn ta fashe da dariya kamar ta san me suke mawa, dariyar ta ta ne ya sa suka sake fashewa da dariyar suma kamar marasa lafiya.



Ranar kamu ne 'yan Yerwa da ba su fi 10 ba ne suka tafi daga Mommy, Mommy Hafsat, Mommyn Kano da Ummu sai Ya Budu da Insiyyah, Najwah, Fadwah da Ainah da gulma da d'aukan rahoto ya kaita sai Hafeezah da suka d'au wankan kashe kala cikin lesussuka masu tsada ga k'amshin dake tashi suka kuma tafi da turaren siyan baki da kudad'e. Kowacce ta d'auko falleliyar motarta mai numfashi suka nufi wurin taron da aka yi a Arewa house.



Har aka fara taron ango yana kwance a kan gado gefenshi Nadeefah ce tana masa maganar tafiya Kamu don Ummu ta shaida mata da sun wuce, kallonta yayi ya na mai ce mata " ai ba dole ba ne sai an je so ki ƙyale ni''.


"Amma ka san ana zuwa wurin ko?".


"Masu zuwa suyi ta zuwa ni ba inda zan je sai ka ce wani yaro".


"Auren so fa zaka yi ai dole kaje wurin ko don nuna mata muhimmacinta gareta, besides in kai ba auren fari bane a wurinta na fari ne kar ka b'ata ranta da k'in zuwa".


''Me kike nufi da auren so ne?".


"Ya......" Kiran wayarshi ne ya katse mata maganar da tayi niyyar yi, kusan a tare suka dubi wayar da Cherrie ke yawo bisa screen d'in. Ajiyar zuciya ta sauke tana kawar da kanta daga kallon wayar bai d'aga na har ta katse, tashi zaune tayi tana cewa " ka tashi ka shirya".


"Zan je amma first sai kin gaya min me kike nufi da auren so".


"Auren so ne mana saboda dai kai ka kagani kake so har kuma kaji sha'awar ajiyeta a cikin gidanka".

"Don kuma auren so ne sai in ta yawo wurin event d'in bikinta kamar mara kai".

"Ya kenan, kai dai ka tashi kar a yita jiranka".


"Ok ke ma ki shirya mu je da ke".


"Ni babu inda zani kam".


"Me kika ce?".

"Cewa nayi taronku ne in je in ɓata muku farincikinku bayan ba wanda ya ɓata min nawa".

"Ohh really? Toh in baki zuwa nima ba zan je ba".


"In dan ta nine gwara ma ka tashi ka tafi don ni kam babu abinda zai sa in je".


"Ko da ni nace?".

"Gwara ma kar kace angon Fareesah".


''Wai wife kin daina kishina ne?".

"Kusan haka".

Ajiyar zuciya ya sauke yana mai jin babu dad'i, mik'ewa yayi a hankali yana cewa " shikenan toh jirani in fito in kika shirya ni sai mu fita tare" ok ta furta tana sauka daga gadon, kan sofa ta wuce ta zauna ta na gyara kayan jikinta da ya d'an tattare saboda kwanciyar da tayi.



Ya d'an jima a toilet d'in kafin ya fito yana k'amshin ruwan da ta had'a masa, tashi tayi ta amshi towel d'in hannunshi ta taya shi goge jikinshi da kan shi. Taje kan shi tayi ta shafa masa mayukan kai masu dad'in k'amshi har da hair spray ta bi kan kana ta d'auko masa Ash colorn kayan da ya ciro zai saka taya shi tayi suka saka ta bishi da turaruka da kanta ta saka masa agogon Hublot na fata bak'i haka takalmi dahularshi shi da suka kasance bak'ak'e da su. Sosai yayi kyau musamman ma gemunshi dake k'yallin man da aka shafa masa. Dubanta yayi itama tana kallonshi tana lumshe idanu shima lumshe na shi yayi yana kissing bakinta da tun d'azu yake shiga idonshi, bai ja shi da tsawo ba ya saketa yana cewa " muguwa turani kike yi in tafi da buƙatar ki ko?".


"Ni ban tura ka ba, kuma tun d'azu da ake maganar ai ba abunda kake ji".


"Tun lokacin nake ji mana" ya furta da shagwab'ar da bai san ya iya ba.


Shafa gemun tayi tana cewa " toh kayi hak'uri kaje ka dawo, in ka dawo zan baka".


"Promise?".

"Ka san ina cika alƙawari".


"Ok, Babe sai na dawo" ya furta yana kissing kanta  ya juya ya bar d'akin da kallon mamaki ta bishi ganin yanda ya fita cikin sanyin jiki  a k'asan zuciyarta ta furta " ohh namiji munafiki ne wallahi, ji yanda yake abu simi-simi kamar ba shi yace yana son Fareesahr ba. Har da wani ce min babe ko yaushe aka fara haka oho".



Baki ta tab'e ta maida towel d'in ta fita daga d'akin zuwa inda ta baro Yusairah ita d'aya duk ta had'a kashi, fitarshi bai fi 15minutes ba sai ga su Zulfaah sun zo nan suka tayata zama suka sake cireta daga damuwar da shiru ya d'an fara haifar mata.


Shi da Farhan da Elsadeeq suka tafi wurin taron don shi dai Adnan yace ya nemi mai taya shi hidima ba shi ba, sai ga su sun taimake sh. 'Yan yerwa sun yi lik'i sun kuma bada kud'i masu yawa na siyan baki da abubuwan al'ada sai after 6 kafin suka bar wurin zuwa gida.


Shi ko bai shigo ba sai bayan magrib don dama bai settling 'yan matan amarya ba, Farhaan ne ya amshi account number d'aya ya saka mata kud'in idonshi k'yar yana kallon 'yan matan da suke ta zuba kaud'i ko zaa yaba. Tab'e baki yayi don bai ga wacce tayi masa a ciki ba, ko Fareesahr ma bai san yanda Islaam ya kwasota ba amma ko d'aya ba tai masa kalar wacce zai iya aure ba balle Burhaan da ya fiso k'yacci da iyayi. Haka dai suka tarkata kayan su suka koma gida a nan suka iske matansu nan fa suka dasa hira ba su suka bar gidan ba sai kusan 10, suna tafiya ko ya fara abinda ya fita da muradi da asuba ma sai da ya kuma kafin suka kwanta bacci.



Ita ta fara tashi lokacin gari yayi tarwai da haske sauka tayi ta nufi toilet wanka tayi ta fito da bathrobe ko mai bata shafa ba ta fita, a parlor ta tarda Yusairah zaune don da ta tashi barinsu tayi kan gadon ta fita tayi zamanta. D'aukarta tayi sai da ta fara shayar da ita kafin ta kinkimeta zuwa toilet d'in d'akinta wanka tayi mata ta shiryata cikin wata plain gown ta yara itama ta cire robe d'in ta sa half gown pink kafin ta fito, zaunar da ita tayi kan kujera ta sanya mata cartoon a tab ita kuma ta fara gyaran gidan. Special gyara tayi a kowani sak'o na gidan ta tabbatar ko ina ya d'au saiti, kana ta had'a musu simple breakfast ta shirya a table. 



Wanke-wanke tayi ta maida komai inda yake sannan ta fara kiran carterers d'in da ta bawa aikin abincin biki, an tabbatar mata da komai yana tafiya dai-dai kafin ta samu zama gefen Sairah da ta barci ya kwasheta dama haka take ta na da saurin bacci ta na da saurin tashi. Zamanta bai fi da minti biyu ba ya fito daga ciki sanye da Calvin Klien boxers brown babu ko riga jikinshi sai mik'a yake yi, murmushi ta saka ta na cewa " good morning Yaa".


"Uhmm morning, shi wannan Yaan yak'i fita daga bakinki ko?".


"Ya fita ya je ina?".

"Ko ina ma madam".

"Abu-Sairah?" Ta tambaya tana k'umshe dariyanta ganin yanda yake yatsine.


"Ai gwara ki cigaba da cewa Yaa d'in har k'arshen rayuwa, ban san Abu- Abun nan".


"Uhmm na ji".

Bai tanka ba ya k'araso yana kai wa kwance kan shi a bisa cinyarta yana mata magana, basu wani dad'e suna hira ba bacci ya sake d'auketa gyara mata kwanciya yayi shi ma ya kwanta a k'asa yana rik'e da hannunta har baccin shima ya d'auke shi. Tab'a mata k'irjin da ake yi ne ya sa ta bud'e idanu, Sairah ce tana tab'e fuska cikeda shagwab'a. Tashi zaune tayi tana rik'ota shayar da ita tayi shi ma mik'ewa yayi ya zauna wasa yake mata har ta k'oshi ta koma wurinshi tana ta cewa " PaaPaa" murmushi yayi yana cewa " Sweetheart".

Dubanshi tayi tace " PaaPaa a kawo breakfast ne?".


"Bari in yi brush first".


Mik'o princess yayi ta k'i zuwa, dariya tayi tana cewa " ka ga gulmar Sairah ko?".


"Ƙyale ta, bari mu je".


Wucewa yayi zuwa ciki itama toilet ta shiga kuskure baki tayi don ta yi brush mouth wash ta saka ta dawo, tana fitowa shi ma ya dawo dining ya nufa itama can ta wuce. Serving d'in Buttered yam and chicken tayi sai banana pudding da lemon and mint tea kana tayi serving kanta, bismillah yayi yana ci yana bawa Sairah pudding d'in har suka kammala. Sauka yayi daga table d'in ya barta ta gyara wurin first ko zama bata yi ba ta nufi d'akinshi gyarawa tayi ta canja masa zanin gado ta saki turare kafin ta dawo, kallo ta tarda suna yi itama tayi zaman tayashi.


Wurin 12 YaBudu ta iso gidan da yaranta, zuwan ne ma ya saka shi wucewa ciki bayan sun gaisa itama d'aki ta tafi ta shirya cikin wata elegant atamfa bak'a mai adon red da white. D'auri ta kashe ta fito parlorn ta zauna suna hira, ba a dad'e ba sai ga jama'a sun fara shigowa gidan to 1 aka kawo abinci YaBudu ce ta cire na walimar Islaam d'in aka kai d'akinshi kana sauran aka bar shi a kitchen duk wanda ya zo yaci. 


A lokacin ne ta tashi ta canja kaya zuwa wata kampala 'yar dakar maroon and milk color dinkin half bubu da ya karb'i jikinta da straight skirt, kwalliya ta zauna ta yi light makeup ta kashe d'aurin da ya kafu da kyau a goshinta. Videos ta fara yi sai ga kiranshi ya shigo wayarta ba ta d'aga ba ta fito ta nufi d'akinshi tana jin su Suleim da zuwansu kenan suna mata tsiya, shiga tayi da sallama a zaune bakin gado ta tarda shi sanye da towel.


Tsayawa tayi tana cewa " me kuma nake gani haka?".


"Ke nake jira ki shirya ni ai".


Da mamaki ta dube shi har zata ce wani abu sai kuma ta fasa toh kawai ta fad'i tana wucewa gaban mirror cream ta d'auko ta taho bakin gadon shafa masa tayi a natse making sure ba ta yi squeezing kayanta ba. Yanda ya saba shiryawa haka ta masa har ta boxers da singlet ita ta zab'o masa daga sabbin collections da ya siyo, farar shadda ta d'auko masa wacce akai masa d'inkin hannu sak'ar Mali ta taya shi sakawa. Ya zura wandon takalmi ta d'auko masa brown don zaren aikin brown ce, falmarar shi ta d'aura masa a kan rigar ta tsaya tana kallonshi. Taje kan tayi ta sa masa hula zanna bukar mai adon brown da milk a jiki har babbar rigar ta sanya masa kafin ta d'aga wayarta ta fara masa video tana mai cewa " ango ya fito".


Harararta yayi yana cewa " ke ko?".

"Allah kayi kyau ne ango masha Allah".


"Wife mana".

"Allah fa kaje ku gaisa da su Mommy suna parlor".

Ajiyar zuciya ya sauke yana rik'e hannunta har parlorn suna fitowa aka fara d'aga wayoyi kowa yana musu video ana gud'a, murmushi ta d'inga yi tana danne abinda take ji a zuciyarta. Gaisawa suka yi da mutane aka d'an musu addua kafin suka nufi koma inda suka fito. Abincin ya fara sawa aka fita da shi aka kai masa mota kafin ya dogare a k'ofar fita yana cewa " toh zan wuce".


Yak'e ta sake yi tana cewa " toh Allah ya sa a k'ulla alkhairi ya sa mu zame maka abokan zama na gari, ya baka ikon yin adalci ya kuma k'ara bud'i".


" Ameen Wife, ya kuma miki albarka ya rufa miki asiri yanda kika min ya kare miki gabanki da bayanki".


"Ameen Hubby " ta amsa tana juyawa rungumeta yayi tsam ta bayan sai da suka d'auki tsawon mintuna kafin ta zare jikinta tace " ana jiranka fa PaaPaa".


"Bakinki da PaaPaan nan ko?".


"Ni dai sai ka dawo".


Juyawa yayi ya fita ita ko ta samu wuri ta zauna tana mai k'ok'arin korar heat d'in da take ji a jikinta, innalillahi ta dinga maimaitawa kafin ta samu ta dawo dai-dai tashi tayi ta fita inda su Suleim suke zamanta cikin mutane ya d'an rage mata damuwa hakan ya sa har aka gama d'aurin auren ma bata sani ba. 



Sai da su Mommy suka tashi tafiya kai lefe kafin ta sani ma, tashi tayi ta canjo kaya zuwa lace simmer green da gray a jiki, d'inkin riga da skirt aka mata ya zauna a jikinta da kyau. Wani hoton suka sake mata tana zaune sai ga kiranshi ya shigo gyaran murya tayi a hankali tace "an d'aura ne?".


"Kina lafiya dai ko".

"Yea I'm good an d'aura ?".


"Yeah".

"Toh Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi".

"Ameen ya rabbi, in zo ne?".


"Ka yi mene?".

"In ganki mana".

"Ka zauna can, bye".

"Ok bye" ya kashe wayar bai san menene ke jan shi gareta a kwanakin nan ba amma koma menene ya fi komai daɗi a rayuwarsa. Komawa yayi cikin mutane dama gidan su amarya zasu shiga ayi pics ya kasa jurewa sai da ya ji daga gareta kafin hankalinshi ya kwanta. Zulfaah ce ta saka dariya tana cewa " Ina sonki matar nan, ana k'aro miki kishiya ana d'aukinki".

Fari tayi tana cewa " toh ya son ranki" k'awayenta su Deeyah dake d'akin suka saki shewa suna cewa " Allah ya taimaki giwar mata" shak'iyanci dama suka zauna yi shiyasa suka baro parlorn da a cike yake da 'yan uwa sahu-sahu. Haka aka dinga hidima kusan 5 sai ga motocin kawo amarya wanda Babansu da cewa yayi tun 3 zaa kawota sai da aka d'an lallashe shi kafin ya yarda shi ma dai masu kai lefe suna zuwa aka ce su jira ana sallahr asr aka had'o su da lefen back to gidan amarya, ko bud'ewa ba a yi ba na iyaye kawai aka cire aka maida mata nata mota.



Suna shigowa gidan direct part d'in Lele aka kaita lokacin ma tana can ciki bata san me ake yi ba, cewa suka yi sun kawo amarya wurin uwargida nan ne aka shiga aka kirawo ta lokacin ta canja kaya zuwa wani lace d'in gold d'inkin Abuja Bubu wanda yaji aikin hannu mai matuk'ar kyau. Burnt coffee colorn viel ta d'auko da takalmi ta fito parlorn kusan danginta mutuwar zaune suka yi da ganinta, nan gefen Mommy Hafsat ta zauna gaishesu tayi cikin natsuwa.


Inna ce ta bud'i baki tana cewa " k'anwarki muka kawo miki amana gata nan, girma ya riga da ya hau kanki sai da hak'uri da kawar da kai, kema kuma kin san mun miki fad'a ban da raini ko rainuwa a tsakaninku ku had'u ku kwantarwa mijinku hankali sai ku zame masa ababan alfahari. In kuka had'a kai kamar kun had'a kan 'yay'anku ne".


"In shaa Allahu Baaba" Lele ta furta cikin muryarta mai tarin natsuwa da sanyi.


Ummy ce ta yi gyaran murya tana cewa " hakaza kuma muna son jan hankalin amarya akan rayuwarta tare da mu, kin ga nan Nadeefah bata da matsala da kowa tun daga babba har yaro ga girmamawa da kuma kyauta muna masu jan hankalinta akan ta kwaikwayi halayenta sai ta zauna lafiya da kowa bayan haka muna mata fatan alkhairi and we welcome her to Yerwa Allah ya sa abokiyar arzikinshi ce".


"Ameen" suka amsa cikin yanayin da ke nuni da kamar maganarta bai musu ba, Mommy ce ta jagorance su zuwa part d'in ta aka bar 'yan Yerwa suna cigaba da sha'aninsu. Jan jikinta tayi ta koma ciki daurewa tayi ta cigaba da fira, ba a da'de ba bayan kawo amaryar aka fara dad'ewa kowa na tafiya gidanshi. Ko kafin 6 kusan kowa ya tafi sai su Zulfaa da Salmah da kuma friends d'in ta wanda su suka dage suka gyara gidan har wanke-wanke suka yi suma bayan magrib kowa ta wuce gidanta bayan sun sake mata nasiha aka tafi aka barta kuk'i daga ita sai Sairah dake ta wasanninta. TV kawai ta kunna tun tana jiyo motsin 'yan kawo amarya har ta ji d'if alamun kowa ya tafi gida.



Kusan 9 sai ga Burhaan ya dawo lokacin har ta kashe komai ta shiga wanka da niyyar kwanciya, tana fitowa daga wanka ta tarda shi zaune a gefen gadonta. Welcome tayi masa ta nufi gaban mirror normal routine d'in ta na bacci tayi tana shirin saka nighties yace " ina tafe da bak'uwa ne fa tana parlor put something decent I want to see you for like 15 mins sai ki kwanta".


Ok tohm ta furta tana bud'e closet arabian gown ta zura ba tare da ta sanya bra ba kana ta yafa gyalen, tare suka jera zuwa parlorn da amarya ke zaune tana sanye da dogon hijabi. Zama tayi kawai shi ma ya zauna a kujerar gefensu bai zauna kusa da kowa ba. Sannu ta furta a hankali ba tareda ta dubi gefen da take ba, gyaran murya yayi hakan ya sa duka suka d'ago cewa yayi " Fareesah baki gaisheta ba".


"Ina wuni ?".


"Lafiya lau, ya taro" ta amsa a natse.


Gyad'a kai yayi yai ijaza da basmala kafin ya d'aura da sallama duka amsawa suka yi kowa tana kallonshi duban Nadeefah yayi yana kiran sunanta amsawa tayi tana sake sunkui da kai, yayinda shi kuma ya d'aura da fad'in " zan fara dake a matsayinki na babba a cikin gidan nan fad'in da nayi kece babba ba wai shaci-fad'i bane face addini da al'ada da ya baki wannan matsayi wanda nake kyautata miki zaton zaki iya karb'a ki rik'e da hannu biyu toh kamar yanda nake zato daga gareki ina rok'onki don Allah ki rik'e kar ki yarda wani b'araka ya faro daga gareki".


In shaa Allah ta amsa kanta har yanzu a k'asa.


Juyawa yayi kan Fareesah ya kira sunanta kamar yadda yayi wa Lele itama ta amsa tana dubanshi '' ke kuma a matsayinki na k'arama ina so ki kiyaye ki kuma natsu kar ki sake wata matsala ta b'ullo in ji da kwai hannunki a ciki, kiyi respecting matata a matsayinta na mataimakiyata a cikin gidan nan kamar yadda na fad'i zan kuma maimaitawa ba wai ban son ta bane ya sa na aureki ba Aa ina sonta ina kuma jin dad'in zama da ita kawai ra'ayine da kuma so kema da nake miki. Kuma na san halinta wallahi in dai har kika bita toh baza ki tab'a samunta da kowani irin matsala ba ne in shaa Allahu da fatan zaki kiyaye".


"In shaa Allah" ta furta tana mai jin babu dad'in maimaita mata wai matarshi bata da matsala da ake tayi ko kafin su fito ya gaya mata 'yanuwanshi sun gaya mata d'azu and here is he again reminding her. Duban Lelen yayi yace " ke kuma kar ganin nace baki da matsala ki tsiro halinda ba naki ba ne please ki tsaya tsayin daka wurin gina min gida, sai maganar kwana when I'm done with the 7 days zan maida shi 2-2 days is that okay with you?".



"Duk yanda ka ce".


"Ok tohm Allah ya muku albarka" adduoi yayi masu yawa aka shafa kana ya dubi Lele da har yanzu bata saki fuska ba yace" babu dai wani abun ko?.


"Babu gajiya ce kawai nayi and I want to sleep".


"Sannu da k'ok'ari wife, na shigo miki da kifi and akwai chicken ban san wanda zaki ci yanzu ba".


"Ina ganin sai da safe kam don yanzu I'm full".


"OK toh shikenan bari mu tafi, ki taso ki rude k'ofar "

OK ta furta ta tashi tana bin bayansu don ita Fareesah yana cewa bari mu tafi ta mik'e a k'ofar fita daga parlornshi ya tsaya ita dai amarya waje ta yi itama ta ja tunga ta tsaya, a hankali ya rad'a mata " kiyi addua ki ma princess good night".


"Good night" ta amsa tana tura k'ofar da ya fita key ta murza ta kashe light, jingina tayi da jikin k'ofar tana sakin kukan da tun safe take tare shi.............



Hello lovelies yaya kuke ya gidajen naku an yi sallah lafiya? Toh Allah ya maimaita mana ba dawowa nayi ba I just come to say hi ne don har yanzu ban da waya amma 3in1 page nan na muku I'm sure zai kashe muku k'ishin na baya da na barku da shi?


Wainda suka kira da masu messages Ina godiya ainun wannan shafin naku ne Allah ya bar k'auna da zumunci,sai kun sake ganina da wani shafin ko a kusa ko nesa.

Love you All.

Deejasmah🎭🔮