Chapter 23
Daren ranar haka Zahra ta gagara bacci. Sai can wajen asuba bacci barawo ya ɗauke ta. Ibrahim kuwa ko zuwa gidan bai yi ba, a waje ya kwana.
Wajen ƙarfe shida na safe alarm ɗinta ya fara bugawa, hakan yasa ta farka da ƙyar. Addu'ar tashi daga bacci tayi, sannan ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet. Brush tayi tare da alwala, daga nan ta fito ta shimfiɗa sallayarta ta yi sallah.
Bayan ta idar, azkar ɗinta ta fara yi a hankali. Da ta gama, ta zauna kan sallayar tana kallon wani waje, hawaye na bin kuncinta. Jin kamar bacci zai sake ɗaukarta yasa ta koma kan gadon, domin bata jin zata iya zuwa makaranta a ranar.
Can cikin baccin da take yi ne ta ji ƙarar shigowar message. A hankali ta buɗe idanunta, ta ɗauki wayarta. Firdausi ce.
Da sauri ta buɗe message ɗin.
"Ki shirya yau. In Sha Allah yau zamu haɗu da Lovie Dovie."
Tsaki Zahra ta ja tsaki tana juyawa gefe.
"Bana jin zan sake yaƙi da wata saboda Ibrahim."
Ta faɗa a hankali.
Sai kuma ta sake buɗe idanunta da sauri. Wani tunani ya faɗo mata. Gwamma ta yi hakan, ko ba komai zata cusa masa baƙin ciki ne.
Bacci sosai ya fara cin ƙarfinta, hakan yasa ta sa alarm na ƙarfe goma sannan ta kwanta. Nan da nan bacci ya sake kwashe ta.
A ɓangaren Ya Umar ma ba a ce ya samu bacci ba. Gaba ɗaya daren jiya ya kwana cikin tunani. Asuba ma sai da Abbah ya tashe shi zuwa sallah. A ransa yake jin kamar ba su kyauta wa Zahra ba da suka aura mata Ibrahim.
Lokacin breakfast, dukkansu suna zaune a dining suna karya. Mami ce ta lura hankalin Ya Umar kamar baya tare da su.
"Ya Umar, lafiya dai?" ta tambaya.
Da sauri ya kalleta, sannan ya kalli Mummy da Abbah. Nan take ya ƙirƙiri murmushi.
"Lafiya lau Mami, kawai kai na ne yake ɗan ciwo."
Abbah ya ce,
"Daga gani ma kamar baka samu bacci jiya ba. Da ƙyar ma ka tashi sallah."
Mami ta girgiza kai.
"Toh ya kamata ka ga likita kafin ciwon ya shiga jikinka."
Ya amsa da,
"Toh Mami."
Ita dai Mummy tana zaune tana saurarensu, amma ko kalma ɗaya bata ce ba.
A haka suka gama breakfast ɗin, amma tunanin Zahra ne ya ƙi barin ran Ya Umar. Har ya gama cin abincin, zuciyarsa na can wajen ƙanwarsa da kuma abin da zai yi wanda zai sa Ibrahim ya gane kuskurensa.
Shi ne ya fara miƙewa daga dining ɗin ya wuce ɗakinsa. Yana shiga ya ɗauki wayarsa ya yi dialing number ɗin Zahra wanda ya yi saving da Our Angel ❤️.
Kiran na shiga, sai ya ji muryarta cike da bacci.
"Hello Yaya."
Nan take ya sauke ajiyar zuciya. Wani irin relief ya ji ya mamaye shi.
"Kina lafiya?"
"Alhamdulillah."
"Sorry na tashe ki a bacci ko?"
Kallon agogon da ke gefen gadonta Zahra tayi. Ganin saura mintuna goma ƙarfe goma yasa tace,
"A'a Yaya, dama ƙarfe goma nake son na tashi."
"Alright. Amma zaki shiga school yau ko?"
"Eh."
"It's good. Ki samu ki tafi, ki zama so lively."
Wani ƙaramin murmushi tayi.
"Thank you."
Ya Umar yace,
"If there's anything, just let me know baby."
"In Sha Allah."
Daga haka suka yi sallama.
Zahra ta ajiye wayar sannan ta wuce toilet. Wanka tayi, tana fitowa ta shafa lotion tare da fesa turare mai sanyin ƙamshi. Daga nan ta nufi wardrobe ta ɗauko wata baƙar abaya mai matuƙar kyau ta saka.
Ba ƙaramin kyau tayi ba.
Ta ɗauki tot-bag ɗinta ta zuba wayoyinta a ciki, sannan ta sanya baƙin flat shoe a fararen ƙafafunta.
Sauka tayi ƙasa.
Farida na mopping parlorn lokacin.
Da ganin Zahra sai ta miƙe tsaye.
"Ina kwana Anty."
"Lafiya lau Farida, ya aiki?"
"Alhamdulillah."
Kai ta gyada kawai sannan ta nufi hanyar fita.
Da sauri Farida tace,
"Amma Anty baki yi karin kumallo ba ne?"
Zahra ta juya ta kalleta.
"Bana jin yunwa ne."
Farida ta haɗe fuska.
"Amma fa rabonki da abinci tun jiya. Wallahi yadda na ajiye abincin jiyan nan haka nake zuwa na same shi."
Murmushi kawai Zahra tayi.
"Idan na dawo zan ci."
Daga haka ta juya ta nufi ƙofa.
Farida ta bita da kallo har ta fita.
Sai kuma ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta juya da sauri ta nufi ɗakinta.
Wayarta ta ɗauka.
Ganin missed call yasa ta yi saurin kiran number ɗin.
Ana ɗagawa tace,
"Afuwan, ina aiki ne."
Ta yi shiru tana saurare.
Sai kuma tace,
"Eh, yanzu ta fita."
Bayan wani ɗan lokaci ta sake yin shiru.
"Amma ana ganinta ansan ba lafiya ba. A yadda ta fita kam"
Ta sake sauraron mai maganar sai kuma ta ce
"Toh In Sha Allah."
Sai kuma ta ɗan yi murmushi.
"Amma zata yi dare fa, dan yanzu idan ta fita makaranta tana daɗewa kafin ta dawo gidan."
Daga haka ta kashe wayar tana kallon screen ɗin na wasu daƙiƙu kafin ta ajiye ta ta koma bakin aikinta
Lokacin da Zahra ta isa makaranta, har an gama first lecture. Duk da ta yi sauri a hanya, hakan bai hana ta tarar da ɗalibai suna ta fita daga hall ɗin ba.
Motarta tayi parking a inda ta saba, sannan ta sauka a hankali. Ba tare da ta damu da shiga neman kowa ba, ta nufi wani cool down da ke kusa da department ɗinsu.
Zama tayi a ɗaya daga cikin kujerun wajen tana kallon ɗaliban da ke wucewa.
Wayarta ce ta fara vibrating. Ciro wayan tayi taga Firdausi ce sai ta ƙyale kiran.
Bayan ƴan mintuna kuma sai ga wani.
Tsaki Zahra taja sannan ta ɗaga.
"Hello."
"Madam, ina kike ne?" Firdausi ta tambaya.
"Ina makaranta mana."
"Na sani. Ina a makarantar?"
Zahra ta kalli wajen da take zaune
"Ina cool down ɗin kusa da department."
"Okay, ki zauna nan. Gani nan zuwa."
Kafin Zahra ta ce wani abu, Firdausi ta katse kiran.
Bata jima sosai ba sai ga Firdausi ta iso.
Tana zuwa ta zauna kusa da ita
"Kinga fa, tun safe nake ta kiranki."
Murmushi Zahra tayi.
"Bacci nake yi."
Firdausi ta kalleta sosai.
"Kin yi kyau yau wlh"
"Thank you." Tace a takaice
Sai dai kafin ta ƙara magana, Zahra ta dafe cikinta a hankali
Firdausi ta kalleta da sauri, ta ce
"Lafiya?"
Zahra ta sauke numfashi
"Wallahi yunwa nake ji."
Firdausi ta zaro ido.
"Yunwa? Shine kike zaune bayan kin dan condition dinki?"
Kai ta gyada
"Har kamar zan yi amai."
Da sauri Firdausi ta miƙe tsaye.
"Toh tashi mu je cafeteria yanzu."
Ba gardama Zahra ta mike
Ita kanta ta san jikinta na buƙatar abinci
A tare suka nufi cafeteria ɗin makarantar
Wajen cike yake da ɗalibai, kamar kullum
Da ƙyar suka samu waje suka zauna.
Wata ce ta ƙaraso wajensu
Firdausi ta kalli Zahra.
"Me zaki ci?"
Zahra ta ɗan yi tunani kafin tace,
"Ina son jollof rice da grilled chicken."
"Abin sha fa?"
"Fresh orange juice." Ta ce