Namiji Ƙanin Ajali (Book 01)

Chapter --- 14

by @amdeeytejjdunique587

Bismillahir Rahmanir Raheem.

***Namiji Ƙanin Ajali***

By

Amdeey Tejj d'Unique

>Page---- 1️⃣4️⃣.

Muna cikin hirar mukaji sallama,tare muka kai duba zuwa ƙofar shigowa gidan, wasu yarane su biyu mace da namiji macen ce babbar wacca zata kai shekara goma zuwa sha ɗaya, namijin ne zai kai bakwai zuwa takwas dukansu sanye da uniform na islamiyya,suka ƙaraso macen ta zube a jikin goggo bayan tayi wurgi da jakarta akan tabarmar da muke zaune.

"Washhh goggo nagaji"ta faɗi

namijin ne yace''goggo kin san meye yau bata kawo hadda ba malam Harisu ya zaneta da wannan dorinar tasa"

Tayi narai -narai da ido ta miƙe zaune sannan tace"inace gyara kawai yamin so biyu amma ya dinga duka na kamar jaka,kuma yafi dukana akan waɗanda basu bayar ba gaba ɗaya"tayi maganar kamar zatayi kuka,dan idanuwanta har sun kawo ruwa.

"Wannan Malam Harisu ya saki a gaba wato baiji gargaɗin da mishi akan dukan min yara ba kenan?,ina wayata ɗakko ki kira min Da-Dai tunda ya hanani zuwa to ya kira makarantar koma yazo yaje a ɗauki mataki akansa tun wuri,dan bazan ɗauki zalunci da cin zali ba"magana take cike da masifa,nidai nayi shiru bance komai ba dan na fahimci irin kakanni nanne wanda basaso a taɓa jikoki,

Namijin da fahimci cewa shine Kamal macen kuma Nabila yace"wallahi goggo ƙaryane bulala biyu ya mata sauran da basu kawo ba kuma ya musu biyar biyar''yaron yayi dagaji kuma kasan gaskiya ya faɗa

''Kai rabani da mutumin da yaƙi jininka musamman ma ita da akayi masa gargaɗi kanta,a cikin biyun da ya mata sai yasa zalunci tunda haushinta yake ji yaƙi jininta''

Yace''goggo kedai dama bakya ganin laifinta ay, amma ni dana kawo ya bai taɓani ba''

''Kai dai kasani kuma,ai na fahimci kaima munafiki ne,tunda da kai za a haɗa baki a zalunci ƴar uwarka,ke tashi ɗauko min salulata''tayi maganar ga Nabila

Nayi murmushi kawai a raina ina jinjina rigimar tsohuwar,Nabila ta tashi zaune ta kalleni sannan tace"laaa goggo baƙuwa mukayi?ina wuni"ta miƙa min gaisuwa

Nayi murmushi sannan nace"Lafiya lau Nabila,kina rigima yaushe zaki ganni shi kam Kamal ai har ya gaisheni"dan daya shigo saida muka gaisa kafin ya ƙarasa wajen goggo,ta ɗanyi dariya ta sunkuyar da kai.

Ta miƙe ta shiga ɗaki,bata jima ta fito ta miƙawa goggo waya tana faɗin"gashi kiyi magana ya ɗauka"

"Ki samin murya dai,dan kinsan bana son jin magana can-can kamar ana min tsegumi,ni kuma ba hali bane tom"

"Kai goggo kefa har yanzu baki waye ba''

''Eh gara kar in waye, indai wayewa irinta wancan babar taki mai aƙidar Turawar ce"tayi maganar tana kara wayar a kunnenta.

Daidai nan aka ɗaga wayar akayi sallama''yauwa wa'alaikum,kai Da-Dai kaji wannan Malamin na makarantar su wannan yarinyar Labila ya sake dukanta ko,to ka kira makarantar koma kazo da kanka dan ina ganin sai anje ga hukuma tukun''

''Haba goggo ai kya bari mu gaisa tukun ko''aka furta cikin wata kamilalliyar murya mai cike da nutsuwa da kwarjini a cikinta.

Ta katse shi''kai barni tukun ba mun gaisa ba ɗazu, idan ma bamu gaisa ba ma gaisa daga baya yanzu dai barni in shigar da ƙorafina tukun''

"To amma dai baki je ba ko?''yayi magana a karo na biyu.

''Eh banje ba bakace kar naje ba, amma wallahi idan ya cigaba sai dai kaji labarin na kai shi ofishin jami'an tsaro''

''To kiyi haƙuri za a mishi magana, ina Nabilar take?''

''A a bazan bata ba dan nasan ba ganin laifin shi kakeyi ba,kamar ma kafi sonshi akanta,yauwa sai batun wannan yarinyar kuma''nan tabashi labarina ta kuma gaya mishi tana son ya ɗauki nauyin aikin.

''Amma goggo kin tabbatar da gaske takeyi?kinsan mutane ba abin yarda bane,dan wasu sai suzo suyi ƙarya dan abasu kuɗi kawai''

''A a wannan da ganinta baza tayi haka ba,kasan ni ina gane mara gaskiya a ido ma kawai, kuma idan ma ƙarya tayi ai mu da zuciya ɗaya muka bata ya rage nata,kasa Allah kawai a ranka kayi taimako dan Allah''

''To shikenan goggo tunda kin yarda da ita,zan turo miki a account ɗinki gobe sai Nabila ta ciro a bata"

''To Allah ya kaimu, amma kasan bana son batun asusun baturen nan ko,nafi gane a bani a hannu"

''To goggo ki aika Nabila wajen Murtala idan taje tace ya kirani''

"Yauwa yanzu naji batu''

Ta sauke wayar ta kalli Nabila tace"kin dai ji me yace,ki tashi kije ki karɓo,yauwa ɗiyata tashi kuje tare kinga kuɗin suna da yawa''takai maganar gareni da tun ɗazu nake murmushin dramarsu da jikokinta,jin batun amincewar zai taimaka min kuwa kamar nayi tsalle na dire saboda murna,tare muka fice nida Nabila bayan munyi sallar magariba,bamu yi tafiya mai nisa ba duk da akwai ɗan tazara sai dai ba sosai ba, mukayi sallama ya amsa bayan mun gaisa Nabila ta zayyano masa abin da ya kawo mu,sai da ya kira shi ya tabbatar, kuɗin da yake wajensa baza sukai ba hakan yasa yace muje mu dawo idan yayi sallar Isha zaije ya karɓo kafin nan mun dawo,muka amsa mishi kafin muka juya muka nufi gida batare da sanin mai zamu tarar ba, wanda da nasan abin da zai faru da ban tafi ba,da na tsaya har sai ya dawo ya bani kuɗin, amma kashhh akace rashin sani yafi dare duhu.

Nidai farin ciki kawai nake yi ina tafiya,ina hamdala ga Ubangiji da ya kawo min mafita,nasan yanzu haka Habibu yana nan hankali a tashe ƙarshe ma yayi min faɗa, amma nasan idan yaga abun da nazo dashi zai sakko tunda dama abun da muka zo nema kenan,da wannan tunanin muka ƙaraso ƙofar gidan,da sallama muka shiga turus na tsaya ganin goggo a tsaye tana kaika dawo,tana jin sallamata ta juyo cike da bala'i da masifa tace''ke ki fita maza maza ki barmin gida,ki koma inda kika fito''

Jikina ya ɗau rawa zuciyata ta soma bugawa da ƙarfi kamar zata faso ƙirjina,in fita kuma?me ya faru?kodai wani abun na mata?,na yiwa tambayoyin da nasan sai a wajenta zan samu amsarsu,naga dai har muka fita daga gidan nidai ba abinda nayi mata balle ince.

Bakina yayi nauyi jikina yayi sanyi na rasa kalma a bakina sai da ƙyar na haɗa yawun bakina na lalubo kalma,kamar wata me koyan magana murya na rawa nace''gog--gogg--go mem me ya faru?''nayi tambayar da ƙyar kamar ana fusgarta

''Komai ma ya faru,ki fice min daga gida kafin na saɓa miki baza kija min masifa ba''tayi maganar tana nuna min ƙofa

Na zube kan ƙafafuna na haɗe hannaye na waje ɗaya nace''goggo bance sai kin taimakeni ba, amma idan laifi na miki ki gaya min kuma kiyi haƙuri ki yafe min iya kulawa da kika nuna min ma ya isa nagode miki kuma hakan ya nuna min ke mutuniyar kirki ce, amma idan wani abu ma aka gaya miki akaina da yasa kika sauya ra'ayi ina so ki sani Wallahi bani da halin banza, kuma ni banzo da cuta ko niyyar cutar da wani ba'' na ƙarashe maganar hawaye na ɓalle min na sunkui da kai ina share hawayen,na lura jikinta yayi sanyi amma kamar wacca ta tuna wani abu sai ta kau da kai gefe ta cigaba da ficikon na bar mata gida,haka na tashi jiki a sanyaye gwiwa kamar an kwaɗa min ice na fice hawaye yaƙi daina zuba a idona........

Mu haɗu a Page na gaba.....

See you next time......

Bye Bye.....