Chapter 24
Wajen kwana uku kenan Ibrahim bai tako gidan ba, ba kira, ba message,
ba kuma wata alama da zata nuna yana tunanin dawowa
Da farko abin ya dinga ci wa Zahra tuwo a ƙwarya, amma sannu a hankali ta fara sabawa
Kullum idan ta tashi daga makaranta, gidan su take wucewa kai tsaye. Zama da Mami, Abbah da Ya Umar ya zama wani abu da yake rage mata damuwa.
Duk da ciwon da ke zuciyarta, amma akwai lokutan da take mantawa da Ibrahim gaba ɗaya idan tana tare da iyalinta, Duk da ga matsin lanbam Batoul.
Yau ma kamar yadda ta saba, ta tashi da safe, ta yi sallolinta da shirye-shiryenta kafin ta nufi makaranta.
Da ta isa, ta haɗu da Firdausi a harabar department ɗinsu.
Tun daga kallon farko Firdausi ta gane yau Zahra ta ɗan fi kwanakin baya walwala, ta fara dawowa ainahin pretty Zahratyy dinta na baya
Bayan sun gama lecture na farko ne suke zaune a wani cool down
Firdausi ta matsa kusa da ita ta ce
"Na yi magana da Lovie Dovie."
Zahra ta ɗaga kai ta kalleta
"Me tace?"
"Mun yi chatting jiya da dare”
Zahra ta haɗe gira.
"Toh?"
Firdausi ta ɗan yi murmushi
"Tace ta dawo gari”
"Okay” kawai Zahra ta ce a takaice dan bata kaunar wannan maganar
"Kuma ta amince mu haɗu yau bayan lectures” Cewar Firdausi
Nan take fuskar Zahra ta canza
Ta ce "A'a, babu inda zani”
Firdausi ta zaro ido
"Meye a'a?"
Haɗe rai tayi ta ce "Bana zuwa."
"Why?" Firdausi ta tambaye ta
"Firdausi na gaji da wannan maganar." Ta ce Tana girgiza Kai
"Wallahi bana son ganin kowa da zaina tunamin shi”
Firdausi ta matsa kusa da ita
"Listen to me, Zahra…”
Kai Zahra ta girgiza.
"A'a."
"Ki saurare ni mana” Firdausi ta ce
Shiru Zahra tayi Tana kallon wani wajen daban
Firdausi ta ci gaba.
"Ba wai saboda yarinyar ba ne, ko shi kansa Ibrahim din”
"Toh?" Zahra ta ce
"Saboda ke."
Zahra ta haɗe gira tana mata wani kallo ta ce
"Yaya saboda ni?"
Firdausi ta ɗan yi murmushi.
"Kin manta yadda kika yi kuka kwanakin baya?"
Zahra ta kau da kai
"Kin manta yadda Ibrahim ya raina ki a gaban mutane, nuna bayi da mata tamkar con fuska ne Zahra”
Shiru tayi ba tare data ce mata kala ba
Firdausi ta dafa hannunta
"Toh yanzu kina da damar da zaki nuna masa cewa ba zai iya wasa da ke yadda yake so ba, ta Duk inda ya buga kwallon sai dai ya fadi ba dai ya ciki ba”
"Bana son ɗaukar fansa” ta ce ba tare data kalli firdausi ba
Firdausi ta yi dariya.
"Wannan ba fansa ba ne, Zahra”
"Toh meye?"
"Reality check." Cewar Firdausi
Zahra ta kalleta
Firdausi ta ci gaba.
"Kin san me yasa yake jin zai iya yin duk abin da yake so?"
Zahra ta ce "Why?"
Firdausi ta ce "Saboda yana tunanin komai zai ƙare da haƙuri."
Ta ɗan yi shiru.
"Yanzu karon farko zai gane cewa akwai sakamakon abubuwa”
Zahra ta fara tunanin maganar firdausi
Firdausi ta sake cewa,
"Mu tafi kawai Zahra, muje muga yadda abun zai kasance”
Zahra ta ce "Firdausi..."
"Please." Firdausi ta katseta, ta kama hannunta.
"Ko ba komai ki zo ki ji me zata faɗa."
Na wasu daƙiƙu Zahra bata ce komai ba, sai daga ƙarshe ta sauke numfashi
"Okay."
Firdausi ta yi murmushi ta ce
“Yauwa, ko ke fah Zahra”
"Amma idan na ga bana jin daɗi zan tafi."
"No problem."
Daga haka suka ci gaba da lectures ɗinsu.
Bayan an gama lectures na ranar, suka yi sallama da sauran friends ɗinsu.
Firdausi da Zahra suka wuce parking space
"Straight." Cewar Firdausi ta faɗa tana ɗaure seat belt
Zahra ta tada motar
"Kinga dai ban san me kika shirya ba."
Firdausi ta yi dariya
"Za ki sani nan da ɗan lokaci”
A haka suka kama hanya.
Bayan kusan mintuna talatin da tafiya, suka isa wani babban garden da ake yawan zuwa shakatawa.
Wajen ya yi kyau sosai, ga ciyayi kore, ga manyan bishiyoyi, da kujeru a wurare daban-daban
Zahra ta yi parking, ta kashe motar.
Sai ta juya tana kallon Firdausi.
"Anan?"
"Eh." Firdausi ta amsa.
Suka sauka tare
Yayin da suke shiga cikin garden ɗin, Zahra ta fara jin wani irin bugun zuciya.
Ba ta san me zata gani ba, ba ta san me zata ji ba
Amma abu ɗaya ta sani...
Ayau akwai wani abu da zai fito fili, dole ta sake posting hotonta da Ibrahim ko zai tafi viral
A tare suka shiga cikin garden ɗin.
Idanun Zahra suka fara kaiwa kan yarinyar tun kafin su ƙarasa. Zaune take a wani gefen wajen, sanye da wasu matsattsun kaya, riga da wando ne a jikinta, sai kanta data daura vintage scarf, tana ta danna waya
Firdausi ta ja numfashi
"Ga ta can."
Ba tare da Zahra ta ce komai ba suka nufi wajen.
Da suka isa, Firdausi ce ta fara magana.
"Hello."
Yarinyar ta ɗaga kai.
"Hello."
Idanunta suka sauka kan Zahra, ta tsaya kallonta
Kallo irin wanda ba a iya gane ko na mamaki ne ko na ƙiyayya ba, sai kallon take yi, tun daga kanta har ƙafafunta.
Zahra kuwa ta zauna cikin nutsuwa kamar bata lura da kallon data ke mata ba
Firdausi ta gyara zamanta.
"Yaya dai?"
Yarinyar ta ɗan yi dariyar gefen baki.
"Lafiya, Ashe dai kuke son gani na”
Amma idanunta suna kan Zahra ta karasa maganar
Firdausi ta lura da hakan
"Kin san dalilin da yasa muka kira ki ko?"
Kai ta girgiza.
"A'a, ai sanin gaibu sai Allah”
Firdausi ta ce,
"Maganar Ibrahim ne, Wanda kike tare da shi, wato khalil”
Nan take fuskar yarinyar ta canza.
"Toh? Ai nariga da nayi sensing hakan”
Firdausi ta nuna Zahra
"Wannan ita ce matarsa”
Yarinyar ta kalli Zahra, sai ta sake kallonta, daga ƙarshe ta ce,
"Na sani, na mata farin sani a media, ai shiyasa Nace miki nayi sensing abun daya kawo ku”
Zahra da Firdausi suka kalli juna
Firdausi ta haɗe gira.
"Kin sani?"
"Eh." Tace a takaice Tana tauna cingam
"Yaushe kika sani?" Firdausi ta ce
"Wannan kuma ruwana ne" Ta ce ba tare data kalle ta ba
"Bangane ba?" Firdausi ta ce
Ta ɗaga kafaɗa.