RAGAYAR DUTSE

PAGE 10

by @nanahaleema11

 *RAGAYAR DUTSE.*


              ©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*

*Page 010.*



A hankali ya tura ƙofar ya shiga yana cewa, "Rehaan ya kamata ka dakatar da Alma, me...." 


Sai maganar ta tsaya ganin Rehaan cikin duvet ya rufe fuskarsa. Ya ƙarasa ya janye duvet ɗin ya ce, "lafiya ka ke?." 


Kafin ya basa amsa ya taɓa wuyansa ya ce, "your are runing tempureture, me ya same ka haka?." 


Rehaan ya miƙe zaune daƙyar ya ce, "bana son tafiya nigeria Jazy."


Jay ya ɗan yi tsaki ya ce, "ka cika maimaita magana ɗaya wallahi, ka san dole sai ka je, meye na wanna maganar?. Ka tashi mu tafi airport" ya faɗa yana miƙewa daga kusa dashi. 


Sai ya kuma juyowa ya kalle sa ya ce, "waccan yarinyar Alma, ya kamata ka dakatar da ita haka, dan yanzu haka tana downstrais. Ni ban yarda da ita ba wallahi, ka yi a hankali kar ta ɓallo maka ruwa."


Rehaan ya fesar da iska ya yaye duvet ɗin da ya rufe jikinsa, ya ziro ƙafarsa ya sakko ya miƙe tsaye yana furzar da iska. 


Jazy ya kai hannunsa ya riƙe gashin Rehaan ta baya ya ce, "Mamy ta ce ka cire gashin nan fa." 


Ya buge hannunsa ya ce, "wallahi bazan cire ba, ai ba da ra'ayin kanta ta faɗa ba, tsarin wannan tsohuwar ne" ya faɗa yana saka takalmi zai fita. 


Jazy ya ce, "ina zaka je? Ka zo ka ɗauki abinda zaka ɗauka mu wuce."


Ya ɗan juyo ya ce, "zan je wajan Alma, zan dawo yanzu" ya faɗa yana fita daga ɗakin. 


A hankali yake sauka downstairs ɗin yana kallon ta a zaune, tana ta kalle-kalle kamar baƙuwa a gidan. 


Ya ƙaraso ya tsaya ya ce, "Alma what up?." 


Alma jin muryarsa sai ta miƙe tana takowa inda yake a hankali, ya haɗe rai ya ce, "don't you dare touch me." 


Ta ɗan marairaaice ta ce, "i'm sorry Ray, it's not my fault, i love you


Ya sake haɗe rai ya ce, "amma na faɗa miki bana son wannan shirmen ko? Kin san hakan haram ne a musulumci ko?." 


Ta ɗan kama kunnenta ta ce, "im sorry, i will never do it again. Forgive me." 


Ya sake kallon ta ya ce, "what are you doing here?."


"To apologize."


"Alright." 


Ta ɗan matso kusa ta ce, "Would you like us to go out for dinner?." 


Ya ɗan girgiza kai ya ce, "im leaving now. I'm going back nigeria."


Ta zaro ido waje ta ce, "nigeria!." 


Ya gyaɗa mata kai, ta langwaɓar da kai cikin damuwa ta ce, "can i go with you?."


Ya harɗe hannu a ƙirji yana kallon ta kafin ya ce, "No Alma, that's is not possible." 


"Why?."


"You can't go with me."


Sai kawai ta faɗa jikinsa ta rungumsa tana kuka, ya ɗan sauke ajiyar zuciya ya cire ta daga jikinsa ya ce, "Alma ki nutsu, bazai yu in je da ke nigeria ba, bazan jima ba zan dawo." 


Zata sake shiga jikinsa ya riƙe hannunta ya ce, "Alma!."


Ta ɗan yi baya, ya saki hannunta sannan ta ce, "yanzu ni ya zan yi? Bazan iya rayuwa a nan baka nan ba. Ka je dani."


Ya sake girgiza kai ya ce, "bazai yu ba, ki je zamu dinga magana a waya." 


Zata sake yin magana Jazy da yake tsaye yana kallon su ya ce, "Alma please ki je, bazai yu ya tafi dake ba, ki bar gidan nan yanzu." 


Ta kalli Jazy suka haɗa ido, ta ɗauke kai dan ba shiri suke yi dashi ba, tsoronsa ma take ji. Ta kalli Ray ta ɗaga masa hannu ta fita. 


Tana fita Jazy ya fara yiwa Rehaan masifa ya ce, "wai me yake damunka ne? Me yarinyar nan ta yi maka take neman lalata maka tarbiyya ne?."


Ya ɗaga kai ya kalle sa ya ce, "Ta ke lalata min tarbiyya, like how?."


"Wannan hug and kisses ɗin ba lalacewar tarbiyya ba ne?."


"Amma ka san is normal ko?."


"A addininka ma normal ne kenan?."


"Ka san yin hakan for no reasons ba halina bane, ita ɗin ma ina dakatar da ita. Ka daina yi min ihu malam, kana saka min ciwo" ya faɗa yana raɓasa ya wuce ya hau sama.


Yana ta yatsine fuska haka ya ɗan haɗa ƙaramin box ɗinsa. 


Ya ɗauki abinda zai yi amfani dashi ya fito ya tarar da Jazy a tsaye yana danna waya. 


Ya ɗan kalle sa ya ce, "Jazy kar ka faɗawa kowa zamu je, don Allah." 


Ya kalle sa ya ce, "akan me?."


"Kawai bana so, sannan kar ka kira ko wanne security. Ka bari mu je." 


Ya wani kalle sa da mamaki ya ce, "ta ya hakan zai faru? Kana so ka ce ko Mamy baka so ta sani?." 


Ya ɗaga kai ya ce, "Har Mamy, har Riyya kar ka faɗawa." 


Jazy ya ce, "Amma na riga na sanar Bilal, your Personal Assisant." 


Ya ɗan rutse ido ya ce, "ka faɗawa duniya kenan, yanzu Bilal zai yaɗa a duniya zan dawo nigeria. I need privacy, ni ba ɗan film ba a dinga yawo da hotunana a duniya? Let me call him" 


Jazy ya ce, "Fine. i will let him know. Amma ka san dole sai an tafi da security ko?."


"Shiyasa bana so a san na je ai, in babu wanda ya sani ai babu wata damuwa." 


Ya ɗan gyaɗa kai ya ce, "Okay." 


Housemaid ɗin gidan ne ya fitar musu da boxes ɗin zuwa mota, suka sakko ƙasa suka kulle aparmeat ɗin suka basu key ɗin, sannan suka shiga mota zuwa airpot.


Alma kuwa tana fita mota ta hau ta nufi zuwa gaba da gidan kaɗan, tana tsayar da mota ta shiga Gidan. Yana ganin ta ya miƙe tsaye ya ce, "ya ake ciki? Meye a ƙasa?." 


Ta girgiza kai ta ce, "Ya ta fi Nigeria yanzu." 


Ya zaro ido waje ya ce, "Nigeria! Ya aka yi baki sani ba sai yanzu? Meyasa baki faɗa mana zai tafi nigeria ba sai yanzu?."


Alma ta ce, "ban sani ba." 


Cikin tsawa ya ce, "meye amfanin alaƙar ku da baza ki san inda zai je? Meye amfaninki da baza ki san abinda yake shiryawa?." 


Ta ɗan dafe aki ta ce, "tun ranar da wannan abun ya faru ban sake zuwa ba, haushina ya dinga ji ko wayata baya ɗauka." 


Ya dafe kai da duka hannunsa saboda lalacewar plan ɗinsa, ya kalle ya ce, "kin lalata komai, kin ɓata komai Alma!." 


Alma ta ce, "Zan gyara komai Sir, zan gyara bazan bari wani abun ya sake faruwa ba. Zan gyara, ka yafe ni." 


Ya nuna mata ƙofa alamun ta fita. Ta juya ta fita jikinta a sanyaye, amma ta yi ƙudurin gyara komai ɗin.


Ya ɗauki glass cup ya yi cilli dashi ya fashe, ya girgiza kai yana runtse. Har yanzu ya kasa samun galaba akan Rehaan, har yanzu ya kasa cika burinsa a kansa, ko yaushe tsallakewa tarkonsa yake yi, amma nan gaba bazai tsallake ba, zai iya aikata komai dan ganin bayansa, zai iya aikata komai don Rehaan da komai nasa ya durƙushe.


******


Tunda ta dawo daga wajan aiki take lura da kallon da Mama take yi mata, bata nuna ta gane ba ta ɗauke kai ta cigaba da abinda yake gabanta. 


Bayan sallar magrib Mama ta kira ta, Islaha ta zo ta zauna tana jiran me zata ce mata. 


Mama ta ce, "Islaha!."


 Ta ɗaga kai ta kalle ta Mama ta gyara zama ta ce, "wani aiki na samo miki na ƙaruwa, wanda zaki taimaki kanki ki raya maraicinki. Ki adana abubuwa masu kauri ko dan hidimar aurenki. Wannan gidan tv da ki ke aiki me kike samu a ciki? Wahalar banza ki ke yi tunda ba wata fitacciya ba ce ba."


Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, Mama ta cigaba da faɗin, "Wannan aikin kuwa zaki samu kuɗi masu kauri, ki taimaki kanki ki taimake ni, dan akwai mutane da yawa da suke son aikin nan amma na hana su na ce ke za a bawa, saboda ke ce tawa, in kika samu kamar na samu ne. Kin san nawa ne albashin ki?."


Islaha ta girgiza kai alamun bata sani ba, Mama ta yi murmushi ta ce, "Naira dubu ɗari uku harda asirin, duk wata za a baki wannan kuɗin a matsayin na aiki. Kuma ba wani abin zaki yi ba, kullum kina cikin ac a kwance, kina cin abinda ki ke so, sannan ga kyauta da zaki dinga samu a kai a kai. Ki faɗa min aikin da zaki samu a garin nan da zai kawo miki wannan kuɗin."


Islaha so take kawai Mama ta katse maganar, ta ɗan yi ajiyar zuciya kaɗan tana so aje ƙarahe dan wallahi ta gaji. 


Mama ta gyara zama ta ce, "Zaki yi aikin nan Islaha? Baza ki watsa min ƙasa idona ba?." 


Islaha ta ce, "Mama wanne aiki ne?."


"Jeddah zaki je, aiki zaki je ƙasar saudia, amma a birnin Jeddah. "


"A can zaki samun wannnan kuɗin da nake faɗa miki hankali a kwance, babu wahala balle fita kullum, kina gani sai sake baƙi ki ke yi saboda yawo a napep. Can kuwa kina zaune a gida mai kyau, ga abinci, ga data, ga kuɗi, ga ac. Kafin ji dawo kin sake yin kyau, babu lallai Saheer ya gane ki, saboda kyau. Daman ga fatar ki mai saurin ɗaukar hutu” ta ƙarasa faɗa tana jifanta da murmushin yaudara.


Ta sake cewa, "Yanzu abinda zai faru, gobe ki shirya a kai ki a yi miki komai da komai."


Islaha ta kalli Mama jin abinda take faɗa, ta ga har wani murmushin yaudara Mama take yi mata. 


Islaha ta ɗan gyaɗa kai tana taɓe baki kaɗan ta ce, "Mama aikatau kuma?." 


Mama ta ce, "eh, amma ba irin ko wanne aikatau ba ne ba, wannan aikin mai aji ne Islaha, aiki ne wanda za ki samu nima in samu. Kin ga tuwona maina. Kuma daman kina da miji a hannu, da kin dawo sai a fara batun aure, ba sai kin jima a can ba, ko na shekara ɗaya ki ka yi ai an samu, ko?."


Islaha kai tsaye ta ce, "A nemi wata Mama, ni kam bazan iya ba." 


Mama ta ce, "za ki iya Islaha, mutane nawa na tsallake na kawo miki? Saboda ke ce tawa, kuma ke sirikata ce. Aikin nan ba na dogon lokaci za ki yi ba, aiki ne na shekara ɗaya kacal, zuwa lokacin kinga auren ku yazo, sai ki yi auren ki da jari mai kauri a hannun ki, kin huta takaicin namiji.”


Islaha ta ce, "Na gode da zaɓata da ki ka yi Mama, amma gaskiya bazan je ba!." 


Mama ta kalle ta, ta haɗe rai ta ce, "ina lallaɓa ki kina cewa ke wallahi baza ki je ba? Kuɗin nan fa ba ni za ki nemawa ba, amfanin ki ne." 


Islaha ta kalle ta ta ce, "shiyasa na ce bazan je ba, aikin tv ya ishe ni Mama, amma bazan iya zuwa.....!" 


Mama ta katse ta cikin tsawa ta ce, "Dallah malama rufe min baki! Wacece ke da har zaki ce baza ki iya zuwa aikatau ba? Me ki ke dashi? Me ki ke samu a wata da zaki kalle ni ki ce ke baza ki iya zuwa ba?."


Islaha a sanyaye ta ce, "Gaskiya na faɗa miki Mama, bazan je ba gaskiya."


"wallahi ki ka sake yi min magana sai na tsinka miki mari, sai na ragagargaza miki ƙasusuwan jikin. Ni za ki kalla ki ce baza ki je ba, ni za ki faɗawa haka? Ina magana kina cewa baza ki yi ba?." 


Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, Mama ta yi ƙwafa ta ce, "Kina zaune ana ciyar dake a shayar dake, suttura ma wanda za ki aura ne yake yi miki, bakya tsinanawa kan ki komai. Dan wulaƙanci da rashin mutunci, ni za ki dinga kallo ki ce min wai baza ki je ba? Ni ki ke kallo kina faɗawa maganar nan?."


Islaha ta sunkuyar da kai ƙasa bata ce komai ba, dan ko yanka ta Mama zata yi wallahi baza ta je ba.


Mama ta dinga zazaaga masifa ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba. 


A lokacin Saheer da Baffa suka shigo da sallama, suka same ta tana ta zazzaga bala'i ga Islaha a zaune a kusa da ita. 


Baffa ya ce, "Lafiya ki ke ta faɗa ke kaɗai?." 


Mama ta ce, "ni da wannna ragowar gidan marayun ce!." 


Islaha ta sauke numfashi, cikin jin zafin wannam suna da Mama take kiran ta dashi. Wai ko a ina suka samu labarin ta yi fasiƙanci a gidan marayu oho, ko faɗa musu aka yi ana lalata yara a gidan marayu dai bata sani ba.


Mama ta ɗora ta ce, "ni zan samo mata aikin ƙaruwa, aikin da zata samu kuɗi, itama ta samu rufin asiri da abin kashewa, shine zata kalle ni tace min wai ita bata so? Ni zata kalla ta dinga faɗawa wannan maganar banzar?."


Baffa ya ce, "to tunda ta ce bata so ba shikenan ba? Tunda ta ce bata da buƙata ba shikenan sai a haƙura ba?. Kin ga kin huta, sai ki kai wacce ki ke so ba ita ba."