RAGAYAR DUTSE

PAGE 11

by @nanahaleema11

*RAGAYAR DUTSE.*

                ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 011.*


A Abuja suka sauka, daga nan suka hau jirgi zuwa Yola. Tunda suka sauka a airport yake jin duniyar kamar tana juya masa, yana zaune ana duba passport ɗinsa, ya saka nosemask da baƙin glasess, ya kawo Face cap ya saka dan baya so a gane sa. 

Motocici ne guda biyu a ajjiye suna jiran fitowarsa. Bilal da driver da Mansur, sai mai kula dashi Shams suka ƙaraso wajan, duk da ba dan sun ga Jazy ba bazai gane sa ba, ya kulle fuska gabaɗaya ba a gane shi.

Cikin girmamawa suka ce, "welcome Sir." 

Maimakon ya amsa sai ya kalli Jazy, ya ya kalli Bilal, da yaren fulani ya ce, "ina fatan baka faɗa 
ba?."

Cikin girmamawa ya ce, "yes Sir, ban faɗawa kowa ba." 

Ya gyaɗa kai ya kalli Jazy har zai yi magana sai ya fasa ya yi musu alama da su tafi. 

Ya kalli Jazy ya ce, "ni fa bana son zuwa gida, mu je hotel mu zauna, zuwa da safe sai mu koma." 

Jafar ya ce, "kana da matsala wallahi, yau muka saba shiga gida yanzu? Wai me yake damunka ne?."

"Nima ban sani ba Jazy, kawai bana so in je yanzu. Hotel zan je in kwana ,gobe ko jibi sai in je gida." 

Ya harare sa ya ce, "baka da hankali, har sai jibi ma?." Ya yi shiru bai ce komai ba. 

Jazy ya ce, "Rehaan ka zo mu je ka shiga mota mu tafi, bana son wannan abinda ka ke yi."

"Wallahi baza ni gida yanzu ba, ku je kawai, ni hotel za a kai ni." 

Jin ya ce wallahi sai Jazy ya ce, "Tunda na karɓi amanarka daga wajen Mamy dole na yarda, amma da baka isa ka saka ni ba wallahi. Fine, mu je gabaɗaya, amma da safe zamu je gidan." 

A hankali yake takawa zuwa wajan motar, suna zuwa Mansur ya buɗe musu ƙofa suka shiga, Shams ya shiga gaban motar aka ja motar. 

Sai bayan sun fita sannan Jazy ya faɗa musu hotel ɗin da zasu kai su. 

Rehaaan ya ce, "bana so kowa ya san na dawo, har Mamy." Suka amsa cikim girmamawa.

Ya yi shiru yana kallon titi, jinsa yake yi uncomfortable, sam baya ƙaunar zuwa Nigeria bai san meyasa ba, gashi dai a Nigeria danginsa suke, uwa da uba da ƴan uwa duk suna Nigeria, amma ya fi son rayuwarsa a turai ya fi masa komai daɗi. 

Baya son dawowa gida ko kaɗan, saboda ba yi jin daɗin zaman gidan, tunda kusan kowa na gidan ba ƙaunar zamansa yake yi a ciki. 

Shi mutum ne mai son sakewa da ƴan uwansa, yana so ya ja ƴan uwansa a jiki sosai, ya nuna musu ƙauna, ya kashe musu abinda yake dashi. Babu inda yake yi masa daɗin zama kamar cikin family, a nan kaɗai yake sakewa ya yi hira kamar ba shi ba. Amma su ba haka ne a ɓangarensu ba. 

Ajiyar zuciya ya yi a lokacin suka tsaya a hotel ɗin. Jafar ya rufe ta sa fuskar, dan in dai aka gansa an ga Rehaan, tun suna yara a haka suke har kawo gobe. Sai da ya gama reserving rooms sannan ya dawo suka shiga tare.

Yana shiga ya cire facemask da glasses ɗin, ya kalli agogo a lokacin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, ya ɗan yi shiru yana kallon waje ɗaya. Jazy ya taɓe baki ya fita daga ɗakin zuwa na sa.

Daƙyar ya samu ya miƙe tsaye ya yi wanka ya canja kaya ya kwanta, yana tunanin abinda shi kansa bai dai meye ba.

Ya rasa wanne irin tunani ma ya kamata ace ya yi, yana son ganin Mamynsa amma baya son zuwa gidan, yana son ganin Abba da Riyya da Banisha amma ba ya son zuwa gidan ko kaɗan.

Ya miƙe zaune ya kunna bedside lamp ya harɗe hannu a ƙirji ya yi shiru. Whatsapp call ne ya shigo wayarsa da number nigeria, ya duba ya ga Alma ce, ya ɗan yi tsaki ya kashe power wayar ya yi shiru. 

Buɗe kofar aka yi ya ɗaga kai suka haɗa ido da Jazy ya shirya cikin night wear shima, ya ƙaraso ya ce, "baka kwanta ba?."

Ya girgiza kai ya ce, "ban sani ba Jazy, bana jin daɗi gabaaɗaya. Ina so in ga Mamy, amma bana son zuwa gidan kwata-kwata." 

Jazy ya ce, "ka dinga addu'a Ray."

"Ina yi Jazy."

"To ka kwanta." 

Ya ɗan dafe kai ya ce, "kaina yana ciwo, ina son shan tea Jazy." 

Jazy ya gyaɗa kai yana harararsa ya ce, "sai ka sha ai, malam ni ba yaron ka bane, ka yi abinda ka ke so da kanka.”

Ray bai ce komai ba, ya ɗauke kai bai sake kallonsa ba.

Har Jazy sai fita sai kuma ya kasa, jin ya ce kansa yana ciwo sai ya waiwayo ya ce, "in kawo maka tea ɗin?."

Ya ɗan murmusa ya ce, "Ka gaji kaima, ka dawo nan mu kwanta, ina jin kamar ana ganina." 

Ya zauna a kusa dashi ya ce, "Don Allah ka nutsu, ko yaushe in ka zo ƙasar nan halin da ka ke shiga kenan."

Shiru ya yi baice komai ba yana sauke numfashi, Jay ya ce, "ka nutsu ka dinga addu'a, komai zai zo ya wuce ya zama labari, kamar bai faru ba." 

Ya gyaɗa kai bai ce komai ba. Ya ce, "zan je entry na samo maka tea ɗin."

"Ka bar sa kawai, zan kwanta" ya faɗa yana kwanciya tare da rufe ido. 

Jazy ya miƙe ya kashe masa hasken ɗakin ya fita cike da tausayinsa a wannan yanayin. Indai zai zo gida haka ake fama, ya dinga ɗarare jikinsa kenan, yana jinsa kamar baƙo, yana ji kamar akwai abinda zai same shi. 

Wani lokacin ya dinga mafarkai marasa daɗi, ko ya ce yana ji kamar ana bin bayansa. Ko da ya zo ƙasar kasuwancinsa ya tsaya cak, sai dai Jazy ya cigaba da kula masa. Ga yawan ciwon cikin da aka kasa maganinsa, ga ciwon kai da yawan zazzaɓi. 

Rehaan yana bashi tausayi sosai, dan ya san duk ɗaukaka ce take jawo masa haka, duk da wani lokacin yana sane yake wani abun, shiyasa yake share shi.

   ******

     Ƙarfe biyu na dare wayar Islaha ta yi ƙara, ta buɗe ido cike da bacci ta kalli wayar ta ga number Chairman. 

Ta goge idonta ta miƙe zaune sosai, a bayyane ta ce, "Chairman kuma! Anya lafiya?."  Ta furta kafin ta ɗauka wayar ta yanke. 

Aka sake kira ta tsaya tana kallo cike da mamaki, kafin ta ɗauka ta saka a kunne. 

Daga can ɓangaren ya ce, "Sorry Islaha, na tashe ki daga bacci ko?." 

Mamaki ya hanata magana, dan ta yi tunanin mistake ya yi. Ta ce, "Chairman lafiya?."

"Lafiya. Na samu labarin Rehaan ya shigo garin nan yau ɗin nan, kuma ya sauka a diamond hotel. Babu ɓata lokaci Islaha, zan turo Saleem da Muslim ƙarfe huɗu da rabi na dare, zaku tafi hotel ɗin, sai ki yi magana dashi koda bayan sallar aduba ne."

Islaha ta ƙwalalo ido waje cikin mamaki ta ce, "Ƙarfe huɗu fa Chairman! Kana nufin kafin ayi sallah kenan?."

"Eh Islaha, hakan za a yi, sai ku tattauna dashi in ya fito sallah. Yawanci suna fitowa shiga masallaci, kin ga sai ku haɗu a wajen."

"Amma Chairam cewa ka yi yau ya shigo garin nan, kana ganin ya dace mu je a yanzu? Ni sai nake ganin zai fi a basa lokaci, kar mu je ya ga haukan mu akan hakan."


"Ko ya ga haukanmu ɗin babu komai, mu ne muke nema Islaha, wannan dama ce mai kyau mu ka samu, dan haka bazan yi wasa da ita ba. Ki ɗauki iv nan da na ba ki, sannan ki shirya, ki saka id card ɗinki ku tafi. Saleem da Muslim zasu zo ku tafi. Bana so a samu matsala Islaha, i trust you, shiyasa na zaɓe ki. Don Allah kar ki bani kunya."

Islaha ta ce, "Amma Chairman abin ya yi wuri, a ganina a bashi lokaci ya huta sai mu je a same shi. Ka ce yau ya dawo, kuma mu je yau?."

"Gobe zaku je ba yau ba, tunda na tabbatar baza ku samu ganinsa ba sai zuwa safiya."


"Meyasa baza a bari sai bayan sallar asuba mu tafi ba?."

"Islaha in baza ki iya aikin nan ba na bawa wani, ya ina yi magana kina katse ni kamar wani yaron ki?."

"Sorry Chairman, ba haka nake nufi ba. Allah  ya kaimu lafiya." 

"Ki shirya da wuri, zasu zo ku tafi. Kar a samu matsala Islaha" yana faɗa ya yanke wayar ta bi wayar da kallo.

Islaha ta ajjiye wayar a gefe ta ce, "Ikon Allah, ko meyasa Chairman ya dage akan interview da mutumin nan oho. A kansa zan fita kafin sallar asuba, kuma in na je babu tabbacin zan gansa. Kuma ai sai ya ga shirmen mu, a ce mutum ya dawo yau kuma mu je masa ko hutawa bai yi?. Mtsw! Chairman yana da matsala wallahi" ta faɗa tana sauka daga kan katifar.

Ta miƙe tsaye ta riƙe ƙugu ta ce, "wai ƙarfe huɗu, ai gwara kar na koma in yi alwala na yi sallah. In lokacin ya kusa na yi wanka. Amma bara na faɗawa Hamma" ta faɗa tana ɗaukar waya ta kirasa.

Abin mamaki call waiting alamun waya yake yi, ta cire wayar daga kunnenta, ta duba ta ga dai da gaske shi ta kira, kuma waya yake yi.

Mamaki ya cika mata zuciya, ta tafi tunanin da wa yake waya a tsakiyar daren nan? Ta san shi ba ma'abocin waya bane, ya fi son chat akan waya amsa waya, dan ko ita sai su kwashe awa biyu suna chatting amma wayar minti talatin ta gagare sa. 

Shiru ta yi alamun tunani, ta zubawa wayar ido tana jira ya kira ta shiru bai kira ta ba, dan ta sna ya ga shigowar kiran ta.

Sai can kusan minitina goma sannan kiransa ya shigo, ta ɗauka ta saka a kunne. 

Kafin ta yi maganaya ce, "Bodde am lafiya? Wani abun ne ya same ki?" Ya tambaya a ruɗe yana jiran amsa.

Maimakon ta amsa sai ta ce, "da wa ka ke yin waya a tsakiyar daren nan?."

"Bosa ne fa, kin san yana china, shi a can ba dare bane." 

Ta yi shiru bata amsa ba alamun bata yarda ba. Saheer ya ce, "ba ki yarda ba?." Nan ma bata amsa ba ta yi masa shiru.

"Zan yi screenshot na tura miki ki gani, kar ki yi zargin da wata nake waya" ya faɗa yana ƴar dariya dan ya san Islaha akwai kishi mai yawa.

Saheer ya kuma cewa, "Islaha ki amsa min, lafiya kuwa?."

Daƙyar ta ce, "Lafiya lau. Dama Chairman ne ya kira ni yana faɗa min Mr Ray ya shigo gari."

"Shine me? A daren nan zai katse miki bacci ya ce miki Rehaan ya shigo ƙasar nan?."

"Yana so mu je diamond hotel mu same shi, zai turo da mota ƙarfe huɗu da rabi za mu tafi. In an yi sallar asuba sai mu samu ganinsa."

"What! Ƙarfe huɗu da rabi fa ki ka ce? Wacece zata fita a wannan lokacin?." 

Ta ɗan sauke numfashi ta ce, "ni mana."

"Ke da wa?."

"Ni da Salim da Muslim."

"Wannan shegen Muslim ɗin mai kallonki ɗin nan ko?." 

Ba ta amsa ba, ya ce, "Baza ki je ba Islaha, babu inda zan bari ki fita a wannan lokacin." 

Ta ɗan rufe ido ta buɗe ta ce, "Hamma ya zama dole in je, tafiyar aiki ce."

A fusace ya ce, "Tafiyar aikin tafiya neman rahama ce? Dan shi Chairman ɗin bashi da hankali, ƙarfe huɗu na dare zan sallama ki ki fita keda wasu mazan da ba ƴan uwanki ba?." 

Jin ya fusata sai ta sassauta murya ta ce, "ba wannan tunanin zaka yi ba Hamma, kai ka faɗa min in na samu damar ganin Mr Ray har na yi interview dashi nasara ce a gare ni, kuma ga lokacin ya zo na ji ka fusata kana ta faɗa."

Saheer ya ce, "rainin hankali ne bana so, dan hauka irin na Chairman ɗin kawai sai in barki ki fita da daddare?." 

Ta ce, "babu abinda zai same ni, daman na kira na faɗa maka ne."

"Mtsw! Allah ya kaimu, in lokacin ya yi ki kirani, zan faɗawa Baffa sannan zan fito." Ta ɗaga kai ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya.

Alwala ta yi ta shinfiɗa sallaya ta tayar da sallah, bayan ta idar da adadin yadda take so ta yi karatun alkur'ani ta cigaba da lazumi har ƙarfe uku da rabi ta yi. 

A lokacin ta tashi ta fita zuwa kitchen ta ɗan dafa ruwa ta zo ta yi wanka, ta shirya cikin abayar da Hamma ya siya mata a sallar da ta wuce. 

Ta ɗauki facemask ta saka saboda sanyi da ƙura, saka facemask har ya zamar mata jiki, in ta fita babu shi tana samun matsala. Ta ɗauki wayarta da handbag ta saka iv a ciki, ta zauna tana jiran su kira ta a waya.

Ga Islaha zata je neman Rehaan, ina so ku tuna bata san fuskar Rehaan ba😂💃🏻💃🏻 ga mutuniyar taku bata da kirki.

Nana Haleema✍🏻
***