TAURARI BIYU

Taurari biyu

by @queenmeemi

TAURARI BIYU
 (Two Stars)


Meemi Basheer



*Sabon labari, daga meemi bashir Taurari Biyu (Two Stars) zai ringa zuwa muku a shafina na* *Arewapen app. Username:* #queenmeemi#
Haka kuma a Wattpad* #queen-meemi da kuma WhatsApp group da channel.



*Bisimillahir-rahmaninr raheem.*


Chapter 1


Babbar mota ce ta fito daga tashar motar  wani karamin gari Mai suna Quezzam da ke  ɗaya daga cikin garuruwan ƙasar Aljeriya. Motar cike take da mutane, mabambantan yaruka, Tuareg , Zabarmawa, Fulani, Kanuri, Buzaye,hausawa da sauran masu shigowa ƙasar don ci-rani. Da dama Akwai Tuareg  da ke fita fatauci daga Quezzam zuwa wani ƙauye da ke kan iyakar Nijar da Aljeriya mai suna Assamaka, inda yanzu ma suka nufa.
Mutanen cikin motar na ta korafi kan yadda direban ke yawan tsayawa akai-akai, abin da ke janyo musu ɓata lokaci a hanya Kenan. 

Tsaki na yi tare da kallon agogon hannuna na ga har ƙarfe goma sha biyu na rana ta yi. Na lumshe ido domin ina son yin barci, wanda ya zama min al’ada idan zan yi tafiya mai nisa.
Amma surutun Ruman, wadda ke zaune kusa da ni, ya hana ni barcin. Na muskuta tare da juyar da kai, na ɗan bugi bayanta don ta yi shiru. Ita ma ta san ba zan iya barci cikin wannan hayaniyar ba, balle ga matsin da muke ciki da yadda motar ke rangaji a tsakiyar Sahara.
Na ji an daki ƙafata da ƙarfi, har sai da na ji zafi. Na buɗe ido da sauri, na sauke su kan mutumin da ya buge ni. Idanunsa suna cikin rawani, amma sun ja sun yi jajir.
Na Harare shi tare da dauke kaina, Sai na samu kaina da sake kallonsa, take na Ji wani irin rashin yarda da shi ya mamaye zuciyata. Na gyara zamana, na ci gaba da kallonsa kai tsaye. Shi ma ya kafe ni da ido.
Sai na kau da kai cikin rashin jin daɗi. Wani yanayi ya mamaye ni irin wanda nake ji idan ban yarda da mutum ba. Da alama ya fahimci wani abu, sai ya gyara rawanin kansa ya ɗaga shi kaɗan, sannan ya dubi wani kusa da shi ya jinjina masa kai.
Jikina ya ɗan shiga  rawa, na shiga murza hannuwana a cikin hijab. Ban san dalili ba, amma na kasa daina kallonsu.
Bayan doguwar tafiya, direba ya sanar da mu cewa za a tsaya domin sallah. Ya tsaya a wani ƙaramin gida da yake shi kaɗai a wajen, muka fito gaba ɗaya.
Ni da Ruman muka yi alwala, muka yi sallah. Wasu kuma suka fara cin abinci.
Na ja gefe na tsaya ina cin gurasa da lemon roba da na taho da shi. Sai na Ji tashin magana sama sama cikin yaren tuareg , juyar da kai na yi ba tare da damuwa ba! maganganun su suka ringa ratsa kunnuwana, na samu kaina da son leƙawa
Na matsa kusa sosai ina sauraro.
“Ina ganin mu kawar da shi idan mun isa Asamaka. Bayan mun gama aikin da aka aiko mu, ba zai wuce awa biyar ba ya mutu.”
Kaina ya ɗaure. Ban fahimci abin da suke nufi ba, amma na tabbatar akwai wani abu mai haɗari. Na yanke shawarar sa musu ido.
“Kowa ya shiga mota, za mu ci gaba da tafiya!” direba ya yi Kira, kowa ya shirshiga. 

“Iman! Ki zo da sauri!” Ruman ta kira ni.
Muka shiga motar, aka ci gaba da tafiya. 
Bayan awa ɗaya, muka fara hango mashigar shigar assamaka . Sai ga mutumin nan ya tashi yana magana da direba, yana gargadinsa kada ya ɓata musu lokaci.
Na sake Ji  mamaki.
Sai na ce a raina _Me ya dame ni da su?”_ Amma duk da haka, zuciyata ba ta bar ni ba.
Da muka isa Asamaka, kowa ya sauka ya kama gabansa.
Ni kuwa, idanuna na kan mutanen nan. Amma abin mamaki, da na sauka ban gansu ba.
Ruman ta ja hannuna:
_“Ke, mu tafi mana!”_
Na ce: _“Dan jira.”_
Sai na hango su suna sauke da wani babban buhu daga bayan mota, suka nufi wata hanya.
Na bi su da kallo… zuciyata na bugawa da ƙarfi.
Ba tare da tunani ba, na ajiye jakata na bi bayansu.
Sun shiga wani kangon gida Na buya a gefe ina kallonsu. Ba da daɗewa ba suka fito, ɗaya ya yi wa ɗaya alama, suka juya.
Na juya zan gudu, sai na ji an bugi kafa data na faɗi! Kasa Tim!. 

Mutumin nan mai jajayen idanu ne ya tsuguna a gabana ya shiga kallona Yana mirgina kai
_“Idanuwanki ina son su.”_
Ya faɗa yana jan hijabina.
Na miƙe da sauri cikin fushi:
_"Ba ka da kunya ne?”_

Ya zuba uban jajayen idanuwansa tare da fara jera min tambayoyi cikin tsawa. Tsoro ya kama ni sosai.
Caraf ya kama wuyana Ya shake ni.
Na fara kakari, Ina kokarin kwace hannun sa. 

Wani daga cikinsu ya ce:
_“Ka barta! Mu tafi. Wataƙila tarko ce.”_
Ya sake ni Cikin fushi
Nan na shiga tari ina neman numfashi.
Mutumin ya yi murmushi, ya nuna ni da yatsa sannan ya girgiza Kai, ya tashi tsaye Suka tafi.

Na sauke ajiyar zuciya.
_"Allah ya Isa_ na fada Ina murza wuyana, cak na Mike na shiga Kade kasar jikina, na kalli kangon na tasamma shiga. 

ina shiga cikin kangon.
Na hangin babban buhun da Naga sun shiga da shi, na karasa wajen da sauri na tsaya Ina kallo kurr! 

Tsoro ya kama ni ganin kamar  buhun Yana motsi. Na matsa kusa a hankali…
Da kyar na sunkuya na  shiga bude buhun, da kyar na kwance  na ga hannu ya fito daga ciki!
Jinai na firgita. 
Na buɗe buhun sosai na tabbar Mutum ne!
Duk jikinsa ya kumbura da raunuka, jini ya bushe a fuskarsa.
Na razana.
Amma ganin kamar yana numfashi na tashi 
Na fita da sauri, na samu Ruman dake faman nema na. 
Tai saurin tarata _Ina kika shiga ne_
Na ce _Ki zo muyi taimako_
Ta ce:
_Ni dai ba zan shiga ba, wanne irin taimako?_
Na nace.
Na shiga fada Mata abinda ya faru a takaice. 
Ta wani irin ja da baya tana dafe kirji no ba da ni ba, ta juya tana kallon baya cikin tsoro. 
Na uban saki tsaki saboda haushin da ta bani nasan halinta na tsoro _banza_ kawai na ce Mata tare da juyawa na yi hanyar gidan gidan faruq, wanda muka zo assamaka saboda shi. 

Ina isa gidan, na yi karo da shi a ƙofar zaure. Ina haki yana tambayata lafiya, kawai na shiga faɗa masa komai cikin firgici.
Bai ɓata lokaci ba ya biyo ni. Muka ƙarasa kangon.
Da ya ga mutumin, shi ma ya firgita. Ni kuwa na tsura masa ido na ce,
"Kawu Faruq, kamar fa Akhi..."
Na faɗa cikin rawar murya ina matsowa kusa da mutumin. Na sake kallon fuskarsa cike da raunuka da tabon jini. Zuciyata ta fara bugawa da ƙarfi.
Na durƙusa a gabansa, na ɗan share jinin da ya bushe a gefen fuskarsa. Daidai lokacin ne na tabbatar da abin da idanuna suke gani.
"Wallahi Akhi ne..."
Na faɗa cikin muryar kuka. Hawaye suka cika idanuna, na sake kallonsa cikin rashin yarda.
"Wallahi Akhi ne..."
Na maimaita, sannan kuka mai tsanani ya ƙwace min. Na dafe ƙirjina ina girgiza kai kamar zuciyata za ta fito.
Shi ma Faruq ya tsaya cak yana kallon mutumin. Fuskar sa ta canza gaba ɗaya.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..."
Ya furta cikin firgici.
Abin da ya daki zuciyarsa kenan. Ya rasa tunanin abin da zai yi, domin ya san shekaru da dama sun shige ana ɗaukar cewa Akhi ya mutu. Babu mamaki ko mai kama da shi ne, amma idanunsa da zuciyarsa suka kasa yarda.
Jikinsa na rawa ya fita. Ya kira wasu maza uku, suka ɗauke shi suka kai shi gida.
Duk na shiga tashin hankali mara misaltuwa kan dalilin da yasa Akhi ya faɗo hannun waɗannan azzaluman. Tambayoyi marasa adadi suka fara yawo a raina.
Ta yaya Akhi ya tsira?
Su waye mutanen nan?
Me ya sa suka yi masa wannan azaba?
Ina ya shafe duk waɗannan shekarun?
Da sauri na dauko wayata na kirawo Ruman dake can cikin kasuwa tana sayar da kayan da muka taho da su domin cin kasuwa. Tana ɗagawa ta shiga surfa min bala'i kan me yasa ban dawo mun fara sayarwa tare ba, tana cewa kayan sun yi mata yawa.
"Dallah malama, yi min shiru!" na katse ta cikin fushi. "Ai ga shi nan, Akhi ne, na fada tare da katse wayar.