Shimfiɗa
by @zeeykumurya
BARA A KUFAI
*SHIMFIƊA*
Garin ya yi shiru kasancewar yamma ce sakaliya kowa ya tafi gurin nema, mata kuma kamar yadda al'adar garin take a lokacin ne suke samun zarafin zama su huta a gidajensu.
Sannu a hankali ƙaramar yarinyar take takawa tana kurɗawa ta lungu da saƙo cikin galabaita, ƙafarta babu takalmi, gabaɗaya jikinta ya yi fututu kamar wadda aka yi tatar koko a kanta, gashin kanta mai danƙare da ƙasa ya cukurkuɗe ya danƙare kamar ba na mace ba, ga shatin bushashshen hawaye kwance akan kuncinta. A cikin wani shagon sayar da kayan masarufi ta ja tunga tana sassauke numfashin wahala, cikin muryar yara mai cike da rauni ta dubi mai kantin ta ce. "Inu na zo ka mun ka ba ni biskit ina jin yunwa ni da MA'U da HABU." Da sauri mai kantin ya ɗago daga awon fulawar da yake ya dubi matasa biyu da suke jiran shi cikin faɗuwar gaba, duk ya ga hirarsu suke yi amma sai da zuciyarsa ta buga gudun kar su fahimci wani abu daga zancen yarinyar, yana rarraba ido ya zabga mata harara tare da faɗin. "Koma waje ki jira baban naku ba ya nan."
"Ina jin yunwa, ka mun ka ba ni biskit." Ta sake maimaitawa da iya gaskiyarta.
Tsawa ya doka mata ya ce ta je waje ta jira, da sauri ta fice har tana tuntuɓe ta samu waje ta rakuɓe tana leƙen shi.
Ɗaya daga cikin matasan ne ya dubi Inu ya ce. "Yarinyar nan shegen kwaɗayi ne da ita, kowa ta gani sai ta ce masa suna jin yunwa, ƴar ƙarama da ita amma ta iya roƙo." Inu da har lokacin bai dawo daidai ba daga razanin da ya shiga ya ce. "Hmm, ni fa babansu ne yake siya musu biskit a nan kullum, shi ne fa daga ta gane take zuwa ta dame ni tun kafin ya zo."
"Ai ta wuce haka indai wannan ƴar ce."
Matashin ya sake maimaitawa yana keɓe fuska.
Shi dai ɗayan bai ce komai ba ban da tsura wa yarinyar ido da ya yi. Da rawar jiki Inu ya miƙa musu fulawar suka yi masa sallama suka tafi. Sai da ya tabbatar sun bar layin sannan ya leƙo ya dudduba ya ga babu kowa, a tsawace ya kira ta, ta tashi da sauri ta shiga shagon tana bin ko'ina da kallo.
Cikin mugunta ya ranƙwashe ta a ɗaɗdauɗan kanta tare da zare mata ido, yana toshe hancinsa da ƙasan rigarsa ya ce. "Don ubanki ba na ce kar ki ƙara zuwa ki yi magana idan kin ga mutane a shagon ba?"
Idanunta cike da hawaye ta shafa kanta tana jin azabar da ke ratsa ta, cike da yarinta ta ce. "Ka ce na dinga zuwa kullum idan na ji yunwa kana mun, za ka ba ni biskit kuma za ka kai ni inda UWANI take, kuma ka ce kar na faɗa wa kowa." Tsaki ya ja ya kama hannunta ya hankaɗa ta ciki, sai da ya rufe ƙofar shagon ya saka sakata sannan ya tsugunnar da ita ya yi mata abin da ya saba, duk da hawayen da take da kakkaucewar da take saboda ƙugin da cikinta yake yi mata bai ƙyale ta ba sai da ya gama biyan buƙatarsa.
Da kuka ta tashi tana goge bakinta da ya yi mata wani iri, ga nauyin da yake yi mata a kullum idan ta zo gurin Inu ya yi mata abin da ya ce sai ya yi sannan zai dinga ba ta biskit.
Guda ɗaya ya ɗauko mai ƙaramin kuɗi ya miƙa mata bayan ya buɗe ƙofar shagon, da azarɓaɓi ta karɓa tare da ƙura masa ido. A tsawace ya ce. "Wuce ki tafi, kuma idan kika kuskura kika faɗa wa wani sai na yanka ki, na ƙi kai ki gurin uwanin kuma." Kai ta gyaɗa masa a tsorace, ta ɗauke idonta daga kallon shi, ta mayar kan tulin biscuit ɗin da ke zube a ma'ajiyarsa.
"Uwar me kike jira wai? Ba za ki wuce ki tafi gida ba sai na zane ki?"
"Ba ka ba ni na Ma'u da Habu ba."
"Sai dai na uwarsu, wuce ki ban guri! Shegiyar yarinya mai warin tsiya!"
Ya faɗa yana zaburo mata.
Da sauri ta fice tana waigen shi, hannunta riƙe da biscuit ɗin da ya ba ta, ta riƙe shi gam kamar za ta cusa shi cikin fatarta. Inu ya biyo bayanta a hanzarce don tabbatar da babu kowa, ya yi sa'a kamar kullum don a al'adar mutanen garin irin wannan lokacin bana zirga-zirga ba ne a gare su.
Tana fita aka fara kiran sallar Magriba, babu tsoron komai duk da duhu ya fara kawo kai ta naushi hanyar gida cikin murnar samun biscuit.
Ƙaton gida ne ginin jar ƙasa mai ɗauke da ƙaton tsakar gida, da raɓe-raɓe ta shiga gidan tana ɓoye biscuits ɗin a cikin ɗaɗɗaudar rigar jikinta, babu wacce ta kalle ta a cikin matan gidan bare ta tuhumi daga inda take, jikinta na rawa ta ƙarasa kusa da banɗaki hango ƙanwarta Ma'u zaune a gurin cikin tsakiyar ƙasa da ruwan da suka haɗu suka jagwale, gabaɗaya ta ɓata jikinta, duk da duhu ya fara kawo kai amma ƙudaje ne kawai suke farati a jikinta, fuskarta sharkaf da hawaye da majina, tana ta auna jiƙaƙƙiyar ƙasar gurin a cikinta, cike da zumuɗi MAIRO ta fito da biscuits ɗin hannunta ta ce. "Ma'u ga biskit Inu ya ba ni." Ƙara fashewa da kuka Ma'u ta yi tare da miƙa wa ƴar'uwar tata hannu, zama Mairo ta yi a kusa da ita ta fara kiciniyar ɓare biscuits ɗin, da ƙyar ta iya yaga ledar gabaɗaya, biscuits ɗin ya tarwatse a cikin ƙazantar gurin, ba su damu ba suka saka hannu suka fara wawa suna ci haɗe da ƙasar, kaɗan Mairo ta rage ta kama hannun Ma'u da ke koyan tafiya suka nufi inda ɗakin mahaifiyarsu yake, a bakin ƙofa suka tarar da Habu a kwance yana numfarfashi, cike da kulawa Mairo ta fara saka masa guntun biscuit ɗin a bakinsa, Ganin haka Ma'u ta miƙa mata hannu tare da ƙara volume ɗin kukanta.
"Wannan nasa ne, ki yi shiru anjima zan ƙara karɓo mana wani, ai Inu ya ce da mun ji yunwa na je ya mun ya ba ni."
Laraba da ke bin su da ido tun daga shigowar Mairo har zuwa yanzu ta share hawayen fuskarta, wani irin abu take ji a cikin ranta da ba ta san ya za ta kwatanta shi ba, idan za ta furta shi a baki sai ta ga kamar ya fi ƙarfin ta kira shi da tausayi, wannan ƙananun yaran da duk ba su wuce a saka su a baya a goya ba su aka bari da ɗaukar nauyin kansu? Su aka bari da yi wa kansu hidima? Hawayen da ya ƙi tsaya mata ta share ta fara tafiya tana satar kallon su, ɗakin kusa da ita ta nufa da sallama, matar da ke ciki ta amsa mata tare da faɗin. "Shigo mana Laraba, sai ka ce baƙuwa za ki tsaya daga bakin ƙofa?" Ƙoƙarin da ke taso mata ta danne ta ce. "Ina sauri Adama zan yi sallah, don Allah wata alfarma na zo nema a gurinki." Da mamaki Adama ta ce. "To me ya faru? Allah ya sa lafiya?" Ƙasa da murya Laraba ta yi ta ce. "Don girman Allah da darajar iyayenki ko rabin malmalar tuwo ne ki sanwa yaran can, ko iya ƙaramar ce ki bawa." Kamar wadda aka faɗa wa saƙon mutuwa haka Adama ta yi da fuska.
"Ba zan iya ba gaskiya, don ni ma ba isa ta zai yi ba ni da nawa yaran, wanda ya yi cikin da aka haife su ma ya hana su sai ni zan ɗauki nawa na ba su."
"Kar ki duba wannan Adama, Allah za ki duba da halin da yaran nan suke ciki."
A harzuƙe Adama ta ce. "Ban da shi Laraba, don Allah ki ƙyale ni! Haba! Wato kin gama bin ragowar matan gidan ba wadda ta kula ki shi ne za yau kika dawo kaina ko? To alƙur'an duk nacinki sai dai ki yi ki gama amma ba zan bayar ba, idan kin ji haushi ki ba su naki."
Wani murmushi Laraba ta yi mai ciwo ta ce. "Babu wanda bai san ƙadamin da nake ciki ba a gidan nan game da yaran nan, amma daga na yi muku magana a kansu sai ku rintse ido ku dinga faɗa mini magana don kun san babu yadda zan yi." Tsare da ta zo gilmawa ta dubi Laraba a sheƙe ta ce. "To ai ke ɗin ce kamar mayya, ki cire hannunki daga rayuwarsu ki zuba musu ido kamar yadda kowa ya yi amma kin gagara." A fusace Laraba ta ce. "Ba zan yi ba, kada Allah ya sa ki ba su ɗin, ai ba fin uwarsu kuka yi ba da Allah ya ɗauke ta ya bar ku, kuma ba ku yi alƙawari da shi zai bar ku ku rayu da naku ƴaƴan har abada ba, kowa zai je inda ta je, ba sauri ta yi ba kamar yadda mu ma ba jinkiri muka yi ba, lokaci ne kowa da nasa." Ta ƙarasa maganar cikin zafin rana da ya bayyana a dukkan jikinta saboda rawar da yake yi. Tsaki Tsahare ta ja tare da zunkuɗa goyon bayanta da ya zazzago ta ce. "To mu dai kar ki ƙara saka mu a cikin sabgar su, ke da kika ga za ki iya ki je ki yi ta yi." Wani kallo kawai Laraba ta yi musu tare da girgiza kanta ta bar gurin.
Har aka yi Isha su Mairo suna zaune a bakin ƙofar bolar ɗakinsu sauraye na dafdala a fatar jikinsu, matan gidan kowacce ta yi shimfiɗa a ƙofar ɗakinta tare da yaranta suna cin tuwon dare gami da zabga hira, har lokacin Ma'u kuka take mai haɗe da tarin yunwa.
A hankali Mairo ta haɗiye wani yawu saboda hango ƙatuwar lomar da Hatsare ta cilla a bakinta, kasancewar kowacce mace da fitilar ƙwai a gabanta ya sa haske ya wadata a tsakar gidan, miƙewa ta yi ta koma kusa da su ta tsaya tana kallon kwanukan gabansu kamar za ta faɗa ciki. Murfin langa Adama ta ɗauka ta wurga mata tare da faɗin. "Mayya! Ai idan ba ki zo kin yi mana ƙerere aka ba ba cika ƴar cikin Uwani ba, kullum sai kin zo an kore ki amma gobe sai kin dawo." Baki cike da tuwo Tsahare ta ce. "Kin manta gado ne Adama? Ai gado ba karanbani ba, ai mu kuma mun shiga uku a gidan nan, Malam ya auro mana jaraba ta tafi ta bar mu da mugun iri."
Cike da matsanancin tsoron su Mairo ta koma inda ta baro, ta fara cikiniyar ɗaga Ma'u da ta kwanta tana birgima a ƙasa.
"Ki yi shiru ki daina kuka, Inu ya ce zai kai mu gurin Uwani, za ta dawo ta ci gaba da ba mu abinci da yi mana wanka."
Laraba da ta tasa kwanon tuwo a gabanta ta kasa ci ta share hawayen fuskarta da haɓar zaninta, ba ƙaramin danne zuciyarta take ba na ganin ba ta je inda suke ba, hankalinta gabaɗaya yana kan Habu da ba shi da lafiya, tun bayan rasuwar mahaifiyarsu yaron bai ƙara wata da cikakkiyar lafiya ba, don ko magana dainawa ya yi sai dai ya yi ta bin mutane da ido, haka zai wuni a shimfiɗe a ƙasa, a nan zai yi fitsari da komai, shi ya sa ko tunkarar inda suke ba mai son yi saboda wari da hamamin da suke, babu mai yi musu wanka bare tsarki da wanke baki, hakan ya sa kowa yake kyarar su a garin, ƙalilan ne masu tausaya musu. A sace Mairo ta tashi ta je randar Adama ta ɗebo ruwa ta sha ta kawowa ƙannenta ragowar, kurɓa ɗaya Habu ya yi ya dawo da shi tare da biscuit ɗin da ya ci, Ma'u kuma ta shanye ragowar tass tana sakin ajiyar zuciya.
Ƙarfe tara da mintuna Malam Sadi ya turo kekensa ya shigo gidan fakan-fakan yana muzurai, matan gidan da ragowar ƴaƴansa suka yi masa sannu da zuwa, ya amsa a cikin yana ƙara ɓoye ledar da ya shigo da ita a cikin malunmalun ɗinsa ya nufi ɗakin amaryarsa Atika. Yana shiga ya saki fuska ya fito da ledar da ya ƙunshe yana faɗin. "Amarsu ta ango, duk mai son zaman lafiya a gidan to ya yi miki biyayya." Murmushi Atika da ke kwance akan gadon ƙarfenta ta saki ta tashi zaune ta yi masa sannu da zuwa. Jiki na rawa ya miƙa mata ledar hannunsa, yana dariya da lasar baki ya ce. "Na san ba ki son tuwo shi ya sa na yi miki tsarabar tsire mai zafi, maza ki afa kafin na zagaya bayi na fito mu kwanta ko?" Ta ɗaga masa kai a kunyace tana murmushi.
"Baba muna jin yunwa sosai, Ma'u tana ta kuka Habu ya yi amai."
Siririyar murya Mairo cikin kuka ta ratsa dodon kunnensu, da matuƙar mamaki Malam Sadi ya juyo ya dube ta, Atika ta toshe hancinta da sauri tare da ɓata fuska kamar ta ga kashi. Daƙuwa Malam Sadi ya yi wa Mairo, cikin tsawa ya ce. "Ungo nan ƴar jakar uba! Shegiyar yarinya mai ƙashin tsiya, bana hana ki bi na kina ce mini kina jin yunwa ba? Uwar cin masifa da kwaɗayi!" Cike da ƙyama Atika ta ce. "Don Allah kar fitar da ita daga ɗakin nan, wannan warinta zai kashe ni." Diɓiɓicewa ya yi ya kama kunnen Mairo ya murɗe da ƙarfi, ta wage baki za ta yi kuka ya dalle mata bakin tare da fuzgar hannunta ya hankaɗa ta waje.
"Ƴaƴan jaraba da masifa dangin matsiyata, ban da fatara uwarku ta mutu amma ko ɗaya daga cikinku su kasa ɗauka saboda suna yi mini baƙinciki da hassada, to su gani a kansu, kuma ƴar'uwarsu suka wulaƙanta ba ni ba, wahalar da suke so su ga ina sha a kanku ba za su gani ba, mugun fatansu ya ƙare a kanku da su."
Da Ma'u mairo ta yi tuntuɓe a bakin ƙofar ɗakin, wadda ta biyo bayanta tana kuka, ita ma kukan ta saki ta rungume ta suka faɗi a ƙasa.
A zuciye Malam Sadi ya buga musu tsawa.
"Ku tashi ko na janyo tsumagiya na zane muku jiki, ku je can ku yi ta koke-kokenku amma ba a nan ba, shegun yara ƙananu da ku amma kun iya makirci."
Da sauri Mairo ta tashi ta ja hannun Ma'u suke bar gurin cikin tsananin tsoron mahaifin nasu, sau uku suna faɗuwa ƙasa kafin su kai ƙofar ɗakin nasu, saboda yunwa da ta galabaitar da su, da Ma'u da take ta ƙanƙame ta tana ɓoye fuskarta a jikinta, saboda azabar tsoron Malam Sadi da take, ko muryarsa ta ji razana take saboda yadda yake kyarar su da zare musu ido, kamar musulmi da kafiri haka yake da su, yana ganin su zai yi cikin-cikin fuska ya fara mururai, don kawai kar Mairo ta ce ya ba su abinci, tsanar da yake nuna musu ko matan nasa ba sa nuna musu kamar ta, yana ganin su wahala ce babba a gare shi, ga haushin dangin mahaifiyarsu na ƙin ɗaukar su da suka yi da ya shafe su, cike da takaicin su ya koma ɗakin Atika don ya rarrashe ta, ya san tana can ta cika ta yi fam don ta sha faɗa masa ba ta san ko ganin yaran bare suna shigar mata ɗaki, shi ko a yanzu ba shi da abun lallaɓawa kamar ta a duniya, don budurwa ce sakin wawa ya samu ya aura wata biyu da suka wuce.
Ɗahiru ɗan Yayan Malam Sadi da gidansa yake jiki da jiki ne ya shigo da kwano a hannunsa, bai kalli kowa ba a cikin matan gidan ya nufi inda su Mairo suke ya ba su, da sauri suka fara ci hannu baka hannu ƙwarya, sai da suka kusa gamawa sannan ta fara saka wa Habu a bakinsa yana haɗiyewa, bayan sun cinye Ɗahiru ya shafe kanta ganin yadda take ta murmushi da suɗe hannu.
"Da safe ma za ka kawo mana abincin? Kullum sai Ma'u ta yi kuka ta ce yunwa, ni ma haka, kuma Uwani ta tafi, Baba ya ce wai ta mutu an binne ta, ai za ka kai mu inda take ko? Ta dawo ta dinga yi mana wanka, Ma'u ta daina kuka, Habu ya daina rashin lafiya."
Fuskarta ya shafata ya ce. "Babu abin da ba zan yi muku ba Maryama, don shuka sai da ban ruwa idan ana so a yi girɓa mai kyau." Daga haka ya kashe fitilar hannunsa, ya lallalube mata jiki sannan ya tashi yana faɗin. "Allah ka kai damo ga harawa." Tare da jan dogon fito mai haɗe da dariya, da farinciki ya ɗauki kwanon ya tafi, ta bi shi da kallo jikinta a sanyaye saboda abin da ya yi mata.
Washegari sai da gari ya yi haske sannan suka farka, don ba ƙaramin ƙoshi suka yi ba daren jiya wanda suka manta rabon da su yi kamar shi.
A al'adar garin yau ranar Kamu ce, akwai wani ƙaton kogi a bayan garin da ake zuwa duk bayan watanni uku ana kamun kifi, kuma maza kowa yana yi matasa da manya, mata kuma suna yin abin siyarwa sukai tare da yin kallon kamun da sauran wasanni, daga an yi sallar asuba ake zarcewa a fara, shi ya sa gidan shiru da suka tashi, kowacce mace ta yi abincin da za ta siyar ta tasa ƴaƴanta a gaba sun fice, Laraba ce kaɗai da ta kasa tafiya ta bar su ba ta fita ba.
Da rigima kamar kullum Ma'u ta tashi, Mairo ta kama hannunta ta kai ta bakin banɗaki ta wanke mata baki ta cire mata rigar jikinta ta ajiye akan wani dutse don ta bushe, sai da suka sha ruwan sannan suka baro gurin, Mairo tana ta murna yau su Adama ba sa nan bare su dake su don ta taɓa musu ruwa, a kwancen da Habu yake ta buɗa bakinsa ta dinga ɗura masa, duk da tana ganin rabin ruwan fitowa yake daga gefen bakinsa amma yarinta ba ta saka ta yi tunanin wani abu ba bare ta daina ba shi, har sai da ya ƙware ya fara tari sannan ta rabu da shi tana faɗin. "Yau za mu sha ruwa da yawa tunda Adama da Tsahare ba sa nan." Da murnar haka ta ɗauko wa Ma'u wasu kayan a ɗaki da suke ta zabga zarni da warin ɗauda ta saka mata. Ta koma ta mayarwa da Tsahare kofinta ta shiga banɗaki ta yi fitsari, kukan da Ma'u take da yadda take bin ta ya sa ta sunkuya ta goya ta suka nufi hanyar soro, har ta wuce Habu ta dawo kusa da shi ta ce. "Zan je gurin Ilu ya mun ya ba ni biskit sai na dawo mu ci ka ji?" Ido ya ƙura mata hawaye na gangarawa ta gefen fuskarsa, tana numfarfashi saboda nauyin Ma'u ta sunkuya ta share masa hawayen tana cewa. "Zai kai ni gurin Uwani ma mu dawo tare, ka daina kuka, kuma da yawa zan kawo maka biskit ɗin, ita ma Ma'u zan ce ya yi mata ya ba ta, har da alawa ma zan ce ya ba mu." Ta ƙarasa maganar da karsashi da zumuɗi.
Wata mummunar faɗuwa gaban Laraba da ke leƙen su ta tagar ɗakinta ya yi, tunda daga lokacin da Mahaifinta da mijinta suka gina mata katangar ƙarfe tsakanin ta da yaran take wasan ɓuya da su, saboda suna ganin ta za su taho gurinta ko su yi ta kallon ta da idon neman agajinta kamar yadda ta saba ba su a baya, maganar zuwa wajen Ilu da Mairo ta yi ce kawai take yawo a kanta, har suka fice daga gidan ba ta iya ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ba.
"Innalillahiwa'inna'ilaihi raji'un! Na shiga uku! Allah kar ka tabbatar da abin da nake hasashe akan yarinyar nan, me take nufi Ilu zai mata ya ba ta biskit a ƴar mitsitsiyarta?"
Ta yi maganar a ruɗe tana dafe ƙirjinta, fitowa ta yi da sauri ta tsaya tana hangen Habu, wata irin azalzala zuciyarta take mata akan ta je ta duba shi, ta ba shi abinci ta yi masa wanka, ta rungume shi ya ji ɗumin wani a jikinsa, sanin ba ta da wannan damar ya sa ta sulale ƙasa ta yi zaman daɓaro, tana hawaye ta ɗaga hannunta sama ta fara magana cikin rawar murya.
"Ya Allah ka kare wannan bayin naka, Allah ka dubi maraicinsu ka kawo musu ɗauki, Ubangiji ka tallafi rayuwarsu ka kare su daga sharrin duk mai sharri, ka raya su ka sa su zamto ababen alfahari a gaba." Ta shafa addu'ar sannan ta tashi ta ɗauko kujera ta zauna ta zabga tagumi, duk yadda take son zuwa wajen kamu amma ta ji duk ya fice mata a rai, duniyar ma gabaɗaya ba ta yi mata daɗi, tausayin su Mairo da son tallafawa rayuwarsu shi ne babban burinta a yanzu, a kullum lamuran Malam Sadi tsoro suke ƙara ba ta, don al'amarin nasa ya wuce mamaki, ta rasa inda za ta ajiye shi a matakin rashin imani da son kai, ta yi da na sanin aurensa babu adadi, maganganun Mahaifiyarta ne kawai suka saka take zaune a gidansa har yanzu, amma da tuni ta tsige ƙaddararren aurensa ta yi gaba, musamman da Ubangiji bai nufa sun samu ƙaruwa ba har yanzu. Numfashi ta sauke ta yi fatan Allah ya dawo da Mairo da wuri ko don ta kula da ɗan'uwanta.
Direct shagon Inu Mairo ta nufa, a wahalce ta ƙarasa saboda yunwa da nauyin Ma'u, duk da ta tarar da shagon a rufe amma haka ta nemi guri suka zauna don ta jira shi, suna zaune tana ta rarrashin Ma'u da ke kukan da ya zamo babban amininta ta hangi Kattume ƴar gidan Adama, ita ma ganin su ya sa ta ƙaraso gurin tana faɗin. "Kowa yana gurin kamu yana kallo amma ke kina nan? Me kike yi a nan?"
"Inu nake jira ya ba ni biskit."
Da kulawa Kuttume ta ce. "Ai ba zai dawo yanzu ba saboda kamun da suke, tashi mu je ku yi kallo kuma, ni ma na koma gida ƙaro wa Adama kwano ne." Ba musu Mairo ta tashi ta bi ta tana janye da hannun Ma'u don ta gaji da ɗaukar ta.
A inda Adama da Tsahare suka baje hajarsu suka ja burki, a ɗan nesa da su Mairo ta tsaya, Ma'u ta fara jan hannunta tana nuna mata Ɗanwaken da Adama take ta zuba wa jama'a, sanin halin Adama ya sa ko motsi Mairo ba ta yi ba.
A hankali Ma'u ta matsa kusa da Adama ta tsugunna tana kallon ta, a fusace ta ɗago za ta yi magana wani irin wani ya bugi hancinta, da sauri ta tashi ta miƙar da Ma'u da ta nutsu tana kallon guri ɗaya alamun wani abu take yi.
"Kan uban nan! Kashi kika yi? A gaban abincin siyarwar tawa saboda kin sha baƙinciki da hassada a nono? To kuwa wallahi sai kin ci ubanki! Sai kin cinye shi tass!
Baki Tsahare ta keɓe ta ce. "Kar ki raga mata daga ita har yayar tata, don ƙila ma ita ta turo ta ta yi, ko uban me ya kawo su ma inda muke oho?" A fusace Adama ta tsinka wa Ma'u marin da ya sa ta kifa akan ƙazantar da ta yi, tsabar gigicewa da azaba sai da ta shiɗe, Mairo ta yi kanta da sauri tana kuka ta ɗago ta, Adama ta haɗa su gabaɗaya ta daka sannan ta kore su.
Duk inda suka je suka tsaya sai an kore su saboda wari da ƙudajen da ke bin su, hakan ya sa suka koma can bayan ruwan inda ba mutane suka zauna a kan wani dutse, Mairo ta rungume Ma'u a jikinta cikin hawaye.
"Kai! Me kuke yi a nan?"
A zabure Mairo ta ɗago ta dubi mutumin da ya yi musu tambayar, cikin kuka da tsoro ta ce. "Adama ce ta kore mu saboda Ma'u ta yi kashi, kowa ma idan muka tsaya a kusa da shi haka." Shiru ya yi yana ƙare musu kallo, lokaci ɗaya ya juya ya fara bin wajen da kallo kamar wanda aka tsikara.
"Ina Babarku?" Ya tambaya yana ƙoƙarin ɗaukar Ma'u.
"Uwani ta tafi ta bar mu, Baba ya ce wai ta mutu, Inu kuma ya ce zai kai ni gurinta, ni ina so na gan ta, na faɗa mata ta dawo ta dinga ba mu abinci, kullum muna jin yunwa."
Tsugunnawa ya yi a kusa da ita duk da warin da yake shaƙa daga gare su da ke ƙoƙarin yi masa illa ya ce. "Kina so na kai ki gurin Uwani yanzu?" Da sauri ta gyaɗa masa kai ta ce. "E, kuma muna jin yunwa ka ba mu abinci." Murmushi ya yi ya ƙara bin gurin kallo.
"Taso mu je na kai ki." Ya yi maganar yana ɓanɓare Ma'u daga jikinta, wadda ta ƙi yarda ya ɗauke ta. Kuka ta fasa mai ƙarfi, bai sake ta ba har sai da Mairo ta miƙe, ya ajiye ta a ƙasa ya ja hannun Mairo da sauri cikin tafiya mai haɗe da waige har yana tuntuɓe.
"Mu tafi da Ma'u, ka ga tana kuka." Ta faɗa tana waigen ƴar'uwar tata da ta miƙe tsaye tana miƙo mata hannu, bai kula ta ba har suka ƙarasa gaɓar kogin, inda masu tsallakowa daga wasu garuruwan su zo suke sauka, da ido ya yi wa wani alama, da sauri ya tashi cikin rawar jiki ya janyo kwale-kwale ya shiga, shigar da Mairo da tsoron ganin ruwa ya cika ta ya yi, sannan shi ma ya shiga, a hankali ta ɗaga kai ta hangi Ma'u da take tahowa, sautin kukanta gabaɗaya ya cika gurin, ita ma kukanta ta fara ta ce. "Ka bari na ɗauko Ma'u, ga ta can ta biyo mu tana ku...." Matse hancinta da ya yi da wani farin ƙyalle ya sa sauran maganarta maƙalewa, lokaci ɗaya jikinta ya shika ta daina kukan da take, idanunta ƙur akan ƴar'uwarta da ta faɗi a ƙasa tana gunjin neman ɗauki aka fara tuƙa kwale-kwalen, tun tana iya hangen Ma'u da garinsu har ta daina, ta daina ganin komai sai ruwan da suke tafiya a cikinsa da mutanen da suka ɗauke ta, a raunane ta juya za ta yi wa wanda yake riƙe da ita magana, amma duhun da ya mamaye ganinta da duniyarta ya sa ta kasa furta komai, lokaci ɗaya komai ya tsaya mata cak, daga nan ba ta ƙara sanin inda kanta yake ba.