BARA A KUFAIFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

BARA A KUFAI

  • 1views
  • 37chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Shimfiɗa

BARA A KUFAI *SHIMFIƊA*Garin ya yi shiru kasancewar yamma ce sakaliya kowa ya tafi gurin nema, mata kuma kamar yadda al'adar garin take a lokacin ne suke samun zarafin zama su huta a gidajensu. Sannu a hankali ƙaramar yarinyar take takawa tana kurɗawa ta lungu da saƙo cikin galabaita, ƙafarta babu takalmi, gabaɗaya jikinta ya yi fututu kamar wadda aka yi tatar koko a kanta, gashin kanta mai danƙare da ƙasa ya cukurkuɗe ya danƙare kamar ba na mace ba, ga shatin bushashshen hawaye kwance akan kuncinta. A cikin wani shagon sayar da kayan masarufi ta ja tunga tana sassauke numfashin wahala, cikin muryar yara mai cike da rauni ta dubi mai kantin ta ce. "Inu na zo ka mun ka ba ni biskit ina jin yunwa ni da MA'U da HABU." Da sauri mai kantin ya ɗago daga awon fulawar da yake ya dubi matasa biyu da suke jiran shi cikin faɗuwar gaba, duk ya ga hirarsu suke yi amma sai da zuciyarsa ta buga gudun kar su fahimci wani abu daga zancen yarinyar, yana rarraba ido ya zabga mata harara tare da faɗin. "Koma waje ki jira baban naku ba ya nan." "Ina jin yunwa, ka mun ka ba ni biskit." Ta sake maimaitawa da iya gaskiyarta. Tsawa ya doka mata ya ce ta je waje ta jira, da sauri ta fice har tana tuntuɓe ta samu waje ta rakuɓe tana leƙen shi. Ɗaya daga cikin matasan ne ya dubi Inu ya ce. "Yarinyar nan shegen kwaɗayi ne da ita, kowa ta gani sai ta ce masa suna jin yunwa, ƴar ƙarama da ita amma ta iya roƙo." Inu da har lokacin bai dawo daidai ba daga razanin da ya shiga ya ce. "Hmm, ni fa babansu ne yake siya musu biskit a nan kullum, shi ne fa daga ta gane take zuwa ta dame ni tun kafin ya zo." "Ai ta wuce haka indai wannan ƴar ce." Matashin ya sake maimaitawa yana keɓe fuska. Shi dai ɗayan bai ce komai ba ban da tsura wa yarinyar ido da ya yi. Da rawar jiki Inu ya miƙa musu fulawar suka yi masa sallama suka tafi. Sai da ya tabbatar sun bar layin sannan ya leƙo ya dudduba ya ga babu kowa, a tsawace ya kira ta, ta tashi da sauri ta shiga shagon tana bin ko'ina da kallo. Cikin mugunta ya ranƙwashe ta a ɗaɗdauɗan kanta tare da zare mata ido, yana toshe hancinsa da ƙasan rigarsa ya ce. "Don ubanki ba na ce kar ki ƙara zuwa ki yi magana idan kin ga mutane a shagon ba?" Idanunta cike da hawaye ta shafa kanta tana jin azabar da ke ratsa ta, cike da yarinta ta ce. "Ka ce na dinga zuwa kullum idan na ji yunwa kana mun, za ka ba ni biskit kuma za ka kai ni inda UWANI take, kuma ka ce kar na faɗa wa kowa." Tsaki ya ja ya kama hannunta ya hankaɗa ta ciki, sai da ya rufe ƙofar shagon ya saka sakata sannan ya tsugunnar da ita ya yi mata abin da ya saba, duk da hawayen da take da kakkaucewar da take saboda ƙugin da cikinta yake yi mata bai ƙyale ta ba sai da ya gama biyan buƙatarsa. Da kuka ta tashi tana goge bakinta da ya yi mata wani i...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters37
premium16
22

21

Premium
Updated 8 days agoAvailable now
23

22

Premium
Updated 8 days agoAvailable now
24

23

Premium
Updated 8 days agoAvailable now
25

24.

Premium
Updated 8 days agoAvailable now
26

25.

Premium
Updated 5 days agoAvailable now
27

26.

Premium
Updated 8 days agoAvailable now
28

27.

Premium
Updated 8 days agoAvailable now
29

28.

Premium
Updated 6 days agoAvailable now
30

29.

Premium
Updated 5 days agoAvailable now
31

30.

Premium
Updated 5 days agoAvailable now
32

31.

Premium
Updated 5 days agoAvailable now
33

32

Premium
Updated 3 days agoAvailable now
34

33.

Premium
Updated 3 days agoAvailable now
35

34.

Premium
Updated a day agoAvailable now
36

35.

Premium
Updated a day agoAvailable now
37

36.

Premium
Updated a day agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play