BARRISTER SUHAIL

25

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


Ina ganin comment din ku yan team iman da zeenah masu cewa zeenah ta kyalewa iman miji kar ku manta Iman ta aure mata saurayi😂😩 kuyi wa zeenah ta adalci mana dan Allah ko ku bata baku tausayi ne saura naji wata magana🤒 ni dai ina bayan Zeenah kuma in sha Allah sai ta auri Suhail🏃🏼‍♂️

بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----25

Abba ya zare gilashin dake idanunsa yana kallon Suhail tamkar bai ji abin da ya fada ba.

“Aure za ka kara?” ya maimaita a hankali

Kai Suhail ya gyada.

Shiru ya ratsa falon na wasu dakiku.

Daga bisani Abba ya ce,

“Suhail, duka kwana nawa kenan da aurenka da Iman its just a week shine za kazo min da maganar kara aure anya kana cikin hankali ka kuwa"

Suhail ya sauke numfashi

a nutse ya fara wa Abba bayanin Zeenah tun Lokacin haduwar su a Oxford University  da kuma yadda ta nuna masa soyyaya har kawo wannan lokacin da take jiran ya aure ta

Abba ya jingina da kujerar da yake zaune 

“Subhanallah" ya furta

ya kalli Suhail ya ce"Miyasa tun farkon da na kawo maka Maganar auren Iman baka fadamin kana da wacce kake so ba"

"Abba bana so kaga Kamar na birjerewa umarnin ka ne"

Suhail ba ƙaramin tausayi ya ba Abba ba ganin yadda ya fifita buƙatar sa fiye da tashi bai damu da ko wani hali zai shiga matsawar ya faranta ran Abbansa

Abba yayi gyaran murya ya ce"ita yarinyar ƴar ina ce"

"ɗiyar Alhaji ibrahim makama tsoho jami'in farin kaya"

Abba ya jinjina kai cike da mamakin sunan 
"amman Suhail kana Ganin a ƙananun shekarun ka zaka iya kula da mata biyu kuwa, Ka san nauyin adalci tsakanin mata"

"na sani Abba kuma in sha Allah zanyi bakin kokarin wajen yi masu adalci kamar yadda na taso naga kanayi"

"to shikenan,Allah ya baka ikon yi masu adalci, zan yi kokarin samun mahaifin ta akan Maganar ,ya batun ita matar taka tasan da Maganar ƙarin auren ko kuwa"

"Eh,Abba nayi mata bayani kamar yadda na maka" a wannan gaɓar bashi da wani tsabi illa yayi karyar dan ita kadai zata fidda shi idan har ya nuna bata yarda tabbas sai dai ya haƙura da Auren"

Abba ya ce"kafin inje in samu mahafin yarinyar inaso kazo min da ita Iman ni ina so na ji daga bakin ta"

"To abba,zan kawo ta"

Sallama ya yi masa ya fita 

har ya nufi part din mami sai ya fasa kawai ya hau motar sa ya koma gida

Zaune take a falo tana karanta wani littafi da Hafsat ta taba bata.

Jin motsin bude kofa yasa ta daga kai

Suhail ne ya shigo

Sai dai yau fuskarsa babu walwala

Kallon sa tayi na dan lokaci kafin ta 

 da hankalinta kan littafin

Suhail ya zauna a daya daga cikin kujerun falon

ya ma rasa tunanin da zaiyi ya san idan Abba ya tambayi iman baza ta iya mashi karya ba 

kallon ta yayi ya ce"ki shirya gobe zan muje wajen Abba"

sai da gabanta ya fadi ya ajiye littafin 

“Meya faru?”

Da sauri ya ce,

“Babu komai"

Amma yanayin fuskarsa ya nuna mata akwai wani abu da yake boyewa 

ganin bayan san fada mata ta share sa 

Zeenah ce kwance a dakin ta har yanzu zuciyar na tunanin abinda Suhail yayi mata

mummy ta turo kofar dakin bakin gado ta zauna tana karewa diƴar ta kallo ganin irin ramar da tayi kwata-kwata taƙi cin abincin ruwa kadai take iya ja.

zuciyarta ta cika da tausayi Zeenah tabbas da wani da dauke wani damuwa data roƙi Allah ya maido damuwar da zeenah take ciki gare ta

Zeenah ta ƙira sunan ta 

ɗago jajayen idanunta tayi ta saka cikin na mahaifiyar ta ta ce"Har yanzu kina tunaninsa ko"

hawaye ya soma saukowa daga idanun ta "mummy kina ƙoƙarin na cire Suhail a raina amman kullin kamar kara min son shi  ake mummy ina jin kamar zuciya zata buga"

hannun mummy ta kamo ta saka dai-dai zuciyar ta ce"mummy kinji yadda zuciya ta ke bugawa ƙila mutuwa zanyi"

rugumeta tayi " ki daina fadar haka Zeenah bazaki mutu ba in sha Allah sai kinyi aure kin haifa min cika duk cikin yara hudu dana haifa ke kadai kika rage min idan kina mutu ina kike so in saka raina"

Zeenah kuka Mummy ma cikin su an rasa wanda zai ba wani haƙuri

Bayan wani lokaci Mummy ta share hawayen da ke fuskar Zeenah 

ta kira precious a waya ta girka wa zeenah cous-cous jollof da papper soup din hanta

cikin minti Talatin precious ta jero abincin a tray ta kawo 

A hankali Mummy ta fara bata abincin kamar ƙaramar yarinya


taci fiye da rabin abincin haka yayi wa mummy dad'i sossai

a daure a rinƙa comment da like Please shike karfafa mana gwiwwa

da a rinƙa page biyu kullum da a rinƙa dogon page guda wane kuka zaɓa