NADAMAR DA NA YI

Nadama page 4

by @mrsomar

   NADAMAR DA NA YI🙆🏼

        

         

Fatima Isa

           

       

Edit...2026

Love story 2015🥰

Free book

               Page 4

*Duk wanda ya ce ya na yi da kai to dole ka yi, duk wanda ya ce maka yana sonka tabbas ya gama maka komi haƙika yan kebbi amana ta ne dan sunada karamci sosai, dole ku zamo masu karamci domin Hafsat Bawa and Samira AlHassa fana and Jiddah Aliyu sun fito daga wajanku haƙika wannan page na sadaukar muku dashi ko yi yanda kuke so dashi*

       •••••

    >>>>...>>>>.>.>>>....>>>>

Mota ce ta danno kai cikin harabar gidan motar ta haɗu ƙirar ( Land cruiser) wanda ta amsa sunanta mota black ce ga tinted tasha baƙi, baka iya ganin wanda dake ciki. Direct wajan da ake parking motoci mai tuƙata ya nufa cikin sauri wanda ke mazaunin driver ya fito ya nufi bayan motar da alama zai buɗewa mamallakin motar ne, ba wani ɓata lokaci ya buɗe marfin motar.

Sai da ta fara duro da ƙafarta ƙasa kafin ta ida fitowa da gangar jikinta sanye take da black gown anyi mata aiki da white stone fuskarta sanye take da eye glass shekarunta zasu kai 37 zuwa da 38 tayi kyau babu laifi.

Tana ganin Fatima da Faruok ta wani haɗa fuska kamar an aiko mata da sakon mutuwa, cikin isa ta isa wajansu tana wata yatsina kamar irin taga kashi. Saida ta kalli Faruok sama da ƙasa kafin ta ce.

"Munafukan banza wallahi an dai ji kunya."

Wani irin kallo Faruok ya yi mata sannan ya É—an yi murmushi wanda daka ganshi kasan na takaici ne.

Hannu ya maƙawa Fatima ba musu ta miƙa mashi nata cikin isa ta mike tsaye tana kallon matar dake magana.

Wata irin dariya matar ta saki tana cewa.

“Gaskiya ne Faruok kun fa burgeni dan wannan salon naku a film kawai ake yinsa”

Saida ta ɗan tako daidai inda suke ta ɗaure fuska kamar bata taɓa dariya ba ta ce.

"Amma kada ka manta Fatima ina gaba da ita a gidan nan, akwai wanda suka fita shekaru ba'a aurar dasu ba balle ita idan kana son matar aure zaka iya auran ko da Hafsat ce amma banda Fatima."

Faruok saida ya cije lips ɗinshi na ƙasa.

Sannan ya dubi Fatima yaga idonta na kansa ya fara magana cike da iza da ƙasaita tamkar baya so.

"Humm Fatima mace tamkar da dubu tarbiya ilimi asili NAGARTA da dai sauransu, shiyasa duk namijin da yarasa Fatima dole yayi babbar asara. Uwa ta gari nake son zaɓawa ya'yana ba wanda idan sun girma ba so dinga dana sanin zaɓa masu mahaifiya da na yi wanda bata cancanta ba."

Fuskarta ya É—ago yana kallon cikin idonta dukda Fatima idan ya yi magana tanajin zafi amma taji daÉ—in maganarshi cikin irin salonshi ya ci gaba da magana.

"Aunty zee kenan ba zaki taɓa fahimtar meye so ba har sai kin samu wanda ya nuna maki shi sannan zaki fahimta. Hmm wait for a moment, let me remind you that fatima will soon be my wife.

Duk idan na tuna haka a kullum na kanyi murna because Fatima is my life, ko ba haka ba my baby girl?"

Murmushi ƙarfin hali Fatima tayi dan kawai kada aunty zee ta gane abinda ke zuciyarta. Ido Faruok ya lumshe a hankali ya furta.

"Oh my God, baby, that smile of yours is killing me."

Wani irin haushi ne ya sake shiga zuciyar Aunty zee cikin fushi ta finciko Fatima ta É—aga hannu zata wanka mata mari Faruok ya rike hannunta yana huci."

“How dare you touch my wife's face? if you ever do that again, you'll regret being my sister. Wallahi idan baki kama kanki ba zan manta dake yayata ce na shuka maki rashin mutumci.”

"Wow Faruok that's great. Because of this dirty girl har zaka iya buÉ—a baki ka faÉ—a min magana.

Ni Zee Bashir Lamido. Gaskiya ne."

Tsaki Faruok ya yi ya haÉ—a hannun Fatima danashi suka nufi cikin gida suka barta tsaye tana bala'i.

Sai da suka isa parlour Fatima ta fizge hannunta daga cikin nashi ta nufi É—aki da gudu tana kuka faÉ—i take.

”Daddy why did you do this to me?

Me yasa zaka rabani da rayuwata, na tabbata rayuwata gab take dana rasata indai na aure Faruok ba Musaddik ba. Ni wallahi duk halin da Musaddik yake ciki ina son shi a haka dan shine zaɓin zuciyata"

Haka ta dinga kuka tana surutai da ba mai bata hakuri.

Daddy yana fita daga gida direct wajan mai buga I.V ya nufa yanda yayi rantsewa kuwa haka yasa aka buga a take a gabanshi.

***

Around 9:am

Na safe dinning table ne mai É—auke da kujeru mai cin mutum 12 daka ganshi kasan na family house ne.

Su 7 ne zaune wajan Dad Mom Fatima Mom Hafsat aunty Zee daga gefanta Faruok ne sai Hafsat sai kanwar Hafsat din mai suna Iman.

Bayan sun zauna ne Jumai mai aikinsu ta  gabatar masu da abinda aka dafa bayan ta gama gabatar musu da abincin.

Daddy ya dubi kujerar da Fatima ke zama yaga babu ita da sauri Daddy ya dubi Mom fuska a É—aure ya ce.

"Ina Fatima kowa ya fito ita bata fito ba?"

"Tana É—akinta Alhaji."

"Go and tell her maza ta fito kafin ranta ya ɓace."

     “To Alhaji”

 

Ta meke zata tafi Faruok ya ce da sauri.

"No Mom barshi na kirata."

"Ban saka ba ita nasa ta kirata."

Cikin sanyin jiki Mom ta nufi É—akin Fatima saboda tasan halin Daddy idan ranshi ya É“ace babu kyau, to ya zatayi 'yarta taja mata. Tana tura Ć™ofa ta hangota Ć™wance ta   kifa kanta da alama ba barci take ba.

"Idan kin gama rashin mutumci naki sai ki fito Alhaji na kiranki tunda haka kika zaɓawa rayuwarki.."

Bata ɗago kaiba ta maida ƙofa ta rufe. Kafin ta isa itama Fatima ta fito tun daga nesa Faruok ya kura nata ido dan ganin yanda fuskarta ta kumbura da gani kuka ta ƙwana ta na yi.

Take zuciyarshi ta yi sanyi tausayinta ya kamashi bayan ta zauna cikin murya ƙasa-ƙasa ta ce.

“Ina kwananku?”

Babu wanda ya amsa mata ciki daÉ—in rai sai Faruok babu wanda ya damu da ita sai Faruok da yaketa kallonta cike da shauki.

su ko sauran breakfast É—insu kawai suke hankali kwance.

Hafsat kam ba magana da ta kalli Faruok sai taga idonshi na kan Fatima.

Ganin Faruok babu wanda yace ma Fatima ga abinci yasa ya É—auki Plate É—in gabanta zai fara zuba mata da sauri ta É—aga mashi hannu ta ce

“No, thanks. I I'll do it myself.”

Tana rufe baki ta jayo flask É—in ruwan zafi ta haÉ—a tea ta fara sha da kaga yanda take shanshi zaka gane dole kawai yasa take sha dan yanda kasan tana shan magani haka take kurbar tea É—in.

Ganin yanda take shane Faruok yayi ƙarfin hali dan kawai taci abinci ya fara faɗin.

"Yummy wow Mom wannan abinci yau ya yi daÉ—i ko a Saudi banci irin wannan abincin ba."

Murmushi Mom tayi ta kalli 'yar tata dan tasan duk saboda ita yake maganar.

Fuska ta ya mutsa baifi sau uku ta kurba ba, ta aje tashi tayi tana shirin tafiya Daddy ya watsa mata wani irin kallo mai wuyar fassarawa da sauri ta sadda kanta ƙasa ta juya zata bar wajan ya daka mata tsawa.

"Stop! Where do you think you're going?"

Muryarta na rawa ta ce.

  "Dad na Ć™oshi."

"Bashina tambaye ki ba."

Hawaye ne suka fara sauka a idonta take kamar an buÉ—e fanfo Faruok ji ya yi kamar ya rungumuta ya fara lalashinta dandai babu dama.

"Dad É—aki zanje kaina ke ciwo."

Tsoki Dad yayi ya ce.

"That's ur problem. Da mahaifiyarki taje kiranki bata faÉ—a maki ina kiran ki ba?"

  "She told me."

"Au ta faÉ—a maki shine zaki tafi, to jeki abinki.

Yanda ya ce ta tafi ko marar hankali ya gani yasan ranshi ya yi matuka ɓace dan kamar zaiyi kuka.

Duk da Fatima na kan bakanta amma jikinta ya yi sanyi saboda yanda taga Dad nata mai kaunarta lokaci É—aya ya sauya ya zama abin tsoro a gareta.

Hafsat da su Aunty Zee wani irin dadi suke ji ganin Dad na wulakanta su Fatima. Cikin sanyin jiki ta koma inda take zaune ta zauna ta ce.

"Am sorry Dad please."

Take kuka yaci ƙarfinta duk da mahaifin nata ya tausaya mata har cikin ranshi amma bai yarda ya nuna mata ba. Faruok cikin sanyin murya ya ce.

"Please, sis, stop crying. I'm sorry about what happened yesterday. Everything will be fine, I promise you. Nasan duk saboda ni kike zubar da hawayenki to daga yau na hakura da auranki kije ki aure wanda kike s..."

Magana Faruok ta tsaya ne dan jin dukan da Dad ya kaiwa dinning yana faÉ—i.

"Baku isa ba au harda kai za'a watsa min ƙasa a ido?"

Mom Hafsat ce tayi karfin hali ta ce .

"Amma Alhaji dakayi hakuri da auran."

"Keep quiet Hajara. This matter is none of your business."

Yana rufe bakinshi ya jayo wata bag dake kusa dashi ya ciro IV masu yawa ya watsa kan dinning ya ce.

"Mai dubawa zai iya dubawa amma insha Allahu next week za'a É—aura maku aure."

Babu wanda cikin su bai yi mamaki ba da ganin Iv Fatima ko ido ta zaro jiki na rawa ta fara bin iv da kallo tabbas ko mafarki take bazata taɓa mantawa da sunan mahaifinta dana Yaya Faruok ba, ga sunansu nan ya baiyana baki a buɗe hawaye yaci gaba da safa da marwa. Babu wanda ya iya magana hatta Faruok dukda yaji daɗi irin hallacin da Dad ya nuna mashi amma yanzu yana tsoron irin zaman da zaiyi da Fatima.

Tana mikewa zata bar wajan tayi lum zata faÉ—i da sauri Faruok ya tareta ta faÉ—a jikinshi lumfashinta ya É—auke take..

Masu karatu baku tambayan suwaye wannan family'n ba?

#Love

#yaudara

#Cin amana

#Kiyayya

#Fatima

#Farouq

#Musadiq

#Hafsat

#bilal

#Aunty zee