PAGE 86 - 90
by @swrites22
"Tab ya Asif Allah sai dai gobe yau mun gaji sosai fa, wadda aka Kira da umm manan tace aikuwa aunty faeza ma tace tana so ta zaga garin nan kuma kinsan kece idonmu a garin dan haka ke zakiyi jagora , dariya tayi tana tashi zaune tace ai kawai kuyi kungiya kwanku da kwarkwatar ku gobe afita dan ba biyana zakuyi ba wanna yace yau wanna yace gobe kawai Ku hadu muje gaba daya, wai ma ina su aunty faezan ne ?
"Suna gida muka barsu wai zasu huta Amma gobe nasan duk tare zamu zo .
"tho shikenan Allah ya kaimu gobe kowa yazo da shirin sa sai kafar ku tayi ciwo kuma ba'a mota zamu ba sayyadar ku zaku daka , dariya sukasa hajjo tace kede har yanzu baza ki fasa yawo ba ko.
" kaii hajjo yaushe na zo ne da har kike cewa na fiya yawo yaune fa first fita na, Asif yace gaskiya hajjo karki mana buqulu ki bari a nuna mana gari mu da muka dade bamu zo ba kuma duk kishiyoyin naki basu san gari ba kinga kuma ance ai da dan gari a kan ci gari kar muje mu bata ko muyi wani dajin lion ya samu na lunch daga zuwan mu gwara dai ta mana jagora kafin su emir su karaso ya hana ta dan jiya Adnan ke chemin suma suna hanya a cikin satin nan.
Kamar saukar guduma haka taji ambaton emir din da Asif yayi najwa tace tab ya Asif kama daina saka emir a list dan ba zuwa zaiyi ba ni kuwa hajjo yaushe rabon daki ga emir ma kuwa ?
Kyabe baki hajjo tayi tace " ke rabu da dan nema ai inanan zai zo ya sameni Ko na rike amaryar tasa tun da shi kauyen yake gudu rabon sa danan fa tun rasuwar Junaid shima sau daya ya shigo yayi gaisuwa saiji nayi ance ya tafi, Asif yasa dariya ai kuwa kin samo weak point din kina rike masa Mata zai maki dirar ungulu ba shiri zaki gan shi, itadai seena tashi tayi ta shige daki saboda yadda ta rasa nutsuwar ta tunda Asif ya ambace shi.
Kwanan su seenah biyar a gembu su daddy suka iso ciki kuwa harda sadam da daddy ya tuso shi suka taho , unexpectedly suka iso ba tare da sun sanar da su ba , karfe 5 suka sauka a gembu in da suka yiwa gidan hajjo tsinke.
ummi na shara a tsakar gida suka shigo da sallama, da fara'a ummi ta tarbe su tare da shimfida masu tabarma suka zauna gaishe da daddy tayi sannan suka gaisa da Nina da umma har tana tsokanar umma da fadin " hala dai yau aunty umaimah batan Kai kikayi ,Adnan da sadam ne suka gaisheta ta amsa tana musu ya hanya daddy yace ni wai ina hajjo ne dan nasan in dai ba ruwa ba abinda ke tashin ta a nan wajen yar dariya ummi tayi tace hajjo tana bacci barin fada mata nina tace a a barta Fatima ai ba'a tashin babba idan yana bacci in ba ta kama dole ba Adnan yace ummi ina bakin na kune nagan ki ke daya ?
" Ahh su najwa ai dazun kuwa suka tafi can gidan da kuke sauka anan sukayi sallar azahar wai sai gobe zasu dawo, tana rufe bakin ta hajjo ta fito daga daki tana fadin "muryar wa nakeji haka kamar su Hamza
"mu ne hajjo.
" aaa lale lale maraba sannun ku da hanya yanzun kuke tafe .
gaisheta suka shiga yi ta amsa tana fadin "yau kuma umaimah ce a gida na haka kin kyauta, da sauri umma tace dan Allah hajjo ai min afuwa nasan ni Mai laifi ce , murmushi hajjo tayi " bakomai ai yau kin wanke laifin ki tunda gaki gidan tsohuwa .
Adnan ne ya gaisheta ta amsa sannan sadam ma ya gaisheta dakuwa ta masa "ungo naka aaa lalle na yarda da maganar aseef wato da yake yanzu Kana da ajjiya a garin shine kabiyo sahu ko yaushe rabon daka tako kafar ka gidan nan iye to haseenan ma baza ta koma ba ehee kaji da kyau.
dariya yayi yace "ayi hakuri hajjo aiki ne yayi yawa saisa bana samun lokaci.
"ah ah kawai kace Kaine agogo sarkin aiki shi mahaifin naka baya aikin ne kai dai kawai baka son zuwa sada zuminci to ko Kaso ko Kaki nice uwargidan dole azo kamun kafa, dariya sukayi gaba daya umma tace hakane hajjo ai da tsohuwar zuma ake magani dole saiya kama kafar uwar gida sannan a barshi da amarya Adnan yace ai hajjo dakin hakura da wanna Mai gidan domin shi baya yinki dama kin hakura kin sauke buri ni sai nayi manage .
"kaci malafar garin ku ni na wuce maneji yaro ko kakan naka saida yayi sa'a ya sameni a zamanin mu ma rububi na ake in gayama kaji bare Kai .
duk dariya suke sadam harda rike ciki sosai yake jinshi cikin nishadi ashe haka zuminci yake da dadi kaji ka cikin Yan uwa ma ana wasa da dariya wani abune, haka suka ringa hira har dare sannan suka wuce masaukin su.
Su seena kuwa da Matan su Nabil da aunty fatima sai hira suke ana ta tafka musu hayaniyar suce kawai ke tashi ba zaka iya cewa ga muryar mutum daya ba , ga kuka da Ife ifen Yara da suke Wasa suma .
Sallama su daddy sukayi amma hayaniyar su ta hana suji sai ganin su sukayi kawai agaban su , da ihun murna su najwa suka rungume daddy kafin sukayi Kan nina itama suka gaishe da umma, gaggaisawa aka fara yi daddy yace ina mahmahn taku najwa ce ta mike da fadin
" barin kirata daddy aikuwa seena ma ta mike da gudu najwa tayi hanyar dakin mahmah ganin haka yasa seenah taka kujera ta dirqa hade da shan gaban najwa suka fara rige rigen shigewa, umma na musu maganar dare ne subi a hankali amma basu ma san tana yi ba seenah tayi wuff ta shige.
tare suka fito da mahmah sun sata a tsakiya daidai lokacin su Nabil suka shigo Parlourn suma nan hira ta barke a tsakanin su sai 12 kowa ya wuce makwancin sa .
Washe gari sadam kuwa ganin rana tayi kasa hakuri yayi Ya samu umma da tambayar hajiya ni kuwa ina seenah naga duk su najwa a wajen ita ban ganta ba .
" eyyer seenah tana bacci emir bata tashi ba, kamar ba zaiyi magana ba har ya tashi sai kuma yace hajiya please in ta tashi ki turomin ita ina can bangaren.
Har kusan 12pm seenah na bacci hakan yasa Amal matar Muhammad daka Mata duka a kafa ba shiri ta zabura ta tashi tana murza Ido ta kalli amal din dake sawa yarta Kaya da alama wanka ta mata tace haba aunty amal ina bacci na mai dadi zakizo kitasheni dan kawai ki hanani jin dadi nah toh in na tashi da sassafen nan Mai zan Miki .
" Amma ke dai ko kasa kika rako duniya sai haka wani irin bacci ne haka duk mutanan gidan nan sun tashi ke kina nan kina bacci kalli time ki gani kuma nasan anayin lunch gaba daya gidan hajjo zamu wuce kinga saiki zauna ki ci gaba da baccin ke kadai.
duba takai Kan agogon bangon dake dakin ba shiri ta mike da sauri har blanket na neman kwarfeta tace
" kaiii Ashe gaskiyar ki aunty Amal har 12 innalillahi da gudu ta shige bathroom aunty Amal na fadin kibi a hankali dai.
Ko da ta fito bata samu kowa ba a dakin, shiryawa tayi cikin wani less orange and green ya sha stones dinkin skirt da riga fitted hakan yasa kayan yi Mata das kamar a jikin ta aka dinka , parking din gashin ta tayi kasa², kallon najwa data shigo tayi da fadin
" yauwa better half zo ki dauramin dan kwalin nan karasowa tayi ta dauki dankwalin tana fadin
" ke dai kullum sai an daura maki dankwali.
" ke ni fa bana son Mita in zaki daura min ki daura in baza ki daura ba in nemi wata ta daura min .
" lalle ma toh idan kinji haushi ki koya mana sai ki huta da mita shi Wanda ya iya ai ya huta, shuru ta mata har ta gama daura Matan , tsaye ta Mike tana kallon kanta a mirror sannan ta juyo wajen najwa tace
" kwantar da hankalin ki nima dai zan koyi daurin nan soon ko dan wanna masifar taki na huta da gori.
" oho kuma ya rage naki
" to shikenan zaki gani ta dauko dan kunne tasa sannan ta fara barin turare najwa tace
"Dan Allah kiyi hakuri haka Allah da dame asma acikin mu da kin dade da kaishi lahira wai ke ko hawa kanki ba yayi .
tabe baki tayi ba tare da tace Mata ci kanki ba tazira takalmin ta tayi waje.
lunch ta samu ana girkawa plate ta ja ta diba Wanda zata iyaci ta dawo dinning ta zauna , Saida ta gama ta wuce parlourn ciki nan ta samu su ninan zaune sai jikokin mahmahn dake Wasa, gaishe su tayi mahmah tace badai sai yanzu kika tashi ba?
" whl mahmah ni banma san lokaci yaja har haka ba saida aunty amal ta tashe ni .
"kinyi breakfast Nina ta tambaya mahmah ta chafe da " wani irin breakfast kuma yanzu ai saidai Lunch umma tace seenah kin hadu da emir ne a waje ?
"a a hajiya.
" to kije can bangaren nasu dazu yazo yana neman ki nace kina bacci da toh ta amsa tana tashi dan bata jin za taje wanna Kiran .
A bakin kofa taci Karo da manan tana rarrafe daukan ta tayi ta koma parlourn Inda ta tarar da ya nafisa da umm manan din sai najwa suna hira kadan² neman waje tayi ta zauna tana Wasa da manan din, afnan ce ta shigo tana fadin
" seena kizo emir na kiranki basar wa tayi kamar bata jiba taci gaba da abinda take , umm manan tace wai seenah bake naji ana Kira bane, turo baki tayi tace "to ni aunty huda in ma naji mai zanje inyi masa , kama baki aunty hudan tayi tace
" aaa lalle seenah to yanzu zuwan ne baza kiyi ba ko mai ? " kaii aunty Huda kin fiya takura ni haka nace maki baza ni bane ta mike tana gunguni za tayi waje tace kawo manan din nan karasawa tayi ta dangwara Mata ita ta fice tana jin su nafisa na dariya.
Yana zaune a wata farar kujera ta roba karkashin bishiyar mangwaro yayi facing din kofar part din yaga fitowar ta idonsa kyam a kanta ko kiftawa ba yayi yadda take tafiya tana motsa dan bakin ta da alama gunguni takeyi.
Adnan ne ya fito daga bangaren su ganin ta ya sashi tsayawa suna magana kusan 5 minutes sannan ya wuce, hango shi da tayi yasa ta nufo wajen nasa shi kuwa a lokacin ya gama kulewa ganin shi ya kirata amma ta tsaya tana hira wato ma bata dauki Kiran nasa wani important ba.
Dai dai wajen kansa ta tsaya tace gani dagowa yayi ya kalleta ta ya dauke kansa da fadin " uwata ai da rufeni da duka kika yi ko, kikazo kika min tsaye aka , turo baki tayi ba tare da tayi magana ba sake kallon ta yayi
"wai zaki zauna ne ko kuma ya ya ba tare data kalle shi ba tace kabani wajen zaman ne .
" ita wancan kujerar maiye amfanin ta ko jira kike sai na tashi na daukeki na zaunar , kwafa tayi ta ja kujerar ta zauna .
"na kiraki kin tsaya kina hira saboda kin raina mutane ko shuru tayi ina maki magana kinyi shuru
" to ni mai kake so ince na farko kace na tsaya hira ni kuma ya adnan ne kawai ya tsaya Yana fadamin abu .
"ohk shi adnan din ya fini ne shuru tayi magana nake maki kinyi shuru nace adnan yafi ni mijinki bam barakwai taji Kalmar har yasa ta maimaitawa "mijinki" Ashe maganar ta fito fili yace eh ko ba haka bane .
shuru ta sake yi yace seenahh.. kafin yace wani abu tayi saurin cewa hakane.
" toh maisa kika taho baki tambayeni ba, "kaman yaya kenan? Kin fini sani ai kinsan babu kyau mace tafita ba tare da izinin mijin ta ba idan kuwa tayi hakan toh fushin Allah Yana samun ta har sai ta dawo ta nemi yafewar sa kinsan da haka ?
" eh tace cikin kosawa da zaman dan duk a wani takure take jinta.
"ba eh na tambaye ki ba kin sani ko baki sani ba kamar zata daura hannu aka tace na sani " to maisa kika tafi har wani gari baki fadamin ba, kasa² tace " wayyo Allah na yau na bani, murmushi yayi har dimple dinsa na lotsawa yace " na yafe maki amma karki Kara irin hakan.
Kwalla ta fara sharewa itafa bata san takura wani irin in zata fita saita tambaye shi kuma .
Gyara zaman sa yayi yace " miye na kukan kuma cikin rawar murya tace " ai ai banje gidan naka ba da zaka kafa min dokar fita kuma wai inna fita baka sani ba Allah zaiyi fishi dani har sai na nemi yafiyar Ka.
" to ai seenah indai har da igiyar aurena akanki to sai kin nemi izinina, kuka tasa haikan murmushi yayi tare da tasowa ya dawo gaban ta fuskar ta ya kamo ya fara share Mata hawayen Yana fadin
" daina kukan to na yafe maki duk Inda zakije amma ki sani banda yawon daya wuce qa'ida kinji, juyar da kanta tayi gefe tana ci gaba da kukan ta , ya sake kamo fuskar ta make hannun nasa tayi yace wani abu zan fada maki daina kukan kinji shuru tayi , yace bakyaso kiji kin juyowa tayi , komawa yayi ya zauna ya zuba Mata Ido juyowa tayi suka hada Ido kasa tayi da nata tana turo dan bakin ta gaba ciki² tace inaji .
dariya tabashi amma ya gimtse ya fara Mata magana akan hakkin miji dake Kan matar sa , shuru tayi har ya gama yace kinji ko ? eh tace cikin sanyin jiki .
"good girl to tashi kije idan zasu tafi gidan hajjo karki bisu kijirani bata bashi amsa ba ta tashi ta wuce ya bita da murmushi cikin wani irin farin ciki marar misali shi kansa ya tabbata yanzu wani irin son seenah yake Wanda bai taba tunanin zaiyi Mata irin sa ba.
Tana shiga ta tarar har sun zubo lunch sunaci harara ta makawa najwa " kin kyauta shine ko kijirani , hararar ta Najwa tayi da fadin "injiraki kamar yaya na sani ko acan zakuci ke da mijin naki , zama seena tayi Kan kujera tana fadin "ke ni ba abinda naci bansan zakulo zance .
"oho kuma ke kika sani najwan ta fada tana cigaba dacin abincin ta , taso wa tayi ta dawo kusa da najwan "better half wai fushin na miye ne .
"ban sani ba ai da kinyi zaman ki a can din , " toh maisa zan zauna a can ke ni ko zuwan da nayi ma bada son raina naje ba kawai ba yanda zanyi na dawo ne tunda naje shi kuma wanna yayan naki da shegen surutu.
"Naga alama ai saisa har nai ta kiran ki kinaji kika ki dagawa saboda kina tare da emir soyayya dadi murmushi seena tayi dan ta gane kishi najwan take, tasan najwa na sonta sosai ko uwa daya uba daya suke sai haka dan sun sha fada akan friends dinta idan ta fuskanci tana son su sosai yau kuma ya fada Kan yayan ta gani take kamar zata rage sonta ne
"haba better half kin manta ban fita da waya ba whl tana daki kema kinsan in naga kiranki ba emir ba kowaye a gabana saina amsa kuma ko da aikawa kikayi a kirani zan tashi na barshi ko Mai zai faru dan Allah kar kiyi fushi kinji ban san zuwan nawa zai bata maki rai ba da bazan ma jeba ai a gabanki ko lokacin da Afnan tace Yana kirana aunty huda ce ta matsa saina tafi murmushi najwan tayi da fadin " shikenan odahalf ya wuce dama na dauka kina ganin kiran ne kikaki daga wa.
" kin tabbata ya wuce , daibo abincin tayi ta nufi bakin ta dashi "oya bude bakin, dariya tayi sannan ta bude, aunty Fatima tace zama kiyi ki bari ne mutum da matar sa ace za'a masa iko da ita lalle kuna da aiki , ke kuma ki tsaya idan mijinki ya kiraki sai najwa ta baki umarni kinji tunda ita ke auranki.
Ba Wanda ya kara magana har suka kammala cin abincin suka tashi suka wuce daki, basu jimaba suka fito ko wacce na kumbure² " aunty Huda tasa dariya da fadin
" har anyi fadan Kenan (da yake ko a Kano sunfi zama gidan ta saisa tafi sanin halin su) , aunty faeza tace fada kuma wani irin fada ana zaune kalau?
Cikin dariya aunty hudan tace aunty faeza wa'anna ai sai ki barsu halinsu saisu saisa dazu da suna maganar su bansa baki ba , aunty faeza ta sake cewa duk soyayyar nan kamar za'a hadiye juna ?
"Ahab yanzu za'ayi fada anjima a shirya sai a raba hali yafi sau goma daga fitowar rana zuwa faduwar ta kuma kina shiga fadan nasu kiji kunya, aunty Amal tace to ai kaunar kenan bakiga ko a abokanai idan kika ga ba'a fada ba to zaman bana tsakani da Allah bane haka kafin nayi aure nida kanwata shiifa kullum cikin fada muke .
hira suka cigaba dayi a tsakanin su.
Ko da aka tashi tafiya su suka fara yin gaba dan su nina sunce zasu biyosu daga baya, ganin ba seena a tafiyar tasu yasa najwa kallon aunty amal tace aunty amal seenan fa ? " Zata taho dasu nina shuru tayi cikin rashin jin dadi kamar itama tace ta fasa .
Shiga dakin nasu Nina tayi dan duba charger ta da najwa ta dauka dazu taga seenah zaune tana game .
"ha a baby dama kina nan ai na dauka tare kuka tafi ?
" ah ah Nina wai emir ne yace Kar na bisu injira shi
" toh akan mai zai takura maki zaki tafi yace sai kin wani jira shi wanna ai takura ce bari zaizo ya sameni haka kawai ta dauki charger data gani a jikin socket din bakin kofar ta fice.
Tashi seenah tayi tana tsalle akan gadon " nasan yanzu Nina zata masa fada ai mutum daga zuwan Ka zaka dameni toh da dakai nake fita wanna ai jalala ne .
Kusan 30 minutes da tafiyar su najwa sadam ya shigo parlourn nina kadai ya samu zaune tace dama kaina ke jira karaso Ka zauna , waje ya nema ya nema ya zauna Yana fadin
" Allah yasa ba laifi nayi ba .
.
" toh sarkin masu laifi na duniya wani dalilin yasa Ka hana seenah tafiya tare da su najwa ?
Dan shafa kansa yayi yace "Nina nifa ba ina nufin wani abu bane just inaso ta dan zagaya dani gari ne kinga ni na dade ban zo ba, tashi tayi tace ni dai na fadama kar ka takura min yarinya kuma ba kanka na rawa ba kabi a hankali karka ce zaka nuna iko .
" in sha allah Nina tana inane ta fito mu tafi
"tana dakin su ta fada tana karasa barin parlourn.
Tana kwance tana game ya shigo dakin ciki² yayi sallama tare da karasawa bakin gadon ya tsaya hade da harde hannayen sa a kirji ya zuba Mata Ido jikinta ne ya bata kamar ana kallon ta dan juyowa tayi taga mutum tsaye a kanta a dan tsorace ta tashi tana gunguni balle Mata baki yayi da yatsunsa Yana fadin " zagina kike ko? Cikin tabara ta bare baki hadi da sa kuka dariyar da baiyi niyya bace ta subuce masa aikuwa kamar zugata yayi ta sake Kara volume hadiye dariyar yayi ya zauna kusa da ita da sauri ta mike tana kokarin barin dakin, fisgota yayi sai gata dare² Kan cinyar sa kici kicin kwace kanta ta fara amma ta kasa yace ki nutsu in kina so na sake ki , kamar wadda ruwa ya cinye tayi tsit ajiyar zuciya ya sauke da fadin
" miye aka Miki na kuka kalan kimin sharri wajen Nina ace wani abun na miki dama yanzu ma kin Kai karata, turo baki tayi gaba tace toh ba kai bane, ni mai kuma nayi?
" Toh ba kai bane Ka bugemin baki, " to ai nima zagina kikayi , "ni Allah ba zagin ka nayi ba ni to Ka cikani .
" to sai kin fadamin mai kikace "
" Ni kawai fa cewa nayi mai sa zaka shigo ba knocking .
" toh akwai wata ne cikin dakin da ba muharrama taba Wadda ya zama dole saina nemi izini in zan shigo shuru tayi yayi murmushi da fadin
"toh tashi ki dauko mayafin ki mu wuce .
" to Ka sakeni mana kabi Ka kanainayeni kuma Ka wani ce in tashi.
Sakin ta yayi da sauri ta tashi ta dauko gyalenta kallon ta yayi daga Inda yake zaune yace canja wani, kallon gyalen tayi ita ba taga aibun saba dan ya sauka har ciki tace miye laifin mayafin ?
"yayi karami ya bata amsa a takaice cikin jin haushi ta cire gyalen ta wurgar ta dauki wayar ta ta nufi kofar fita seenahh!! ya kirata tsayawa tayi ba tare data juyo ba mikewa yayi ya karaso ya tsaya ta bayan ta har tana jin saukar numfashin sa kan wuyan ta yace kin fasa zuwanne ?
eh ta fada a dan hassale , cikin tausa murya yace shikenan toh tunda kinfi son wancan din dauki mu tafi dama dan naga kayan sun kama jikin ki sosai ne bai kamata ba saisa nace ki canja amma tunda wancan din kike so dauko mu tafi juyowa tayi suka hada Ido dauke kanta tayi ta wuce.
A maimakon ta dauki gyalen na farko saita canjo da wani medium size Wanda yafi wancan din tazo ta wuce shi ba tare data ce masa komai ba murmushi yayi yabi bayan ta saida ta shiga ta fada wa su Nina sannan ta fito ta sake wuce shi Yana tsaye a parlourn tayi waje kamar bata ganshi ba bin bayan ta yayi har suka fice daga parlourn.
ganin ta rage tafiya yasa shi shiga gaba ya nufi parking lot cikin jerin gwanon motocin dake pake a wajen ya bude wata black BMW X6 m60i ya shiga sannan ya bude Mata ta ciki ta shiga yaja motar suka fice daga gidan.
Dan juyowa yayi ya kalleta fuskar ta na kallon wajen window a hankali ya Kira sunan ta seenahh! ummm ta amsa ba tare data juyo ba shuru yayi Yana juya maganar da zai furta can kuma yace I'm sorry for everything I don't m..... I know ta katseshi dan jim yayi sai kuma ya sake cewa did you forgive all that I have done it's ohkay ta sake fada still idonta na kallon titi murmushi yayi cikin jin dadi bai taba tsammanin abun zai zo masa da sauki haka ba.
A bangaren ta kuwa maganar ce bata so tayi nisa saboda wasu dalilai nata guda biyu na farko bata san recalling abinda ya wuce saboda takan shiga bacin rai especially last meet dinsu kafin yayi tafiyar nan da maganganun da ya dinga jifanta dasu Wanda suka kasance very harsh a gareta na biyu kuma maganar sa na jefata wani hali da tunanin ta ya gaza dauka .