BARRISTER SUHAIL

26

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----26 

Washe gari 

Tun safe iman ta tashi yayi shara tayi mopping ko ina a gidan ta jona electric burner turaren da aunty Fauziya ta bata ta saka kan kashe mi wani sanyayyen Kamshi ya mamaye gidan gaba daya

Kitchen ta koma ta fara ƙoƙarin hada masu breakfast ta jima tsaye a Kitchen tana tunanin abinda zata girka kafin ta yanke shawarar tayi fried yam da sauce sai coppe tea wanda tayi musamman don Suhail 

bayan ta gama haɗa komai ta koma daki wanka ta shiga bayan ta fito ta shafe jikin da mai light make up ta fito da wata ash and red din atamfa ayi mata dinkin doguwar riga mai beat work 

atamfar ta yi matukar yi mata kyau daurin dankwali tayi ta fita dai-dai lokacin Suhail na fitowa daga dakin sa 

"Ina kwana" ta fada ba tare da ta kallesa sa ba

"lafiya qlau Ya jikin"

"Da sauki"

ya jima yana kallon jikin ta ganin komai tasa kyau yake mata tamkar dan ita akayi su bai taɓa ganin mace tayi irin wannan kyaun cikin Atamfa ba dan Ko zeenah zaiyi wuya ka ganta da atamfa ko lace daga abaya sai ƙananun kaya.

"breakfast dinka na kan dinning" kamar daga sama yaji Iman ta fada kuma ta hade fuskar kamar ba daga bakin ta Maganar ta fito ba

murmushi gefen baki yayi ya ce"okay muje kiyi serving dina" 

yana gaba tana biye dashi a baya kan ɗaya daga cikin kujerun dining ya zauna bayan ta gama serving din ta juya zata koma ciki 

ya ce"ke bazakiyi breakfast din ba"

"sai anjima zanci"

ajiye cin abincin yayi ya ce"to idan baza kici ba nima na koshi"

ganin da gaske ƙoƙarin tashi yake yasa ta koma ta zauna badan ranta yaso ba 

tana ƙoƙarin zuba nata a wani plate din daban ya riƙe hannun ta kallon sa tayi ya daga mata gira ɗaya ya ce"tare zamu ci"

bata da wani choose daya wuce taci abinci haka ta rinka daukar doyar tana kaiwa baki kamar zatayi kuka 

da kyar taci guda ta rabi ta tashi ta ce"ta koshi"

suhail ya ce"ki shirya zamu je wajen Abba" 

"okay" ta fada

Suhail sai ya gama cinye abincin ya koma Dakin sa wanka yayi ya shirya kansa cikin wani milk din vowel ya feshe jikin da turrarrukan ya fito

kofar Dakin Iman yayi knocking tana kwance kan gado ya ce"ki sameni mota"

Doguwar abaya ta dauko Ash color har kasa ta saka takalmi da jaka ta fita tana zaune cikin mota yana jiran ta

front seat ta shiga ya tada motar suka tafi.

a kofar gate din yayi parking suka shiga yana gaba tana biye dashi a baya har suka karasa part din Abba

yana zaune tare da Mami kasancewar ranar take da girki sallama yayi Abba ya basu izinin shigowa 

Suhail ya fara zama gefen Abba Iman ma ta zauna kusa dashi har lokacin kanta na ƙasa 

tun shigowar Mami ke kallon su to kodai Suhail Matsala ya samu da matar sa irin wanann samakon haka 

Abba ya kalli Suhail ya ce"har kun iso kenan"

"Eh Abba"

Iman ta dago kanta a hankali ta ce"Abba ina kwana"

"lafiya qlau Khadija ya gidan naku,ina fatan komi lafiya"

"Alhamdullilah Abba"

juyawa tayi wajen mami dan ta gaishe ta mami ta haɗe girar sama da ƙasa Tamkar taga abun ƙi 

"ina kwana"

shiru tayi ba tare da ya amsa ba 
Abba ya kalleta ya ce"Maryama bakiji ana gaishe ki bane"

"naji kawai banga damar Amsawa bane,kai tunda ka amsa ai shikenan"

shiru Abba yayi yana kallon ta 

Suhail ya gaishe da Abba ko kallan mami baiyi ba yayi hakan ne dan ya rama abinda Mami tawa Iman 

"Suhail ni bani da mutuncin da zaka gaishe sai ubanka ko dai Diyar malamai sun fara shanye ka"

"good morning"

ka rike morning dinka bani da bukata idan kaga dama kace Ni Maryama ba haihuwar ka nayi ba"

Abba ya kalli mami ya ce"maryama idan bazakiyi shiru ba ki fitar min daga daki"

dan haushi mami ji tayi kamar zata fashe ganin disgin da Abba yayi mata gaban Iman

Abba yayi gyaran murya ya kalli Iman ya ce"khadija Suhail yace kunyi Magana akan auren da yake so ya kara ko"

da sauri ta dago fuskar ta kalli Abba kamar bata abinda ya faɗa ba Suhail aure 

kallon Suhail din tayi duk yadda taso ta kalli fuskarsa ta ƙasa

Abba ya ce"ya ce kin amince to bayan yarda ba shi yasa nace kuzo tare dashi"

murmushi ta ƙanƙaro ta ce"Eh Abba ya faɗa min"

a yadda tayi maganar zaka gane karyar take kamar sai yanzu ne ma take samun labarin auren

Mami sai raba ido take ganin bata gane inda maganar Abba ta dosa ba Suhail din nr zaiyi aure.

Abba ya ce"masha Allah Allah ya tabbatar da Alkhairi ya baku zaman lafiya"

Mami ta kalli Abba ta ce"Alhaji Suhail din ne zai kara aure"

"Eh" kawai ya faɗa a takaice 

Mami ta juya wajen Suhail ta ce"wacece zaka aura Suhail"

"Diyar Alhaji ibrahim makama"

wata irin guda ta saki gaba lokaci daya suka kalleta ba kamar iman da tun maganar farkon da Abba taji kamar an chaka mata kibiya tun daga ƙasar zuciyar har zuwa maƙogoronta 

Mami ta ce"Ibrahim makama dai dana sani Ashe yana da diya mace kasan shekarar da nayi aikin hajji tare mukayi da Matar sa hajiya zainab diyar ta ce"

kai kawai Suhail ya daga

Mami ji tayi duk wani bakin cikin ta ya gushe duk wani haushin Suhail dake ranta ya wanke kansa ashe itama dan ta zai auri yar gidan Attajiri irin ibrahim makama Alhamdullilah ko ba komi ita yanzu ta sami surukar daga gidan masu kudi.

sai murmushi take ita kadai Abba ya dubi Suhail ya ce"dauki matar ku tafi"

idanunta suka cika da hawaye har komai ya fara mata dishi-dishi”da kyar ta iya kai kanta bakin mota 

Suhail ya shiga ya tada motar shiru ya mamaye motar ba wanda ya tan kawa ɗan uwansa

kofar gidan Malan Suhail yayi parking har suka tsaya ma basan ko ina suke ba 

kallon yayi ya ce"kije ciki anjima zan zo na dauke ki" 

sai lokacin ta lura da ina suke da sauri ta buɗe Murfin kofar ta fita ba tare data rufe ba a tsakar gida ta iske Ammi tana shara da gudu ta ruga jikin ta rungume ta saki kuka da tun a falon Abba take riƙe shi 

Ammi hankalin ta matuƙar tashe ta kalli Iman ta ce"Iman lafiya keda kuka zo"

batayi magana ba ta cigaba da kukan Ammi ta kaita daki ta mata Maganar duniya amman taƙi magana Ammi ta ce"ke banasan iya shege taya kin shigo kina kuka tun a waje nake tambayar kin ƙi bani amsa kinga bari na kira Malan yazo ƙila shi kin fada masa abinda ke faru"

hannu Ammi ta kamo dan kar ta kira Malan ko yazo bata san mizata fada masa ba 

"Ammi kawai banda lafiya ne" 

murmushin yaƙe Ammi tayi ganin damuwa karara kwance a fuskar Iman wanda na a iya rashin lafiya ta tsaya ba

"kuma baki da lafiya shine zaki shigo kina kuka"

goge hawayen fuskar tayi tare da sakin murmushi wanda iya karsa baki ta ce"Ammi ina Malan"

"ya fita" ta fada daidai lokacin tana miƙewa fita tayi baranda ta katse kwallar dake zubo mata haƙiƙa Iman na cikin tashin hankali abinda ta guda tun farko kenan kar a jefa mata ɗiya wani yanayin gashi bikin ko sati bai rufa Iman ta shiga damuwa wanda har ta soma koyan ɗabi'ar da bata dashi wato karya

sai da ta gama kukan wanda duk akan tausayin Iman ta koma bakin famfo ta wanke fuskarta ta koma ciki 

zaune ta samu iman tana game a wayar ta ta ce"da wa kuka zo"

"shi ya kawo ni ya ce anjima zai dawo"

"Allah kawo shi lafiya zaki ci dumamen tuwo"

"a'a ban jima dayin ƙari ba sai dai anjima"

"to shikenan bari na naje na karasa aikina"

Tashi Iman tayi ta ce"muje na tayaki"

Ammi na shara Iman tana wanke-wanke a haka malan ya dawo ya tarad dasu 


Hmmmm wani team iman ya kishi yake nema ya hallaka kune 😂😂😂💃🏿💔🤒 Irin wannan zafin kishi haka kuma kun iya cika baki a juri zuwa rafi dai hada masu uwargida mai mai capacity to Gaskiya ni dai banga capacity ba amman naga Authority a wajen Amarya zeenah🏃🏼‍♂️

Yau posting ɗaya zaku samu shiyasa nayi d yawa