GADAR TSAUTSAYI 7
by @nusybee143
Page 7
Da kallon banza Surayya ta bi ta, sannan ta dubi Hajiya Ruƙayya tana faɗin "Mamie wannan matar makira ce fa
Sai wani sumu-sumu take yi na munafurci
Duk abin da take yi da sanin Abba,ko ma na ce shine ya sahale mata,amma wallahi ba zata rinƙa taɓa Ni ina ƙyale ta ba"ta kalli buckets ɗin da Ummeey ta kawo ta yi fatali da ɗaya,alkakin da yake ciki ya zube,ta cigaba da sababi "yanzu haka ma wani barbaɗen ta yi a cikin wannan tarkacen da ta kawo kamar ana yunwa,ni wallahi komai da ta kawo min ma mayar mata shi zan yi,ta je ta bawa ƴarta, wadda mugun abin da take yi wa ƴaƴan mutane ya koma mata"
Hajiya Sa'adatu ta dube ta cikin kwantar da murya ta ce "kwantar da hankalinki Surayya,babu wanda ya isa ya yi muku wani mugun abu a duniya, yanzu ba sai anjuma zan mayar mata da kayanta,mu gaya mata ba ma bukata gaba ɗaya,ki kwantar da hankalin ki"
Hajiya Ruƙayya ta dube ta ta ce"A'a Hajiya Sa'adatu!
Kar ta haɗa mu da alhaji,a maimakon haka gwara mu zubar a shara,idan ma wani mugun abin ta yi Allah ya mayar mata kanta, kamar yadda ya mayar mata wancan karon"
Iman da ta fito daga ɗakin ta taɓe baki tana cigaba da danna wayarta,ita yanzu lamarin matar nan ya daina ba ta mamaki ma
Tsam Saleem da yake kallonsu ya miƙe, ba tare da ya yi magana ba ya fice daga ɗakin,sauran suka bi shi da kallo, Hajiya Ruƙayya ta ce"ji shashasha!"
Iman ta ce"manta da shi Mamie,zai dawo hanya ne,na ga yana nuna cewa shi na Allah ne "
"Mu kuma na shaiɗan ne kenan?"a cewar Surayya tana watsa mata wani kallo
Dariya Iman ta yi ta ce"oh Allah!
Ni fa ba da ke nake ba,amma kin ga abar maganar,mu je mu ƙarasa shiryawa, jirginmu ya kusa ɗagawa"babu musu suka miƙe suka shiga don ƙarasa shiryawa
Bayan awa guda suka fito cikin shirinsu don tafiya, Ummeey ma ta fito lulluɓe da ƙaton mayafinta a kan tsadadden lace ɗinta,ta dube su tana murmushi, kafin ta ce"ƴan makaranta!
To Allah ya kai ku lafiya,kun yiwa drivern magana?"
Babu wanda ya kula ta,sai Saleem, ɗa ga Alhaji Rufa'i ya ɗago yana kallonta, cikin girmamawa ya ce"ba driver bane zai kai mu Ummeey, Mummy ce,sai Mamie da zata raka mu"
Ummeey bata damu ba ta ce"to shikenan babu matsala,a wacce motar za mu tafi ne?"
Kai tsaye Hajiya Atika da ta zo wajen ta ce"a'a Hajiya Zainab,ba waje"ta dube su fuska babu walwala ta ce "ku wuce mu je ko?
Hajiya Zainab sai mun dawo mu kuma "
Jikin Ummeey a sanyaye ta ce"to Allah ya kai ku lafiya ya ba da abin da aka je nema,takwara, Allah ya tsare ya taimaka,a yi ta dagewa ko?
Allah ya kawo babban rabo na alkhairi"babu wanda ya sake kallon ta suka juya suka wuce suka bar ta a tsaye,har sun yi gaba Hajiya Sa'adatu ta dawo da baya,tana dubanta fuska a ɗaure ta ce"au!
Sai hakuri fa Hajiya,kayan da kika aiko yaran sun ce ba sa ci,to kin san sha'anin yara,shine kawai na ce a zubar,amma an gode "daga haka ta juya ta bar wajen ba tare da ta sake saurarar Hajiya Zainab ba
Da kallo sake da baki galala Ummeey ta bi ta da kallo, kafin ta ja ƙafarta jiki a sanyaye ta koma ɗakinta,sai da ta shiga sannan hawaye Masu zafi suka wanke mata fuska
Daɓas ta zauna a kan kujera, hawaye Masu zafi wasu na korar wasu,bata damu da sharewa ba saboda yadda zuciyarta ke tafasa da raɗaɗi
Ba tana jin zafin zuciyarta kawai don abin da aka yi mata ba, A'a har da tuna tata tilon ƴar da bata san inda take ba yanzu haka
Bata da wani ɗa da zata kalla ta ji sanyi na cin mutunci da gori da take fuskanta daga wajen kishiyoyi da dangin miji,ya ɗaya ta tilo ta haifa a duniya,itama wata mummunar ƙaddara ta raba su da ita ta wata bahaguwar hanya, wadda hakan ya janyo mata kallon wulaƙanci da ƙyama tsakanin kishiyoyinta, kowacce da kalar yadda take bayyana zargin gazawa ta fuskar bawa ƴarta tarbiyya
Bata da uwa babu uba,babu yaya babu ƙani,yayarta ɗaya gare ta, wadda tsawon shekaru goma sha biyar kenan da ta koma Egypt da zama,har yanzu ko sau ɗaya bata taɓa kawo ziyara na
Hakan bai ba ta damar sanar da ita halin da take ciki ba,a maimakon haka ma sai ta zaɓi ta yi ta addu'a babu dare babu rana,da niyyar Allah ya dawo mata da farin cikinta da ta rasa,ko da ace Shaheeda bata raye Allah ya yi mata rahama, sannan ya kawo mata sauƙin wannan wulaƙancin da take fuskanta
Ta so ta ja yaran kishiyoyinta da na dangin mijinta wadanda ƙaddara ta zaunar da su a waje ɗaya (maliya estate),amma hakan bai yiwu ba, sakamakon bambancin da iyayen suke nunawa kiri-kiri,yau da gobe tun yaran ba sa ɗauka har suka fara ɗauka,daga nan sai abubuwa masu kama da raini da wulaƙanci suka biyo baya
Tana sane da cewa idan ta kai ƙorafi wajen Alhaji Yusuf Maliya za'a ɗauki mataki,amma hakan zai sake haifar da wutar ƙiyayyarta da baƙin cikin ganinta a gidan, sannan kuma duk da hakan wasu ba sa yin abin da ya dace ɗin duk da tsanani irin na Alhaji Yusuf, kamar Surayya,har shakkar shiga shirgin yarinyar take yi ko da tsautsayi,don ma watarana idan ta yi mata banza take yi da ita
Lokacin da Shaheeda tana gidan babu wanda ya isa ya taka ta ya zauna lafiya, bata shiga sabgar kowa,daga karatunta sai na bincikenta,amma muddin aka samu wanda ya raina mata uwa lamarin ba zai yi daɗi ba, musamman da ya kasance ita ce ta gaban goshin Alhaji Yusuf,ko ɓoye soyayyarshi a gare ta baya iyawa sam
Dalilin haka ya janyo mata ƙiyayya daga wajen sauran ƴan uwanta,na yadda mahaifin nasu yake tattalinta,babu yadda Ummeey bata yi ba ya daina nuna mata wannan soyayyar ƙuru-ƙuru amma ya ƙi,da ya gaji sai ya ce "Zainab na ga ke ma kina adawa da babbar ƴata magajiyata!
Ko ke ma hassadar kike yi mata?
Kishi kike yi da ita?"daga lokacin ta ja baya da su, saboda akan Shaheeda Alhaji Yusuf Maliya bai ƙi ya ɓata da kowa ba,har mahaifiyarsa, wadda ta ɗorawa Shaheeda tsana hakanan babu gaira babu dalili
Har zuwa yanzu Ummeey tana kawar ƴarta,duk da maganganu masu zafi da muni da ta fuskanta daga wajen mutane hakan bai saka ta karaya ba,a kowanne lokaci tana fatan dawowar ƴarta,tana fatan ta sake waiwayarta,idan ma ta Allah ya kasance akanta tana fatan Allah ya ji ƙanta
Rayuwa kenan!ko ina makomar cikin da ta zo da shi a ranarta ta ƙarshe a gidan?hawaye Masu zafi suka zubo mata, Allah sarki Shaheeda!
A fili ta ce "ya Allah! Allah ka dawo min da Shaheeda Lafiya!idan kuma ta bar duniya Allah ka yi mata rahama!!!
Allah na san kana sane da ni, Allah na bar komai na rayuwa ta a hannunka, Allah ka yi min sakamako na alkhairi!!!"ta sanya hannayenta ta rufe fuskarta tana cigaba da kuka a hankali
*ROCKY ESTATE, KANO STATE, NIGERIA*
*HAISAM*
"Daddy!
Daddy jiya fa baka kawo min chaculate ɗina,kuma ka yi min alƙawarin za ka zo min da ita"
Kallon Amna ya yi, wadda kiri-kiri ta dasa masa rigima akan chaculate,ya ce"ho mamana!
Babu excuse ne wai?ki koma wajen Nanny ɗinki yanzu,zan tafi aiki, I promise yau dai zan zo da ta jiya da ta yau,idan kuma kika ƙi sai na ƙi tahowa da ita"
"Daddy you said promise ko?"ta faɗa tana kallonshi don son tabbatarwa
"Yes my dear!
I said promise,ki koma ciki,bana son ki rinƙa wasa da school,idan ba ki ci exams ba zan fasa siya miki new teddy fa"
Shagwaɓe fuska ta yi tana faɗin "Please Daddy!"ya ce"to koma ciki, ki gayawa Nanny ta ƙarasa shirya ki ki tafi wajen driver ya kai ki school,Ni zan wuce aiki,sai na dawo ko?"
Tana murmushi ta ɗaga masa hannu tana faɗin"Daddy Allah ya kiyaye hanya"yana murmushi ya ce"Ameen sweetheart!
Ke ma Allah ya kiyaye hanya"ya ja motarshi ya nufi gate,yana hango ta ta jikin madubi tana ɗaga masa hannu tana murmushi
Yana fita daga Rocky estate,ya hau titi kenan ya ji ƙarar wayarshi alamar shigowar saƙo,tashin farko bai yi tunanin komai ba,daga baya sai ya yi tunanin ko ɗaya daga cikin ƴan teams ɗin su ne waɗanda za suyi aikin kama Roxy,don haka sai ya yi tunanin ya buɗe idan ya samu wajen tsayawa
Babu jumawa hold up ya riƙe su,ya tsayar da mota ya ciro wayarshi yana duba message ɗin da aka yi masa
Sabuwar number ce,bai yi tunanin komai ba ya buɗe content ɗin message ɗin
"Kafin ka yi tunanin shiga rayuwar wani ka fara tsare taka jami'i,fatan nasara
NOCCM."
Shiru ya yi yana kallon wayar na ɗan lokaci, kafin ya yi wani yunƙuri wani message ɗin ya shigo
"Kada ka zauna kana nazari akan abin da ba shi da amfani,ka tuna cewa ba kai kaɗai kake rayuwa ba!
NOCCM"
Da gaggawa ya fara kiran layin,amma ya ji a kashe,yana ajiye wayar wani message ɗin ya shigo wayar,amma da wata number ɗin
"Ƙoƙarin kira kake yi?
Kar ma ka wahalar da kanka wajen kira,ba za ka samu ba,ka yi abin da aka saka ka
NOCCM"
Da sauri ya turawa Awwal number ɗin da aka kira shi kira na biyu,da gajeren message"Awwal yi min tracking wannan number ɗin"
Amma message ɗin yana shiga wani ya shigo wayarsa"bibiyar number ɗin za kayi?kar ma ka wahalar da kanka ba za ka samu ba
NOCCM!"
Yana kammala karantawa ya ja tsaki,amma bai kai ga jan numfashi ba wani message ɗin ya shigo da wata number ɗin ta dabam"a maimakon wasarere da za ka yi da saƙona,ko yunƙurin bibiya ta,ina son ka tuna cewa akwai yarinya ƴar shekaru biyar da ta fita zuwa makaranta ita da drivernta mintuna kaɗan da suka wuce,ya kamata a ce ka yi tunani akanta
NOCCM!"
Cikin Wata iriyar gigita da razana ya daki stearing motar ta shi yana kallon wayar tashi cike da kaɗuwa, kafin ya yi azamar fara kiran layin drivern Amna
Sai dai kuma wayar tana ta ruri amma ba'a ɗaga ba, hankalinsa ya tashi,take ya mayar da akalar kiransa ga Musa,Musa yana ɗagawa bai jira komai ba ya ce a gaggauce"Musa Please ka yi min tracking number ɗin Umar drivern Amna,yanzun nan"
Musa ya ce"I'm sorry Sir!
Amma ba ni da numbern "
Haisam ya daidaita nutsuwarshi yana goge gumi,ya ce"bari na tura maka"ya kashe wayarshi
Babu jumawa ya tura,yana turawa Musa numbern sai ga message ta wayar drivern Amna
"Don't bother yourself,wayar tana hannu na,ka yi ta ran ƴarka shine mafitarka,idan ka gwada taurin kai kuma ta baƙunci lahira, kuma yanzu ka fara ganin hakan
NOCCM!"
Cikin wani irin tashin hankali ya fara sauke numfashi da ƙarfi "kafin da ƙyar harshensa ya fizgo kalmar 'Hasbunallahu wa ni'imal wakeel!"ba tare da tunanin komai ba ya juya akalar motarshi zuwa makarantar su Amna
A bakin makarantar ya yi parking,ya fito kai tsaye ya nufi gate ɗin makarantar zuciyarsa cikin tsananin fargaba,a ranshi yana addu'ar Allah tsare masa ƴarshi ya yi masa maganin wannan azzalumar
A office ɗin headmaster ɗin makarantar ya sauka,bayan sun gaisa ya buƙaci ganin ƴarshi, ba tare da headmaster ɗin ya kula da yanayinsa ba ya ce
"Eh Rasheeda Haisam madaka tana cikin class ɗinsu yanzu haka,bari a kira ta"take ya aika a zo da ita
Babu jumawa sai ga su sun dawo da ita, Amna ta taho da gudu ta ɗane shi tana faɗin"Daddy!
Ka je aikin?
Yanzu muka zo makaranta,a hanya wasu mugaye suka tsare mana mota,ina ta kuka, uncle Farouk ya ce na daina kuka,ɗaya har da ce min beautiful baby I love you,suka ƙwacewa uncle Farouk waya suka tafi,shine uncle Farouk ya ce na daina kuka,shine ya kawo ni makaranta
Shiru ya yi yana jan ajiyar zuciya yana shafa kanta, kafin ya ce"to bari na koma ko?
Ko wuce ki je ki cigaba da karatu,me ma kika ce kina so?"
Ta ce"teddy da chaculate "
Haisam ya ce"consider it done ranki ya daɗe!"malamin da ya kawo ta ya ja hannunta suka tafi,ya dubi headmaster ɗin ya ce"idan driver dinta ya zo a ce su jira ni,zan zo da kaina na dauke ya"
Headmaster ya ce"okay Sir!"daga nan ya yi musu sallama ya tafi
Wannan karon ko da yana driving da ya ji shigowar message bai yi wasa ba ya duba, sabuwar number ce dai,cewa aka yi
"Na san yanzu hankalinka a kwance yake saboda ka tabbatar da cewa ƴarka tana cikin ƙoshin lafiya ko?
Ka kwantar da hankalinka, saboda wannan ba hari bane, gargaɗi ne, gargaɗi ne na abin da zai iya faruwa idan baka daina bibiyata ba because......
NOCCM!"
*Haisam zai daina bibiyar Roxy kuwa??*
A cikinsu wanene zai yi nasara tsakanin doka da laifi?*
#Nusy_bee