NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)

CHAPTER 38(something's in the air).

by @deejasmah

A hankali yace " tunanin siyan motar ne bai zo min tuntuni ba, saboda na ga kina da shi".

"Ko guda goma nake da su ai matsayin naka daban ne da sauran, but yanzu ai kayi tunanin siyan ko?".

"Ki yarda da ni Nadeefah ba fa don Fareesah zan siya ba, in ma baki yarda ba mu yi haka mana. A fara kawo naki sai a kawo nata daga baya".

"Saboda rashin adalci? Bayan albarkacinta nima zan ci? A kawo gabad'aya mun gode" ta furta tana zare jikinta gabad'aya daga rik'on da yayi mata,  sai dai bata wuce ba saboda kashedin da yayi zamewa tayi ta zauna a kan kujerar da yafi kusa da ita.

Biyota yayi inda take zaune yana cewa " Nadeefah mana, ki yarda da ni".

"Na yarda Yaa mu je in yi serving d'inka".

Kallonta yayi da kyau yana mai cewa " sai kin saki ranki zan ci abincin" idanu ta wara tana cewa " na saki raina fa Yaa, besides ni ban d'aure fuska ba i'm okay ko baka gani ba?".

"Na fa san ko ke wacece Wife, to kiyi murmushi okay?". D'an murmushin da ya fito da lob'awar kumatunta tayi tana cewa " now, let's go". Hannunta ya rik'e cikin na shi suka nufi dining d'in, serving d'in shi tayi da kanta ta zauna. Cikin sanyi suka ci abincin babu yanda ta saba jan shi da hira ko ta takalo shi, suna gamawa ta kwashe kayan ta kai kitchen ta wanke ta fito.

Yana zaune kan one sitter yana waya, hannu ya mik'o mata ta kama tana kallon fuskarshi. Jan ta yayi ya zaunar kan cinyarshi yana mai cigaba da wayar, ido ta zurawa gashin kan shi dake k'yalli tana mai mamakin yanda bai gajiya da gyaran kai da kuma yanda in yayi sabon aski ko gyara bai cika son ta tab'a ba a da amma a yanzu har so yake ta tab'a kan. Hannunta ta tura cikin gashin tana d'an mik'ewa kad'an ta fara kitsawa, murmushi yayi a can k'asan mak'ogwaronshi yana mai rad'a mata " hannayen ki sun yi daɗi a kan " kamar ba waya yake yi ba. Itama irin murmushin tayi tana cigaba da abinda take yi.

Bai ma dad'e ba ya ajiye wayar suna canja wata tasha maganar mota kuma aka kasheta a nan wajen, a d'akinshi suka dire sauran batu sai ma da suka natsa ne suka d'auko Sairah daga parlor aka kashe wuta suka sake kwanciya cikin juna kamar sa maida juna ciki. Washe gari tare suka tafi da ita asibiti kai breakfast shi ma kamar jiya ba su dad'e ba suka koma gida, d'akinta ta wuce shi kuma ya duba Fareesah ya dawo suka sake kwanciya sai after 2 ya kwashesu su duka suka tafi asibitin kamar ranar farko ma yau ba ta saka musu baki a hira ba sai jan Yusairah take da wasa ita ko 'yar garin ta k'i zuwa ta mak'ale Babanta sai Lele ce ma tayi driving zuwa clinic d'in.

Tana gama parking ta fita da niyyar d'auko basket d'in abincin da ta kawo, bai fito ba ta cikin madubi ya dubi Fareesahn yace " ke baki kawo komai ba ne?".

"Me zan kawo?".

"Tambayata kike? Ba ki san mara lafiya zaki zo dubawa ba? ".

"But baka ce in kawo ba".

"Sai nace? Sai nace fa kika ce? Ke baki da hankalin kawo abinci asibiti sai na saka ki? Ita Nadeefahr sakata nayi?".

"Ai ban sani ba ne shiyasa, i'm sorry gobe zan kawo".

"Kar Allah ya sa ki sani Fareesah, sannan kar ki fara tunanin kawo mai wani abu don bai buk'ata ki rik'e kayanki asibitin ma ba ki sake fitowa".

"Haba babe, i'm sorry".

Tsaki ya ja ya fito yana buga k'ofar da k'arfi, Nadeefah da har ta kai main entrance d'in shiga ward d'in su Abba ne ta waigo tana kallonshi. Ganinshi tayi yayi mugun d'aure fuska zata iya rantsuwa da huci yake yi daga yanayin fuskar shi, duban gefen da Fareesah da ta fito daga motar tayi itama da d'an fushi a fuskarta don gani take yi kawai ya shirya tijarata ne a cikin familyn shi just saboda ƙaramin abu wai abinci saboda wata tsiya ce a abinci da don bata kawo ba zai zama masifa. In ma bata kawo ba ai wasu suna kawowa ba kuma wai na ta ake jira ba, ko ita matarshin da take wahala ai neman gindin zama ne da S mai lank'wasa in ba haka ba miye wani na kai abinci bayan akwai su da yawa da har za a sakata a gaba kan shi. ( wai neman gurin zama? Da alamu dai Fareesah bata san wace Lele da capacityn ta ba. Ba ta san Lele 'yar gaban goshin Yerwa ba ce ba kuma ta buk'atar wani gindin zama daga kowa ko tayi wani abu da zai saka a sota daga Allah ne da kuma halayyarta da suke natural tana da kirki da girmama kowa, uwa uba mugun soyayyarta ga familyn na su so Fareesah ta natsu kafin askarawan Yerwa su cimmata a kan Nadeefah👽).

Shi ko dalilinshi na magana saboda ganin yanda Nadeefah take k'ok'ari ne ranar farko har da fruits d'in ta a manyan ledoji, duk da ya san ba zai yi comparing d'in su ba don ita ƴar dangi ce amma kuma atleast sai ta kwatanta ko sau d'aya ne ko don shi ɗin ma don in ta kyautata musu shi tayi mawa. Tsaki ya kuma yana sake rik'e Sairah da kyau ita kuma ganin Lelen na dubansu sai ta saki fuska tana k'ok'arin jerawa da shi gudun ta zargi wani abu, bai ko kula ba ya bi bayan Lele da ta shige yana amsa gaisuwar maaikatan da ke kaiwa da komowa a ward ɗin.

Yau da d'an sauk'in hayaniya a parlorn kasancewar su Baba Tijjani suna ciki sai dai kamar yanda suka zauna jiya haka yau ma suka yi, su Ya Budu circle d'in su daban haka su Fadwaah da Najwaah suma sai Suleim da Zulfaa da suke wata maganar. Tana shiga Zulfaa tace " yau dai kinyi latti Babe".

"Toh ta tsaya shirya Ya Islaam kin san ita take da girki".

"Kai dan Allah, ki ce kin zauna saitawa Yayanmu hanya while ......." Ta kasa k'arasawa ganin Islaam d'in ya shigo duk da ba da k'arfi take ba amma ba a hankali take yi ba kun san Zulfaa akwai karad'i. Shi ko kallo d'aya ya musu yana amsa gaisuwar ta su, dariya ta saka tana cewa " zaki sani ne " itama dariyar tayi tana yin k'asa da murya tace " ga tinkiyarki nan tahowa" girgiza kai tayi tace " Allahu yahdiki". 

Bayan shi ta bi a dai-dai k'ofar shiga main parlorn suka had'u da Safwaan dake fitowa yana ganinta ya washe baki yana cewa " Oyoyo Auntyna dama ke nake ta jira tun d'azu".

"Lallai ma Yaa Safwaan d'in nan toh sai dai ka yi ka gama ko cokali ba ka samu" ta k'are tana murgud'a masa baki, harararta yayi yana cewa " in kin isa me nake, don ma kin ga nace miki Aunty".

"Ai dama na san ba don Allah kace ba, dad'in abun ma ni ma ban so".

Zai bata amsa Burhaan da a sama yake yace " zaka ba mutane hanya ko zaka tsaya kana zuba ne?".

Matsawa yayi daga hanyar suka shige shi kuma ya karb'i basket d'in hannunta yana cewa " mu je kin ji K'amshi" shiga suka yi da sallama, nan suka tarda kusan kaf iyayen a zaune sai Umma dake gefenshi da alamu hira suke yi don har Abban murmushi yake yi,  shigowar tasu ne ya sa duka suka dube su Lele da murmushinta mai kyau take cewa " Wani sabon re-union ake yi a clinic d'in nan kenan".


Daddy senator dake gefen Abbu yace " sai fa reunion".

Safwaan yace " kuma suka kore mu waje ba".

"Kai da ka mak'ale ka k'i fita?" Fad'in Baba Adam yana murmushi Umma ko cewa tayi " ba aikenka ma aka yi ba? ". Kai ya dafe yana cewa " na manta ne fa, K'amshi amanar abincina a hannunki yanzu ma zan dawo".

Duka suka saka dariya jin yanda yayi maganar kace wanda yayi sati bai ci abincin nan ba, kai Umma ta girgiza tana cewa " tunda baka ci abinci ba ne zaka gaya min". Juyawa yayi ya fita yana cewa " ni dai kar a tab'a min abincin K'amshi ahh toh". 

Sai lokacin suka samu natsuwar gaisawa da juna suna mai sake tambayar jikin Abban, duka a sake suka amsa gaisuwar suna tambayar Fareesah ya gida. Ita ko Lele kallon Abbu tayi tana cewa " Abbu ban ga Ummu ba".

"Su na hanya da su Tayyib". Kai ta gyad'a ta wuce kusa da Abba abincin ta ajiye tana cewa "Abba yanzu za a saka abincin ko sai anjima?". 

"Sai anjiman dai after ten fa nayi breakfast an sake min FBS ne". 

Sai lokacin Islaam yayi magana yana mai cewa " ba su zo k'arban sample d'in da wuri ba ne?".

"Jiya da urine suka yi yau ne suka yi da jini".

"Still zasu iya yi 8 or 9". Baba Adam da yake Dr. ne yace "ba su yi latti ba ai". Kai ya gyad'a yana cewa "yeah".

Sun d'an jima a d'akin har Ummu da su Tayyib har da ma ElSadeeq da jiya ya shigo da dare suka shigo room d'in nan fa Farhaan ya dinga saka su dariya musamman da Safwaan ya dawo suka had'u da Dalhat. Babu kalar shakiyancin da basu yi ba, sai da Islaam yace su fita waje sai kawai 'yan wajen kamar an kirasu suma suka shigo, haka ya zauna ya zura musu idanu suna yi su Abba na biye musu sai da aka kira Asr kafin kowa ya fita daga d'akin zuwa masallaci.

Yau bai wani zauna ba don fitarsu suka yi da su Farhaan, sai kusan magrib suka dawo shi ma yana duba Abban ya fita suka tafi zuwa gida. Kamar jiya yau ma simple dinner tayi musu na fried cous-cous with assorted meat Zob'o ta had'a da yaji kayan k'amshi ta saka shi a fridge. Wanka tayi ta zura bodycon ta tada sallahr isha'i, da ta idar zama tayi ta shayar da Sairah sai da tayi gyatsa ta cireta wanka ta yi mata wanda kafin ma ta fito har ta tayi bacci kayan barci ta saka mata da diaper ta kwantar da ita.


A parlor ta tarda shi zaune yana kallo zama tayi gefenshi tana masa barka da dawowa, amsawa yayi yana tambayarta princess shaida masa tayi da tayi barci da kai ya amsata ya cigaba da kallo. Dubanshi tayi tana cewa " ba yanzu zaka yi dinner ba?" Ajiyar zuciya ya saki yace " mu je tohm" tsura masa ido tayi ganin kamar ranshi a b'ace ne tace " Ya akwai abinda yake damunka ne?".

"Babu" ya amsa yana mik'ewa, hannunshi ta kama tana murzawa a hankali tace " ka yi hak'uri tohm, dan Allah". Kallon idanunta yayi yace " ba fa abinda kika min".

"Amma wani ya b'atawa annurin gidanmu rai, in fuskarka ba bata da haske ina mu kuma zamu je mu ga hasken? Duk yawan lights and chandeliers d'in gidan nan d'aukewa suke yi don murmushin ka ne maɗanfarar ɗorewar hasken su" ta furta tana shafa kafad'anshi cikin sigar lallashi.

Numfashi ya sauke a hankali ya kai hannu ya rungumota zuwa jikinshi, a hankali yace " ta ya kike son in cigaba da fushi?".

"Dama ai ba ma son fushinka Yayanmu, Alphan mu " ta amsa tana sake rik'oshi hannunta a bayan shi tana shafawa sama da k'asa while bakinta yake saitin kunnenshi don d'age tayi da k'afafunta tana hura mai kunnen kamar yanda akewa yara in ana rarrashinsu. Hakan kuma affecting d'in shi yake yi sosai, cirata yayi sama yana cewa '' daga lallashi kuma sai tura saƙo?".

Dariya tayi tana cewa "baka so ne?".

"Ni ko nake so duk da ɗaga min hankali da yake" ya amsa da wata murya a hankali, zare jikinta tayi tana pecking d'in shi a cheeks tace " let us eat" uhm ya amsa yana rik'e hannunta suka k'arasa kan dining d'in, a sake suka ci abincin tana ta bashi labari don ya sake duk da ta san ya daina fushin amma tana son yayi mata 'yan wasannin da ya sabawa kan shi a yanzu kuma tayi nasara don sosai ya saki jikinshi suna gama cin abincin dai bai je d'akin Fareesah ba wanda ba ta sani ba don a tunaninta ya mata sallama kafin ya shigo d'akin nata.

Washe gari around 10 aka sallami Abba hakan ya sa ba ta fita ba sai 3 don Islaam d'in ma bai nan tunda ya fita da safe bai dawo ba, lunch dai ta ajiye masa should incase zai dawo gidan da wuri. Ta baza wanka ta d'auki 'yarta sai Yerwa, a nan gidan Umma ta sauka sai da 4 ta wuce gidan Ummu nan ta dinga shiriritar dake a halinta suna ta ta rigimarsu da Dalhat. Shi dai Tayyib kai ya girgiza kawai don ya tabbatar babu ranar da zasu daina wannan rigimar, yanda ka san su ne aka haifar rana d'aya ba da shi ba. D'aukar Sairah yayi yana sake lafewa a cikin kujerar idanunshi kan wayarshi da yaketa latsawa.


Magrib ta kwashi jiki zuwa gidan Hajjah ita d'aya ta sameta yau abokan hirar tata ba su zo ba, tana shiga ta ware hannaye tana cewa " ga tagari nan a bayar muguwa". Baki ta murgud'a tana cewa " ai kuma tunda kika samu wannan karin maganar mun bani Hajjah, kai jama'a" ta k'arashe tana mai dafe kanta.

Dariya Hajjahr tayi tana cewa " toh k'arya aka yi ba muguwar bace?". 

"Bari dai in koma in da na fito Hajjah, da alamun ba'a buƙata ta yau".

"Duk inda zaki tafi Allah ya tsare ni dai ki bar min tagari".

"Ai dai ni na haifeta don haka ban bayassuwa, ki je ki nemi wata tagarin".

Yana ce ta fito daga kitchen tana sakin dariya kamar cikinta zai k'ulle jin maganar da Lelen tayi itama Hajjahn rik'e baki tayi tana k'ok'arin danne dariyarta. Ita ko ganin suna mata dariya sai tayi k'wal da idanu tana cewa " kwa maidani mahaukaciya mana, dama ai Hajjah bata nemo ni ba ni na kawo kaina".


Ta furta tana juyawa da nufin barin mata gidan don sosai take jin haushin wannan karin maganar, ta kuma ji zafin yanda Hajjahn tayi amfani da shi. Yana ce ta danne dariyarta tana cewa " uward'akina ayi afuwa mana, wasa ne fa Hajjahn take miki".

"Wani irin wasa kuma Yana kina ji tana kirana da muguwa kina cewa wasa".

"An kira ki d'in Lele ba dai har ni kike gayawa cewa ita 'yarki ba ne".

"Eh mana, tunda ni muguwa ce to a bar min duk kayan da ya fito daga hannuna ehe".

"Dad'in abun nima dai na haihu da na shiga uku da gori".

"Kiyi ta haihuwan mana, ai dai baki haifi Sairah ba".

"Amma na haifi Isufa".

"Uhmmm, toh ai kowa ya sani ba sai kin tuna min ba".

"Nima na san kin haifi Yusairah ba sai kin tuna min ba".

"Yana wai waye ya zo gidan nan ne yau?".

"Y'ay'ana ne suka zo me aka yi" Hajjah tayi karaf ta amsa kafin Yanar ta bata amsa, k'wafa tayi tace " ba su kad'ai ba ne suka zo an samu wasu masu adawa da ni da ke sun zo gidan nan and sun fara k'ok'arin shiga tsakaninmu wayyoni Hajjahta" ta k'are tana sakin wani ihu mara k'ara.


Dariya Hajjah tayi da jin abinda ta fad'i tace " ai ko sun kyauta don kin isheni dama".

"Toh wallahi Hajjah kin ja ma ba inda zan tafi, ina nan sai dai su mutu".

"Ashe baki da zuciya ".

"Ko ma menene ma a ce, ai ba gidanki bane ke kad'ai , nima ina da d'aki a ciki".

"Nan kuma kikayi k'arya don nan gidan mijina".

"Masu miji".

"Eh kema ki tafi naki gidan mijin".

"Naji gidan mijinki ne amma ba inda zani in ma na ga dama in kwana ba kuma don ke zan kwana ba".

"Ba dai zuciya dai Lele in da ni ce ke da gidan mijina zan tafi yanzu".

"Ba inda zan je" ta furta tana ajiye Sairahn ta nufi hanyar kitchen tana cewa " na ma lura akwai abinda aka ajiye a gidan nan shiyasa ake korata". Dariya suka saki ita dai ta shige jim kad'an sai ga ta da bowl da ta sako Alalen manja da suka yi sub'u-sub'u da su sun kuma ji kayan had'i da zafinsu don da ba a dad'e da saukewa ba, ta zabga danderu a gefe  tace " ai na sani dama kora da hali ake son yi min".


"Waya ce ki tab'a mana abinci?" Inji Hajjah tana rik'e da Sairahn da ta ajiye da zata shiga kitchen d'in, baki ta murgud'a tace " Hajjah ni fa ba wurinki nazo ba yawwa".

"Hajjah a dai yi hak'uri haka".

"Yana, ki daina bi ta kan wannan uwar rikicin yaya ne ban yi da ita kan zuwa gida na ba tun da aka yi bikin nan ba, sai wulak'antani take yi kamar ni nace a mana kishiyar".

"Ni fa Hajjah fa 'yan zuwan nawa ne basu zo ba, but kin san nayi missing ɗinki kuma ma ni ko ke kika ce a min kishiya ai ko a jikina tunda ni dai mijina bai canja min ba sai ma soyayyan da ya k'aru so ko a jikina" ta furta tana juya idanu.

Dariya Hajjah ta yi ita ko Yana ta wuce kitchen cewa tayi " zo ki bani in shaa mutumiyar, ashe haka aka yi?".

Baki ta murgud'a ba tareda ta dubeta ba ta cigaba da cin abincinta, Hajjah tace " kin ga abinda nake fad'a miki ko? Komai in bawa ya fawwalawa Allah sai kiga ya warware kamar ba a yi ba, yanzu in da kin d'agawa Islaam hankali da ba wannan zancen ake yi ba".

"Haka ne Hajjah but babu sauk'i fa, har yanzu ma ina fama da hakan na kasa sabawa".

"Ai ba sabawa ake yi ba juriya ce sai kiga kamar ba a yi ba".

"In shaa Allah" suna kamo wata hirar, ba ita ta bar gidan ba sai after magrib shi ma sai da Islaam ya kirawota yana shaida mata duk inda take ta koma gida yanzu. Cikeda tsokana tace " ni fa kwana zan yi" amsa ya bata da "kar ki yarda in dai baki kwana ba" yana kashe wayar dariya tayi tana mik'ewa sallama tayi wa Hajjah ta wuce gidan Ummu shi ma ba ta wani zauna ba a sama-sama tayi mata sallama ta wuce gida.

Tana parking yana fitowa daga part d'in da alamu masjid zai wuce don ana shirin tada sallahr ishai, bai dubeta ba yayi wucewarshi ita kuma k'ofar da ya fasa sawa key ta bi ta shiga ciki.


Wanka tayi ta yiwa d'iyarta itama dukansu ta kimtsa su cikin shirin baccin da ya dace da yanayin da ake ciki, kana ta sanya hijabi ta hau kan dadduma ta tada sallah. Tana kan daddumar ya shigo cikin d'akin zama yayi yana wasa da Sairah dake nan zaune kan carpet tana kallo, da ta idar ma kamar kullum ta dad'e sai da ta kammala abinda ta saba kafin ta taso ba tareda ta cire hijabin ba.


Dubanta yayi yana cewa "na zaci ai kwanan da kika ce zaki yi?".

"Na so kwanan ma, jin har da bak'ar magana ne ya sa ban kwanan ba" ta amsa tana kaiwa zaune fuskar nan a marairaice kalar tausayi.

"Ke yanzu in aka barki sai ki kwana?".

"Da gudu ma, baka san yanda nayi missing kwana a can ba".

"Toh ki daina mafarkin kwanan, don abu ne da ba zan taɓa bari ba" ya bata amsa cike da seriouness.

"Haba Yaa, but why?" ta sake fad'i a marairaice.

"Muna gari d'aya sai kawai in barki ki kwana a wani gidan? Ai lalacewata bai kan nan ba".

"Yayana ba fa lalacewa ba ne, gidan mu ne fa or gidan Hajjah bai wuce ɗaya daga cikin ba fa ni d'aya ba ce yanzu kuma yau ba girki na bane".

"Da yake amfaninki a gidan bai wuce ranar girkinki ba ko? Sai ki tashi yanzu ma ki koma" ya na fad'in haka ya mik'e ya nufi k'ofa, mik'ewa tayi itama tayi ta biyo shi zuwa parlor tana cewa " Allah Yaa ina son kwana ne".

"Ai nace ki koma kuyi kwanarku".

"Ba da gaske kake yi ba, gatse kake min".

"Au da gaske kike so in faɗi? Ke fa na lura kan nan naki har yanzu da sauranshi".

"Allah Yaa kaina a dai-dai yake".

"Toh nima nawa a dai-dain yake ba kuma zan yarda muna nan gari ki kwana a wani gida never, ta ya ma hankalina zai kwanta kina wani gidan ni ina nan? Ko baki san sukunin samunki a ƙarƙashin inuwa ta kad'ai wani babbar arzik'i ba ne ko da ba kullum muke kwana tare da? Na ki sani ba ko?".


K'amewa tayi a tsaye tana tunanin mai maganganunshi suke nufi ta gaza, murza hannunta da ba ta san yaushe ma ya rik'e ba ya rankwafo ya d'an yi kissing lips d'in ta for some minutes yana cewa " good night" daga haka ya juya ba tareda ta gama dawowa hayyacinta ba, da idanu ta raka shi har ya fita ajiyar zuciya ta sauke tana jingina da jikin k'ofar da ya fita tana mai jin wani abu a jikinta in ta fahimci mai yake nufi tohm yana nufi bai son tayi nisa da shi balle har ta kwana a wani gidan ba na shi ba, kuma zamanta a cikin gidanshi yana nufi wanisalama gareshi?.

Lumshe kyawawan idanunta tayi tana cewa " i too love you Yaa Islaam ina fatan hasashena ya zama gaskiya wato ka fara jin abinda nake ji a kanka Allah ya sa ranar nan ta kusa zuwa kusa". Ta dad'e a tsaye cikin shauk'in k'aunar da ya sake tada mata wanda dama ba wai nisa yayi ba, adana shi take yi tana mai jiran ranar da zai gwangwajeta da na shi soyayyar don itama ta fito masa da tanadin da tayi masa na so da k'auna mafiyin wanda take nuna masa a yanzu don a tanadin da tayi masa ko kaso 20 bata nuna ba. 


(Au yanzu duk wannan love da ake kashe Islaam da shi bai kai rabin tanadin da aka yi masa ba, ashe randa za'a nuna masa ko 50% ne sai ya kusa mutuwa. Islaam d'an gatan Lele).

Juyawa tayi ta shige ciki bayan ta rufe d'akin, kwanciya tayi ta rungume Princess tana mai sake nink'aya a kogin son mijin nata da jin ina ma yau ranarta ne yayi mata wannan kyakkyawar albishir d'in? Da sai ya manta inda kan shi yake shakka babu a daren nan, ta dad'e a wannan yanayin kafin barci ya kwasheta.
2 days tsakani aka kawo motar ta su, lokacin da aka kawo both ita da shi suna office. Da yake a nan wurinsu Maheer Yerwa ne aka kawo motocin sai suka kai masa gida kai tsaye bayan sun musu duk abinda ya dace,  Umara aka bawa car keys d'in suka juya suka tafi.

Ya rigata dawowa don 3:30 ya shigo dudduba motocin yayi iri ɗaya ce Mercedes Benz ce dukansu color ne ya banbanta su d'aya black ce d'ayar kuma Ash duka tinted glass har da plate numbers d'in da da kanshi ya kai musu duk an saka, ba abinda ya ragewa motocin nan sai had'uwarsu da masu su. Ita kuma Fareesah bai ma da tabbacin ta iya driving balle a kai ga samun license, bayan haka babu abinda ya rage keys d'in ya amsa ya zuba a cikin motar shi ya shiga wajen Fareesahr.


Sai da tayi Asr a office ta dawo a matuk'ar gajiye don tayi aiki yau sun sauke kaya ga lissafin da suka yi. Kanta har ciwo yake mata hakan ya sa ko da ta shigo bata lura da motocin ba parking kawai tayi tayi wucewarta ciki.


A nan waiting room kan sofa suka baje ita da Sairah har ma da jakar da ta fita da ita tana maida numfashi kamar wacce tayi dogon tafiya a k'asa d'in nan, sai da ta d'an samu sukuni kafin ta rik'e hannunta suka wuce ciki. Rigar jikinta ta cire ta bar best kawai ta sanya kan skin tight d'in ta fito, kitchen ta shiga tana nazarin abun dafawa ganin tunanin bazai fishhe ta ba sai kawai ta fiddo basmati rice ta ajiye. Sauran kayan had'inta ta fiddo da duk abinda zata buk'ata kasancewar tana da veggie mix ya sa bata yanka su ba sai peas da ta k'ara don tana son shi sosai.


A cikin abinda bai fi 50 minutes ba ta kammala egg fried rice da ta wadatu da veggies, sausage da ma liver. Kazar da zata had'a Spathcock chicken roast with herb potatoes ta kammala dressing tana shirin sakata a oven ya shigo kitchen d'in, hannu ya d'aura a k'asan mararta yana mai sak'alota jikinshi.


Waigowa ta d'an yi tana sauke ajiyar zuciya tace " barka da dawowa" kai ya d'aga yana cewa " ke za ai wa barka ai, as for me tun kafin Asr na dawo kuma da alamu kin gaji".


"Sosai, Yaa yau na gaji sosai saboda kayan da aka sauke yau. Sai da muka yi sorting komai  ga kuma kayan azumi da za a kawo maybe gobe".

Murmushi yayi yana cewa " gaskiya aikin da yawa wife, Allah ya k'arbi ayyukanki ya baki lada ya kuma k'ara bud'i".

"Ameen Husband dukanmu baki d'aya, ina so mu je umrah ni da Sairah fa".

"Ki bar shi ki je Hajj mana, amma banda Sairah don lokacin yayeta zaki yi ai ko".

"Bayan sallah zan yayeta in shaa Allah, sai sa nake son mu je tare".

"Bari mu gani tohm" ya amsa yana d'aga hannunshi daga mararta zuwa kafad'unta yace " now guess what?".

"What, Yaya" ta tambaya cike da murna 

Turb'une fuska yayi cikin wasa yana cewa " guess aka ce madam, ba wai ki tambayeni ba".

"Allah Yaa ba wani iya guessing nayi ba".

"Ba wani nan " janye jikinta tayi daga na shi a kunyace tana buga k'afa a k'asa tana cewa " ni dai Yaa, ni dai" shi ko dariya ya sake mai d'an sauti kad'an yana kallonta cike da bayyanniyar birgewa. 

Sai kawai ta juya ga abinda take yi kazar da ta ajiye akan baking tray, sai kawai ta saka a oven tayi setting time. Gloves d'in hannunta ta cire tana d'auraye hannun har lokacin dubanta yake yi, hannunshi ta rik'e tana cewa " Yaa ba ka gaya min ba".

Jan hannunta yayi suka fito waje, sai da ya d'auko mata hijabi ta sanya kafin suka fita wajen tsayawa tayi tana zurawa motocin idanu like wow duk da tana da wacce ta fisu tsada amma tana jin ba'a taɓa mata kyautar motar da ta shiga ranta kamar wannan ba. Tsalle ta daka ta rungume shi tana kissing d'in fuskarshi ta koina, ba tareda ta damu da in da suke ba bai ko hanata ba sai jin wani nishad'i yake yi na yanda take farinciki da kyautar shi wanda bai expecting ba don ya tabbatar ta fi k'arfin wannan motar. Sai da ta gama tsalle-tsallen a jikinshi kafin ta d'ago kai tana cewa " Thank you Yaa, Allah ya k'ara bud'i ya biya buk'atu".

Ameen ya amsa yana cewa " now wanne kika zab'a the black or the.....?". 


"The black ofcourse" ta amsa tana tsalle dama saboda ita ya kawo black d'in sun tab'a magana da Fareesah tun kafin aure ta nuna masa tana son Ash ko silvern car ita kuma ya lura da yanda take son hawa bak'ar Lexus d'inta tun ta gida sai farar Aventadorn da ita ce aka basu ta biki ita kuma electric car ce babu ruwanta da fuel chaji kawai ake mata, dukansu shidan da su Farhaan farare aka kawo musu ita kuma d'ayar red d'in Mercedes d'in ba ta cika hawa ba sai ta fi wata ma bata dubeta ba duk da kuwa ta fi Lexus d'in sabunta.

Keys ya mik'a mata a ɗokance ta amshe bud'e motar tayi ta shiga sauke glass tayi tana cewa "zaka shigo in ɗan ɗana ka?". Murmushi ya saki yana cewa "sosai ma kuwa, na ko gode" bud'e sid'e d'in passenger yayi ya shiga, jan motar ta fara tana murmushi kamar zata cinye cheeks d'in ta dake lob'awa. A kan street d'in su take ta shawagi sai kawai ta tuna ta bar yarinya a gida da abu a oven da sauri ta juya motar zuwa gida, tana gama parking sai da ta kamo shi ta sake kissing kafin ta fito daga motar tana sake maimaita thanks.


Tare suka fito daga motar ita tayi sauri ta wuce ciki shi kuma ya nufi part d'in Fareesah don bai shaida mata da an kawo mota ba ya bari ne Lele ta fara zab'a, ita ba ma ta san za'a siyan mata motar ba balle.

San da ta koma ciki saura minti biyu a time d'in ta sakawa oven d'in sai kawai ta kashe don ta tabbatar da ya kammalu ta fara had'a herb potatoes d'in da gravy da zasu ci da shi sai morrocan salad mai d'an yawa ba ta da k'arfin yin wani drink sai kawai ta had'a normal mint, lemon and apple mojito kamar kullum a kan chiller ta d'aura shi da cups d'in ta kwashi kayan ta fita.

Babu kowa a parlorn sai kawai ta shirya dining a tsanake amma banda chicken d'in da drink kana ta kinkimi Sairah da ke barci suka shiga ciki, wanka ta samu tayi fitowarta ana kiran sallah sai kawai ta hau dadduma sai da ta idar tayi shafa ta shirya cikin wata velvet gown brown mai k'aramin hannu ya kuma bi jikinta da kyau ya zauna cif ba ta kai ga fitowa ba ma Sairahn ta tashi sai kawai ta koma toilet da ita wankan barci tayi mata ta shiryata sai da tayi ishai ta fito.


Shi ko yana shiga part d'in Fareesahr tana zaune da kayan da ya barta da su fitted gown da ya mugun zaunawa a jikinta kamar ba ita ba, ya ko bi curves d'in jikin ya manne da kyau kanta ba d'ankwali sai veil da ta yafa d'an k'arami kallo take yi a zee prime hankali kwance. Daga bakin k'ofa yace " Cherrie".

D'agowa ta yi da murmushi tana cewa " Lifeline, na zaci ka wuce fa".

"Yes, yanzu zan wuce wani abu zan nuna miki kafin in tafi".

Lumshe idanu tayi ta bud'e tana cewa " in taso kenan?".

Kai ya gyad'a yana cewa " sure " da sauri ta taso ta k'araso wurinshi hannunta ya rik'e suna jerawa zuwa wajen sai d suka kusa wajen motar ne ya sa hannayenshi duka biyun yana rufe mata fuska, a haka suka k'arasa a tsanake kafin ya tsaya yana cewa " you ready?".

"Yes Babe" ok ya fad'i yana zare hannun daga fuskarta da mugun mamaki take bin motar da kallo, matsawa tayi daga jikinshi ta jingina da motar shafawa tayi ta juyo tana cewa " you don't mean it Babe!!".

"Yes i do, taki ce Cherrie" ya fad'i yana girgiza mata car keyn dake hannunshi, da sauri ta amshi keyn tana cewa " omggg, Fareesah taki ce, taki ce ". Zuba mata idanu yayi tana d'okin bud'e motar shiga ciki tayi tana shafa seats komai ya nuna kuɗin da aka siye ga ga shi kalar da take so, turo kai tayi ta window tana cewa " Babe ka zo ka d'ana ni a motar nan, abun haushin ban iya driving ba".

"Ai yanzu dole ki iya" ya bata amsa yana duk'awa dai-dai glass d'in da ta sauke.

"Dole kuwa".

"Toh ya kika ganta" ya tambaya jin har yanzu bata ce uffan akai ba, sake washe baki tayi tace " tsaf Babe, daidai yanda nake son mota. Ka san ban son colors d'in mota nafi son matured color" tana furta hakan tana scanning motocinsu dake parke a garage d'in duka babu na banza sai kawai idanunta ya fad'a kan ta Nadeefah, dubanshi tayi tana cewa "Babe wancan ta waye?".

"Ta Auntynki Nadeefah ne".

A take duk murmushin da ke kan fuskarta ya d'auke yayinda takaici ya maye gurbin shi, wai ta Nadeefah ita wai yaushe ne wannan matar zata daina mata shiga sharo ba shanu ne. Ya za'a yi mijinta ya siya mata kyautar amarci amma sai an had'a da wata munafuka wai Nadeefah?.

Kallon fuskarta yayi ganin ta sauya lokaci guda yace " lafiya?".

"Oh yeah" ta amsa sannan cikin sanyin jiki ta fito daga motar ta nufi cikin gida, ido ya tsura mata yana mamakin sauyawar nata ya bi ta a baya don bai san dalili ba. A inda take zaune d'azu ya tarda ita tana zaune tana jijjiga k'afafu, tsayawa yayi a kanta ya rik'e k'ugu yana cewa " me aka miki ne Fareesah?".

D'ago kanta tayi tana cewa " nothing".

"Nothing kike ce min? In kawo muku motoci kina tsaka da dubawa kika bar wurin, ba ma haka ba babu ko kalmar godiya kamar aikena kika yi?".

"Ai ba aikenka nayi ba ban kuma saka ka ba, ni ban so kaje ka had'awa 'yar Lelen kan gabad'aya".

"Wacece 'yar Leleta".

"Your wife mana na ji ma Lele kuke kiranta saboda tsabar gata".

Dubanta yayi da kyau don bai san raini yace " ke Fareesah ban wasa da ke fa, na siyan mata haka kema na siyan miki iri ɗaya, design ɗaya color ne kawai ya bambanta ku shi ne kike wata maganar banza?".

"Maganar banza a ina Babe? Motar kyautar amarci fa ka siyan min amma saboda ka nuna min ban kai koina ba ka had'a da ita bayan duk wasu motocin alfarma tana da su a cikin gidanka, toh laifi ne tunda nace ka had'a mata duka? Kamar a kaina aka fara auren mai mata komai matarka ko irin d'aukin amarcin nan ba kayi a kaina sai ita...." Ta kasa k'arasawa don wani irin kuka ne ya ci k'arfinta, shi ko a mamakance yake kallonta da kyau. 


Bai tab'a tunanin Fareesah tana da irin wannan mugun tunanin a kanta ba, yoh don kawai ya aureta sai ya wulak'anta Nadeefah ko me take nufi?. Kai ya gyad'a yana zama gefenta bai ce mata uffan ba sai da ta gaji don kanta ta share hawayen kafin yace " au da ke tunaninki saboda ina d'aukin amarci sai in banzartar da matata? Well, kin yi kuskure don ba zan tab'a aikata hakan ba . Ba ma a kanki ba ko a kan wata ce, and maganar motoci da kike yi duka a cikin motar Nadeefah babu wacce na siya da kud'ina da kayanta ta zo gidan nan. Wancan  Aventador wedding gift ɗin mu ne daga Daddy Senator dukanmu ya bawa mu shida, sauran biyun kuma nata ne na gida ban tab'a bata kyautar mota ba saboda tana da su bata taɓa complain saboda ban siya ba. Haihuwar Sairah na so bata but she said hidima yayi min yawa in bar shi tun da ba wai babu ba ne, that woman tana jin tausayina fiyeda tunaninki tana kuma girmamani so babu ta yanda da zan wulak'antata ko in wulak'anta d'aya a cikinku kan d'aya saboda so ne ya sa nake zaune da ku ba komai ba".


Nisawa yayi don yayi magana mai tsayi ya sake kallon yanda ta tsume yana cewa " so tunda kin ce baki so zan had'a mata sai ya zama first car na Sairah sai da safe" yana fad'in haka ya juya zai fita da sauri ta kamo shi tana cewa " i'm sorry Lifeline ban san da haka ba ne, forgive me".

"Baki san da haka ba just because kishi ya rufe miki ido ko kika fad'i? In ma ni na siya mata all the cars da suke waje ina ruwanki? Kud'inki ne ko ke kika tayani nemansu huh? Zaki saka ni a gaba kina magana ba kece amarya ba ko ta k'arshen gida ce in dai na siya miki abu duk ƙanƙantar shi sai na siya da ita ko da kuwa na siyan mata wanda ya fi shi a baya gwara ki san da haka tun yanzu".


"Na sani yanzu please Lifeline i'm sorry, ban kumawa".

"You are not sorry Fareesah, zaki zama sorry indai kikace zaki yi kishi da Nadeefah da duk kan abinda take yi ba ki ga komai ba. Now sake ni!" Ya furta da mugun tsawa don ran shi har tafasa yake yi saboda abinda tayi masa.


Ita ko k'in sakinshi tayi sai wani kukan da ta sake fashewa da shi kamar zata shid'e saboda shi, sai kuma kukan ya tab'a shi don yana son kayan shi bai kuma daina ba balle yace amma fa tayi masa laifi mai muni. Ya tuna yanda Nadeefah take amsar duk kan wani abu da ya kawo da zuciya ɗaya bata tab'a kushe abinda ya kawo mata ba, ko da tana da miliyan d'in shi sai ita ne sarkin k'orafi da ganin an mata ba dai-dai ba yanzu in irinsu Adnan da Farhaan suka ji ba sai su yi masa dariya da Allah ya k'ara ba?

Da sauri ya zareta a jikinshi ya nufi k'ofa, lokacin ana kiran maghrib sai bai nufi cikin gida ba ya nufi waje yau a masjid d'in yayi alwala ya shiga sahun gaba. Da aka idar da sallahr ma zama yayi a masallacin ya d'auki Qur'an dan zuciyarsa tana zafi ya d'an dad'e yana karatun kafin ya dawo dai-dai sai da aka yi isha'i kafin ya fito zuwa gida. A k'ofar masallacin ya had'u da su Farhaan suna hira shi da wani d'an unguwarsu Engr Bello da ElSadeeq, sallama yayi dukansu suka amsa suna juyowa a tare Farhaan ya waro idanu a mamakance yace " bawan Allah dama kana ciki?".

"Ga zahiri" ya amsa yana tsayawa ta gefensu suna gaisawa suna cigaba da tafiyar, Farhaan ne ya sake cewa " Allah ya taimaki mutumina angon mata biyu wannan murjewa haka? Anya nima ba ta biyun nan zan nemo ba?".

Kamar yace masa kar ya fara sai kuma ya fasa yana cewa " ga ka ga su nan Allah ya bada sa'a". Engr Bello ne yace " mata biyu ba na mai k'aramin kai ba ne Haji Farhaan akwai abokinmu da yayi duk sun bi sun susuta shi daga nan na tsorata". 


Dariya duka suka saka jin yanda yayi maganar kamar har yanzun ma a tsorace yake, ElSadeeq ma yace " sai ko irinsu Islaam, ni dai mijin Hajiya ne". Farhaan ma yace " ni kam zan shiga layin jarumai irinsu Islaam, mutumina ka ci lafiya" ya k'arashe yana sake bugunshi a kafad'a, harararshi yayi yana cewa " ka fa raina ni".

"Ni fa burgeni kake yi wallahi, zero tension" kai ya girgiza da zai iya da ya bud'e musu cikinshi don ya lura dai shima ciwon kan nan sai an d'aura masa wanda ta gefen Lele da mugun sauk'i kan na Fareesah, sai dai yin shirun ya fiye masa sauk'i don bai kamata ace aure ko wata bai shige ba ya fara k'orafi kan matar son kamar yadda Umma ta lak'aba mata.


Ba su dad'e ba suka raba hanya kowa ya shige cikin gida, yana shigowa wayarshi tana ringing cirowa yayi ya duba Cherrie ne ke yawo a kan screen d'in tsaki yayi kawai ya shige part d'in shi. Labule ta sauke tana mai jin babu dad'i don dama tun d'azu take tsaye tana jiran shigowar na shi, komawa tayi ta zauna tana mai kama bakinta da bai da control zuba kawai yake yi toh ita wani tsautsayi ne ya ja mata ma tace bata so? Ga shi ta ga samu tana shirin ganin rashi.


Wayarta ta sake jawowa tana kiran sisternta ringing biyu ta d'aga tana cewa " y'ar halak yanzu nake shirin kiranki sai kuma nace ban san ko kece da miji ba yau".

"Ba ni bace da girki ba ya gidan?".

"Meya faru na ji muryarki haka?".

"Miye ma bai faru ba Aunty, mota fa ya kawo min benz amma bakina yasa na ce ban so".


Wata k'atuwar ashariya Aunty Aseeyahr ta k'unduma tana cewa " garin wani ganganci ke Fareesah?". Kwashe komai tayi ta bata labari ta d'aura da cewa "ban san cewa motocin duka na gida ba ne da ban yi haka ba".

"Ko duka motocin gidan nata ne ke ina ruwanki da jin haushi? Kina ganin a kaf family ni d'aya ce mai mota ita ma 206 ce kuma da salaryna na siya ke kin samu benz ba zaki godewa Allah ba sai iskanci ne ya biyo baya, toh yanzu tunda ya fasa bayarwa sai ki cigaba da zama haka da tsinannen bakinki da baya haila ba ki san indirectly yake gaya miki alfarmarki taci shiyasa ya siya mata motar ba?".

"Haba dai Aunty?".

"Ya za ai ki natsu ki fahimci karatun bayan ke kishi da bak'in ciki ya rufe miki idanu?".

"Aunty ni fa ba wannan yasa na kiraki ba, i know that nayi kuskure hanyar gyara shi ake nema".

"A tunaninki akwai hanyar gyaranshi ne?".

"Aunty na san ba za'a rasa ba shi yasa na kira".


"Ba'a rasawa.........." Ta jero mata hanyoyin da take ganin zai fisshe su, washe baki tayi cikeda jin dad'in shawarar tata tace " yawwa Auntyna Allah ya bar min ke, thanks much".

"Allah ya sa a dace and sai kin k'ara kulawa zan kira da safe in ji yanda kuka k'are da shi" ok ta amsa suka katse wayar ita ko lumshe idanu tayi tana jin kamar an dawo mata da motar tata an gama.


Sanda ya shigo d'akin a parlor ya samu Nadeefah zaune tana kallon wani indian movie pink, tana jin shigowarshi ta waigo tana kallonshi tace" welcome back Alpha".


Ajiyar zuciya yayi yana dubanta yace " thanks dear" ya k'arashe yana zama gefenta kai ta d'aura kan dantsenshi tana cewa " gajiya ce or what?".

"Kai na ne kamar yake son yin ciwo wife".

Dafa kan tayi tana cewa " sorry Husband lemme serve dinner sai ka sha magani" ok ya amsa ta tashi nan ta kwaso abincin da komai ta jera a kan carpet serving d'in shi tayi a tsanake nan ko ya saki jiki ya kwashi abincin tsaf har da k'arin Spathcock chicken d'in sosai. Da suka kammala ta kai kayan kitchen ta d'auraye a nan d'akinshi ta d'auko masa paracetamol ya had'iya don da gaske kan shi yana ciwo sosai, wanka yayi ya kwanta itama kashe komai tayi tazo ta shige jikinshi basu dad'e ba barci ya kwashesu.


Ba tareda ya nemi komai daga gareta ba wanda ba ƙaramin daɗi taji ba don ita ma ta gaji a ranar ainun, sai da ya dawo asuba sa'annan ya baje kolin celebrations d'in da ba suyi ba na mota. Da suka zauna breakfast kuma sai yake mik'o mata d'ayan keyn motar wai ta Sairah ce, dubanshi tayi a tsanake tace " saboda fa matarka ka siyo ba don ita ba toh ka maida mata kayanta in wata brand d'in take so sai ka maida Yerwa motors d'in".


"Ba damuwarki ba ne wannan madam na bawa 'yata".

"Gaskiya bai kamata ba Yaa, kar ka zama mara adalci a tsakaninmu mana".

"Ni nace ke na bawa?".

"Ai dai Sairah bata kai lokacin driving motar ba, yanzu sai dai ni in hau wannan kuma rashin adalci ne wato ni ka had'a min biyu so ka barshi kawai".


"Nadeefah kar ki shiga maganar nan".


"Wata zaka siyo mata ne?".

"Ba wadda zan siyo mata tunda tace bata so, ba kuma huruminki bane".

"Yaa ko ka ajiye keyn nan zan maida mata don ni ma ban amsar abinda tayi rejecting don ba ajina ba ne".

"Oh really?".

''Yes Yaa, kawai saboda matarka tace bata son abu shi ne ni zaka kwaso k'afafu ka kawo min ni kuma da yake ban san abinda nake yi ba sai in k'arba ko?" Ware idanu yayi yana sauraren ita kuma nata falsafar wai bata amsar abinda Fareesah tayi rejecting bayan ita ta k'i amsa ne saboda ita. Kai shi yau yana ganin halayyar mata kala-kala komai kayi a wurinsu baka fita ba.

"Ni dai ba ke na bayar ba saboda Sairah ne ban kuma aikeki ki kai mata ba" ya furta with finality yana mik'ewa sai da ya kai bakin k'ofa yace sai na dawo Allah ya tsare ta furta ya juya ya fita. Ita ko da ta kammaka breakfast d'in kwashe kayan tayi ta maida kitchen, wankesu ta yi tsaf ta goge sannan ta dawo parlor ta zauna wayarta ta d'aga tana kiranshi d'agawa yayi yana cewa " ya aka yi?".

"Dan Allah Yaa ka maida mata motarta please in ka hanata baka mata adalci ba, ka yi hak'uri da duk abinda ya faru".

"Nadeefah...!"

"Dan Allah Alpha kayi hak'uri".

Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa " toh ki bata key ɗin zan ce ta zo ta karb'a".

"Toh Yaa Allah ya sanya alkhairi, ya dawo mana da kai lafiya" ta furta tana ajiye kan wayar tana mai cewa " haka kawai in amsa a shafa min kashin kaza? Besides ajina ma sai ya zube na maida kaina k'asa kenan".


Tana nan zaune aka yi knocking k'ofa mik'ewa tayi ta bud'e mata k'ofar ganin Fareesah ne ya sata sassauta fuska tace " bismillah".

Wucewa tayi ita kuma ta biyota tana k'are mata wani irin kallo tana mai mamakin kyan jikin Lelen, zama tayi itama ta zauna tana gaisheta cikin daure abinda yake taso mata tace " ina princess".

"Tana bacci, ya gidan".

Amsawa tayi tana cewa " uhmm dama shi ne yace in zo in amsa key".

Dining taje ta d'auko mata tana cewa " ga shi nan ya manta da shi ne i think".

"Aa ai da nace wai ya k'ara miki ne naji yace wai bai tab'a siyan miki bane sai jiya shi yasa naji babu daɗi shi ne fa ranshi ya b'aci wai ai yana sane " ta furta cikin son tura haushi sai dai ga mamakinta murmushi Lelen tayi tana cewa " eh ya gaya min ni kuma nace kar ayi rashin adalci tunda ke baki da ko guda d'aya ne".

Zaro idanu tayi jin martanin da tayi mata cikin rashin sanin abun fad'a tace " toh thanks" ta mik'e tana fita da idanu ta rakata tana mai nazarinta sai kawai ta kwashe da dariya tace " ita wannan wai ni zata sakawa damuwa irin zata cusa min haushin nan, bata san na haddace duka halin Islaam a kai na ba? Hehehe wai ni za a wa bariki?" Ta k'arashe tana sake kwashewa da dariya.


Ita ko komawa d'akin tayi tana cizon yatsa meyasa ta gaya mata wannan maganar ga shi nan ita an gaya mata wacce ta fi nata zafi, meyasa bata yi using shawarar Aunty Aseeyaah ba ta biyewa Suoby k'awarta ? Tsaki ta kuma tana mai sake jin haushin Lelen yana sake kama mata zuciya.............

Love you All.

Deejasmah🎭.