RAGAYAR DUTSE

PAGE 12

by @nanahaleema11

*RAGAYAR DUTSE.*


                ©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*

*Page 012.*




Ƙarfe huɗu da rabi daidai Saleem ya kira ta, ta ɗauka ya shaida mata suna ƙofar gidansu. 


Ta yi ajiyar zuciya ta kira Hamma, bugu ɗaya ya ɗauka alamun jiran kiran yake yi, ta ce, "sun zo." Ya amsa ta kashe wayar ta fito falo.


Gab da zata fita daga falon ta ji muryar Mama tana cewa, "aje a dawo, a taho da kuɗi masu yawa, dan wannan fitar da alama ta musamman ce, tunda bata tashi yi ba sai tsakiyar dare. Maza aje a dawo, ina nan ina jira, saura a dawo ace min  babu kuɗi, a kyauta aka bayar." 


Islaha ta ɗan runtse ido ta buɗe, ta kalli Mama ta ce, "Kirana aka yi daga wajan aiki, na ɗauka kina bacci ne shiyasa ban faɗa miki ba." 


Ta zabga mata harara ta ce, "ko ba wajan aiki ba? Ko da yake wajan sana'a ai wajan aiki ne. Sai kin dawo." Islaha bata ce komai ba ta fita daga falon.


Tana fitowa ta ga Hamma a tsaye yana jiranta, ta ƙaraso tana kallonsa kamar yadda yake kallon ta. 


Kafin ta yi magana ya ce, "sai wani ƙhamshi ki ke yi, bayan da wasu mazan za ki fita bani ba" ya faɗa fuska a ɗaure.


Ta yi murmushi tana sunkuyar da kanta ƙasa, ita bata ji ƙhamshin ba amma shi ya ji. Bata saka turare mai ƙarfi, saboda yanayin da take fama dashi.


Ya ɗan yi tsaki ya ce, "ki jira ni na je na shirya na zo na bi ki, bazan iya barin ki tafiya ke kaɗai ba."


Zai wuce da niyar zuwa ya shirya ɗin, ta yi sauri cewa, "Hamma baka yarda dani bane?." 


Ya juyo ya ce, "ba rashin yarda bane ba Islaha, bazan iya haɗa ki da mazan da ba ƴan uwanki ba, ku yi tafiya a cikin wannan daren. Gashi ke kuma kin je kin yi kwalliya, sai ƙhamshi ki ke yi kamar zaki je biki. Bazan iya ba, kafin ki dawo zuciyata zata iya bindiga, gwara mu je a yi komai a kan idona."


"In kana cewa haka sai naga kamar akwai rashin yarda a tsakanina da kai. Me zai same ni har da zaka so ayi komai a kan idonka Hamma? Me zan ka ke tunanin zan aikata wanda bazan iya yinsa a gabana idonka ba?." 


Ya ɗan sauke numfashi ya ce , "kishi nake da hakan, musamman da ki ka ce min da wannan Muslim ɗin, in iya Saleem ne da sauƙi, amma Muslim ɗin nan ba ƙaunarsa nake yi ba."


Ta ɗan yi murmushi ta ce, "ka yi haƙuri, zuwa nan da anjima zan dawo. Ka ga suna yi min waya" ta faɗa jin wayarta tana ƙara. 


Ya ɗan sauke numfashi ya ce, "zan yi magana da Chairman ɗin, wallahi in muka yi aure bazan lamunci wannan shirmen ba."


"An gama ranka ya ɗaɗe."


"Kuma hotel ɗin za ku je?."


"Eh."


"Bana so wallahi."


Ta kalle sa ta ce, "kar dai kaima kana cikin masu cewa in aka ga mace a hotel abu ɗaya ne ya kai ta? Kar ka zama ɗaya daga cikin masu ɗabi'ar ƴan arewa, musamman hausawa da fulani. Mace aiki baya kaita hotel, sai abu ɗaya."


"Ba haka bane, ni fitar ce bana so." Bata ce komai ba ta yi shiru. Ya bita da kallo sannan ya ce,


"Ban da rashin kunya, don Allah ki yi haƙuri. Kar ki je a ɓata miki rai ki ta faɗa ana kallon ki. Na san halinki, koda an yi miki ba daidai ba ki daure."


"in sha Allah, bazan yi ba."



"Mu je in raka ki." 


Ta yi dariya suka jero shida ita har ƙofar gidan.


A nan ya ga mota ajjiye tana jiranta, ya ƙarasa har bakin motar. Saleem da yake ciki ya ce, "ni na san Hamma bazai bar Islaha ta fito ita kaɗai ba, dole ne ya zamar mata escort." 


Saheer ya murmusa ya basa hannu suka gaisa, suka gaisa da Muslim da yake zaune a gaba sannan ya ce, "kawai dan babu yadda zan ne, shiyasa har na barta ta fito yanzu. Kuma zan samu Chairman ɗin na ku, haka kawai tsakiyar dare a ce fito aiki, kawai saboda gayyatar wani interview?. Yanzu in interview ɗin ce ina jin kwana zata yi kenan ko?."


Saleem ya ce, "to ya za a yi? Abinda aka jima ana nema ne bai samu ba sai yanzu. In Chairman ya rasa damar hira da wannan bawan Allah ai zai iya yin zazzaɓi. Ga shi Islaha tana da sa a sosai, in dai ta yi invinting sai an yi accepting."


"Bazai dinga takura min mata ba wallahi, sai a canja mata waje ta koma bayan camera."


"Haƙuri za a yi Hamma" ya faɗa yana dariya ya kalli islaha ya ce, "Islaha shiga mu tafi." 


Islaha ta shiga baya, Saheer ya kalle ta ya ce, "ki kula da kanki, kin ji?." Ta ɗaga kai tana murmushi. 


Saheer ya ce, "Safeera fa? Ba tare za ku je ba?." 


Saleem ya ce, "ka san ita a ɓangaren record ta ke, irin wannan tafiyar ba a cika yi da ita ba." 


Saheet ya ce, "nima ɓangaren zan saka ta koma, bazai yu ta dinga fita ko ina ba." Saleem ya yi murmushi ya ja motar suka tafi.


Sai bayan motar ta tafi sannan ta gaisa dasu, Saleem ya ce, "an taso ki babu shiri ko?." Ta 


ɗan yi murmushi ta ce, "ni da na ji kiransa wallahi tsoro ne ya kamani. Gaskiya Chairman yana son gayyato mutumin nan, ban taɓa ganin guest ɗin da ya mayar da hankali akan nemansa kamar wannan ba."


Saleem ya ce, "To ba gama garin baƙo bane, kowa zai zo ace shine na farko da ya fara hira dashi a channel ɗinsu da yaren hausa."


"Allah ya bamu sa a a kansa." 


Ya amsa da amin suna cigaba da tafiya. Ba jimawa suka ƙaraso bakin hotel ɗin, aka buɗe musu gate suka shiga suka yi parking. 


Sai a sannan Muslim ya ce, "To a nan zamu tsaya ko zamu shiga ciki?."


"Zamu shiga mu yi reserving room Islaha ta zauna, babu daɗi a barta a reception a zaune kowa yana ganinta. Daman ya ce a kama ɗaki ɗaya a zauna saboda bamu san lokacin barin mu nan ba, tunda lokacin sallah ya kusa sai mu shiga masallaci, ita sai ta shiga ciki ta zauna."


Islaha da mamaki ta ce, "wai a taƙaice a ina Mr Ray ɗin yake? A ina zamu gansa?."


"Waye ya sani Isalaha? Abinda na sani kawai tabbas yana cikin hotel ɗin nan. Amma floor ɗin da yake da room number ba mu sani ba. Amma Chairman ya ce zai turo mana."


"Ikon Allah, wannan shine zuwa gona babu fatanya" Muslim ya faɗa yana kallon Saleem.


Saleem ya ce, "mu je mu kama ɗakin, in mun kama sai ta je ta zauna, in fito daga sallah sai mu je mu same ta." 


Muslim ya ce, "ɗaki a nan fa yana da tsada, haka ya bada kuɗi a kama?."


"To ba so yake yi ba? Mu je" ya basa amsa yana fita itama ta fito tana gyara zaman id card ɗinta a wuyanta. 


A hankali suke takawa zuwa ciki, Saleem ya ƙarasa ya karɓi ɗaki ya dawo wajan ya bata card key ɗin ya ce, "key ɗin ƴan gayu ne, ba a haɗa sa da waya, in ba haka ba bazai buɗe ba sai kin dawo."


Ta yi dariya ta karɓa ta ce, "tare zamu je?."


"A'a ki je kawai, in an idar da sallah sai mu zo mu san abinda za a yi." 


Ta girgiza kai ta nufi elevetor ta shiga zuwa floor ɗin da room ɗin yake.


       A lokacin Rehaan ya fito daga ɗakin yana tsaye a ƙofar room ɗin sanye cikin kayan bacci ya ɗora rigar sanyi mai hula a kai, ya saka hular ya rufe kansa har kusan rabin fuskarsa ya rufe. 


Neman ɗakin da Jazy yake yi, dan shi bai san a wanne ɗaki yake ba ga shi ya kira sa yana bacci.


Ɗakinsa yana kallon elevetor, tana buɗewa ya kalli wajan a tunaninsa Jazy ne. Suka haɗa ido da Islaha da ta fito daga elevetor tana kalle kalle, tana so ta ga room ɗin da zata shiga.


Islaha ta ɗauke idonta daga kansa tana kalle-kalle har ta gano ɗakin. 


Ta gabansa ta wuce ta buɗe ɗakin ta shiga ba tare da ta sake kallon sa ba. Shima tunda ya kalle ta sau ɗaya bai kuma kallo ba, daman ya yi tunanin Jazy ne shiyasa ya kalle ta. Bai jima a tsaye ba ya koma ɗaki.


Islaha tana shiga ta ƙarewa ɗakin kallo, ta yi ajiyar zuciya ta cire facemask ɗin ta zauna tana kallon ɗakin. Kiran sallah ta ji ana yi, ta shiga banɗaki ta yi alawala ta fito ta tayar da sallah har aka yi asuba. 


Tunawa ta yi ta bar handbag ɗin a mota, kuma a ciki iv card ɗin yake, ko yaushe zasu iya ganin Ray, da buƙatar riƙe iv card ɗin a kusa, yadda da an haɗu a miƙa. Ta ɗan yi tsaki ta miƙe ta fito daga ɗakin da hanzari. 


Tana kulle ƙofar ta juyo ta ji ta yi karo da abu, ta ji saukar abu kamar ruwa a jikinta, ta kalli jikinta ta ga black tea ne ya zube mata a jikinta. Ga paper cup ɗin da tea ɗin yake ciki a ƙasa yana gangawara a ƙasa. Allah ya taimaka babu zafi, amma ya ɓata mata jiki. 


Ta ɗago ta kalle kalli abinda ta buge dashi har ya zuba mata tea ɗin hannunsa, ta ga ba ita yake kallo ba wani wajan daban yake kallo kamar ba da ita ya yi karo ba. Ya zagaye ta zai wuce, har yana tsallake cup ɗin bai ce komai ba. 


Islaha ta kallesa, ta kalli cup ɗin da jikinta, ta ga in ta yi shiru fa ya raina mata hankali, gwara ta magantu. A nutse ta ce, "excuse me, Didn't you realize you bumped into me?!" ta faɗa tana kallonsa


Rehaan kamar bai ji ba, ya ɗauko waya yana kiran number Jazy. 


Islaha ta zuba masa ido cike da takaici da baƙin ciki, ta kalli kanta ta ga yadda ta ɓaci da tea ɗinsa, ta sake kallonsa cikin ɓacin rai da hasala. Duk da bata ganin fuskarsa dan ya ɓoye rabin fuskarsa da hular sanyi, amma zata iya gane kammaninsa, dan ɗazu ta gan shi a tsaye har haɗa idanu sun yi.


Ta zagaya ta tsaya a gabansa, ta yi snapping fingers ɗinsa suka ba da sound, dan ya bata attention ɗinsa sosai. Islaha ta ce, "kurma ne kai? Baka ji ka buge ni bane, ko baka ga ka zuba min da tea ba?." 


Ta ƙasan ido Rehaan ya kalle ta, ya sake ɗauke kansa kamar ba ya jin yaren da take magana dashi, kuma yana tsaye bai bar wajan ba, kuma bai kalle ta ba.


Islaha ta ji takaici ya mamaye mata zuciya, ta ji kamar ta yi tsalle ta dinga dukansa har sai ta wuce takaicinta. 


A fusace ta ce, "wallahi ba dan sauri nake yi ba, sai na koma na je na siyo tea, na zo na watsa maka a jikinka dan ka ji abinda na ji. Dan wualaƙanci, ka zuba min abu a jikina kuma ka ƙi kallona balle ka bani haƙuri? Waye kai?."


A duk duniya kalmar da take tsayawa Rehaan a rai bata wuce kalmar waye kai ba, yana ganin kamar raini ne a kalle sa a ce waye shi. Yana daga cikin the most popular people a arewa, amma a kalle a ce waye shi, duk sai ya ji kamar an raina masa wayo.


Hakan ya saka ya ɗago fararen idanunsa ya kalle ta. Ita kuma ta nunasa da yatsa ta ce, "Kar ka yi fatan mu sake haɗuwa, in mu ka haɗu abin bazai yi maka kyau ba, dan wallahi ko a ina na ganka sai na ɓata maka rai da lokaci, kamar yadda ka ɓata min yanzu. Bana ɗaukar raini da wulaƙanci, ko waye kai daidai nake da kai. Na ƙyale ka yanzu dan ina sauri, kuma na yiwa Hamma alƙawarin bazan yi faɗa ba, da sai na tara maka jama'a wallahi, sai ka ji ina ma baka zo hotel ɗin nan ba!."


Rehaan kamar ba jinta yake yi ba, hankalinsa yana kan waya ya mayar da ita ƙaramar mahaukaciya.  Duk da kalmanata suna shigarsa, amma ba shi da lokacin da zai ɗaga ido ya kalle ta. 


Takaici ya sake kamata, ta yi ƙwafa ta bar wajan tana mita.


"Haka kawai an taso ni tun asuba akan inviting wani banza Rehaan Yola, ni ban ga Rehaan ba,  a banza da wofi wancan ƙaton banzan ya ɓata min rai. Ko ina Mr Rehaan yolan oho. Mtsww! Shirme!."


Elevetor yana buɗewa Jazy ya fito, ta ɗan kalle sa suka haɗa ido, ta ɗauke kai ta basa hanya ya wuce ita kuma ta shiga.


Tana shiga elevertor aka buɗe wani ɗakin, wani namiji ya leƙo yana dariya ya ce, "Beb you forgot your facemask, me yasa ki ke gudu?. I love you." A tare Jazy da Ray suka kalli wajan, sai aka kulle ƙofar aka koma ciki..


Nana Haleema✍🏻