Sawun Giwa

02

by @ammimalami99


~~~


YK Ventures

Yelwa


Office ne babba, irin kato sosai dan tafiya ce mai tsawo tsakanin kofar da zaka tura ka shigo zuwa karshen office din. A bangare hagu na ofishin katuwar shelf ce data cinye bangon gabaki daya daga sama har kasa yayinda manyan kwalika na littafai da abubuwan kawa suke ajiye a kasan wajen alamar dake nuna har yanxu jeren office din bai gama kammaluwa ba. A tsakiyar ofishin ta barin hagu doguwar kujera ce da zataci wajen mutane biyar zuwa shida ta fata launin kasa mai duhu wato brown. A dayan barin dama wasu kujerun ne guda biyu na leda wanda kallo daya zaka musu ka shaida laushin su sai wata karamar itama da akayita kamar stool dan dora kafa. A tsakiyarsu center table ne sai kasansu kuma katon carpet mai tsawo da fadi. 


Bangon daman ofishin tagogi ne na gilashi manya suma daga sama har kasa kafin ka karasa can karshen inda nanne teburin mammalakin ofishin yake. Babban teburi ne dake daukeda na'urar apple mai shfaffiyar fuska tareda keyboard da dai sauran ababen bukata a kowani office. Bayan kujerar teburin shima gilashin taga ne daga sama har kasa dake bada cikkakken view na wajen kamfanin da kuma gine gine. 


El-Yakoub yana zaune a kan kujerarsa idanuwansa na bin layin rubutun dake na'urarsa yayinda kansa yake jingine jikin kujerar yana juyata ahankali. Farar dress shirt din suit ce a jikinsa da bakin tie yayinda hannayen rigar suke a nannade. Bakar rigar suit dinsa kuwa tana rataye jikin abun ratayar dake gefen kujerarsa. 


Daga inda yake zaune karar knocking ta iso zuwa cikin kunnuwansa kafin bayan y'an sakanni na wajen ya tura katuwar kofar ofishin ya shigo ciki. Ya dago kansa daga kallon screen din na'urarsa izuwa ga wanda ya shigo din. 


Habeeb ya cigaba da takowa cikin ofishin har izuwa karshensa ya tsaya gaban teburin El Yakoub kafin ya sauke tulin files dinda ke hannunsa. 


"Iya wa'ennan kawai na samo, zuwa gobe idan sauran sun sauka saina tattaro su" 


Yake fada yana buga yatsan sa daya saman files din. 


El Yakoub ya girgiza kansa "Gobe yayi nisa, kace kawai ya rubuto komai ya turo sai ayi printing". 


Habeeb ya d'an zaro idanuwansa kafin yayi y'ar dariya yace 


"Yanda kake tsammanin kowa kaman kai ne ya daina bani mamaki, kasan ina fada wa Mahmoud haka na rantse kashe wayarsa zaiyi bazan sake samunsa ba" ya karasa da dariya kafin ya waiga bayansa yana kallon tsakiyar ofishin. 


El Yakoub yayi murmushi kawai kuma yana kokarin bashi amsar maganarsa Habeeb din yace 


"Wai ba'a shigo da kujerun da yakamata a ajiye gaban teburin ka bane". 


El Yakoub yayi danne danne da mouse dinsa wani shafin email ya bude a fuskar na'urar kafin yace 


"Nace suje su dawo anjima aiki nake banason su dameni". 


Habeeb ya gyada kansa yana zagayo teburin zuwa gefen inda El Yakoub ya juyo masa da fuskar na'urar dan ya karanta rubutun dake kan shafin. Ya girgiza kansa da sauri yace 


"Ina banida time, yanxu ma daka ganni sauke maka files dinnan dama kawai zanyi na fice akwai cargon Lagos daya sauka yanxun nan zanje kamfanin logistics dinnan na saka hannu kasan munyi maganar dakai ai". 


El Yakoub ya daga yatsunsa ya shafa goshinsa idanuwansa na lumshewa cikin tarin gajiyar da ya kwaso dan jiya da safe saukarsa Bauchi kenan daga Abuja kuma direct office ya wuto. Ayyukan sunyi yawa saboda sabon branch ne ya buda a Bauchin ga hayar sabbabin ma'aikata da kuma tafiyar da komai kan tsari sai abubuwan suka sake chakude masa gashi har yanxu bashida secretary dan wannan aikin ma yakamata ace secretary dinsa ne zaiyi sa. 


"Shiyasa nace maka kayi kokari ka samo min secretary". 


Habeeb ya dan cije bakinsa kafin yace  "Nima kaina fa banida secretary dinnan, gashi nan da girma na sai kai komo office dinka nake"


"Ni da kai wayafi bukatar secretary" El Yakoub ya basa amsa. 


Habeeb yayi ya'r dariya kafin yace 


"Interviews din ai duka jiya akayisu, gobe ne yakamata dama a tura emails ga wa'enda suka samu aikin sai su fara jibi". 


"Jibi yayi nisa, a san yanda za'ayi a tura emails dinnan yau su fara aiki gobe kawai karka manta fa inada deadline". 


Habeeb ya girgiza kansa dan shima tsakani da Allah ayyukan sun masa yawa 


"Well zanyi kokarin yin hakan, kaga na manta ma akwai wata da bata samu zuwa interview ba jiya" 


"And?" El Yakoub ya tambayesa kai tsaye yana janyo files uku na sama da Habeeb ya ajiye masa. 


"Ahamad ya kirani da kansa ya roka mata alfarmar sake wata interview din yau". 


El Yakoub ya buda files din yana dubawa. 


"Toh zatazo sha daya kuma kaga ni yanxu akwai inda zanje". Habeeb ya karasa fada 


"Kuma dole kai zaka mata interview din, what happened to HR?" 


Habeeb ya girgiza kansa yana gyara tsayuwarsa zuwa kafarsa ta hagu yace 


"Everyone is busy man, HR tun jiya suka gama interview dinsu yanxu ma sorting canditates sukeyi da kuma onboarding wanda aka zaba so basuda lokaci". 


El Yakoub ya tattare girarsa jin wannan bayanin yana cigaba da buda shafin file din dake hannunsa. 


"Toh yaya kenan, zataje ta dawo ne?"


Habib ya d'an sosa kansa "A'a da wai ina tunanin ka mata interview din kawai". 


Sai a wannan lokacin El Yakoub din ya dago ya kallesa. Ya masa wannan kallon da Habeeb ya sha ganin irinsa a iya tsawon lokacin da suka dauka suna aiki tare. Shekaru 10 sukayi suna aiki tare wannan ne ya saka suke da shakuwa mai karfi a tsakaninsu sam bazaka kallesu kace CEO ne ba da mataimakinsa bazaka kuma kallesu kace wai shekaru bakwai ne a tsakaninsu dan dukda shi Habeeb din dake shekara talatin da tara bazai nunawa El Yakoub kyawu ba koh kuruciya. 


El Yakoub din sam bazaka kallesa ba ka dora masa shekarunsa wata kila ma saika zabge shekaru goma daga asalin wa'enda yake dasu. Tun yana girma kuwa dama fuskar yara garesa dan a shekara ashirin da biyar ma sai kace d'an sha takwas ne idan bakasan asalin shekarunsa ba. Shiyasa kowani lokaci Habeeb yake yawan tsokanarsa na cewar zasu tsufa shiko yana nan da kuzarinsa dan koh shi dayake da mata hadda yara biyu yanaji a jikinsa cewar girma na zuwa amma shi ba'a ganin alamar haka a tattare dashi. 

Habeeb ya katse kallon tun kafin El Yakoub din yayi magana 


"Ka mun wannan taimakon kwara daya kawai Saraki na rokeka" 


Ya karasa yana hade hannayensa kafin yayi saurin juyawa daga wajen zai fice daga office din. 


El Yakoub ya kada kansa irin zaka gane kafin ya jiyo muryar Habeeb na cewa "Zan musu magana su shigo da kujerun nan ba kowa ne soja kaman kai ba".


Ba shiri d'an karamin murmushi ya kubcewa El Yakoub kafin ya maida hankalinsa kan files dinnan. 



~~~


Sha daya saura minti ashirin ta iso kamfanin. Mai adaidaita ya sauke ta gaban ginin kamfanin. Ta daga kanta tana karewa katon ginin kallo bayan ta basa kudinsa. Mutane ne a wajen suna fita da shiga dan hatta katuwar kofar kamfanin da akayita da gilas a wangale take yayinda wasu ma'aikata suketa shiga da desk desk da katun katun kwalaye. 

Har wata katuwar trailer ce pake a gaban wajen ana sauke manyan teberrukan office daga cikinta. Zuciyarta ta zurma ahankali cikin kirjinta cikin taraddadin abunda zata sama a ciki. Ta lalubo addu'ar neman nasara wajen ubangiji kafin ta taka kafarta ta tsakanin hayaniyar mutane zuwa cikin kamfanin. 


Sunanta kai tsaye receptionist ya tambaya bayan ta sanar dashi abunda ya kawo ta. 


"Aisha Mukhtar Bappah" Ta fada masa kai tsaye. 


Yayi dube dubensa kafin ya dauki waya ya kira yana magana wanda sam hankalinta ba kansa yake ba yana kan masu shigo da manyan kwalika suna karya wata kwanar da zata fitar dakai daga harabar ofishin. 


"Ki d'an jira a can" Ya fada gareta yana nuna mata jerun waiting chairs dinda ke jere a gefen wajen inda wasu y'an mata biyu ke zaune. Ta karasa ta zauna ahankali bayan ta dafa kujerar sanyin karfen yana ratsa hannunta. Kujera daya ce tsakanin ta da dayar matar shiyasa tun kafin ma ta zauna takejin sautin muryarta yana shiga kunnuwanta saidai bata maida hankali kan maganar ba saida ta zauna. 


"..idan ba tsoho bane ya za'ayi ace hotonsa daya bai taba hawa yanar gizo ba"  Wacce tafi kusa da ita take fada. 


Dayar ta amsata "Nima abinda nace kenan dan a yanda naji labarin y'an jarida ba'a ma bari suje kusa dashi bare ma su samu ganawa dashi koh daukar hotonsa tsabar security". 


 "Toh fa iko sai Allah" matar ta fada tana kada kanta kafin ta cigaba


"Sai kace bazai mutu ba, nifa a wani labarin ji nayi ance ya haura hamsin ma". 


"Ke kuwa dama duk wanda zai tara irin wannan dukiyar kema ai kinsan shekarunsa sun ja tunda kudin nan ba daga kasa ake tono su ba". 


"Toh wai matarsa fa" Matar ta sake tambayar kawarta cikin gulma da son jin kakap. 


Ta gefenta tayi dariya kafin tace "Shi kansa mai kamfanin ba'a gansa ba sai matarsa".


"Bare ma kuma yara" Matar ta amsata. 


"Wannan daga gani zaiyi girman kai" Ta sake fada. 


"Girman kan ma" Dayar ta bata amsa suna dariya a tare. 


Aisha ta lumshe idanuwanta ahankali tana mamakin yanda mutane suka maida rayuwarsu. Basuda aiki sai hangen rayuwar wasu. Koh tunanin kansu basayi kullum cikin maganan wasu, wance tayi kaza, wane yayi kaza. Suna bata lokacinsu a banza wajen gulma da hangen hangen abunda ba'a saka dasu ba. Yanxu shi wannan dinma basu sansa ba ma amma gulmarsa suke ina ga wanda suka taba gani toh. Ita sai taji ma ya burgeta da yake boye kansa daga duniya dan kudi da suna wasu ababene dake tube rayuwar bawa, sai ya zamana komai kayi a idon jama'a wasu ma jira suke kayi abu suyi maka chaa. Tana cikin wannan tunanin receptionist din ya kiraye sunanta, ta mike ahankali idon matan nan suka juyo zuwa kanta. Bata ma kaiga karasawa wajen nasa ba yace mata ta haura sama zuwa floor na uku. 

Ta gyada kanta kafin ta karyar kwanar daya nuna mata zuwa benen da masu daukar kayan nan keta kaikawo. Kasancewar elevator dinma ba'a gama gyaranta ba yasaka dole ta nan kowa zaibi. Ta haura sama zuwa third floor din kaman yanda ya fada wanda yasha bam bam da duka floors din kasan data baro. Dan shi wannan maimakon tulin desk desk da kuma kofunan wasu ofishoshin data gani a wa'encan d'an fili ne da wasu manyan kujeru da aka ajiye na zama. Maimakon bango kuma tagogi ne daga sama har kasa na gilasai wanda yasaka haske ya cika wajen kake kuma iya hangen sararin sama da kuma gine ginen waje. Wani dogon zagayyayen tebur ne gefen damanka wanda ya kusan kai kirjnta inda wata mata ke zaune tana sarrafa na'urar gabanta. Ta karasa wajenta ta fada mata abunda ya kawo ta 


"Okay Miss Aisha abi?" Matar ta tambayeta dan Christian ce ba musulma ba. 


Aisha ta gyada kanta. Matar ta daga telephone dinda ke gefen teburinta tasa a kunnenta tayi danne danne kafin tayi magana 


"Sir, she's here". 


Shiru kafin ta sake cewa "Okay sir". Ta ajiye telephone din ta sake wani danne dannen a na'urar wanda ya dauki kusan minti daya kafin ta dago ga Aishar tace


"Okay so ma, you see that door there" 


Ta fada tana nuna mata wata kofa dake gefen wani katon kofar glass wanda kallo daya zakayiwa cikin da ake hangowa kasan cewa meeting room ne.  


Ta gyada kanta tana kallon kofar da matar ke nuna mata "Once you enter there's an open office there, you'll see another door that's the CEO's office, just knock and enter". 


Zuciyar Aisha ta bani wani sauti na dumm a kirjinta jin matar ta ambaci CEO. Ita kuwa da tazo interview har me zai kaita office din CEO. Haka kurum taji kafafuwanta sunyi sanyi kalauu dan dama ita she gets nervous so easily. Tunda aka fara maganar interview dinnan bata taba jin komai a ranta ba dan ita irin wa'ennan abubuwan basa daga mata hankali tun a makaranta sun saba presentation kuma wannan yanayin course dinda ta karanta ne dole ka koyi magana gaban mutane da kuma amsa tambayoyi iri iri, rubutu da dai sauransu. Sannan kuma har tutoring tayi amma yanxu haka kurum da taji matar nan ta budi baki ta ambaci CEO sai taji gabaki daya hankalinta ya tashi. 


Ta gyada kai tana sauke numfashi ahankali cikin kokarin kwantar da zuciyarta. Shin CEOn wai ba shine taji matan data baro kasa ba na magana akai? Ba shine akace yanada girman kai ba yakai shekara hamsin? Ita kuwa me zai kaita interview wajensa. Koh dai mutanen basu san interview tazo yi ba. Ko zata kira Ahamad ne ta hadasa ta matar ya sake mata bayani dan kamar receptionist dinnan bai gane bayanin data masa ba ita. 

Ta tura bakar kofar ta glass ta shiga kofar na rufe kanta a bayanta dai dai kuma lokacinda El Yakoub ya dago daga inda yake tsaye gaban wata cupboard yana fito da wani bakin mug na shan shayi. Idanuwansu suka fada cikin na juna na wucewar sakan daya tal kafin ya dauke idanuwansa cikin mamakin wannan karamar yarinyar dake gabansa. Dan shi lokacinda ya buda Cv dinta da Habeeb ya turo masa bayan ya fice daga office dinsa ya duba shekarunta da kuma experiences dinta har ma da kokarinta bai dauka zai ganta y'ar karama haka ba can cikin kasa. 24 fa Cvn nata yace amma a yanda ya ganta nan cikin kallon sakan dayan daya mata sai tayi masa kamar y'ar shekara ashirin. 


"Sit" ya furta ahankali batareda ya sake kallonta ba yana zuba garin matcha dinsa cikin wani karamin kofi. 

Aikuwa kaman yasan abunda Aisha ke tsananin bukata kenan a wannan lokacin dan ta tabbata data kara wasu sakannin a tsaye da saidai ya juyo kawai yaganta kwance a kasa. Kafafuwanta sagewa sukayi data shigo tagan mutum tsaye a wajen saboda batayi tsammanin ganin kowa ba, saima lokacinda ya juyo ya kalleta sai taji kamar ma kawai ta narke a wajen saboda yanda tsnaanin kwarjininsa ya cika mata ido lokaci daya. 


Ta zauna tana sauke ajiyar zuciya kafin ta sake dagowa ahankali tana kallon wajen dan kamar yanda matar ta fada open office ne babba ma kuwa. Katon desk ne da na'ura samansa ga kujera da duk wasu abubuwan bukata. Har wata katuwar shelf aka ajiye gefensa da printer sai wata zagayyayar sofa launin cream inda take zaune akai yanxu da zagayyen tebur shima a gabanta. Ta dayan barin kuma karamin fridge ne da dispenser ruwa a gefen sa. Ga kuma wasu cupboard da aka jera kofuna a ciki kala kala na shan shayi harma da na shan juice mai kofar glass ta yadda zaka iya hango abunda ke ciki. Dayar kuma abubuwan shayi ne da coffee jere a cikinta. Har floating counter akayi inda aka ajiye coffee maker katuwa da microwave inda a nan El Yakoub yake tsaye yana jujjuya koren garin Matcha dinsa da wani d'an kararrammin whisk. Sai sink dake gefensa harma da pamponsa. 


Mamaki ya cika ran Aisha fal dan ita bata taba ganin irin wannan office din ba a rayuwarta. Ya hadu iya haduwa dan wannan ma aka debe teburin za'a iya ajiye gado a wajen shikenan zai koma daki mai kitchen. Ta sauke wata ajiyar zuciyar jin yadda zuciyarta ke cigaba da bugu a allon kirjinta. Toh shi wannan nanne ofishin nasa kenan katuwar kofar dake gefe itace ofishin CEO din da akace taje. Shi shine secretary dinsa kenan tunda yace mata ta zauna. Amma kuma matar ca tayi ta kwankwasa office din CEO din ta shiga amma tunda secretary din nasa yace ta zauna kuma ai ba komai koh. Duka wa'ennan tunanikan ne a ranta yayinda El Yakoub yake cigaba da hada Matchar sa batareda ya sake juyowa ba. 


Sosai Aisha take cikin zullumi har bata san sanda ta lalubo y'ar Nokiarta ba cikin jakarta ta danna kiran Inna kai tsaye tana saureren sautin ringing dinda ke nuna alamar kiran ya shiga. Kuma kamar Inna bazata dauka ba sai gashi ta daukan da sallama a bakinta kamar koh yaushe. Ta amsa tana sauke ajiyar zuciya. Acikin wayar tana jiyo muryar Juwaira dake yiwa Inna maganar da baji take sosai ba.


"Har kin gama intabiyu dinne" Inna ke tambayarta. 


Ta girgiza kanta kamar Innar na gabanta tace "A'a Inna ban shiga ba ma tukunna". 


El Yakoub ya jiyo siririyar muryarta tana shiga kunnuwansa dan dukda ahankali take maganar hakan bai hanasa jiyota ba dan tar yakejin maganar tata kamar tana kusa dashi ne.  


"Toh yaya akayi Aisha, wani abun ne?" 


Inna ta tambayeta dan tafi kowa sanin halin jikar tata. 


"Inna tsoro nakeji kira nayi kiyi mun addu'a". Ta baiwa Innar amsa tana murza saman farcenta wanda tun wancan satin takeson cirewa Allah bai bata iko ba. 


Ta lumshe idanuwanta tanajin yadda Inna ke fadan tsoron me kuma zataji ta kwantar da hankalinta, mey abun tsoro. 


"Inna ance fa tsoho ne kuma kamar yanada tsauri" 


Ta fada dai dai cikin kunnuwansa har baisan sanda ya murmusa ba yana cije lebensa na kasa. Ya bude fridge dinnan yana fitoda kwalin madara lokacinda ita kuma tayi shiru tana sauraren abunda Innar ke fada bayan Innar ta tambayeta shi waye din tace mata mai kamfanin. Saida ya tara kofin nasa a dispenser dai dai wajenda aka rubuta ice ya danna saiga kankara kuwa tana sauka cikin kofin. Karar saukarta cikin kofin glass din ta fito har saida ta daga idanuwanta ta kalli wajen. Hannunsa da layin jijjiyoyi yayiwa zane idanuwanta suka sauka akai kafin tayi saurin daukesu tana amsa tambayar Innar akan mey ya hadata da mai kamfani kuma. 


"Inna nima bansani ba kawai nima cewa akayi nazo ofishin sa inaga shi zai yimin interview din".


"Toh ki kwantar da hankalinki in sha Allah komai tsaurinsa Allah zai doraki a kansa". 


Aisha ta lumshe idanuwanta da takejin kamar kwalla na kokarin kwanciya cikinsu ta gyada kanta tace 


"In sha Allah". 


Ta jingina kanta jikin bangon tana sauraren addu'oin Innar datake amsawa da ameen ameen. 

Shikuwa yana gama zuba madara cikin kankarar ya juye hadin matcha din samansa kafin ya motsa sa da bakin straw dinda kofin yakeda shi wanda ba amfani yake dashi ba. Mamakinta ya dadu a ransa bayan jin duk abunda ta fada a wayar ga Inna wacca yake tsammanin mahaifiyarta ce. Tambaya daya kuwa itace ita duk a ina taji wannan labarin a kansa? Wato tsoho ne kuma yanada tsauri lallai kuwa. Yanajinta tanata Ameen alamar Innar addu'a take mata kenan. Ya cire straw din ya ajiyesa cikin sink yana hango irin addu'ar da Inna zatayi akansa. Wata kila cewa zatayi Allah ya sassauto da tsaurin nasa akanta koh? 

Ya juyo kai tsaye yana sake sauke idanuwansa a kanta yanda take zaune, launin rigarta na sajewa da launin sofar datake zaune akai. Da yanda ta rike karamar wayarta a kunne idanuwanta akan yatsunta datake murzawa. Sai kawai itama ta dago ta kallesa. Yayi saurin dauke idonsa daga kanta itama Aisha ta dauke nata da sauri tana sauke wayar dan sallama sukeyi da Innar sanda ya juyo kuma sai alokacin ta samu damar ganin cikakkiyar fuskarsa. Dogo ne kuma fari dan har ya fita haske ma kuma abu mafi daukar ido a fuskar tasa shine dogon hancinsa daya zauna akan fuskarsa yana sajewa da kammaninsa masu kyau da tsari. Bakin saje da gemu marar yawa ya zagaye fuskar tasa wanda ya d'an surku da kananan farin gashi sai hakan ya kara masa wani kyawu da kwarjini marar misaltuwa. 


Ya karasa kofar office dinsa yana wangale ta dayan hannunsa rike da kofin Matcha dinda ya hada ya juyo ga Aishan yace 


"Come"


Zuciyar Aisha ta sakeyin yin dumm kafin ta mike tana saka wayarta cikin jakarta dake rataye a kafadarta. Bata sake kallonsa ba lokacinda ta raba ta gabansa tana shiga cikin office din da bisimillah a bakinta turarensa mai dadin kamshi da bata taba jin kalarsa ba ya daki hancinta lokacinda ta wuce sa tana shiga cikin tamkeken office din wanda girmansa da tsarinsa ya sakata bude idanuwanta tana kare mai kallo har bata lura da cewan ba kowa zaune akan kujerar da yakamata ace CEO din yana zaune akai ba. 


El Yakoub ya saki bakar kofar glass din tana rufe kanta batareda wata kara ba ya karasa ya wuce inda Aisha tayi tsaye kawai batareda ta karasa cikin office dinba a ransa yana jinjina rashin tsawon ta dan lokacinda ta wuce ta gabansa har tsakiyar kanta yana hangowa.