RAGAYAR DUTSE

PAGE 13

by @nanahaleema11

*RAGAYAR DUTSE.*

                ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*Page 013.*

Rehaan ya bi Jazy da kallo ya ce, "ina ka je?." Jazy ya ce, "na je masallaci mana." 

Ya harare sa ya ce, "nima ai na je, amma ban ganka ba." 

Ya ɗan shafa kansa ya ce, "ana idar da sallah na je na sha tea. Meye ka ke nemana kamar na ci maka bashi?" Ya faɗa ya buɗe room ɗinsa. 

Rehaan ya ja tsski ya ce, "bana so ka dinga yawo, kar a yi noticing muna cikin hotel ɗin nan."

Jazy ya shiga ɗakin sa yana cewa, "kai dan kana ɓoye kan ka ni bazan ɓoye kaina ba, kai ake nema ai bani ba."

"Shine ka je ka sha tea baka taho min dashi ba, nawa da aka kawo min ya zube." 

Jazy ya wani kalle sa ya ce, "Kai! Ba fa yaron goye bane ba kai, in baza ka je ka ka siya ko ka yi order ba ka bar shi. Ni bacci nake ji, sai anjima" ya faɗa yana rufo ƙofarsa ya bar sa a tsaye.

Ray ɗaki ya shiga yana kallon inda tea ɗin ya dan ya ɗan zube masa a jiki, ya ja tsaki ya cire rigar ya ajjiye sannan ya zauna a kan gado. Sai kuma ya jawo wayarsa ya duba ya kuma ajjiyewa bai ce komai ba.

     Islaha kuwa cike da takaici ta sauka groundfloor, a reception ta haɗu da su Saleem suna niyar zuwa floor ɗin. Ta kalle su ta ce, "na manta handbag ɗina a mota, shine zan je in ɗauko." 

Muslim ya ce, "gata na ɗauko miki, na san dole zaki nema ta." Ta karɓa fuskar ta babu walwala. 

Saleem da ya san halinta ya ce, "ya dai?."

"Wani ɗan rainin hankali ne ya buge ni ya zuba min tea, kuma dan wulaƙanci ina magana ya yi min banza kamar bai yi laifi ba. Ji inda ya ɓata min riga, ga abaya mai sauri riƙe dauɗa."

"Ina fatan ba ki mayar masa ba?."

"Kaima ka san bazan zuba masa ido ba ko?."

"Islaha nan fa hotel ne, akwai mutane mabanbanta wanda baki san matsayinsu ba. Ki dinga kula."

Ta ɗan yi tsaki ta ce, "sai me? Dan yana da wani matsayi baza a nuna masa kuskurensa ba?. Tea  ne a hannunsa fa, ya buge ni ya zube min a jiki, ba a hannuna tea ɗin yake ba, amma yi haƙuri ya gagaresa faɗa. Kuma sai in zuba ido ina kallonsa, ya zubawa banza mara gata ko?."

"A'a, ni ban ce ba."

"Ka ma ce ɗin, ka san ba bari zan yi ba. Kuma bai yi kama da ɗan ƙasar nan ba ko kaɗan." 

Saleem ya girgiza kai ya ce, "nidai ina so ki rage wannan tsiwar taki, gidan wani zaki je." 

Ta ɗan harare sa ta ce, "gidan Hamma zan je ai, ya san kuma ya nake. A haka ma na ƙyalesa ne saboda Hamma ya roƙe ni kar in yi faɗa, Allah da sai na tara masa jama'a."

"Daman shi ya taɓarɓara ki ai."

Suka yi dariya a tare, suka nufi elevetor suka shiga zuwa floor ɗin.

Sai da ta sake kallon inda ta ga Rehaan amma babu alamunsa, wajan babu kowa sai waiter da table tana knocking ɗaya daga cikin ƙofofin wajan inda suka yi order abinci. 

Suna shiga suka zaunna akan kujerun da suke ɗakin, ita kuma ta shiga bathroom ta ɗan wanke inda tea ɗin ya zube mata, ta dawo ta zauna a gefen gadon ta ce, "tsakani da Allah awa nawa zamu kwashe a wajan nan? Bamu da tabbacin a ina wannan bawan Allah yake." 

Muslim ya ce, "wallahi har na gaji Islaha, har yanzu babu cikakken information akan inda zamu same sa." 

Saleem ya ɗauki waya ya ce, "bara na kira Chairman, ya kira PA ɗinsa ya faɗa mana ko da floor ɗin da yake ne, in yaso sai mu tara zuwa lokacin sallar azahar."

Ta wara ido ta ce, "har azahar?." 

Saleem ya ce, "muna da mafita ne Islaha? Dole haka zamu yi." 

Saleem ya kira Chairman suka yi magana, bayan ya kashe ya ce, "Sun yi magana da PA ɗinsa,  ya ce zai turo mana hoton wanda suke tare, ya ɗan fi sa sauƙin gani, amma yana da ƴar shariya kaɗan. Ya ce indai mun gansa kamar mun ga Mt Rehaan Yola ne."

Islaha ta gyaɗa ki tana taɓe baki ta ce, "taɓ, ka ce wannan aikinka ne, dan bazai wulaƙanta ni ko ya share ni ba wallahi. Kun san in hakan ya faru da faɗa za a rabu dani. Garin son ganin Ray mu ƙare a police station."

Muslim ya ce, "wallahi aikin ki ne ba mu ba, ga ki a tare damu me zamu yi?. Ai indai da mace a irin wannan tafiyar namiji baya saka baki. Macen ma irin ki, mai kyau da sa a." 

Ta ɗan yi murmushi ta ce, "Aa fa, ni wallahi ba za a wulaƙanta ni a banza ba. Zan iya ɓarar da komai wallahi, sai dai Chairman ya saka a kulle ni" ta faɗa tana ɗaukar wayarta da take ƙara.

Ganin Hamma ne sai da ta yi murmushi sannam ta ɗauka ta saka a kunne ta ce, "Hamma ina kwana."

"Islaha kun gama?."

"Ina fa, har yanzu ban samu damar ganinsa ba. Ba mu san a wanne floor yake ba har yanzu."

"Babu lokacin dawowar ki kenan?."

"Gaskiya babu."

"Kina ina yanzu haka?."

"Mun yi reserving room, ina ciki."

"Su kuma fa?." Ta ɗan kalle su ta ga Muslim ya zuba mata ido, saɓanin Saleem da yake danna wayarsa.

Ta ɗan sauke numfashi, ta yi ƙasa da murya sosai ta ce, "muna tare." 

A ɗan fusace ya ce, "a ɗaki ɗayan ku ke?." 

Ta ɗan girgiza kai ta ce, "eh, da yake muna tattaunawa akan yadda abin zai kasance ne."

"Islaha gaskiya bazan jure wannan shirmen ba, ki zauna ɗaki ɗaya da maza biyu a hotel?."

"Kar ka damu, aiki ne ya kawo hakan. Na san ka yarda dani ai ko?." 

Sai da ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce, "ki kula, zuwa anjima in baki dawo ba zan zo." Kafin ta yi magana ya kashe wayar, ta yi murmushi tana ajjiye wayarta a gefe.

Muslim ya ce, "Isalaha kina son Hamma da yawa." Ta ɗaga ido ta wani kalle sa, sai ta share bata basa amsa ba. 

A lokacin Saleem ya ce, "yauwa, ga hotonsa an turo min. Sunansa Jafar Yola, inkiya Jazy. Cousin ɗin Rehaan ne kuma abokinsa, da babansa da babansa uba ɗaya suke."

Muslim ya karɓa yana kallon hoton Jazy ya ce, "wannan ai na san shi, indai zaka ga Ray to daƙyar baka gan shi ba. Da yawan hotunansu a tare suke." 

Ya miƙawa Islaha ta karɓa tana kallo, ta ɗan buɗe ido ta ce, "kai wannan ai na gan shi.”

A tare suka ce, "a ina?." 

Ta kalle su da mamaki ta ce, "a floor ɗin nan, lokacin da nake faɗa mu ku an zuba min tea, elevator ɗin da ya fito na shiga, har sai da basa hanya ya wuce." 

Saleem ya ce, "oh Islaha! Meyasa baki yi masa magana ba?."

"Ban san shi ba ai, ko guest ɗin na mu ban san shi ba, ban taɓa tsayawa na ƙare masa kallo ba balle na riƙe fuskarsa a raina."

Muslim ya ce, "kai, mun yi wasa da damar mu." Ta ɗan yi shiru ta ce, "Hakan yana nufin Jazy da Ray a wannan floor ɗin suke." 

Saleem ya ce, "Za ki iya gane room number ɗinsa?." 

A tare suka miƙe suka fito bakin ƙofar, tana kallon ɗakunan da suke a kulle ta ce, "ban ga ɗakin da ya shiga ba, amma ina da tabbacin a wannan floor ɗin ya yake."

Saleem ya ce, "shikenan, hakan ma an samu cigaba ai. Mu koma tukunna." 

Suka dawo ɗakin Islaha ta ce, "da na san shine da nayi masa magana, ohh! Yanzu a ina zamu sake ganinsa?." 

Muslim ya ce, "kar ki damu, ba laifi bane ba hakan, rashin sani ne. Amma yana da kyau a nuna miki hoton Ray kar aje shima kin haɗu dashi."

Ta ɗan yi dariya ta ce, "babu baƙata, wataƙila in na gansa zan gane sa." 

Saleem ya ce, "zata gane Ray, ai ba ɓoyayye bane ba." Suka koma suka zauna suka cigaba da tattaunawa. 

Islaha ta gaji da zama, kwanciya take son yi amma bazai yu ba saboda waɗanda suke tare. Duk ta takura, zaman ya ishe ta, har bacci take ji yana ɗaukarta. 

Saleem ya kalli agogo ya ga ƙarfe takwas na safe, ya ce, "ya kamata mu samu tea mu sha. Muslim mu je mu samo abinci mu barta a nan." Suka miƙe suka fita suka bar ta a ɗakin.

Basu jima da fita ba ta taso ta fito tana sake kallon wajan ko zata ga Jazy amma babu kowa a wajan. 

Ƙarar elevetor ta ji sai ta juya tana kalon wajan, ta yi tsaki ganin wraiter tana tura table ɗin abinci. Ta kalli Islaha ta ce, "morning madam." Islaha ta yi murmushi ta amsa, ita kuma ta wuce room ɗin da tazo tana knocking.

Ɗan buɗe ƙofar da take knockinga aka yi, ta ɗan kalli wajan sai ta ga bata ganin kowa sai waiter ɗin da ta shiga ciki da table ɗin. Ƙarar elevator ta sake ji, ta juya ta ga Saleem da Muslim sun dawo.

Saleem ya miƙa mata tea ya ce, "me ki ke yi a nan?." 

Ta ce, "ina dubawa ko zan sake ganinsa." 

Saleem ya ce, "mu shiga ciki, bazai yu mu tsaya a nan ba, har gwara mu mu je kan kujerun can mu zauna mu jira mu gani. Amma mu fara cin abincin." Bata ce komai ba ta koma suka biyo bayanta.

Har ƙarfe goma suna zaune babu labari, duk sun gashi da zaman waje ɗaya. 

Islaha ta ce, "zama a nan bazai yu ba  Hamma Saleem, mu fita mu je mu zauna a kan louge chairs ɗin can, mu dinga kallon masu shige da fice, kar mu je muna nan su bar hotel ɗin. 

Saleem ya ce, "haka ne, mu je." 

Muslim ya ce, "ku je zan fito." Ba musu suka fita suka bar masa ɗakin.

Muslim ya ɗauki wayarsa yana tsaki ya ce, "Ummi kin dame ni, meye wai?." 

Daga can ɓangaren ta ce, "bana so Islaha ta yi nasara a akan wannan aikin shiyasa na damu, ka san abinda zaka yi ka lalata haɗuwarta da Mr Ray."

"Na fi ki sanin abinda nake yi, na fi ki sanin abinda zan aikata. Ki daina takura min da waya, kin san ta da shegen wayo, zata iya gano wani abun."

"Shikenan" ta faɗa tana kashe wayar.

Ya kalli kan gadon ya hango handbag ɗinta, ya ƙarasa ya buɗe ya ɗauko invitation card ɗin da yake ciki, ya ninke shi ya saka a aljihu. Ya ɗauko wani irinsa sak a aljihunsa ya musanya da nata, ya mayar da jakar inda ya ɗauka ya ajjiye. 

Ya girgiza kai yana kallon jakar ya ce, “za ki haɗu da Mr Rehaan Islaha, amma a police station zaki ƙare, dan ni kaɗai na san me na rubuta. Baza mu taɓa bari ki yi nasara akan mu ba wallahi, sai mun ɓarar da duk wata nasara da za ki samu a rayuwar ki, baki isa ki zo a bayan mu ki fi mu ɗaukaka ba. Kina samun damar hira da Mr Rehaan shikenan kin yi mana fintinkau, sai mu gani in hirar zata yu” ya yi ƙwafa yana cize bakinsa sannan ya fito. 

A zaune ya same su suna hira ita da Saleem shima ya zauna ya shiga sahun hirar.

Nana Haleema✍🏻❤️