FARASHIN IZZAH

Chapter 25

by @hauwajaywrites

Ya miƙe tsaye daga inda yake zaune


"Finally." Ya faɗa yana kallon agogon hannunsa.


Zahra ko kallonsa bata yi ba, ta cire key ɗin kofar ta nufi hanyar stairs kai tsaye, kamar ma ba ta gan shi ba haka tayi pretending 


Da mamaki reacton ɗinta ya bita da kallo, sai data kai kusa da matakalar ne ya ɗaga murya


"Malama, dakata anan."


Sauke kafar nata tayi, sannan a hankali ta juya, wani irin kallo ta watsa masa. Kallon da ya nuna bata cikin yanayin da za ta iya ɗaukar rashin hankali, she's ready to exchange words with him


"Me kuma?" Ta tambaya a taƙaice


Khalil ya yi wata irin dariya.

"Nine zan tambaye ki me kuwa"


Ya taka zuwa gabanta


"Wane dalili ne zai sa ki dinga bin girlfriends ɗina kina tayar musu da hankali?"


Zahra ta ɗaga gira


"Au" ta faɗa tana gyara tsayuwarta


"Ita Lovie Dovie ɗinka ta faɗa maka kenan?"


Fuskarsa ta ɗan canza.

"Whatsoever Zahaaaaa..." ya kare maganar da karfi kamar zai dake ta


"Abin da ya dame ni shi ne, me yasa kike bin mutanen da ba su san ki ba? Dole sai kin fada musu Ina da mata dan su rabu da ni?"


Zahra ta yi dariyar rainin hankali 


"Oh wow." Ta fada tana tafe hannu


"So yanzu kai ka zo gidana ne saboda wannan?"


"Answer the question." Ya katse ta.


"What is wrong with you Zahra?"


Nan take ta zaro ido.

"What is wrong with me?"


"Yes." Ya amsa.


"Me yasa za ki dinga shiga rayuwar mutane, dole sai nayi rayuwa da ke kadai ne?"


Zahra ta yi dariya, dariyar takaici


"Khalil, ka tabbata kana son wannan hirar?"


"Very much." Ya amsa


"Good" Ta gyada kai


"Toh ni kuma ina da tambaya guda ɗaya."


"Ask." Ya fada yana folding hannaye 


"Wane dalili ne zai sa married man ya dinga bin mata a waje kamar bunsuru"


Khalil ya haɗe gira, sosai maganar ta dake sa

"Don't start Zahra dan zamu samu big issues wlh"


"No."Ta ɗaga hannu

"Let's start, I'm ready for it"


Ya furzar da iska.

"Kina son drama sosai, amma kar ki yarda nayi maganar da zaki yi kuka"


"Drama? Ai ni bana tsoro Ibrahim"


Ya ce "Okay.. naga alama Baki da tsoro amma kina dab da nadama kuwa"


Zahra ta yi murmushi. Murmushin da bai kai ciki ba


"Interesting."


Khalil ya ci gaba.

"Ina miki warning ki fita harka ta da Duk wacca ta raɓe ni, kuma idan kina son zaman Lafiya stop touching my phone"


"Your business?" Ta katse shi

"Really?"


"Yes." Ya amsa 


"Toh ka daina kawowa har cikin gidana shi harkan naka, taɓa waya kuma ai na daina tunda ba alkhairi kake shukawa ba"


Nan take ya yi tsaki

"Waye yake causing matsala a tsakanin mu idan ba ke ba, a dole sai kin duba wayata kuma ko sau dari zaki duba ba zamu daina samun matsala ba"


"Because you are the problem."

Ta mayar masa ba tare da tunani ba


"Excuse me?"Ya matso kusa da ita

"Repeat that."


"I said you are the problem."

Ta maimaita tana kallonsa kai tsaye


"Khalil, ka daina acting like victim."


"Victim?" Ya yi dariya.

"So yanzu ni ne victim?"


"A'a" Ta gyara masa

"Kai ne culprit."


Wani irin shiru ya biyo baya

Kallon juna kawai suke yi


Khalil ya girgiza kai.


"Unbelievable."


"Ai ni ma abin da nake gani yanzu unbelievable ne" Ta mayar.


"Imagine married man yana defending girlfriends ɗinsa, just imagine fah...."


"Watch your mouth Zahra" Ya faɗa da gargaɗi


"No" Ta amsa nan take.

"You watch your actions first"


Ya ɗan yi shiru kafin ya ce,

"At least they respect me."


Nan take fuskar Zahra ta canza.

"What?"


"Kin ji ni ai" Ya amsa


"At least they know how to talk."


Zahra ta ji wani abu ya tsaya mata a maƙoshi, na wasu daƙiƙu ta kasa magana, sai daga ƙarshe ta yi murmushi, murmushi mai cike da ciwo


"Oh" Shi kenan kawai ta faɗa

Ta gyada kai a hankali

"Oh, I see."


Khalil wani kallo yake mata


Ita kuwa ta ɗauki jakarta a zuciye 

"Congratulations then" Ta faɗa


"What?" Ya tambaya


"Congratulations" Ta maimaita.

"If they make you that happy, good for you."


Sai ta juya.


Khalil ya ɗaga murya.

"Zahra!"


Amma ko juyowa bata yi ba. Kai tsaye ta hau stairs.


"Zahra I'm talking to you!" Ya sake maimaitawa 


Ku waiwayowa bata yi ba balle yasa ran zata kulasa


Tana isa sama ta buɗe ƙofar ɗakinta da ƙarfi, ta shiga ciki tare da banke ƙofar a bayanta


Khalil kumq ya tsaya a parlorn ƙasan, hannayensa a aljihu, yana huci saboda takaici


Ita kuma Zahra bayan ta shiga daki tana tsaye bayan ƙofar ɗakinta, zuciyarta na bugawa da ƙarfi tsabar bakin ciki


Ba saboda maganar girlfriends ɗin ba, sai saboda kalmar da ya jefa mata.

"At least they respect me."


Kalmar ce kaɗai ta isa ta sake karya wani ɓangare na zuciyarta.


Daga ƙarshe shima Khalil ya haura sama zuwa dakinsa.


Yana shiga ya banke ƙofar a bayansa da ƙarfi. Wani irin takaici yake ji kamar zuciyarsa zata faso. Har yanzu kalaman Zahra na yawo a kansa


Ya cire agogonsa ya jefa kan side drawer.


Tsaki ya ja.


A rayuwarsa bai taɓa tunanin wata rana za su kai ga irin wannan matsayi da Zahra ba


A gefe guda kuma, Zahra na zaune kan gadonta.


Hawayen da take hana kanta ne tun a parlorn suka sake kubuce mata, sosai take kuka


Kukan da take yi tun daga zuciya ce, a hankali ta dafe cikinta Saboda wani ciwo da yake mata


"Wallahi na gaji..." Ta furta a hankali.


"Na gama zama da Khalil as miji..."


Tafi awa tana kuka, tunawa tayi bata yi sallar isha'i ba yasa ta share fuskarta da sauri, miƙewa tayi ta nufi toilet


Alwala tayi cikin nutsuwa sannan ta dawo ɗakin, sallaya ta shimfiɗa, ta tada kabbarar sallah


Dogon lokaci tayi tana addu'a bayan ta idar.


Addu'o'in da ita kanta bata san lokacin da ta dauka tana yi ba, tana yi ne tana kuka


Daga ƙarshe ta jingina da bango tana kan sallayar, tunanin rayuwarta kawai take yi.


Can ba tare da ta sani ba bacci ya fara rinjayarta. A haka bacci ya ɗauke ta.


Misalin karfe biyu na dare, wani irin yunwa ne ya farkar da ita, ta buɗe idanunta a hankali


Da farko bata ma gane inda take ba.

Sai can sannan ta tuna, Akan sallayan bacci ya dauke ta


A hankali ta miƙe tana jin jikinta babu ƙarfi, ga ciwon da maranta yake yi, ta gyara hijabin kanta sannan ta fito daga ɗakin


Ta nufi hanyar stairs domin ta sauka zuwa kitchen


Sai dai tana wucewa ta lura da wani abu... Ƙofar ɗakin Khalil a buɗe take.


Ta tsaya tana mamaki, toh ko ya shiga dakin ne jiya daya fita sai bai kulle ba?


Har ta yi niyyar wucewa, sai kuma wani abu ya sa ta waiwaya

A hankali ta ƙarasa bakin ƙofar, ta leƙa ciki


Nan take mamaki ya bayyana a fuskarta

Khalil yana cikin ɗakin, yana bacci


Ba fita yayi ba kamar yadda zuciyarta ta ɗauka ba.


Fitilar bedside lamp ce kawai ke kunne


Kayan da ya sa tun na daren ma bai canza su ba, ya ana kwance gefe ɗaya, wayarsa a ajiye kusa da shi


Alamar dai ya yi bacci ne ba tare da ya shirya ba