TAURARI BIYU

Taurari biyu

by @queenmeemi

TAURARI BIYU
(Two Stars)

Labari, Rubutawa da Tsarawa.

 Meemibashir
#AREWAPEN @queenmeemi 
 
Group link
***


Chapter 2

Duk wani taimako da ya kamata sai da suka ba mutumin nan. Akwai wani babban likita da suke amsar magani a wajensa a ƙauyen, shi Faruq ya ɗauko ya yi masa treatment yadda ya kamata tare da ba shi magunguna. Har goge masa jiki da fuska suka yi, aka canja masa riga.
Sai gashi kamanninsa sun fito sosai. A lokacin har Magariba ta yi. A ranar dai Iman ba ta shiga cikin kasuwa ba, sai Ruman ce kaɗai.
Faruq ya yi mata gargaɗin kada ta shiga inda baƙon nan yake. Ai dai ta yi silar taimaka masa ko! to lada ya isa haka. Domin ya fahimci yadda ta damu da lamarin, abin kuma yana saka masa tsoro, domin ba su san takamaiman waye ba, ko menene silar shigarsa irin wannan hali. Kawai dai jikinsa bai nuna wata matsala ba.
A duk sanda Faruq ya faɗi hakan, Iman kan ce,
"Wai ko ba ka duba fuskarsa ba ne? Akhi ne fa! Kai kanka ka shaida cewa shi ne, amma me yasa kake ƙin yarda?"
Faruq ya ce,
"Saboda Imran ya daɗe da mutuwa. Shekara ɗaya kenan. Na gaya miki ki tsaya a matsayinki, Iman. Kar ki janyo mana matsala ki sakamun acikin matsalsr da ba zamu iya fita ba."
"Kawu Faruq!" na faɗa ina mai fashewa da kuka. "Wallahi Akhi ne, na rantse shi ne!"
Kawu Faruq ya ja tsaki tare da fita daga tsakar gidan yana jin zuciyarsa na bugawa sosai.

Na tsugunna tare da shiga rera kuka. Tabbas na san ko kowa ba zai gane Akhi ba, Abhi zai gane shi, haka ma Ruman.
Na share hawayena tare da miƙewa tsaye. Sai ga sallamar Ruman ta shigo, ta jibge jakarta a gefe na kama mata ta sauke kayan da ke kanta.
"Da baki zo ba ai ba mutuwa na yi ba," ta faɗa tana miƙo min wata kwalba. "Ga zuma nan da kike so."
Na amsa tare da jan hannunta muka shiga ɗaya daga cikin dakunan gidan.
Na ce, "Kalli ki gani."
Ruman ta ce, "Me zan gani?"
Na nuna mata baƙon.
"Kalli fuskarsa. Ba Akhi ba ne?"
Ruman ta saki hannuna ta matsa daidai fuskarsa. Nan take ta ja da baya tana haki.
"Wallahi Ama Imran ne! Wayyo Allah na! Ashe bai mutu ba!"
Ta faɗa tana zubewa ƙasa tana kuka.
"Daman Iman na sha faɗa miki, wallahi Ama Imran bai mutu ba. Duk kowa sai ya ringa kallona kamar mahaukaciya."
Iman ta share hawayenta.
"Alhamdulillah da kika gane. Amma Kawu ya ƙi yarda."
Ruman ta kamo hannuna.
"Babu abin da ya fi mu yi sauri mu koma Ghezzam. Wannan shi ne albishir mafi girma da zai riski Abhi."
Na girgiza kai ina kallon Akhi, wanda ya zama dukkan ruhin iyalinmu.
Na lumshe ido tare da sakin murmushi. Na jata muka fita.
Da wuri muka kwanta saboda gajiya. Ban tashi ba sai Asuba, har ma mun makara saboda shida ta yi.
Na fito na shiga banɗaki na yi bukatuna. Da na fito, na tsugunna ina alwala.
Sai na ji ana tari da ƙarfi.
Na tsaya cak ina sauraro.
Ba haka Kawu Faruq ke tari ba, kuma ba Ruman ba ce domin muryar namiji nake ji.
Sai can na zaro ido.
Ashe har na manta da Akhi mai jinya da ke gidan.
Na yi saurin miƙewa na doshi ɗakin. Da yake akwai hasken fitila, na ƙarasa ciki.
Idona ya sauka a kansa.
Idanunsa a rufe suke, amma yana tari.
Tsananin mamakin yadda har ɗigon da ke gefen idonsa kamar tawadar Allah ya fito sarai ya sa na kasa daina kallonsa.
"Akhi... Wai shi ne?" na furta a raina.
Na ƙarasa daidai kansa tare da zuba masa ido.
Idanunsa a rufe suke, amma zarazaran gashin idanunsa sun yi kyau ƙwarai. Ga girarsa baƙa ƙirin, kamar an tsara ta. Sai lips masu kyau da daukan hankali da hanci mai tsari.
Na ja ajiyar zuciya.
"Akhi, ko a rufe ido zan iya gane cewa kai ne."
Motsa hannunsa ya yi ya ɗora a kansa.
Na bi hannun da kallo. Zarazarran yatsu ne masu kyau, ga ɗan gashin da ya kwanta a saman hannun. Irin na Akhi sak
"Azul," na ce masa a yaren Tuareg, wato sannu.
Da na ga bai buɗe ido ba, sai na miƙe na fita.
Na je wurin da Faruq ke ajiye kayan girki. Na ɗauko ƙaramin gas na kunna wuta, na ɗora ruwa.
Daga nan na koma ɗaki na tada Ruman domin Sallah.
Ta miƙe ta fita.
Faruq ya daɗe da fita tun kafin gari ya waye, domin idan haske ya fara fitowa sai ya dawo. Hakan ya saba yi idan muka zo ƙauyen.
Bayan na idar da Sallah, na ɗauko ruwan zafin na haɗa masa tea a cup, sannan na samu ɗan ruwa mai sanyi na surka a ruwan zafi.
Na ɗauko sabon ƙaramin towel daga kayana na shiga ɗakin.
Na matsa kusa da shi, na fara goge masa fuska, wuyansa da hannayensa.
Ina cikin yi sai na ji caraf an riƙe min hannu.
Na yi saurin sakin towel ɗin saboda tsoro.
Na ɗauka Faruq ne, ya dawo.
Sai ya buɗe idanunsa a hankali.
Bai saki hannuna ba, duk da ina ta ƙoƙarin kwacewa.
Ya gama kallon ɗakin sannan ya maido idanunsa kaina.
Na kama ɗayan hannunsa.
"Sannu Akhi, ka tashi."
Hawaye suka fara zubo min.
Na shiga kiran Ruman.
Ta shigo da sauri, tana cewa 
"Ama ka tashi! Wayyo Allah, ashe ba ka mutu ba Ama Imran!"
Ita ma ta faɗa tana riƙe da ɗayan hannunsa.
Sai ya ringa kallonmu cikin mamaki.
Na ce wa Ruman,
"Ki yi a hankali mana. Kin san bai gama farfaɗowa ba."
Ta ce,
"Yanzu Iman, har kina tunanin zan jira ya gama farfaɗowa? Bayan idona ya nuna min Ama ne? Kin manta jidalin da muka shiga? Wannan shi ne kaɗai hanyar nuna farin cikina da ganin Ama bai mutu ba."
Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka.
Ni kam jikina ya yi sanyi.
Domin yadda yake kallonmu kamar bai san mu ba ya sa zuciyata ta shiga rawa.
Ko dai abin da Kawu yake faɗa gaskiya ne?
Sai dai na yi saurin kawar da tunanin.
Na riga na yarda cewa Akhi ne.
"Sannu," na sake faɗa masa.
Bai ce komai ba.
Ya juyar da kansa yana dafe kansa kamar yana jin nauyi.
Abubuwan da suka faru suka fara dawowa masa ɗaya bayan ɗaya.
Sai ya runtse ido yana jan numfashi.
A ƙarshe ya lumshe idanunsa, hawaye suka zubo masa.
Yanayinsa ya nuna mutum ne mai sanyin hali.
Abin da ya yi daidai da halayen Akhi.
Tausayinsa ya kama ni matuƙa.
Musamman ganin yadda siraran hannayensa ke karkarwa.
Allah kaɗai ya san irin wahalar da ya sha.
Ban san irin farin cikin da Abhi zai yi ba idan ya ga cewa ɗan da ya daina sa ran gani bai mutu ba.
Na ga yana ƙoƙarin tashi.
Sai na miƙe na taimaka masa ya zauna.
"Akhi, wai ba ka ganemu ba ne?" na tambaya ina kallonsa.
Sai ya ce cikin raunin murya,
"Wa ya kawo ni nan?"
Na ji zuciyata ta buga.
Sai dai jin muryarsa, wacce ta yi daidai da ta Akhi, ya sa na ƙara tabbatarwa kaina cewa shi ne.
Na ce,
"Na san za ka yi mamakin ganin kanka a nan. Mun tsince ka ne a cikin wani kango an yar da kai. Shi ya sa muka taimaka maka."
Ya zuba min ido yana kallona.
Ruman ta tashi ta fita tana share hawaye.
A hankali ya buɗe baki zai yi godiya, amma muryarsa ta kasa fitowa sosai.
Na gyada kai cikin fahimta sannan na fita.
Lokacin har hasken safiya ya bayyana.
Ni da Ruman muka zauna a daya dakin Ita ta koma barci, ni kuma na yi shiru ina tunanin abubuwan da suka faru cikin awanni goma sha biyu da suka gabata.
Duk na ƙagu na kira Abhi in tabbatar masa da samuwar Akhi.
Sai dai ina ta jujjuya waya a hannuna, ina kallon ƙofar ɗakin da yake ciki.
Na lumshe ido.
Nan take wani flashback ya dawo min na ranar da aka daure masa wuya har ya daina motsi.
Jikina ya fara rawa.
Domin babu abin da ke tayar min da hankali kamar wannan baƙar ranar.
Sai dai a lokaci guda zuciyata na son amincewa cewa watakila ba Akhi ba ne, kamar yadda Kawu ke faɗa.
Amma na kasa gasgata hakan, tunda dai mun tabbatar da mutuwarsa ne ba tare da ganin gawarsa ba.
Na tashi a hankali na doshi ɗakin.
Har lokacin yana jingine idanunsa a rufe.
Na shiga cikin nutsuwa ina son tabbatar da wani tabo da duk mutanen gidanmu suke da shi.
Wani irin alama ce da duk 'ya'yan mahaifinmu ke ɗauke da ita.
Na tsugunna tare da zame bargon da ya lullube ƙafarsa.
(To be continued...) 

Meemibashir
***