ƘWAI BIYU

Chapter Twenty Three

by @thehealerspen654

BAYAN KWANA HUƊ


Tsawon wannan kwanakin Sultan yana iya bakin ƙoƙarinsa don ganin ya kyautata wa Radiya, amma a wata siga ta musamman ba tare da ta fahimci ainahin abinda yake kwance acikin zuciyarsa ba.


Hakan ya saka ta ɗan saki ranta,  ta rage damuwa, musamman matakin da ya ɗauka na fita da ita wajen shaƙatawa da siyayya a duk lokacin da ya dawo daga office.


Hakan ya ƙara mata kwarjini da daraja sosai a idonta, kuma ta rage ɗari-ɗari dashi, duk da bata saki jikinta sosai ba, amma an samu canji babu laifi.


Misalin ƙarfe goma na dare ta gama shirin kwanciya taji ana ƙwanƙwasa mata kofa, da mamakinta ta miƙe ta buɗe ƙofar. 


"Oga asked me to called you."


Ɗaya daga cikin masu aikinta ce ta faɗa mata cike da ladabi. Ajiyar zuciya tayi sannan tace:


"Where is he?"


"Poolside garden."


"OK"


Radiya ta amsa sannan ta dawo ta sauya rigar baccin jikinta zuwa wata doguwar riga wadda ta rufe ko'ina na jikinta, sannan ta nufi ƙasan benen.


A zaune ta hango shi a baking swimming pool ya zira ƙafafunsa guda biyun acikin ruwan yana wasa dasu, gefensa kuma lemuka ne akan tray da kofunan glass guda biyu a ajiye.


Yana hangota yayi mata nuni da ta zauna kusa dashi. Bata musa ba ta cire takalminta ta zauna, tare da zira ƙafarta itama acikin ruwan.


"Kin fara bacci ko?"


"Na dai kusa."


Jinjina kansa yayi, sannan ya fara ƙoƙarin zuba musu lemo a kofunan tare da miƙo mata.


"Ina da tambayoyin da nake so ki amsa min."


Jinjina kanta tayi cike da mamaki, sannan ta karɓi kofin da ya miƙo mata tare da faɗin "thanks."


Sake kallon ta yayi a daidai lokacin da ta kai kofin lemon bakinta, sannan yace:


"So...tell me, ta yaya kika iya shirya zanga-zanga a makaranta?"


Dariya ce ta kufce mata, wadda sai da ta saka ta furzar da lemon da yake bakinta. 


Sannan ta juyo ta kalle shi tana dariya ta sake ɗauke kanta tare da ajiye kofin hannunta, ta mayar da hankalinta kan ruwan da take kaɗawa da ƙafafuwanta tana murmushi. Sannan ta fara magana:


"You know...ba yabon kai ba, ina da tausayi sosai, abinda ya faru shine, akwai course mates ɗi na guda biyu shekarar farko da muka fara karatu mahaifinsu ya rasu.


Sai muka ji shuru basu dawo school ba, to a lokacin sai naje gidansu suke faɗamin sun haƙura saboda wanda yake taimaka musu ya rasu..."


Ajiyar zuciya tayi sannan ta juyo ta kalli Sultan wanda ya tattara hankalinsa gabaɗaya kanta, ta sake kawar da kanta, sannan ta ci gaba da magana:


"Tun daga ranar abun ya dame ni na dawo na tattara classmates ɗina muka yi magana, na bada shawara akan mu taimaka musu. 


So kowa ya amince yaran suka dawo hostel in fact, suna ɗaya daga cikin  dalilin da ya saka nima na dawo hostel da zama.


A haka muke haɗa musu kayan abinci da kuɗi, sannan idan lokacin registration yayi zamu haɗa kuɗi mu biya musu. To muna cikin wannan manage ɗin, kwatsam aka ƙara kuɗin makaranta.


A nan hankalin mu ya tashi, saboda anyi multiplying komai, tausayinsu ya kama ni, because sauran students suma ƙoƙarin su biya nasu suke yi ballantana su biya musu.


Hakan ya saka ranar wata Monday bayan sallar asuba kawai na fito corridor ɗin hostel da bucket a hannuna da spoon na buga kowa ya fito..."


Dariya ce ta ƙwace mata a daidai lokacin da tazo nan. 


Shima kansa Sultan sai da yayi wani murmushi da sai da haƙoransa suka bayyana, saboda yanayin yadda take bashi labarin ya birge shi matuƙa. 


Sannan uwa uba ga karsashin da yake ji na tsananin tausayin ta da kuma jarumta.


Sai da ta daidaita kanta, sannan ta ɗauki lemon tasha sannan tacigaba da magana:


"Ina bugawa kowa ya leƙo nace haka zamu zauna muna tunanin yadda iyayenmu zasu sha wahala ko kuwa zamu fita mu nuna ƙin amincewar mu?


A lokacin kowa yayi shuru, ai kuwa wata mai suna Sonia Yoruba ce ta fito daga ita sai kneekers tace we can't watch. Tayi wani shouting sai kowa ya zabura daga mu sai nighties muka saka hijab muka fito.


To a dokar makaranta ba'a fitowa a working days ba uniforms, haka muka sakko muka fito muka zauna a gate muka yi ta kiɗa muka ɗakko kayan girkinmu muka yi girki a wajen muna ɗaga placard babu yadda management ɗin makaranta basu yi da mu ba akan mu janye, amma muka ƙi."


Murmushi Sultan yayi sannan yace:


"To ta yaya protest ɗin ya zama publicized?"


Gyara zamanta tayi sannan tace:


"Akwai social media influencers acikin mu sosai, su suka fara posting, immediately protest ɗin mu yaje viral.


Babban abinda zai baka dariya shine, da journalist suka zo aka rasa wanda zaiyi magana..."


"Sai ke?"


Sultan ya katse ta tare da tsira mata idanu.


Dariya ta sake yi sannan tace:


"Eh ni nayi magana, sannan na faɗi yadda na shirya komai. Still management ɗin makaranta suka kirani suka dinga tsoratani, sai dai basu sani ba Radiya duk duniya Ubangiji kawai take tsoro..."


"Sai kuma Abbas."


Ya sake katse ta.


Jinjina kanta tayi alamar "Eh" sannan ta ƙurawa swimming pool ɗin kallo.


Sultan ya lura yanayinta ya sauya sai ya kawar da maganar da cewa:


"Da Abbas ya sani ya kikayi?"


Murmushi ta sake yi, sannan ta gyara zaman ta sosai tace:


"Ai shi baya amfani da social media sosai, sai ranar ƙarshe an gama komai kawai sai na ganshi a school ɗin. Ranar na ga tashin hankali."


Ta ƙarasa maganar tana jujjuya kanta.


"Ina jinki."


Sultan ya faɗa tare ds sunkuyowa dab da ita.


"Tambayar farko da Yaya yayi min itace, 


Radiya Uban waye ya kawo ki hostel? 


Nace Yaya saboda ka samu sauƙin transport. 


Yace Radiya nace miki na gaji ne? 


Nace a'a, Yaya don Allah ka yafe min. 


Yace ina wannan shashashan mijin na ki da har ya barki?


Wallahi Radiya yau kin shiga uku a hannuna..."


Ta sake fashewa da dariya, shima Sultan dariyar yayi sosai saboda yadda take bada labarin ya bashi dariya sosai.


"Nan fa na dinga kuka ina ihu malaman suka dinga regret da sun sani haka nake tsoron Yaya da tun farko shi suka kirawo, da ban jawo musu magana ba, anan ne sukayi suspending ɗi na muka taho guda. 


Bayan kwana biyu wata TikTok influencer tayi video akai na, nan zance ya dawo sabo fil aka fara posting ɗin justice for Radiya..."


Suka sake fashewa da dariya gabaɗayansu.


Sannan Sultan yace:


"Wannan shine one night fame."


Tace:


"Eh mana lokaci ɗaya na zama celebrity, media houses aka dinga kirana interview, ta nan mutanen gari, government officials da NGO's suka shiga maganar. 


Da ƙyar aka sasanta na ƙarasa karatuna. Sannan kuma aka yi sponsoring ɗin yara marasa ƙarfi na makarantar.


So ranar induction ɗin mu wani Dr. Birniwa yace ya ɗauke ni aiki a asibitinsa anan na fara aiki."


Kallon ta yayi sannan ya sara mata irin na sojoji, sannan yace:


"Legendry."


Murmushi kawai tayi, sannan shuru ya biyo baya. Sannan daga bisani ta kalle shi tace:


"Nima ina da tambaya."


Sake zuba mata lemon yayi ya miƙo mata sannan ya kalli cikin idonta yace:


"Ai ban gama tawa ba."


"A'a ka jira sai nayi tawa sai ka ci gaba."


Jim, yayi sannan yace:


"OK, go ahead."


"Meyasa kake son aikin soja?"


Murmushi ya sake yi, sannan ya kalle ta yace:


"Becouse ina son doka da ka'ida."


Jinjina kanta tayi sannan tace:


"But Sauban yace kayi aure matarka ta rasu sannan ka kuma yin aure ka kore su?"


Murmushi kawai yayi sannan ya jawo laptop ɗin sa ya fara nuna mata hoton matarsa ta farko Sarah. Da nasa tun daga ranar da sukayi passing out parade har zuwa matsayin da yake kai a yanzu.


Cike da sha'awa da birgewa ta dinga kallo tare da yi wa matarsa addu'ar Allah yai mata rahma.


Sannan tace:


"Amma meyasa kayi aure da wuri haka?"


"Saboda ina son na haihu da yawa. 


Banda hakan, babu abinda zai saka nayi aure da wuri. Amma kuma sai abun yazo min da jarrabawa. Duk da naji daɗi da muka fahimci matsalar tawa da wuri kuma muka fara bincike da wuri."


Jinjina kanta Radiya tayi cike da tausawa sannan ta kalle shi tace:


"I'm sorry!"


Ajiyar zuciya yayi tare da ajiye laptop ɗin a gefe, sannan ya matso dab da ita numfashinsa yana dukan fuskarta yace:


"I have another question."


Girgiza kanta tayi saboda gabaɗaya yanayinta ya fara sauyawa saboda yadda ya matso dab da ita, ga kuma wani irin kallo mai rikitarwa da yake mata.


Hannunsa ya saka ya shafa gefen fuskarta, sannan ya saka ɗaya hannun na sa ya shafo ƙungunta ta baya tare da manna ta a jikinsa, ya ɗora ƙwayar idonsa acikin ta ta yace:


"When are you ready?"


"Right away..."


Abinda ta furta kenan jikinta yana rawa. 


Saboda ta tuna salon soyayya irin na Sultan.


Kafin tayi aune ya ɗora bakinsa akan nata.


Sai da ya tabbatar da ya gama rikitata, sannan ya miƙe tsaye ya saka hannayensa guda biyu ya ɗauke ta cancakas, ya nufi ɓangarensa da ita.