Sawun Keke
by @auntyindo
Tinda ta ɗaukeshi bai ƙara sanin inda kansa yake ba har sai da Asbah ta yi da ya ji Masallacin cikin gidansu an yi kiran Sallah sannan ya farka.
Tin kafin ya buɗe idanunsa ya ji ɗumin Mutum a kusa da shi, ya yi shiru ya na sauraren Bugun zuciyarta da ya tabbatar masa ba kowace ba ne face Razia. Cikin nutsuwa ya sauke wata nannauyar ajiyar Zuciya kafin ya buɗe idanunsa ya ɗorasu akan kyakkyawar fuskarta.
Bacci ta ke yi cikin mutsuwa da kwanciyar hankali, kallo ɗaya ya yi mata ya gane ba ƙaramin jin daɗin baccin take ba don da alamu ma ta daɗe ba ta yi me daɗinsa, a take kibiyar tausayinta ta soki Zuciyarsa, ya zuba mata ido tamkar ba zai dena kallonta ba, ya daɗe cikin wannan yanayin kafin ya ƙara janyota jikinsa ya ringumeta tsam, ya na jinta har cikin ransa.
Cikin baccinta ta ƙara jin sauyin yanayi don haka ta ƙara duƙunƙuneshi ta ja mumfashi ta sauke ta ci gaba da baccinta.
Mother ta ce shigo Ɗakin cikin suffar Mage, bayan ta zo daf da Gadon ta koma suffar Mutum, cikin tattausar muryarta ta ce "Rislan! kar ka biyewa Razia ka makara a Sallah fa."
Lumshe ido ya yi gami da sauke wani gwauron nishi kafin ya yi magana tamkar wanda aka yiwa dole "Uhm! Uwa zan tashi; ba na so na nesanta da ita ne ta farka."
Mother ta murmusa kafin ta ce "Abinda ya zama dole ne Ɗana, a Masallaci fa har an idar da Sallah."
Bai ce komai ba ya janye Razia daga jikinsa a hankali ya gyara mata kwanciya sannan ya sakko ba don ransa ya so ba, haka kawai yau ya tsinci kansa da son kasancewa tare da ita.
Ya na idar da Sallah ya yi musu Sallama ya wuce wajen su Rahma don jin yadda suka kwana.
Yau Ta kasance Ranar Alhamis, Ranar da wasu ke ɗokin zuwanta wasu kuwa su na cike da fargabar ganinta.
Sheikh Auwal, Babban Yaya, Baba Sa'idu, Akhiee
Daddy, Mommy, Muneeb, Muneer, Husnee...
Malam Kabiru, Malam Usaini
Duk sun hallara a cikin Kotun yayin da ta ɗauki shiru kowa ya mayar da nutsuwarsa akan abinda ke faruwa a cikinta.
Ana kammala sauraren ƙarar Wasu aka karanto ta su Akhiee, Me Shari'a ya buƙaci Matar da Mijinta su fito.
Bayan sun fito inda aka tanadarwa duk wanda zai yi magana su ka tsaya, Mai Shari'a Ya yiwa Husnee tambaya akan da gaske ne an Ɗaura Aure ta amsa masa da eh.
Sannan aka dawo kan Akhiee aka tuhumeshi akan amsa laifinsa sai dai shiru bai ce ƙala ba, juyin Duniya ya yi musu banza har mai Shari'a ya gaji ya ɗaga ƙarar tare da cewa Akhiee ya nemo Lauya.
Da haka aka tashi ba tare da an cimma wata matsaya ba kowa ya san inda dare ya yi masa tare da tunani iri daban-daban, musamman a ɓangaren Husnee wadda ta cika da tsoro da firgici sabida jin ya yi shiru, ta na matuƙar tsoron ya ce zai saketa.
Akhiee kuwa ko ta kansu bai ƙara bi ba shima ya kama gabansa, Su Yaya Babba sai faɗa su ke yi kamar za su ci babu, shi dai Sheikh Auwal ya yi musu banza.
Hajiya Laure
Sanye take cikin lintsumemiyar Atamfa tsadaddiya ɗinkin riga da Zani ta cokara ɗauri ture ka ga tsiya.
Cikin takun Ƙasaita ta fito Falo ɗagwas-ɗagwas kamar budurwar agwagwa. Ma'u da Talatu su na ta ƴan gyare-gyare kasancewar Yamma ce, kafin ta zauna ta kallesu fuska a dake cikin nuna ƙyama da wulaƙanci ta ce "Menene haka? wannan aiki ku ke yi ko iskanci?? wai ba na ce kar wannam ƙazamar ta ƙara shigo mini Falo ba ma??"
Ta ƙarasa maganar ta na tsare Ma'u da idanu. Ma'u kuwa tin da ta ganta jikinta ya ɗau karkarwa domin kuwa mugun tsoronta gami da tsanarta ta ke ji, ko hanya ba ta son haɗawa da ita a yanzu.
Talatu ta rissina gami da cewa "Ayi haƙuri za mu gyara."
Dogon tsaki ta lafta kafin ta ce "Ƙazamar banza tarin najasa; za ku fice ku ban wuri ko sai na daddallawa Yarinya mari?? ƴaƴan matsiyata."
Jiki na rawa Ma'u ta yi gaba ta na kuka ƙasa-ƙasa Talatu ta bi bayanta cikin sanyin jiki.
Hajiya Laure ta yi ƙwafa kafin ta karkace ta yi jaɓar a kan Sofa. wani mugun ihu ta zurmuƙa jin ta zauna akan wani abu tamkar Allura, azaba ta ratsata har tsakiyar kanta, a durƙushe ta miƙe ta ma kasa tashi tsaye sabida azaba gabaki ɗaya mazaunanta sun ɗauki wuta, lokaci guda idanunta su ka ciko da hawayen azaba.
Sai da ta ɗan huce sannan ta juya ta dudduba inda ta zauna ɗin ko za ta ga wani abu sai dai fayau ba wani abu ba alamunsa.
Canja mazauni ta yi zuwa kan kafet don kuwa ta ji attaruhu ko za ta ƙara zaman kan kujerar ba yanzu ba, a ƙasan ma a karkace ta zauna ta na yi ta na yatsine fuska don kuwa har yanzu ba ta dena jin zafi ba.
Ta na nan zaune ta na hutawa ba a fi minti biyar ba ta ji wani irin taku ƙwaras-ƙwaras ya na tinkarota, ta shiga kalle-kalle amma ta ga fayau kamar ba a taɓa halittar mutum ba, tsoro da firgici su ka ɗarsu a Zuciyarta lokaci ɗaya, Talatu ta fara ƙwalawa kira da tunanin ko itace a wajen, jin shiru kuma ga takun ta na ji ya sa ta yunƙura ta miƙe cikin sauri ta nufi hanyar da zata bar Falon.
Garam!! ƙofa ta rufe, nan take wata muguwar dariya irin ta Boka Barore ta karaɗe Kunnuwanta, Ihu ta fara kwararawa sai dai kash!! ta na farawa ta ji kamar an sa buredi an toshe mata maƙogoro muryar tata ta dena fita.
Inuwar Mace ta gani a gabanta ƴar siririya sai yalwar gashi har ƙugu shima ga inuwarsa nan buzu-buzu, Haj Laure ta ƙara zazzaro ido gwale-gwale kamar sa faɗo ƙasa, Zuciyarta na wani mugun duka tamkar ana surfe da sussuka a cikinta.
Da kyar ta samu ta taka da gudu don komawa Bedroom, ta na zuwa ƙofar bedroom ɗin taga wannan inuwar a gabanta, sai juyi take ta na kwarkwasa ga ɗan ƙugun nan tamkar na babe sai faɗin mazaunai ƴan ciri-ciri.
Wani mugun burki ta ja wanda ya sa ta kusa shiɗewa sabida Salon bugun Zuciyarta da ya canja.
Tsere su ka shiga yi ita da Inuwar a Falon ta na gumi ta na kuka ta na majina ta na yarcewa ita kuwa Inuwa ta na ci gaba da razanata, sai da ta galabaita sosai har ta kai ba ta iya tafiyar ta zube a wajen turuss!! sannan inuwar ta matso daf da ita ta na wata mahaukaciyar dariya, ba tare da ta dena dariyar ba take magana cikin murya marar daɗin ji "Ba a raina aikin Boka Barore!!!, sannan ba a cin Amanarsa a canja wuri, ba a zaginsa ko a bayan idonsa!!!!, idan ya fara yiwa mutum aiki har sai ya yi nasara yake denawa ba zai taɓa ƙyale ku ku je wajen wani Bokan bahahahaha!!!!" ta ƙarasa maganar gami da ƙaro sautin dariyarta, Ta kai minti ɗaya a haka sannan ta ɓace tamkar ba ta taɓa wanzuwa a wurin ba.
Haj Laure ba ta iya tashi ba sai ƙara bajewa da ta yi ta kwanta ta saki wani ɗanyen kuka me matuƙar taɓa Zuciya.
Su Ma'u su na fita su ka ci karo da Yazeed ya na ƙoƙarin shigowa, ya na ganinta tana kuka ya yi caraf ya riƙo hannunta, a zafafe ta fara ƙoƙarin fizgewa sai dai ya hanata damar hakan, Cikin sassanyar murya ya ce "Ki nutsu don Allah ki faɗa min abinda ke damunki, Mommy ce ko???"
A tsiwace ta ce "Ni ka ƙyaleni, ka sakar min hannuna ni ba ƴar iska ba ce wallahi, kuma zalumcin da aka yi mini Allah zai saka min."
"Ke Talatu yi tafiyarki" ya faɗa ya na kallonta, ta sunkuyar da kai sannan ta ci gaba da tafiya.....
Aunty Indo