GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)
Gadar giwa
by @auntyindo
*🪻GAƊAR GIWA...🪻*
(Toro ke Buga mata Ganga)
Ep 6
Daga Alƙalamin... Ayeesha Abdulkareem ( *INDO*)
GABA
"Alfarmarka nake nema!" Hamdan ya faɗa cikin sanyin Murya, cikin alamun kaɗuwa Ismail ya nuna Ƙirjinsa yana faɗin "Ni!!!" "Kai ɗin fa!" "Ni kuwa wannan wace irin Alfarma ce kake neman ta a gurina Hamdan Ahmad!"
"Ka bar min Hibba In Aure ta!" "What!!!" Ismail ya faÉ—a a zabure gami da zazzaro ido akan Hamdan!,,, cigaba ya yi da cewa "Wai ko dai kana Shaye-shaye ne dama?, anya a hayyacinka kake?!"
Hamdan ya yi wani murmushi mai ciwo kafin ya ce "A hayyacina nake, kuma ba na shan Komai, Martabarka ce ta sa nake neman izininka! bayan haka da sai dai ka ji ana yi!" Girgiza kai Ismail ya yi gami da furta "Yasalam!!" ya gyara zamansa sannan ya ce "Wai ni?! kuma Hibba dai kake so in bar maka wadda na yi Shekaru ina Dakon Ƙaunarta, anya kuwa ka yi min Adalci Hamdan!" runtse idanu Hamdan ya yi tare da haɗiye ƙululun damuwa wanda ya tokare maƙoshinsa.
Wurin ya ɗauki shiru na Ƴan Mintuna kafin Hamdan yace "Dama na san mawuyaci ne ka yarda!, duk da ban san adadin son da kake mata amma tabbas ina kamantawa da yadda nake son ta!" shiru ya yi tare da cije gefen leɓensa da ƙarfi, kamar ba zai ƙara magantuwa ba sai kuma ya ce "Nima ba a son raina nake ƙoƙarin raba ka da ita ba!, kai ba Abokin takara ta ba ne, ba Abokin gasa ba!, Matsayin wanda zai temake ni nake kallonka, saboda Darajarka a wurin Hibba duk ya wuce nan, idan da Kai Abokin takarata ne kawai ba zan Tsaya neman izininka ba, amma sai gashi ina nema, kuma idan ba ka Amince ba ba zan taɓa Mallakarta ba!" ya ƙarasa maganar cikin matuƙar rauni tuni hawaye ya fara sintiri akan kumatunsa.
sai a lokacin Ismail wanda tashin hankali yasa shi daskarewa wuri É—aya, ya É—an numfasa yace "Wai kana nufin Hibba ce ta sa ka yi hakan?" girgiza kai yayi alamar A'a...
Ismail ya yi murmushi wanda ya tawo tare da zafafan hawaye, "Kar ka ɓoye min gaskiya!, idan ba ita ba ce babu yadda za a yi ka zo kana min kuka don samun Aurenta!" jim! ya ɗan yi kafin ya ce "Ya tabbata Kai take so kenan!, amma Hamdan ba za ka cutar da ita ba? ba za ka sanya ta zubar da hawaye ba?, shin ba za ka taɓa juya mata baya ba Hamdan?!, Za ka iya kula da ita kamar yadda zan kula da ita????, Hibba fa Marainiya ce! don Allah kar mu yi wasa da rayuwarta saboda ganin Mun fi ƙarfinta!" kukan da ya ci ƙarfinsa ne yasa shi dole ya yi shiru da bakinsa...
Wata muguwar bugawa gami da hargitsawa zuciyar Hamdan ta shiga yi, ya buÉ—e idanunsa tas! akan Ismail yayin da wasu abubuwa barkatai suke rikitowa cikin tunaninsa, girgiza kai kawai ya shiga yi yana son furta wani abun amma hakan ya gagara sai wasu zafafan Hawaye da suke yiwa fuskarsa wanka.... ya rasa me yasa a duk lokacin da aka yi masa magana makamanciyar wadda Ismail ya yi sai ya ji wani irin tashin hankali da ruÉ—ani sun shigo tunaninsa, sai ya ji gabakiÉ—aya ya rasa amsa da ze bayar Eh! ce ko A'a!!??, ba ya iya hasashen ta yadda zai cika wannan duk sharuÉ—an da ake Gindaya masa akanta.
Shiru wajen ya É—auka sai shashshekar kuka kawai ke tashi....
Sai da ƙyar Isma'il ya saita nutsuwarsa gami qda dakatar da kukan, ya kalli Hamdan cikin rawar murya irin ta me kuka ya ce "Na yi wa kaina Alƙawarin ba zan bari ta yi kuka ta sanadi na ba!, don Haka kamar yadda take kirana Yayanta zan cigaba da kasancewa haka, kuma zan yi mata abin da duk Yaya na Ƙwarai ke yi wa Ƙanwarsa!" tsagaitawa ya yi ya goge ƙwalla sannan ya cigaba "Na ba ka dama ka Auri Hibba, amma don Allah kar ka zamo makamin Tarwatsa farincikinta, ka yi duk ƙoƙarinka wajen zamo mata Bango a rayuwa!, kar ka bari a wulaƙanta ta,,, idan ka yi min haka ka gama min Komai!!, ina yi muku fatan alkairi!"
cikin matsanancin kuka Hamdan ya ce "Ba Godiya kaÉ—ai ya kamata in yi maka ba! don ka yi min abin da ba kowa ne zai iya yi min ba ko a cikin Dangina, kai ma Allah ya yi maka ninkin Alkairin da ka yi min!, kuma in Allah ya yarda zan cika maka burinka!!"
Jinjina kai Isma'il ya yi gami da miƙewa, cikin sanyi ya ja ƙafafunsa da suka yi masa nauyi ya nufi hanyar cikin Gidan,, Hamdan ma tashi ya yi ya nufi bakin gate don sanin inda dare ya yi masa, yana tafiya yana zabga kukansa wanda tsayar da shi ya gagare shi.
Ido Hajja Halima ta zubawa Tilon Ɗan nata yayin da Zuciyarta ke raɗaɗi da ƙuna don ganin halin da yake ciki...
"Amma Ismail yarinyar da har ta yarda da kai shi ne saboda ka fara zaucewa ka ce wani ya Aure ta?! kai kuma wa za ka Aura kenan??, wai ina hankalinka ya tafi ne?? ya za ka yi da son da kake mata kai kuma??, wani ya rayu kai ka Mutu kenan ko???" ya sani sarai idan bai danne damuwarsa ba babu yadda za a yi Mahaifiyarsa ta danne tata, dan haka ya ƙaƙalo murmushi ya ɗora akan hawayen da yake yi, cikin son nuna rashin damuwa ya ce "Wannan tambayoyi da yawa haka Ummina!" "Kar ka ce za ka maida abun nan wasa Ismail!, ni fa na san yadda ka daɗe kana sonta, kuma ma ai tafi dacewa da kai!, yanzu wa zaka Aura kenan?" "Duk abin da muka tsara muka ga bai faru ba to ba haka Allah ya tsara mana shi ba, maybe tawa Matar daban take shi yasa hakan ta faru, Ummi ke kika ce min in dinga sadaukar da farincikina domin samar da farincikin wanda nafi ƙarfinsu da wanda suke nema a gurina, yanzu ma irin wannan sadaukarwar na yi Ummi, koda Hibba ba ta son Hamdan zan iya bar masa ita, rayuwar Duniya nawa take! ina da damar temaka masa bai kamata in jefa shi cikin ƙunci saboda in samu nawa farincikin ba!!, idan nanyi masa alkairi ni kuma nanyi haƙuri nanyi tawakkali ga Allah da sannu za ki ga ya saka min da Alkairi nima, don Allah ki yarda dani Ummina!".....
Aunty Indo