GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

Gadar giwa

by @auntyindo

Gwauron numfashi ta sauke kafin tace "Shikenan na yarda da kai! Allah yai maka albarka" amsawa ya yi da "Amin sannan ya tashi ya wuce Bedroom"

  Sai da yayi wanka ya gabatar da sallar Magrib sannan ya ɗauki wayarsa ya kunna Data ya zuba mata ido cike da rashin sanin abun yi.
   Cin karo yayi da Saƙon gayyatar Hibba kamar haka "Don Allah Yaya Ismail idan ka samu lokaci ka zo Gidanmu, ina son mu yi magana ne amma ka yi haƙuri ba mai daɗi ba ce, idan kuma kana da uzuri sai mu yi maganar a waya!" sai da ya karanta aƙalla sau biyar kafin ya ba ta amsa da "Zan zo gobe da safe in Allah ya kaimu!"


         BAYA....

   Sai bayan Ƴan kwanaki Hamdan ya samu ya ƙwarara wa kansa Gwiwa sannan ya yanke hukuncin Tunkarar Isma'il cikin shirin Faɗuwa ko Nasara.
    Saƙon neman izinin haɗuwa ya fara tura masa a lambar da Hibba ta ba shi, cikin sa,a ba jayayya Ismail ya amsa tare da cewa ya zo Gidansu sai su yi magana anan.

    Da yamma ya shirya ya tunkari Gidan cikin sanyin jiki da fargaba.
   a harabar gidan akamyi masa masauki cikin wata rumfa wadda aka ƙawata da gujeru da ƴan tsirrai.

    Cikin sakin fuska Ismail ya ce "Hamdan Ahmad Mai Matasa! Matashin Ɗan Kasuwa mai ci a Yanzu Barka da zuwa!" Hamdan ya murmusa ya ce "Wato ka binciko Tarihina ko?!" Cikin fara,a Ismail ya ce "Hakan nauyi ne da ya rataya a kafaɗuna!, ya zama dole na in san waye yake kusantar Hibba, domin ko babu SO Tamkar Ƙanwa take a gurina!" Hamdan ya ƙara faɗaɗa murmushinsa gami da cewa "Gaskiya hakan yana da matuƙar kyau, shi yasa kake na musamman a gurinta!"
   Ismail ya ɗan murmusa ya ce "Amma na yi mamakin ganinka a nan fa!, ina nufin mamaki da ka nemi haɗuwa da ni duk da cewar ni ba wani Babban Ɗan Kasuwa ba ne !" "Oh! kai ma zolayata za ka yi kenan?, Ɗan Kasuwa ai sunansa ɗan Kasuwa da ƙarami da babba duk Ɗaya ne, sai dai ka ce kowa ɓangarensa daban!" "Haka ne! to ya ake ciki ne Allah yasa ba laifi nayi ba Yallaɓai!" Ismail yayi maganar cikin sakin fuska.
 Hamdan ya yi Ƙasa da kai tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, sai da ya yi da gaske sannan ya iya cewa "Alfarmarka nake nema!" ya faɗa cikin sanyin Murya, cikin alamun kaɗuwa Ismail ya nuna Ƙirjinsa yana faɗin "Ni!!!" "Kai ɗin fa!" "Ni kuwa wannan wace irin Alfarma ce kake nemanta a gurina Hamdan Ahmad!" "KA BAR MIN HIBBA IN AURETA!"...............

     Cigaban labari.....

       Hibba, Maama, suna zaune a tsakar gida suna ɗan taɓa Hira Khalil ya shigo tare da sallama, bai jira an amsa ba ya ce "Yaya Hibba Ya Hamdan yana kiran ki!" rass!!!! gabanta ya faɗi, ta ɗan yi gyaran murya sannan ta ce "Kuma da tsohon daren nan?!" "Na ce masa ba kya fita da daddare ya ce wai ki yi haƙuri ba daɗewa za ki yi ba!" Khalil ya ba ta amsa.

   Ɗan kallon Maama ta yi don ganin alamominta, sai kuwa suka haɗa ido karaf!!, da sauri ta yi ƙas da kai ta fara wasa da ƴan yatsunta.
Maama ta ce " Ki je ki ji, amma fa kar ki daɗe ɗin!"
  amsawa ta yi tare da tashi cikin sauri ta zari Hijab ta yi waje.

 Yana tsaye a jikin mota ya yi jugum!! yana tsammanin warabbuka.
Ganin ta fito yasa ya gyara tsayuwarsa gami da zuba mata idanunsa da suke zafi saboda kukan da ya sha.
   Ido ta zuba masa itama suka shiga kallon-kallo... Hibba ce ta yi ƙoƙarin katse shirun da cewa "Yanzu ka zo da daddare haka?" ya jinjina kai kafin ya ce "Na zo ne in gaya miki na samu Ismail mun yi magana, kuma ya ce ya amince in Aure ki, yanzu kawai lokaci za ki sa min!"
     Murmushi ne ya bayyana akan furskarta, ta ɗan juya masa baya gami da jingina a jikin Mota, "Allah sarki Ismail dama na san zai Amince bawan Allah, yanzu shi ke nan kuma na rabu da shi?? shi ke nan mun yiwa juna tazara??!" abin da take faɗe kenan a cikin ranta,,, Hamdan ya katse mata tunanin da cewa "Kin yi shiru, ki ce wani abu mana! yanzu me zan yi nan gaba?!" juyowa ta yi ta ɗan kalle shi ta kawar da kai ta ce "Don ka faɗa kuma sai in yarda ba tare da bincike ba?, zan tambaye shi da kaina" "To na yarda, ai tundɗ da ina da gaskiyata ba zan karaya ba, amma dai da zarar kin tambaye shi sai mu yi Aure ko?!" bata san lokacin da murmushi ya kufce mata ba saboda jin abin da ya ce,,, ganin tana murmushi yasa shi washe baki, sai ya ji ta ce "Sai ka je ka fara tunanin ta yadda za ka shawo kan Danginka, don ka samu an Karɓi Soyayyarka ba shi ne kake da tabbacin Aure ba ai, Hangen Dala ne kake yi!" lokaci guda jikinsa ya yi sanyi tuɓis!! duk annurin fuskarsa ya ɗauke, cikin sanyin murya ya ce "Amma ta yaya zan iya shawo kansu bakiɗaya?!" "Oh tambayata kake yi?, kenan ba ka san yadda zaka gabatar da ni ma a gurinsu ba ko? a haka kake bayanin daga yanzu sai Aure, to akwai sauran aiki a gabanka!, idan kuma ba ka yi sai ka bawa wasu guri!"
  "Ki yi haƙuri ! kawai daman na ɗan nemi shawararki ne, saboda ba ni sa wanda zan yi magana da shi don samun ƙwarin gwiwa, amma karki damu zan yi komai da kaina, yanzu ki koma Gida zan je in yi tunani, duk yadda mukai dasu za ki ji ni!" Hibba ta yi wani murmushi wanda yafi kuka ciwo, ta kwana da sanin ko kowa ya Amince da alaƙarsu to fa Hajiya Madina Mahaifiyarsa ko ta sha Giyar wake ba za ta Yarda ba, don da alama bayan raini da ƙasƙantarwa akwai Ƙiyayyar Maama da Ƴaƴanta a ran matar, a tunanin Hibba kenan....
Ba ta tsaya ba shi amsa ba ta wuce cikin gida, ya rakata da ido har ta shige sannan shi ma ya nufi nasu Gidan.



*Aunty INDO*