GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)
Gadar giwa
by @auntyindo
Daren yau....... Dare ne da ya kasance mai matuƙar tsauri a Rayuwar Mutum uku!, kuma Dare mafi tsayi me cike da ɗumbin Ƙalubale da damuwa!.
Hamdan, Ismail, Hibba, dukkan su babu wanda zai ce ya yi wata runtsawa ƙwaƙƙwara da sunan bacci, sai dai Ɓarawo irin wanda yinsa ma babu Riba.
Washegari....
Tun da wuri Ismail ya cika alƙawarin da ya ɗauka na zuwa Gidan su Hibbah!...
Sai da ta yi kuka mai isarta kafin ta iya sako ƙafarta a Ƴar madaidaiciyar Harabar Gidansu, wani zazzafan abu ta ji ya tsarga mata tun daga tsakiyar kanta har tafin ƙafa da duk ilahirin jikinta lokacin da idanunta biyu suka faɗa cikin na Ismail.
Kasa gaba ta yi sai ta jingina a bango tare da sauke wani gwauron numfashi gami da lumshe idonta dake shirin zubar da hawaye.
Ismail ya murmusa kafin ya tako zuwa inda take cikin yanayin nutsuwa da kamala, a ɗan gefenta ya tsaya kafin ya ce "Ƙanwata barka da Safiya!" jinjina kai kawai ta iya yi, sai kuma ta ce "Ashe Khalil bai ba ka Kujera ba?, bari in ɗauko!" ba ta jira amsar shi ba ta juya zuwa ciki.
Ba daɗewa ta fito da Kujerun roba guda biyu irin na saukar Baƙi, ta miƙa masa guda ɗaya ya zauna sannan ita ma ta zauna.
Shiru ne ya ƙara ratsa tsakani kafin ta ɗan kalleshi ta kawar da kai ta ce "Ina kwana Yaya Ismail!" "Lafiya lau da fatan dai kina lafiya" "Lafiya lau" shirun dai suka ƙara yi har na ƴan Mintuna kafin Hibba ta ƙoƙarta nemo Juriya da jarumta ta ɗora wa kanta sannan ta ce "Ka yi haƙuri da abin da zaka ji daga gare ni don Allah" Ya ɗan jinjina kai yana murmushi cike da son ƙwarara mata gwiwa, ƙasa ta yi da kai ta ce "Kamar yadda na faɗa maka na tsaya na nutsu na saurari Alƙiblar da zuciyata ta kalla" ta ɗan tsahirta kafin ta cigaba "Tabbas ina son Hamdan!, amma ba don ba na sonka ba ne, ba kuma ba ka cancanta ba!, sai dai ba mu muke tsarawa kanmu yadda zamu Kamu da So ba, ka yi haƙuri bisa hakan Yaya Ismail!" ta ƙarasa maganar cikin rawar murya, "Ba laifi kika yi ba bare ki bada haƙuri, hasali ma kin yi abun in yaba miki a matsayina na Yayanki, don na fi so in ga kin tsaya kan Gaskiya, kuma kaifi ɗaya" Jim! ya ɗan yi kafin ya ce "Don Allah ko zan iya samun alfarmar zama Yayanki?!, kamar yadda kike kirana Yaya a Baya ina so hakan ta cigaba fiye da Da don ina so ki Maye gurbin Ƙanwata da ba ta raye!" "Ni ya kamata in nemi wannan Alfarmar ai!, domin kowace Ƙanwa za ta yi alfaharin samun Yaya irinka!, na gode da ba ni farinciki da kake yi a rayuwata kana da matuƙar muhimmanci gareni fiye da yadda bakina zai furta"
Ya murmusa gami da cewa "Hibbah! Allah ya yi wa rayuwarku Albarka, in sha Allah tun daga jiya na kawar da maganar alaƙar soyayya tsakanina da ke, a yanzu sai zallar alaƙar dangantaka, ki ragewa kanki damuwar nan ki yi farinciki Ƙanwata!" gyaɗa kai ta yi tana goge ƙwalla...
Sun dan jima a haka babu wanda ya ƙara magana sannan Ismail ya tashi gami da cewa "Zan wuce, idan akwai wata matsala ki gaya min, ba a matsayin Ismail na Da ba, a matsayin Ismail na yanzu wanda Ɗa ne a Gurin Maa-ma da Abba!" tunda ya fara magana ta zuba masa ido, tana jin wani yanayi na ratsa ta wanda ta kasa bambance Farinciki ne kokuma Damuwar rabuwarsu a matsayin Masoya, Tabbas idan ta ce ba ta son sa ta yi Ƙarya sai dai Hamdan ya danne tasirin duk son da take wa Ismail ɗin.
Ta gyaɗa masa kai tana ƙoƙarin yin murmushi sai dai kukan da yake cinta ya hana murmushin nata bayyana yadda ya dace.
Ki gaisar min da su Maama!" Ismail ya faɗa tare da yin gaba, da sauri ta miƙe tare da furta sunansa cikin wata kalar murya me taɓa zuciyar duk wanda ya ji ta!, ido kawai ya zuba mata alamar yana jinta "Amma ba za ka damu ba ko ?" ya saki wani murmushi wanda ya fito tun daga ƙasan Zuciyarsa, cikin sassanyar murya me cike da nutsuwa ya ce "Zan damu Hibbah!, amma ba damuwar da za ta hana Ƙanwata farinciki ba, damuwar da zata ƙara min Kusanci da Ubangijina domin shi ne zai canja min abunda ke damun Zuciyata! daga So ya koma Ƙauna ta Jini!, ki je gida kuma saura ki ƙi gayawa Maama ina gaisheta!"
ya ƙarasa maganar cikin fara'a, murmushi ta yi tana cewa "Zan gaya mata!"
jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba ya fice.
Cikin matuƙar sanyin jiki ta koma cikin gida ta tarar da Maama tana Karya kumallo, cikin murya me nuna alamar an yi kuka an bari ta ce "Yaya Ismail yana gaisheki!" "Ina amsawa, ya Umman tashi?" "Tana lafiya lau" "To Madallah!" Mama ta faɗa gami da tausa Laumar Buredi da Ƙwai da take ci.
"To fa! Hajiya Maama irin wannan danna Ɗa'ami haka?" Hibba ta faɗa tana Ƴar dariya, Maama ta murmusa ta ce "In ku kun ƙi ci mu se mu ci ai" "A'a nima zan ci" Hibba ta ce tare da kinkimo tray ɗin da ke gaban Maama, "Subhanallahi! ya za ki kwashe min duka!" Maama ta faɗa cikin fara'a cike da son kawar da damuwar Ƴar tata, ai kuwa Hibba ta ƙara fashewa da dariya tana cewa "To fa! Maama kin ƙaro ci da alama, don yadda kike cin abincin nan wani kan wani ya nuna hakan!" ""Ke ni ba ni nan, dama cewa na yi gwara in ci kafin ki zo, don ku cikin Yara gareku yanzu sai ki cinye komai ki bar ni!" ta faɗa tana janyo tray ɗin gabanta, lafewa a jikinta Hibba ta yi tana ƴar dariya gami da sauke ajiyar Zuciya akai-akai.
Jin dumin Mahaifiyarta ya sa ta ji nutsuwa ta ratsa har ƙwaƙwalwarta cikin ƴan mintuna da basu wuce Biyar ba bacci me nauyi yayi awon gaba da ita.
Hamdan
Kamar Mara lafiya haka ya tashi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa, ba damuwarsa yanayin da ya tsinci kansa ba, kawai tunanin ta sigar da ze tunkari Iyayensa da maganar Auren Hibba yake yi, "Fito na fito zan yi da su?, gaya musu gaskiyar Sirrin zuciyata zannyi? kokuma ra'ayinsu ya kamata in bi?" wannan tambayoyin su suka fi yamutsa tunaninsa tun daga dare har zuwa wannan Safiyar, "Kuskure ne yin fito na fito da su, kamar yadda yake kuskure gaya musu Sirrin zuciyarka domin hakan kamar bayyana rauninka ne, wanda da shi za a yi amfani wajen Yaƙarka, dubara ɗaya ce ɓoye Sirrin Zuciya da kuma tambayar izininsu cikin Dubara!" Wani sashi na Zuciyarsa ke ba shi wannan shawarar wadda ta yi matuƙar karɓuwa a sauran sassan zuciyar tashi.
Matakin Ɓoye damuwarsa ya fara ɗauka tare da dawo da hayyacinsa ta ƙarfi da yaji, duk mu'amalarsa da yanayinsa na da yayi matuƙar ƙoƙari wajen dawo da du.
Cikin Ƴan Kwanaki Hamdan ya dawo wanda kowa ya sani a baya, Ammy da Daddy sai murna suke yi Hamdan ya dawo hayyacinsa, musamman yadda ya mayar da hankali akan Kasuwanci, daman shi ne Burinsu akansa sai kuma Ammy da abun ya zamo mata biyu, ta kafa ta tsare wajen hana shigowar wata rayuwarsa bayan Farida Ƴar Ƙawarta kamar yadda suka tsara........
Aunty Indo