GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

Gadar giwa

by @auntyindo




Mutum ne shi me matuƙar jajircewa akan nemansa, ga Basirar tsarawa da iya tafiyar da Kasuwanci, ha kuma Uwa Uba Nasibi da Farin jini da Allah ya ba shi, hakan yasa Daddy ya fi jansa cikin Kasuwancinsa fiye da duk Ƴaƴansa, ya fi nuna masa dukkan wata lugga da Sirrukansa na Kasuwanci, kuma tun daga lokacin da ya ja Hamdan ɗin cikin neman nasa Arziki ya ƙara cin uban na Da, komai Ƙara haɓɓaka yake yi, duk da kuwa shi ma Hamdan a karan Kansa yana da nashi Kasuwancin wato Order Kayan Tufafi da Sararwa Manyan Ƴan Kasuwa, wannan Dalilin ya sa Ammy ta ɗora So da Ƙauna da kuma Ƙazamin Burinta a kansa, ala kulli yaumin burinta ya zama Shugaba a fannin Kasuwancin Mahaifin nasa tun kafin Ƙannensa Ƴaƴan Mamy su yi tasiri a ciki, kuma ko a yanzu tana matuƙar cin gajiyar hakan, don ta silar Ɗan nata ta samu ƙarfi da Martaba, shi kan shi Daddy ya fi martaba ta da nuna mata ƙauna a yanzu fiye da Da, a nashi bahagon tunanin ita ce ta haifa Masa ɗan da yake Alfahari da shi, ita kuwa hakan ƙara mata Ƙaimi yake wajen nuna ƙafafa da faɗin rai da aiwatar da duk abunda ta ga dama, ta taka wanda take so ta ci mutunci wanda ta so.

       Maama tana zaune a Kitchen tana kwashe Tuwon Shinkafa da ta tuƙa Yaro ya yi Sallama , amsawa tanyi cikin ɗaga murya tare da tambayar waye, yaron ya ce "Wai Hibba ta zo in ji Kabeer " dim!! gabanta ya faɗi har ƙasa, "Hasbunallahu wa ni'imal wakil!" ta faɗa gami da tashi daga gaban tuwon nata, jikinta na rawa ta fito tana cewa yaron "Wane ne kuma Kabeer ka je ka tambaye shi daga ina waye shi?" yaron ya amsa tare da ficewa cikin sauri.

 "Ya salam, Ya Allah ka sauƙaƙa wannan lamari, Allah ka sa ba wata sabuwar jarrabawar ce ta shigo rayuwar ƴar nan ba!"
   Tana tsaye tana sallallamin yaron ya dawo yana cewa "Maama wai ya ce Kabeer Mukhtar Ɗan Dubai ne wai shi Yayan Anti Hibba ne" "Ya salam shi kuwa yaron nan har faɗe yake cikin karsashi!" Maama ta faɗa murya ƙasa-ƙasa, ɗan jim! ta yi tana shawara da zuciyarta kafin ta cewa yaron "Ka ce masa Maama tana zuwa!" ba musu yaro ya fita da gudu dan isar da saƙo.

  Sai da ƙyar Maama ta danne zuciyarta da ke bugun Shalugude ta saɓa mayafi ta fita wajen Kabeer, "Ina wuni" ya faɗa yana kawar da kai daga kallonta, cikin rashin nuna muhimmanci.

  " Lafiya lau Kabeer ya su Baban naka da Umman taka?" "Lafiya" ya amsa a taƙaice fuska ba yabo ba fallasa, don shi bai so ganin Maama ba ya so Hibban kawai ya samu, Maama ta yi murmushin takaici a ranta tana jinjina lamarin na Ahalinta, wai Ɗan cikinta ne nan yake gaisheta tamkar wata Baiwar gidansu, wai a hakan ma ta samu Mutunci ne ta silar Ƴarta, kafin yanzu ma ai ba ta samu Darajar da za a ɗaga baki a ce mata Ina wuni ba.

   Nisawa ta yi kafin ta ce "Yaro ya ce kana neman Hibba, gashi Hibban ba ta nan ta je suna a Dangin Mahaifinta, sai na ce bari in fito in ji da fatan dai ba laifi ta yi ba!"  
  lokaci guda Annurin fuskarsa ya ƙarasa gushewa, wani mugun takaici ya kama shi, 
tabbas da ya dan ba ta nan da bai zo a yau ba.
   Mazewa ya yi ya ce "No! ba ta yi laifin komai ba" shiru suka yi kowa da abun da yake tunani.

  Nan take tunanin Kabeer ya canja daga shiru zuwa yin magana ta hanyar gabatar da kansa ga Maama cikin ɗan sakin fuska dan kansa ya kawo haske, a tunaninsa zai iya samun ƙafa ta hanyar Maama don ya tuna yadda ya ga Hibba kar take kallon kowa, za ta iya kawo masa matsala.
   "Maama dama wallahi ina neman Hibba ne saboda ina so mu gaisa, mu ɗan daidaita tsakaninmu mu fahimci juna, na ɗan daɗe ma ina sa ran zuwa to kuma ina shakka kar ta ƙi Yarda da Soyayyata!" Maama ta faɗaɗa murmushinta tana cewa "Ah! ma sha Allah, ai dama irin wannan gwara a yi tambaya maganin zama cikin rashin sani!" ido ya zuba wa Maama cikin rashin fahimta ya ce "Rashin sani kuma?" "Eh rashin sani mana, Saboda an riga an gama Magana da wani daban, ba ma magana ba saura ƙiris ya rage Aurensu don komai ya kammala" wannan ƙaryar Maama ta zunduma masa don ta haka ne za ta raba Ƴarta da Ƙaya.
   
  Dandanan Kabeer ya haɗe rai kamar Dare!, tarin takaici da baƙin ciki suka yi masa katutu, a ƙufule ya ce "Wai da gaske?, kuma yanzu babu wata ƴar alfarma da za a yi min a ba ni dama?" Maama ta girgiza kai ta ce "Ba abu ne mai yuwuwa ba, don in banda an ɗaga Bikin ma da tuni an yi , yanzun haka kuma an kusa in sha Allah, sai dai ka yi haƙuri kawai don Allah kar ka kawo mana tangarɗa!"
   zuba mata ido yanyi kafin ya shige mota a fusace, ko sallama bai yi mata ba ya bawa Motarsa wuta... Wani mugun takaici ya turnuƙe zuciyarsa, ya yi zaton ko dan Kuɗin Mahaifinsa da ƙaunar da ake musu a Family zai sa Hibba da Mamanta su bada haɗin kai, sai gashi ya ga akasin hakan har wani shata masa layi ake, duk sai ya ji ya tozarta, haushi da takaici suka yi cunkus a ransa.

       Haka rayuwar ta cigaba da tafiya kowa da abun da ya dame shi....

    Hamdan
Cikin sanɗa ya shigo Falon Daddy yana kalle-kalle don ganin ba wanda yake kallon sa, sai da ya tabbatar da hakan sannan ya ƙarasa inda Daddy ke zaune yana latse-latse a laptop.

  "Barka da warhaka Dad!" ya faɗa tare da zama a gefe.
Ba tare da ya kalle shi ba ya ce "Da alama dai akwai magana ne, to ina jin ka" Hamdan ya ɗan numfasa tare da aro jarumta sannan ya ce "Maganar tana da muhimmanci sosai Daddy dama ka ajiye abun nan" ture Laptop ɗin Daddy ya yi tare da mayar da duk hankalinsa kan Hamdan don a zatonsa maganar da suka fi yi ce wato ta Kasuwanci.

  "Daddy!" Hamdan ya kira shi cikin sassanyar murya, "My Son! tell me" Daddy ya faɗa shi ma cikin salon shagwaɓa kamar yadda Hamdan ya yi magana.

  ɗan murmushi Hamdan ya yi yana tuno yadda Daddyn nasa zai haɗe rai ya ajiye barkwancin nan bayan jin abun da ke tafe da shi, "Daddy dama akan abin da ya shafi rayuwa ne, ina neman izininku don ina son Auren Hibbah ƴar Mommu Amina!" .

Hasashen Hamdan shi ne ya tabbata, cikin sauri Daddy ya turɓune fuska gami da faɗin "What?!" yana zaro wa Hamdan idanu.


Aunty INDO