PAGE 14
*RAGAYAR DUTSE.*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 014.*
A zaune ya same su suna hira ita da Saleem shima ya zauna ya shiga sahun hirar.
Tun suna zaman daɗin rai har suka gaji, ta koma ɗakin ta sake dawowa ta zauna, suma suka koma ɗakin. Kiran sallar azahar ya saka Saleem da Muslim fitowa daga ɗakin, suka kalle ta tana inda take a zaune.
Muslim ya ce, "zamu wuce masallaci."
Ta ɗaga kai suka sauka ita kuma ta rufe ido cike da gajiya da kasala.
Ƙaramin bacci ne ya fara ɗaukarta, a lokacin Jazy ya buɗe ƙofa ya kalli inda take, ya ganta a zaune akan kujera ta ɗora ƙafa kan ɗaya amma idanunta a rufe.
Ya ɗauke kai, ya fito ya yi knocking ɗakin Ray ya buɗe masa ya shiga. Ƙarar rufe ƙofar da Jazy ya yi ya saka ta buɗe ido, ta miƙe zaune ta nufi ɗakin dan ta yi sallah.
Jazy yana shiga ya bi Ray da kallo da yake sanye da ƙananun kaya marasa tsaho. Ya ce, "har ka dawo daga sallar ne?."
"Ban je ba, a nan na yi."
"okay, ƙarfe nawa zamu wuce?."
"Ban sani ba nima."
Jafar ya zauna yana kallon sa ya ce, "ƙarya ka ke, duk bala'i yau sai mun koma gida wallahi."
Shi dai bai ce komai ba ya waya da ya ɗauka yana dannawa.
Jazy ya ce, "wannan room ɗin na kusa da naka, ashe wani babban ɗan siyasa ne a ciki, ya gayyato wata yarinya ta taya shi kwana, yanzu zancen da nake yi maka ta yi masa sata ta gudu."
Ray ya ce, "Allah ya ƙara, saboda son tonawa kai asiri ne ya saka suke son suke mu'amala da ƴan nigeria. In iskancin ka ke so ka je ka smau baturiya, babu sata balle yi maka video ta yaɗa."
Jafar ya taɓe baki ya ce, "matsalar su ce ba tamu ba."
"Na ga yarinyar, kuma na ga fuskar ta, har bayan ta wuce ya leƙo yana cewa ta manta facemask ɗin ta."
Jazy ya kalle sa ta ƙasan ido ya ce, "zaka taya sa bincike a kamata kenan?."
"Da zan ganta kyauta zan yi mata, ta ci kuɗinta hankali a kwance."
Ya yi dariya ya ce, "ka shirya kawai malam, ina so na ci girkin Mummyna wallahi."
Ray ya kwanta ya ce, "bacci zan yi, zuwa dare sai mu koma."
Jafar ya miƙe ya ce, "wallahi zaka neme ni ka rasa, domin bazan tsaya kana wahalar dani ba. In ba dan Mamy ba, bazan tsaya ina saurarenka kana abinda ka ga dama ba, kaima ka san baka isa ba" ya faɗa yana fita daga ɗakin.
Kallon inda Islaha ta zauna ɗazu ya yi, bata nan amma akwai id card ɗinta a wajan. Kamar bazai ƙarasa ba, sai ya ƙarasa dan ya duba, haka kawai bai yarda da ita ba.
Ya ɗauki Id card ɗin yana kallo, ya girgiza kai a bayyane ya ce, "no wonder, ashe yar jarida ce."
A daidai lokacin Islaha ta fito daga ɗakin ta ƙaraso wajan.
Suka haɗa ido da Jazy, kamar a mafarki ta ganshi yana kallon ta, ta ƙaraso da sauri ta ce, "Good day Mr Jafar."
Ya bita da kallon up and down, ya ƙi yi mata magana sai kallonta kawai yake yi kamar mai son gano wani abun a jikinta. Islaha itama kallonsa take yi kamar yadda yake kallonta, tana jira ya amsa mata.
Kamar bazai ce komai ba, sai daga baya, cikin yanga da jan aji ya ce, "so why are you following me?."
Ta kalle sa tana ɗan murmushi ta ce, "I'm not following you, sir. I don't even know you personally. My colleagues were the ones who showed me your picture."
Ya kalli Id card ɗinta ya kalle ta, kafin ya yi magana ta ce, "zan iya samun lokacinka?."
Fuskarsa babu walawala ya ce, "for?."
"A few questions sir."
Ya ɗan girgiza kai ya ce, "So you've been following me just to ask me a questions?."
"Yes, Mr Jafar."
Ya ɗan taɓe baki yana girgiza kai, zai yi magana ta ce, "don Allah, give me a chance."
A lokacin Saleem da Muslim suka zo wajan suna kallonsu da mamaki. Jafar ya bisu da kallo, ya kalle ta ta yi sauri ta ce, "there are my colleagues."
Ya ɗan kalle su kafin ya ce wani abu ta sake cewa, "please Sir."
Ya ɗan kalle ta ya ɗauke kai, yana kallon ɗakin da Rehaan yake, ya sake kallon ta ya ce, "Okay, come in" ya faɗa yana shiga ɗakin da yake.
Ta juya ta kalli su Saleem, Saleem ya yi mata alamar da ta shiga kar ta ɓata lokaci, ta daidaita nustuwarta ta riƙe handbag ɗinta ta shiga da sallama.
Ya amsa yana zama a akan kujera ya nuna mata wacce take kallonsa ya ce ta zauna.
Ƙarewa ɗakin kallo take yi, ganin kamar ba a hotel ɗaya suke ba, ganin ɗakinsa mai kyau da girma fiye da nasu, komai na ciki luxury, ga sanyi da ƙhamshi mai daɗi da yake yi.
Bayan ta zauna, ya ɗora ƙafa kan ɗaya yana juya id card ɗinta a hannunsa. Kafin ta yi magana ya ce, "Miss Islaha from toron guiwa tv."
Ta girgiza kai ta ce, "Yes, Mr Jaafar."
Sai ya canja harshe zuwa hausa ya ce, "okay ina ina jinki, me ke tafe dake?."
Da mamaki ta kalle sa, dan gaskiya bata ɗauaka yana jin hausa ba, ta ɗauka turanci kaɗai yake ji, ko fulfulde bata saka a ranta yana ji ba, tunda ance ba a nan suke rayuwa ba. Gayen ya burge ta sosai, dan ya haɗu, irin ƙarshen haɗuwar nan.
Ta ɗan yi ajiyar zuciya cikim nutsuwa ta ce, "Sunana Islaha daga toron guiwa tv, na zo nan dan na bawa Mr Rehaan invitation, da neman izinin hira dashi."
Ya ɗan buɗe ido da mamaki ya ce, "ya aka yi ki ka san Rehaan yana nan?."
Ta ɗan yi murmuahi ta ce, "ban sani ba Sir, Chairman ne ya kira ni tun daren jiya, ya ce na shirya zuwa nan na haɗu dashi."
"Shi Chairman ɗin na ku ya aka yi ya sani?."
"I don't know Sir."
"You know, miss Islaha."
Ta ɗan yi murmushi ta ce, "Sir in na sani bazan ƙi sanar da kai ba, ban san ya aka yi ya sani ba."
"Well, in baza ki faɗa min ba za ki iya tashi ki fita" ya faɗa yana nuna mata ƙofa.
Islaha ta ɗan yi shiru, in ta fita ta rasa damar ta, sannan in ta faɗa masa ta zama maƙaryaciya.
Ta ɗan yi murmushi ta ce, "zan iya zuwa na tambayi abokan aikina akan hakan? Amma sai ka bani dama" ta faɗa cikin muryarta mai sanyi tana kallon sa.
Ya ɗaga mata kai alamun ta je, ta yi godiya ta miƙe ta fita.
Jazy ya girgiza kai ya ce, "Lallai akwai ƙaramin yaƙi, ashe har an san da labarin dawowarsa, duk wanda ya yi gangancin fitar da labarin nan shi da Rehaan" ya faɗa yana ƴar dariya sanin halin kayansa.
A hankali ta ɗan yi knocking sannan ta shigo da sallama, ta koma inda ta tashi ta ce, "An samu maganar daga wajan P.A Bilal."
Ya ɗan yi murmushi yana girgiza kai, sannan ya ɗauko waya ya kira Bilal ya saka a speaker.
Bilal yana ɗauka ya ce, "Good day Sir." Jazy ya ce, "gidan tv nawa ka bawa labarin dawowar Ray?."
Bilal ya yi shiru bai ce komai ba. Jazy ya ce, "baka jin magana ko? Me ya ce maka a airport?."
Bilal ya ce, "a yi haƙuri, na riga...."
Ya katse sa ya ce, "ayi haƙuri dame Bilal? Sau nawa kana yi kana bada haƙuri, dan ka ga ina sakawa ya ƙyale ka ko?. Shikenan wannan tsakanin ku ne, bazan shiga maganar ba" kafin Bilal ya ce wani abu ya yanke wayar.
Ya kalli Islaha ya ce, "Miss ƴar jarida, kin samu labarin ya dawo jiya. Kuma sai ku zo interview yau?."
"no Sir, ba mun zo interview ba ne, mun zo mu yi inviting ɗinsa ne, duk lokacin da ya saka mana, a ko ina ne muna maraba da hakan. Mu dai burinmu ya amince mana ɗin."
Ya ɗan kwanta a akan kujerar ya ce, "Kin san babu channel ɗin da ya taɓa hira dashi?."
Islaha ta ce, "shiyasa nake so na zama first presenter da zan fara interview dashi, ina mafarkin hakan a rayuwata Sir."
Ya yi murmushi, dan yanayin yadda take magana da ƙarfin guiwarta ya burge shi sosai.
Jafar ya ce, "meyasa?."
"hira da Mr Reehan ba abu ne mai sauƙi ba, iya tattaunawa dashi babbar nasara ce a gare ni."
Ya ɗan girgiza kai ya ce, "to kuma sai ga ki a zaune a wajan Jafar ba Rehan ba."
Ta sake yin murmushi mai kyau ta ce, "in na ga Mr Jafar kamar na ga Mr Rehaan ne. Wannan zama da na yi tare da kai shima babbar nasara ce, at least a tarihin rayuwata zan ce na zauna da Mr Jafaar har mun yi magana. Ina komawa gida, zan rubuta a diary na."
Ya girgiza kai tana jinjina girman wayonta, ba ƙarya ta iya aikinta sosai. Haka ake son ƴan jarida da iya harshensu, da iya sarrafa magana, sa amfani da yanayin fuskar wanda suke tare.
Ya ce, "ta ya dan kin ga Jafar zai zama kin ga Ray?."
"Saboda duk abu ɗaya, jini ɗaya ba wasa bane."
Ya yi murmushi yana jinjina ƙarfin wayonta, muryata ko rawa bata yi in tana yi masa magana, ko kaɗan babu tsoro a tare da ita. Aikin ya ratsa ta, ta ƙware babu da wanda baza ta yi hira ba.
Ta yi ƙasa da murya ta ce, "I've been here since 4 a.m. and haven't even had breakfast, just because I want to see your cousin. Please, ka bani damar ganinsa."
Da mamaki ya kalle ta ya ce, "dake muka haɗu za ki shiga elevetor ko?."
Ta ɗaga kai ya ce, "ni ce."
Ya ɗan yi murmushi ya ce, "kuma ba ki ga Rehaan ba?."
Ta girgiza kai ta ce, "ban gan sa ba, kana tare dashi?."
Ya girgiza kai da mamaki ya ce, "kafin yanzu, kin taɓa ganin Rehaan?."
"Actually ina ganin hotunansa amma bazan iya cewa ga kamanninsa ba, in na ce ban san shi ba ban yi ƙarya ba. Wannan shine gaskiya."
"Good girl!"
Ya furta yana girgiza kai jin ta faɗa masa gaskiya, dan tabbas ta ga Rehaam bata ganesa bane ba. Kuma gwara hakan, da ta tunkaresa da wata magana da an shiga tara.
"Miss Islaha yanzu dai Rehaan bacci yake yi, ko da ba bacci yake yi bazai amince ba. Kuma Bilal da ya ba ku labari zai koresa ne. Dan ba ya so ya faɗa ba a cika ba."
Islaha ta yi shiru bata ce komai ba. Jazy ya ce, "A taƙaice ban yi miki alƙawarin ganinsa a yau ba. Ba yau ba ma, gabaɗaya wannan zuwan bana tunanin zaki samu damar da ki ke so."
Cikin rashin damuwa ta ce, "zan jira daga nan ko yaushe ne, burina da fatana ya amsa gayyata, ya amince na zama ta farko."
Jay ya ce, "Don't worry, ƙarfin guiwarki da nutsuwar ki, da gaskiyar ki ya burge ni. Dan haka na yi miki alƙawarin ke ce mace ta farko da Rehaan zan yi hira da ita. Sannan da kaina zan neme ki in lokacin hakan ya yi."
Ta faɗaɗa murmushin ta, kyawunta ya sake bayyana ƙarara ta ce, "na gode Mr Jafar, na gode Allah ya saka maka da alkhairi. Ka wuce yadda na yi tunani, yadda aka faɗa min kai ba haka ka ke ba. Na gode."
"ya aka ce miki nake?."
Ta ɗan yi dariya ta ce, "An faɗa min kana da shariya, kuma kirkin ka bashi da yawa" ta faɗa tana ɗan rufe bakinta cikin salon wasa.
Ya yi ƴar dariya ya ce, "wannan sai Rehaan ba dai ni ba. So you can go."
Ta sake yi masa godiya ta ciro iv card ta miƙa masa ta ce, "his invitation card."
Ya ɗan girgiza kai ya ce, "no need, je ki dashi."
Ta yi murmushi ta miƙe ta ce, "thank you for your time, Mr Jafar."