NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)
CHAPTER 40 (Mine💜).
by @deejasmah
Yau ma dai bai wani barta tayi sukuni ba sai da ya fanshe kewarta da zai yi kafin ya k'yaleta, shi kan shi a lokacin ji yake inama taren zasu tafi kamar wancan karon sai dai ya san babu dama. Ko da suka yi asuba komawa tayi ta kwanta cikeda gajiya, amma sab'anin jiya yau da wuri ta farka tana d'aura idanunta a kan fuskarshi dake gab da tata mik'ewa tayi tsaye tana sauka daga gadon.
A gaggauce ta fara gyaran gidan daga nan b'angarenshi ta fara har ta dire a natan, kitchen ta shiga tana mai fito da kayan da ta san zasu lalace kafin ta dawo duk da ma wannan karon bai siya mata kayan azumi ba don bata nan wanda suka rage kawai tayi amfani da su duk da haka kuma sun rage da dama.
Potatoes da doya, su plantain ta fara cirowa ta ajiye a gefe kana ta bud'e freezer da fridge duka kayan miya ta ciro har da canned ones har da su nama da fruits sai da ta tabbatar babu komai a ciki kafin ta kashesu ta goge tsaf. Sake gyaransu tayi ta ciro ledoji tana lullub'e kayan kitchen d'in while k'ananun kuma ta d'auko k'aton kwali daga kitchen d'in ta ta jerasu ciki hasa food flask d'in ta da jugs duka sai da ta tabbatar kowanne ya adanu da kyau kafin ta fito.
D'akinta ta koma suma ta lullub'e komai da leda, kafin ta gama ko ta gaji kashirb'an har da zufanta. Hakan ya sata kwanciya a sofar parlorn da bata sakawa leda ba tana maida numfashi, kwanciyarta sai ga Islaam ya shigo yana d'auke da Sairah da alamun tashi tayi
Hamma tayi tana sake dubansu zama yayi kan carpet yana cewa " duk ke kad'ai kika yi aikin nan?". Idanunta a lumshe tace " toh ya zanyi".
"Kin gama ne?" Ya tambaya yana mik'a mata Sairah, amsarta tayi tana fara shayar da ita tace " nan ne kawai ya rage sai waiting room, yawwa Yaa na fito da foodstuffs gudun kar a lalace sai a kai wa ko Amarya ne".
"Sai dai a bawa su Hamza su raba ita tana da enough foodstuffs" ya fad'i kai tsaye ya san ita da kyakkyawar niyya ta fad'i hakan but yanzu sai kaga Fareesah ta canja abun yanda sai yayi nadamar kai mata su, gwara su Hamza da Umara d'in dama ita take ba su abinci musamman da azumin nan duk da ko yana basu kud'in abinci amma wannan ba damuwarta bane ita dai tana bayarwa ba ma ta jiranshi kiran Umaran take a waya ya k'arba.
Mik'ewa yayi ya nufi can waiting room d'in Sofar ya rufe har da TVn kana ya d'age rug d'in parlorn kasancewarshi fari, a gefe ya jingine da zummar ya fita da shi wurin masu wanki. San da ya dawo ta gama shayar da yarinyar suna kwance kan carpet, dubanta yayi da kyau yana cewa " wai yanda kike kwanciyar nan hala kin manta jirgin 2 zaku bi ko?".
D'ago kai tayi ta dubeshi tace " ai naga da sauran lokaci ne".
"Sauran miye? Yanzu 10:23 fa".
Kallon agogon bangon tayi da sauri tana zaro idanu cikeda mamaki at the tana mik'ewa tsaye tace " na fa zata irin 9 d'in nan ne, na ga baka fita ba".
"Dama ai yau ba zan fita ba, sai na kai ku airport maza dai ki wuce kiyi wankan kin nan mai cin kusan 2 hours ".
Dariya ta saka tana wucewan don ta san gaskiya ya fad'i wankanta sai ya kai 1 hour saboda abubuwan da take yi a toilet, ko da ta shiga Sairah ta farawa wanka ta fito da ita tana k'ok'arin shiryata ya shigo. Ce mata yayi ta wuce tayi wankan shi kuma ya shiryata, komawa tayi tana shigewa ruwan da ta had'awa kanta mai matsakaicin zafi unlike kowace rana yau dai bata dad'e ba ta fito.
Tana fitowa bata wani dad'e ba ta shirya cikin wata Lebanese Abaya faded-black color, hula ta sanya bak'a tana yane kanta da Jersey veil mai d'an girma nude. Ba ta sanya turare ba bayan Khumrahn da ta shafa mai sanyin k'amshi, wanda sai ka kai hancinka gareta ne zaka iya jin shi.
Closet ta bud'e tana janyo trolly mai 2 in 1 wanda ta had'a kayan tafiya sai handbag ta birkin mai d'an girma itama nude wacce a nan ta sanya wayoyinta, da passport d'in ta da dai sauran kayan buk'atu har da lipbalm a ciki sneakers ta zura a k'afafunta bak'ake masu taushi sak'ar kamfanin adidas.
Kallon agogo ta yi har 1 ta kusa, tsaki tayi a fili tana cewa " matsalar Nigerian airports ka je latti kayiwa kanka ka fita da wuri ka sha wuyan jira, Allah ya kyauta mana dai".
Counter ta sanya a hannunta tana jan trolyn ta fito don shi Islaam ya fita shi da Sairah, a parlorn ta ajiye jakar ta koma ciki jacket ta d'aukowa princess d'in ta sake jan jakar zuwa part d'in shi yana ganin shigowarta ya mik'e tsaye yana dubanta cikeda raunin da bai san yana da ita ba. Murmushi ta sakin masa tana k'arasowa jikinshi, hannu ya ware yana sanyata a jikinshi yana sakin ajiyar rai lafewa tayi sosai tana jin itama raunin yayinda kewarshi ya rufeta sosai.
Zareta yayi yana cewa " uhmm, barin rufe d'akunan ko kin rufe ne?".
"A'a entrance door ne kawai a rufe na ga ai kana nan ne, sai sa".
"Ko ina nan a dai rufe koina sai ki ajiye keys d'in a drawer, in zan shiga ciki zan bud'e hope dai kin ajiye min peppered chicken d'in?".
Dariya ta saki tana cewa " yea yana frigde d'in kitchen d'in ka, har da cookies d'in da ka ce ma".
Lumshe idanu yayi cikeda dauriya ya saki hannunta ya juya ya fita, rufe koina yayi da kyau ya kashe wuta kana ya dawo da keys a drawern gefen gadon shi ya ajiye ya dawo parlorn. Kallon agogo yayi yana cewa "ki zauna barin kira Sadeeq d'in in ji in sun shirya".
Wayarshi ya zaro yana kiranshi kamar yadda ya fad'in ringing biyu ya d'aga yana cewa " na fa lura so kake mu rasa flight ko?".
"Dama zaku rasan ai da naji dad'i".
"Toh ta Allah ba taka ba Malam, ta shirya ne ko zaka ajiyeta ne kayita kallo mu mu tafi?".
"Sai kun dawo" ya amsa yana shirin yanke wayar, dariya Sadeeq d'in ya saka jin yanda yake magana. Ya san dauriya kawai yake yi amma har cikin ranshi bai son matar tashi ta tafi ta barshi, shiyasa ranar yake ce masa " in ba zai iya jurewa ba ya bita su tafi ko ta fasa zuwa san da ya samu dama sai su tafi" amma ya k'i gashi koina ba'a je ba har ya fara jin ba dad'i.
Duban Suleim dake gefenshi yayi yana cewa " mu fito da kayan, yanzu zai zo".
"Toh shi ne kake dariya?" Ta tambaya cikeda tsegumi, kanta ya dungure yana cewa " toh amebo ba za'a fad'in ba, oya tashi mu tafi".
"Haba Baby ba ni in sha please".
"Na k'i wayon Madam".
Dariya tayi tana mik'ewa ba tareda nuna damuwa ba ta san in dai Sadeeq ne tana zamanta zai kwaso gulman ya fad'a mata.
Mik'ewa tayi tana nufar d'akinta parlornta da kayan nasu yake a jere tayata yayi suka fito da su suna jiran Islaam.
Shi ko yana gama wayar dubanta yayi yana cewa " d'auko princess mu tafi bari in fitar da trollyn". Da kai ta amsa tana d'aukar yarinyar da tayi barci ta bi bayanshi, booth ya bud'e ya saka kayan kana ya k'arbi Sairah yace " mu je kiyi wa Fareesah sallama" ok ta furta a hankali tana binshi yana rungume da yarinyar, ita kuma hannunta rik'e da jaka sai wayarta.
Knocking yayi sau biyu aka bud'e k'ofar kamar tana jiransu, ganinsu su biyu ya sanyata ware idanunta da d'an mamaki sai kuma ta matsa tana ba su hanya suka shiga. Parlorn tsaf yake itama ba laifi akwai tsafta kan kujera ta zauna suma suka zauna, gaisawa suka yi cikin rashin sabo kana Nadeefahr kai tsaye tace " dama yau zamu wuce ne".
"Uhmm, Allah ya tsare ya saukeku lafiya a nan za'a bar min princess kenan?" Ta tambaya cikeda makirci, Islaam ne ya bata amsa da " tare zasu tafi da ita " ya k'are yana mik'ewa yana d'aurawa da " Kar mu yi latti, bari in sauke su".
Had'iye abinda ya taso mata na takaici tayi tana cewa " ko zamu je in raka ku?". Harararta yayi yace " ba gidan zan dawo daga nan ba, zan je Yerwa tafsir wife mu je" yana fad'in haka ya juya ya fita, d'an yak'e Nadeefah tayi tana cewa " toh sai mun dawo".
"A dawo lafiya" ta amsa, har Lelen ta kai k'ofa sai kuma ta mik'e tana bin ta a baya a dai-dai k'ofar ta tsaya tana waving masu hannu.
Shigewa motar tayi itama tayi mata shi dai ko inda take bai kalla ba, ya ja motar suka nufi gate Umara ya bud'e yana d'ago musu hannu da murmushi a fuskarshi yake cewa " Allah ya tsare Madam".
Da murmushi ta amsa tace " Ameen ya rabb, chief security " ta k'are tana d'an dunk'ula masa kud'i a hannu, suna fita daga gidan ta dubeshi tace " baka kyauta ba Yaa".
"Me kenan?".
"Abinda kayi mata mana, da sai ka barta ".
"Uhmm, ko zaki koma ki kirata ne?".
"Sorry Yaa" ta furta tana rik'e hannunshi ta d'an shafa kad'an, bai tanka ba sai parking da yayi k'ofar gidan Sadeeq yana danna doguwar honk kamar zai fasa gidan. Security ne ya bud'e yana lek'o kan shi ganin Islaam ya sa shi fara k'ok'arin wage gate, da hannu ya nuna masa "no" yana mai sake danna honk d'in.
Sorry ta sake maimaitawa cikeda rauni, hakan ya sa shi dubanta yana cewa " hala kin manta azumi ake yi kuma k'asar zaki bari kike min shag'waba ko?".
Hannu ta kai ta dafe bakinta don ta gane me yake nufi, shi ko sai danna honk da ya kuma ko a jikinshi wanda yayi dai-dai da fitowar Sadeeq rik'e da hannun Afdhal d'aya kuma da na Suleim bayansu kuma maid d'in ta ne Baraka da za'a yi tafiyar da ita yayinda securities ke jan jakunkunan kayan. Bai fito ba ya bud'e booth d'in jera kayan suka yi sallama yayi da su yana nufo inda yake knocking yayi a glass d'in ya sauke yana cewa " wai baka duban agogone halan?".
"Ni ko nake duba, ya aka yi?".
"Sai na gaya maka ka zagaya ka shiga ne ko so kake in fito in d'auke ka?".
"Ba zan biye maka ba, ke Nadeefah fito ki zauna kusa da Suleim kin ji".
"Ta fito ina? Mata tana zaune kusa da mijinta kace ta fito zaka shiga ka zauna kusa da matarka ko zaka yi ta tsayuwa ne?".
"Ai ni ban san matarka ba ce sai ka jaddada min, sai ka dinga tunawa da ni kuma k'anwata ce ita Lele fito kin ji".
"In kai kake da ikonta yanzu zan gani, ko ba k'anwarka ba? Ni kuma ai yayanka ne".
"Yayan ƙaniya, walh Islaam ka bar ganin ana azumi ubanka zan ci ".
Dafe baki yayi yana danne dariyarshi sai dai ya k'i yiwuwa sai da ya saki kayanshi iya son ranshi kafin ya ce " wife shiga baya kin ji" dama abinda take jira kenan ta fito ta shiga bayan ta zauna kusa da Suleim da tun d'azu ta shiga tana ta dariyar dramar Sadeeq da Islaam wato shi ma ba k'yalle ba ne, kawai saboda gizagon da yake arowa yana yafawa fuskar ce tasa ba'a ganewa.
Itama Lele dariya ta saka tana cewa "Babe how far?". Ba ta iya amsawa ba sai da suka yi dariya mai isarsu kafin, sai lokacin ta samu sukunin gaishe da Sadeeq da ya amsa shi ma yana dariyar masifar da yayi Haka ya ja motar yana dariya, girgiza kai Sadeeq d'in yayi yana cewa " Bandq".
Haka suka yi tafiyar cikeda raha, sun shafe mintuna masu dama don daga Yerwa New layout zuwa Kaduna International airport ba k'aramar tafiya ba ce.
San da suka isa an fara screening matafiya hakan ya sa basu tsaya wata-wata ba suka shige ciki, ita ko tsayawa tayi tana karb'ar Sairah da har ta farka daga barci. Dubanta yayi a narke yana cewa ''toh Allah ya tsare hanya, ya sa kuyi ibada karb'ab'biya" yanda yayi maganar ya sanya ta ji hawaye suna taruwa a idanunta.
Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa suka fara zuba, murmushi yayi cikin k'arfin hali yana cewa " miye abun kuka kuma?" Tura baki tayi tana cewa " na fara missing d'inka ne" juya idanunshi yayi karon farko a rayuwarta da shi yace " you know zan yi kewar ki fiye da yanda kike zato, ko mu koma ne?".
Mak'e kafad'a tayi hakan ya sa shi fad'ad'a dariyarshi yana cewa " ashe ma missing d'in a baki ne?". Itama dariyar ta saka tana cewa " ba a baki ba ne, but fasawa ai ba zai yiwu ba in ba wani halin ciwo ba but i'll miss you fiye da yanda zan iya bayani". Hannunta ya kamo ya murza cikin na shi bai damu da masu wucewa ba ya rungumesu duka da yarinyar sai da suka d'auki minutes kafin ta janye tana cewa " Yaa azumi fa ake yi"
"Don ana azumi ba zan rungume matata ba? Ai ni ban yi don in ji wani abu ba sai dai in ke".
"Ni ba ruwana" ta furta cike da kunya.
"Balle kuma ni" shi ma ya furta cikin wata sassanyar murya wacce take bayyana rauni, sakin hannunta yayi yana cewa " ku tafi Allah ya tsare". Da kai ta amsa tana cewa " kai ma Allah ya tsare mana kai zuwa gida". Uhmm ya amsa ya bita da idanu har ta shige ciki ya d'an dad'e a wurin bayan shigewar tata sa'annan ya ja jiki cike da sanyi ya nufi motar shi, ko a motan ma haka ya zauna tsit ji yake kamar wani babban sashe na rayuwarsa ya rasa gabad'aya gwauron numfashi ya sauke kana ya ja motar.
San da ta shiga ciki har duk su Suliem sun gama screening ba ma su kad'ai ba har da sauran matafiyan sai d'aid'aiku ne suka rage, layinsu tabi har sai da aka duba komai nata aka ba ta boarding pass d'in ta da izinin wucewa ciki in da su Suliem suke ta nufa ta zauna tana sauke ajiyar rai.
"Ai na zata shi ma binki zai yi ko ke komawa zaki yi ki fasa zuwa" Suleim ta furta tana dubanta, harararta tayi tana cewa " har ya biyo ni ai, hala baki gan shi ba?".
"Hararata kike yi saboda ga ni sa'arki ko? Matar yayanki nake kuma Auntynki 'yanmata" ta fad'i tana mai tuno hak'ilon Islaam da Sadeeq, hararar tata ta kuma yi tana cewa " Ko ba Auntyna ba? Ni kuma matar yayan mijinki nake " ai daga Suleim har Sadeeq dariya suka kwashe da shi haka itama, Sadeeq ne ya girgiza kai yana cewa " ai Islaam d'an iskan kai ne, ga shi yayi miki abu ya fuske kamar ba shi ba wanda bai san shi ba ma ya rantse maka ba shi ba ne".
"ko ni ma haka na fad'i, Yaa Islaam case" Suleim ta furta tana sake sakin dariya, ita dai Nadeefahn a yanzu ba ta tanka ba sai wayarta dake ringing ta ciro Islaam ne d'agawa tayi ta koma gefe ta bar su nan tana amsawa in da tambayarta yayi ko sun fara shiga jirgi ta amsa masa da basu fara ba sun d'an jima suna wayar da shi kuma ko bayan da suka ajiye sai da ya k'ara kira bayan kamar 10 minutes duk dan ya ji yanda suke cike da bayyananniyar kulawa mara mix.
Kamar yanda suka zata ko bayan da suka yi sallahr azuhur sai da suka sha zama sai 3:17 kafin aka fara sanarwar passengers d'in Arik air su isa harabar tashin jirage yanzu za'a fara onboarding. A haka suka wuce cikin jirgin inda bayan shigarsu babu b'ata lokaci jirgin ya fara haramar tashi. Islaam ta kira ta sanar masa da tashin na su sai Ummu a gaggauce suka yi maganar ta ajiye wayar bayan ta sakata a flight mode tana gyara musu seat belt ita da Baraka da ke gefenta ita kuma Sairah ta gyara mata kwanciya a bassinet d'in da aka providing masu.
Kasancewar jirgin su direct to Mecca ne ga kuma ba su tashi da wuri ya sanya ba su samu isa Mecca ba sai bayan Ishai hakan ya sa ko iftar a jirgi su ka yi, a mugun galabaice Nadeefah ta fito daga arrivals don ko da suka gama check-out sai Baraka ce ta biyota da kayanta.
Taxi suka shiga in da ya kaisu Jumeirah jabal Omar hotel wanda shi ne masaukinsu na kowane lokaci in dai suka shigo Mecca sai kuma Mekkah tower, Sadeeq shi yayi komai na kama d'akin na su kana suka shige ciki d'aki d'aya aka kama musu ita da Baraka wanda ita ce tayi insisting haka da so suka yi a kama mata wani daban wai kar ta takura. Hakan ya sa aka kama musu single room mai double beds su Sadeeq da Suleim kuma single room d'in ne but mai single bed. D'aki suka shiga wanka ta fara yi kai tsaye ta d'auro alwala sai da ta fara yin sallolin da suka riskesu a hanya sannan ta iya zama, kasancewar ta riga da tayi roaming lines d'in ta ya sanya ta d'auko wayarta tana fara kiran Islaam bayan ta duba lokaci.
Bayan barin shi airport d'in ko kamar yadda ya fad'i bai koma gidanshi ba, Yerwa ya wuce kai tsaye yana yin sallahr zuhr ya shige gidan Umma. Babu kowa a parlorn sai k'amshi mai sanyi da ke tashi, kai tsaye ya haye saman shi ma dai bata ciki da alamu dai tana d'akin Abba ne ko tana kitchen duk da ko bai ji k'arar wani a kitchen d'in ba. Ido ya runtse kana ya haye gadon kwanciyar shi babu dad'ewa kiran Nadeefah ya shigo wayarshi, d'agawa yayi a kasalce yake mata magana in da ta shaida masa da sun gama screening amma ba su tashi ba. Sun d'an jima suna wayar kafin ya ajiye ya koma ya sake kwanciya, ba a dad'e ba barci ya kwashe shi ko da Umma ta shigo ta tarar da shi yana kwance tayi mamaki ainun don rabonshi da ya zo mata gida har yayi barci a kan gadonta tun farkon aurenshi da Lele lokacin yana jin gidan ya isheshi in kuma ya zauna ji yake kamar ya kashe Lelen har k'iyama.
Ba ta zauna ba don abu ta zo d'auka ta koma d'akin Abba, san da Nadeefah ta kirashi tana shaida masa tashinsu ma sama-sama ya amsa don barcin bai sake shi ba jin haka ya sanya bata tsawaita wayar ba ta kashe. Ajiyewa yayi a gefe yana cigaba da barcinshi ba shi ya tashi ba sai da aka kira sallahr asr sauka yayi bayan yayi alwala a compound ya had'u da Abba don haka tare suka rankaya zuwa masallacin inda Abba yake tambayarshi Lele. "Sun tashi around 3, ya ba shi amsa".
Murmushi Abban yayi yana cewa " masha Allah, Allah ya saukesu lafiya". Ameen ya amsa masa suka shiga masallacin, ko da aka idar da Sallah zama suka yi suna sauraran tafsirin Qur'anin da Mal. Samaila Babba wanda shi ne babban malami kuma limamin masallacin na Yerwa.
5:30 aka tashi suka fito tareda Abban kamar yanda suka taho suka koma ciki, a balconyn Abban suka zauna suna tab'a hira suna zaunen kusan 6 Safwaan ya shigo gidan don shi azumi bai hana shi yawo. Yini yake a hanya ana yin ishai zai sake fantamawa shi da su Zaheer ba su wannan gidan ba su wancan, har ko gidan Fadwaah da ya raina hakan ne ma ya sa aka saba da shi fiyeda Islaam ga sakin fuska da jan yara a jiki.
Wurinsu ya taho yana cewa " Allah ya taimaki yayanmu angon K'amshi da Fareesah, kuma Abu Yusairah" harararshi yayi yana mai cewa " sanƙira ka zama ne halan?".
"Ai Safwaan kullum lamarin na sa k'ara gaba yake yi, yanda ka san ba girma yake yi ba" fad'in Abba yana dubanshi tsaf, tura baki yayi yana kaiwa zaune a d'aya kujerar da babu kowa yace " toh Abba in ban yi ba, waye zai yi tunda dai kowa is serious in this house babu mai raha. Kar wanda ya damu ko taron masu raha za'a je ni zan wakilce ku..."
"Ai ko baka ji dad'i ba, tunda wakilicin taka a iya gefen shirme ya tsaya".
"Kayya dai Yaya, au Barka da Yamma Abba. Barka da Yamma Yaa". A tare suka amsa yayinda Islaam sai da d'aura da tambayar
"Ka ga halin naka ko?.
Mik'ewa yayi yana cewa " bari dai in ja jiki in shiga ciki, uku-uku nake gani yau azumin nan da ni ake yi " bai ko jira cewarsu ba ya nufi cikin gidan, Burhaan shi ma mik'ewa yayi jin Abba na cewa " kai ma ka zo ka wuce gidanka magrib ta kawo jiki" amsa masa yayi da "toh Abba a sha ruwa lafiya" da kai ya amsa masa ya wuce part d'in Umma yayinda shikuma ya shige na shi sashen, a tsaitsaye ya gaisa da Umman kana ya juya ya fita motarshi ya shiga ya ja motar zuwa gida.
San da ya isa ba a kira sallah ba hakan ya saka shi wucewa ciki, part d'in Fareesah ya nufa bai yi knocking ba ya tura k'ofar tana kwance cikin kujera tana kallon Arewa24 da ake maimaicin shirin gari ya waye. Amsa sallamar tayi tana mik'ewa zaune barka da dawowa tayi masa, zama yayi gefenta kawai idanunshi a kanta kayan safe ne a jikinta bata canja ba yana mamakin yanda ba ta son wanka sosai in ta yi da safe toh sai dare kuma in zata kwanta shi ma ba kullum ba ne wata rana musamman ma in ba ita ke girki ba ba ta yi.
Cewa yayi " yawwa, kin je itn yau?".
"Yes lifeline, around 2 na dawo su Mommyn princess sun sauka ne?".
"Basu tashi da wuri ba so bai yi sun isa ba".
"Ohhh, ayya".
"Barin yi wanka kafin a kira sallah, kema ki samu ki watsa ruwa".
"Tohm, sai ka fito " da idanu ta raka shi a ranta tana cewa " uhmm bari in tashi in yi wankan tunda ya furta, ni fa nafi gane wankan dare da mutum yayi ya kwanta".
Tashi tayi zuwa room d'in ta ta watso ruwan wata boubou gown ta sako ta fito a duniya Fareesah ba ta da kayan da suka wuce Boubou gowns na adire mai santsi, duk da fa akwai kayan shak'e da akwatunan da aka mata na lefe amma tana da matuk'ar mak'on sutura ta fi gane tayi ta ajiya sai in biki gagarumi ya taso sannan a k'wak'wulosu a saka. Ko a gida in aka musu d'inki sai na kowa ya lalace ya bar nata da haske, akwai lokacin da kayanta har rimar sanyin suka yi wani lokacin ko sai kaga tana ciro kayan da ta saka su yage. Ba kuma ta bayarwa ta gwammace su mutu ta zubar.
Ko da ta fito sai da ta d'an jima kafin ya fito tsayawa yayi yana kallon dining yana mai cewa " ki fito da fruits ki yanka min da dates " tasowa tayi tana cewa " na yanka suna kitchen" ok ya amsa ya koma ya zauna, yana zama ana kiran magrib mik'ewa yayi ya koma dining d'in dai-dai tana fitowa daga kitchen da trayn da ta yanka su Lemo da su watermelon da apple sai banana da pear.
Apple ya d'auka ya ci da dabino kafin ya sha ruwa yana cewa " ban san oranges, sai dai in juice zakiyi da shi ba ni ruwa in wuce masallaci" bashi tayi ya bud'e bottle d'in sa kan shi don goran ta mik'a masa shi ya zuba a glasscup ya sha kana ya juya ya fita, tura baki tayi tana cewa " Lifeline da k'orafi wai bai son oranges, uhmm na yi mai juice d'in gobe yau kam lokaci ya k'ure" tana gama fad'in haka ta d'auki lemun ta sha sai da ta sha fruits d'in maishi kafin ta wuce ta yi sallah.
Tana raka'ar k'arshe ya shigo d'akin zama yayi yana kallonta har ta idar, ko addua bata tsaya yi ba ta zare hijabin tana cewa " Lifeline sannu da dawowa, an sha ruwa lafiya?".
"Lafiya lau, ke fa?" Ya tambaya yana wucewa dining, zama yayi ta zo ta bud'e foodflasks d'in ta fara serving d'in shi golden yam tayi (doya da k'wai) da ta ji k'wan sosai. Da yawa ta zuba masa kana ta zuba wani sauce na cabbage da carrot da ya d'auki curry sosai sai k'amshin shi ke tashi ga kuma uban kidney a ciki, a gabanshi ta ajiye kana ta bud'e flask d'in da ta dama kunun tamba ta ji madara itama da gyad'a ( su Hajiya Fareesah ashe an iya kunu hehehe).
Amsa yayi yayi bismillah ya fara ci yana dubanta tana serving kan ta itama, a tsanake suka ci abincin ya ci da yawa don doyar tayi dad'i ba laifi haka kunun in ba k'arya zai yi ba ma zai ce wannan yana É—aya daga abincin ta mai daÉ—i a cikin gidanshi. Komawa yayi parlor da ya gama ita kuma ta kai kayan kitchen ba ta wanke su ba ta dawo tana zama cikin jikinshi tana masa hira, yana amsata rabi yana kallon TV suna haka aka kira sallah yau ma tare suka yi sallahr a nan parlorn in da ji tayi kamar ya d'aura mata wani kaya ne don yanda ta cika ciki da doyar nan ta kawo mata har ciki ba ta son abinda zai rage mata jin dad'i da suka idar ne ya fita zuwa part d'in Lele.
Peppered chicken d'in da ta ajiye masa ya duba inda ya ga ba iya chicken d'in ba ne har da nama ta soya masa mai yawa, ajiyar zuciya ya sauke yana d'aukar d'aya ya saka a baki komai ya ji yanda ake buk'ata. Peppered chicken d'in ya d'iba a wani bowl kana ya maida foil papern ya nad'e ya sake d'iban soyayyen da su cookies ya fito, rufe d'akin yayi ya koma nata.
Mik'a mata yayi yana cewa " ki warming min wannan yanzu please" da sauri ta amsa tana lek'a bowl d'in idanunta kamar za su fad'o k'asa, wucewa tayi cikin mintuna ta dawo da shi a wani bowl karb'a yayi ya fara ci yana cewa ta kawo masa chivita mai sanyi. Yanzu kam har da zuba masa drink d'in tana gyara zama kai kace ba ta tab'a cin nama ba, nan ko suna nan a freezer girke ta dafa ne take ganin asara.
Hannu ta saka a ciki tana d'aukan cinya d'aya tana kaiwa baki, kallonta yayi yana lura da yanayinta gabad'aya bai san kalarta ba. Bai san amfanin ajiyarsu da take ba bayan ba doka yake mata ba ko iyaka, shi fa bai ganin ma ana cin nama a gidan kamar yanda shi yake so. Bai k'i su yini suna ci ba in ya k'are ya k'aro ya kuma siyo tsire da balangu, in ana maganar mayen nama toh Burhaan zai iya amsa sunanshi da cikakken maye.
"Kai Lifeline wannan carterern ta iya pepper chicken wlh, a ina take?".
"Waye a ina take?".
"Carterern nan mana, komai ya ji bai kuma yi yawa ba ga sauce d'in yayi daÉ—i" ta furta babu ko kunya, tsaki ya sake yana cewa " ko kunya baki ji ba kina yaba girkin wata while babu abinda kika rasa a cikin naki gidan".
"Lifeline ai duk girkin mutum akwai wanda ya fi shi iyawa, kuma ma ai carterers su girkinsu daban ne".
"Carterers fa, toh babu wata carterer da na yi ordern chicken Nadeefah ce ta min kafin ta tafi ba kuma kazan nan kawai ta iya ba but duk wani kalan abinci da kika sani da ma wanda baki sani. Ina da mata da ta iya kowani kalan girki ne zan je wajen carterers d'in da da yawansu ba abinda suka iya sai saka curry?".
Kasak'e tayi da naman a bakinta jin maganar da yayi wai babu abinda suka iya sai saka curry wato dai da ita yake yi ta godewa Allah ba carterer bace so ba da ita yake yi ba, hasalima shock d'in jin wai Lele ce tayi kazar ne ya kasa barinta ita wai komai ta iya ne? Haka ranar ta barta speechless da girkinta da har yau ba ma ta san sunan ba, amma ɗanɗanon na maƙale a kanta. Ba kuma wai kazar daban bane da wanda ta saba ci, but yanayin girkin ne ya bambanta da na wanda kowa yake yi cikin sakin baki kamar yadda ta saba tace " Mummyn princess fa?".
"Yes ita fa, kema zaki iya shaida haka tunda kin ci girkinta in zaki gyara toh in kuma kin k'i damuwarki ce and daga yanzu ki daina bani girki babu nama ba kuma wanda aka saka a kan abinci ba real nama nake nufi tunda dai akwai" yana fad'in haka cikeda jin haushinta ya wuce don ji yayi ma naman ya fitan masa a kai, bai san wace kala ba ce Fareesah ita ko d'an irin kishin kai na mata bata da shi komai nata sakaka yake kamar wacce ba ta san mi yake mata ciwo ba.
Ita ko baki ta tab'e tana cewa " d'an zafin kai kawai, ni ban san me mutumin nan yake nufi da ni ba. Wai matar shi ta iya girki, toh ina ruwana in ta ga dama ta fara saida abincin ma zamu yi order. Ina wannan gidan ne ake min maganar yin girki banda kiran fatara, ba zai iya ajiye cook yake masa girki shi ne zai wani tsaya yana min ihu kan wani abinci ba zan dafa varietes ba in ya ga dama ya kawo cook in bai ga dama ba sai ya je wurin ita 'yar wahalar sai ta yi masa shiyasa kullum ko k'iba bata yi" ta fad'i tana cigaba da tura sauran da ya bari a ciki, sai da ta cinye tsaf kana ta lashe kwano tas ta kwashi plate d'in tana kai wa kitchen ta ajiye cikin wanke-wanken da zata yi da safe.
D'akinta ta wuce ta sanya kayan barci ta wuce d'akin shi, yana kallonshi hankali kwance hannunshi rik'e da waya yana jiran kiran Nadeefah don ya san any moment from now zata iya kiranshi. Kwanciya tayi cikin gadon tana kallonshi, tana latsa waya har ta gaji ta ajiye wayar ta fara barci kiran Lelen ya shigo wayar ta shi bud'e idanu tayi tana dubanshi jin yana cewa " wifey".
Murmushi tayi tana cewa "Alpha ya kake, ka sha ruwa lafiya?".
"Ina lafiya, kefa? Ya hanya yaushe kuka sauka?".
"Ba mu dad'e ba Yaa, yanzu nayi sallah zan samu in kwanta ne coffee na had'a ma duk na bi na gaji".
"Ai dama dole ki gaji zaman fa ba nan ba ne, balle ke da abu kad'an ki ce kin gaji ya princess?".
"Ga ta can ta kwanta ita da Afdhal, ya Fareesah?".
"Ta na lafiya, za ki kwantan ne yanzu?".
"Wai haka nake so Yaa, 12 fa har ta yi".
"Ki kwanta maza zamu yi magana da safe ok?".
"Ok Yaa, goodnight".
"Good night wife, Kar ki manta da azkhar".
Ok ta amsa tana ajiye wayar, mik'ewa tayi daga sofa bed d'in da take ta nufi gadon cikin yaran ta kwanta addua tayi ta shafa musu ta shafa ma kanta ta dubi Baraka da lokacin ta idar da sallah tace " ki sha coffee ga shi nan kan table, in zaki kwanta kuma kiyi addua ok?".
"Toh Aunty sai da safe".
Uhm ta furta ta na kwanciya, washe gari ba su tashi da wuri ba bayan sun yi sallahr subh sai da gari ya hantse kafin suka yi wanka suka shirya. Mota suka shiga da kayayyakinsu sai Madina, wannan karon ba a hotel suka zauna ba direct gidan Yayansu Ummu Sameehah da ke Madinan suka sauka mai suna Uncle Marzuq d'an kasuwa ne a nan Madinan yake zaune da iyalanshi matarshi mai suna Kinainah y'ar Sudan ce tana da yara uku duk sunyi aure mata biyu namiji d'aya da shi ne bai yi auren ba yana karatu a al'azhar ta Egypt.
Sun samu tarba ta mutunci in da suna hutawa suka fita zuwa Masjid-Nabiy.
Aikin da ke gabansu suka fara babu b'ata lokaci, time to time suna waya da Islaam da 'yan Yerwa. Nadeefah ta maida kanta gabad'aya a aikin da suka zo yi kwana take yi a masallaci sai an yi asuba take dawowa gida ta yi wanka ta kwanta, lokacin Azuhur ta koma bata fitowa sai gab da magrib shi ma daga ishai ba ta komawa sai washegari. Ba ta cika fita da Sairah ba sai da rana da daren ma kafin ta koma take shayar da ita wanda ba kasafai ta cika amsa ba saboda yanda Umm Fawzan take kulawa da abincin yaran da Sairah da Afdhal har ma da iyayen ba ta bari ba kowa tana ba shi kulawa dai-dai gwargwado.
Hakan ya sa da suka koma Mecca sai da suka yi kewanta sosai, shi ma dai yanda ta saba ibada haka ta cigaba da yi ba b'ata lokaci ko jinkiri.
Islaam ko tafiyar Nadeefah ya sanya ya gane annabi ya faku, don rayuwar gidanshi duk ya sauya kamar ba shi ba. K'iri-k'iri in yana son cin abu mai dad'i ma sai dai ya yi order ko ya tafi Yerwa gidan Umma ya ciyo, don tun da ya mata maganar girki da nama sau biyu ta iya masa ta nuna masa ta gaji aiki na mata yawa. Abun bud'e baki ma daga golden yam sai yamball da fries and egg bai jin an masa wani abu different sai uban shinkafa da kayan taliya da take dafa masa, shi har mamakinta yake yi ko d'an irin d'okin first ramadhan with habibie da ake yi bata yi balle ta yi masa girki irin su chicken roundabout da fish cake sai abincin da ko gidan tsaffin aure ma ana yi kai gidan Umma ma ai sun fi shi samun abincin azumi na gari shi duk kame-kame ne. Daman fa shi Islaam yana matuk'ar k'aunar abinci fiyeda tunanin mutum kuma ya tsani a kawo masa abinci kala d'aya, ga kuma ya samu Lele itama kalar zubin da yake nema da muradi ta kuma taru ta lalata shi da girkinta mai dad'i irin wainda ma bai tab'a gani balle ci ba a gidan Umma wanda su ne suka k'ara masa so da k'aunarta a ranshi fiye da tunanin mai tunani wanda ko shi bai tab'a sani ba abu É—aya ya sani wato a kaf duniya bai da kamar Lele bayan iyayenshi jin ta yake kamar wata tsoka ce mai muhimmanci a jikinshi.
Duk son da yake tunanin yana wa Fareesah ba zai ce babu ba amma ya san ya rage ga halayyarta mara sa kyau da suke sake tallafawa wurin cireta daga ransa gabad'aya, har ya fara jin takaicin aurenta tun ba a je koina ba shi fa gani yake yi d'an son da yake mata bai kai ya aureta ba. Ita ko Fareesah ba k'aramin Nasiha Auntynta Aseeyah take mata ba, nuna mata take yi yanzu ne lokacin da zata k'wace mijinta daga hannun matarshi tunda dai ita bata nan kuma dama ce da zata mori amarci tun da wancan ba wani amarci da ta yi duka-duka kwananta 7 ne fa ta fara raba kwanaki, kuma ba wai fa bata yin nata k'ok'arin ba ne ita a wurinta ta k'ure duk wani manejin kulawa da tattali da zata yi masa gani take yi shi ne bai gani sai buhun k'orafi da yake kinkima yana aza mata a kai so yayi duk abinda zai iya yi shi ya sani. Ko da ya daina yin iftar a gidan da farko ba ta damu ba sai kuma ganin da gaske yake yi ya sanya ta bin duk wata hanyar da zata samu ta shawo kan shi ranar ko sai gata har da jera masa kalolin abinci har peppersoup tayi masa na chicken ta kuma dama masa kunun gyad'a da taji madara tayi haske ga kayan soye-soye nan an baje masa ta kuma yi orange juice kasancewar da juicer a gidan, ranar kam ya tabbatar duk abinda take yi tana sane ba kuma wai bata iya ba ne tsabar k'uiya ce da ganin gari ya mata yawa zagewa yayi ya kwashi girkin suna idar da taraweeh ya jata zuwa cikin d'aki don sosai yake kewar mace a tare da shi don d'aukewar da ya mata har a shimfid'a ne to tunda ta natsu don kanta sai ya more gefe guda kuma yana ta lissafin ranakun dawowar Lele gidanshi.
Agogo ta kalla tana duban lokaci k'arfe 10:36 na dare ya nuna mata, mik'ewa tayi tana gyara goyon jakarta da take saka kayan buk'atunta a ciki ta shafa cikinta da take matuk'ar jin yunwa don yau laban kawai ta sha a iftar. Fita tayi ta zura takalminta ta nufi waje garin busy kowa yana hada-hadarsa yawanci masu fita daga masallacin sun fi yawa, nufar jabal Omar tayi ta lift ta hau hawa na hud'u inda babban wurin saida abinci mai suna "Waleemah restaurant" yake. Murmushi ta yi ta samu wuri daga can gefe tana kallon gari ta gefe, waitern da ya zo kanta ne ya tambayeta mai zata ci gaya masa tayi tana maida hankali kan wayarta chats take replying don duk yau bata hau whatsapp ba tana replying na Islaam da ashe yana online ne yanzu ya idar da sallahr taraweeh shi da Fareesah ta je kawo masa fruit salad d'in da ya sakata had'awa wanda sai da tayi d'an k'unk'uni kafin ta tafi.
Ganin reply d'in ta ya sanya shi kiranta video call babu b'ata lokaci kyakkyawar fuskarta ta bayyana a screen d'in tana murmushi, shima murmushin yayi yana cewa " kina ina haka".
Idanu ta juya tace " ina Jabal Omar, your favorite restaurant".
"Waleemah?" Ya tambaya don ya san shi ya fara introducing d'in wurin gareta last zuwan da suka yi don ita ta fi zuwa wani Raffles palace da ke nan kusa da shahr Mansur, ko Royal diner.
Kai ta gyad'a masa tana cewa " yeah, yau ban yi iftar ba ne ina jin yunwa so zan samu in ci sai in koma room in yi wanka". Don sun gama umrah yanzu hutawa suke yi kafin su koma gida, yanzu ta daina kwana a masjid tana komawa room in tayi barci zuwa 1 sai ta fita da ta yi suhr take komawa tayi barci don barci yayi mata yawa.
"Shi Sadeeq fa?".
"Sun bar masjid zuwa room tun d'azu ni ce zan koma yanzu".
"Uhmm okay, me zaki ci?".
"Pasta Alarabiatta, sai flat bread with chicken curry".
"Ke da kike jin yunwa, wannan ne zai isheki?".
"Shi nake jin ci Yaa, sai tea na gaji da cin abincinsu gobe may be Royal diner zan je in samu in ci local nigerian jollof".
"Uhmm ba su kawo ba ne?".
"Yanzu zasu kawo".
"Kwana nawa ya rage ku dawo?".
"A week Yaa" ta amsa tana murmushi, harararta yayi yana cewa " 4 days dai malama ai ina lissafe".
"Kai Yaa, one week ne fa".
"Kar ki yarda in baki yi week ba".
Dariya ta sanya sosai lokacin aka kawo mata abincinta, kallon dariyar da yayi mata kyau yayi yana cewa " ki daina dariya a cikin mutane ko so kike sai an kalleki ne?".
"Yaa ba fa kowa a nan".
"Ko ma menene dai in wani ya zo fa" ya furta yana amsar bowl d'in da Fareesah take mik'o masa, kawar da maganar tayi ta hanyar cewa " iyye su Alpha 'yan gayu me ake ci".
"Fruit salad, zaki sha ne?" Ya tambaya yana matso da bowl d'in zuwa camera, tab'a baki tayi tana cewa " a sha dad'i lafiya" kana ta fara cin abincin a tare suka ci abincin suna yi suna hira ko da suka gama ma ba su katse ba sai da taje ta biya kud'i ta sauka har ta shiga room d'in su ta had'a shi da Sairah, ta wuce wanka ko da ta fito basu gama wayar ba don bata ma san me suke cewa ba da yarinyar ita da Afdhal suke ta zuba ba kayan barci ta sanya tana zuwa ta kwanta cikinsu sun jima kafin suka ajiye wayar ta koma ta kwanta..........
Love wantiti😂.