Chapter 1
by @reza12
*MATAR MAZA*
_Life Story_
_By S-Reza_
_Fist class writers ass..._
*Gargaɗi⚠️*
_Wannan ba ƙirƙirarran labari bane, labari ne da ya faru a gaske, tun daga farkon har ƙarshe. Kuskure ne yin amfani da wani sashe na daga cikin wannan labarin, ko ɗorawa a wata kafa ta socel media ba tare da izini ba. A kiyaye!._
*Jan hankali...*
Kaman yadda na faɗa muku cewar wannan labari ne da ya faru a gaske, ba wai ƙirƙira bane, dan haka ina so ku biyo ni sannu a hankali banda garaje, har mu kai ga isa gurin da muke son zuwa. Allah ya bani ikon rubuta abun da zai amfani al'umma. Amin.
Ga duk wanda suke buƙatar a tallata musu kayansu zasu iya tuntuɓar mu ta wannan number (*** ko +23408100785178) Please WhatsApp kawai banda kira.
Azima tace "Anything Man kandu Human kandu better and better". (Shin kun yarda da wannan maganar?
*MABUƊI*
Kamar bata son amsa wayar ta ce "Okay, amma yau she ne zaka tafi?" Ta faɗa da muryar ƙosawa da hira da shi. "Ina sa ran dai kamar nan da kwana biyu zan shigo, sai dai a kwai wata bazata da nake son nayi miki ne fa". Ya ƙarasa yana dariya, kuma muryarsa kaɗai na bayyanar da farincikin da yake ciki. "Please bana son bazata wallahi, ko mene ka sanar dani kafin kayi, domin kar a samu matsala, bana ko son jin kalmar nan a rayuwata sam". Sai ya fashe da wata iriyar dariya kamar wani soko. Ta ɗan ture wayar daga kunnenta ta ce "Ji wawa, ya wani wage baki kamar sakali". Ya ce Kar ki damu wannan bazatar mai daɗi ce dama gidan ku da muka je ne..." Da sauri ta tsayar dashi da faɗin "No karma ka fara Please, ban yarje maka ba". Ta na faɗa ta kashe wayar ta na mamakin wannan mutumin. Duka-duka ma yaushe har ta sake masa har haka, ita sam bai ma yi kama da irin mutanen da zata iya wata muamula ta rayuwa da shi ba. Sanin halinsa na hauka yasa ta kashe wayar gaba ɗaya domin kar ma ya kirata, sai dai kuma kar Nuri ta kirata taji wayar a kashe. Lissafi take yi a ranta kar lissafin ta ya kufce saboda wannan mutumin fa. Tashi tayi ta koma cikin ɗaki a ranta tana ƙara jinjina wa wannan mutumin da ƙarfin hali, kawai daga ya ɗan samu sakin fuska da Mace sai ka naimi alaƙa da ita har da wani batun zuwa gida. Dama barci take yi saboda yau bata ma je aiki ba. Ta na kwanciya barci ya sake yin gaba da ita mai nauyi. Acikin barcin ta fara wani irin mafarki wanda ya razana ta. Misalin ƙarfe biyu ta farka da wani irin ihu na tashin hankali, haka kawai taji gabanta ya faɗi dalilin mafarkin da tayi, domin gashi sai dawo mata yakeyi, sai ta riƙe girji tana sakƙowa daga kan gadon duk tayi sanyi domin ji take kamar gaske. Babu abun da ya ƙara bata tsoro kamar tunanin wannan mutumin nata da ya fara zuwar mata a rai, to me wannan mafarkin ke nufi, ta tambayi kanta da kanta. Harda gudu ta nufo palo ta ɗauki wayarta, sai lokacin ma ta tuna ashe ta kashe ta, kuma tasan Nuri da Tomas zasu nemeta. Ta kunna tana jin gabanta na faduwa har lokacin. Wayar na kawowa ta shiga neman number Nuri. Sai dai kafin ta kai ga hakan sako ya faɗo cikin wayar da gudun sa kamar dama jira yake a buɗe wayar. Da sauri ta buɗe tana ganin number sa. A fili ta ce "Hasbunanlahu wa ni'imal wakil" Ta dafe ƙirji saboda yadda rubutun ya daki kirjinta. Sai kuma ta toshe baki da hannu ɗaya tana sake kokarin kiran number tasa. Kira ne daga number Hajiya, hakan yasa ta ɗaga da sauri. Kafin tayi magana ta ce "Ina kika ajiye waya tun ɗazu ana ta kira a kashe, dama tambayar ki zamuyi a lokacin, amma yanzu komai ya wuce an ɗaura auren kaman yadda suka buƙata". Ta faɗa tana murmushin farinci, wanda Azima ta ji murmushin kamar da gaiyya tai mata shi.
Da karfi ta ce "Wai aure da wa Hajiya?" Ta faɗa da wata murya wacce bata saba yiwa uwar tata magana da ita ba. "Ban gane shi wa ba, ya ce cen Ingila da yaje kuka tsayar da magana, kuma ai tun wancen zuwan naki ya nuna yana so amma kika ce kina da wanda kike so, haka ya hakura, dan haka yanzu dai suna zuwa aka daura aure, dama kawun naki yace ya gaji da zaman ki haka". Azima tace "Wallahi ƙarya yake yi, ni fa bamu taɓa yin wata maganar soyayya da shi ba, hasali ma ko maganar aure bamayi da shi ba Hajiya, sannan kuma Hajiya yaro ne fa shi, duka-duka ma zan irga lokacin da mukayi magana irin wannan, kuma ni bana sonsa, wallahi bama irin mazajen da nake so bane Hajiya". Ta ƙarasa tana fashewa da kuka kamar wata karamar yarinya. Hajiya ta saki baki tana sauraronta ta cikin wayar. Azima Ta kashe wayar tana jin wani sabon tashin hankali ganin lissafinta ya kufce, tabbas wannan gay ɗin ya shammace ta. Number Nuri ta sake ƙoƙarin kira amma bata shiga.
Ta daɗe a gurin a zaune ta ko kasa tashi sai tunanin abun take yi. Wai aure, kuma da wannan mutumin, ta faɗa tana kokarin saka shi a mizanin mazan da zata iya rayuwar aure da su, ba laifi yana da kyau, kuma yana da kuɗi sosai, amma duk wannan bai dameta ba, babban abun da yafi tsaya mata yadda har ya samu confidence ɗin da zai aureta batare da saninta ba. Ita ko cikekken kamanninsa ma sai yanzu take kokarin haddacewa a ranta. Sai kuma ta fara tunanin to ma sau nawa suka taɓa magana ta fahimta da shi idan ba lokacin da taje Nigeriya ba, sannan kuma ta faɗa masa bata sonsa tun wancen lokacin, ashe saboda haka ne yasa lokacin da suka isa Nigeria yake ta kiranta. Hawaye taji suna zubo mata dalilin ganin kiransa na shigowa. Ita ko sunansa ma bata sani ba, a number sa ma Naci ta saka masa. Sai ta kurawa number ido kamar shi take kallo. Sai ta fara tambayar zuciyarta shin wai ma yayi bincike a kanta ko dai shima Kyu ne ya rude shi, ya san auranta nawa, sannan ya san dokokinta na aure idan har ta auri mutum. Ita bata damu da ko shi waye ba domin dai tasan ma wannan yaron da shi da auren ba zasu je ko ina ba.
Kaman ta ɗaga kiran ta fara zagin uwarsa da ubansa tun yanzu na haushin ɓata mata shiri da yayi, amma dai ta daure tana tausar zuciyarta. Ta yaya zata iya zaman aure da shi, wanda suka isa suka amsa sunansu ma bata zauna dasu ba bare kuma shi, tasan yana sonta amma shi ɗin bai mata bane, gashi yanzu ya rushe mata shirin auran da take da niyyar yi. Tana cikin haka number Hajiya ta sake shigowa. Ta daga tayi shiru. Ta ce "Muna magana kuma kin kashe waya, to aure dai an daura, saura shima kiyi abun da kika saba, wallahi Azima muddin kika kashe wannan auran zan mugun saɓa miki, dan haka kiyi hakuri kiyi zaman aure, wannan karan ki daure ki bawa mara ɗa kunya dan Allah, ina so ya zama na na karshe duk wahala duk dad'i". Har Hajiya ta gama magana bata iya cewa komai ba. Hawaye taji suna zubo mata dalilin tariyo rayuwar ta da tayi ta baya. Kira ne ya sake shigo mata, hakan yasa ta ɗaga da sauri ganin Nuri ce. Ta ce "Shiri ya kammala, Aure ko gobe za'a iya daurawa, gashi nan muna ma tare yanzu haka, yanzu muka sayo zoben, ko a gurin muna ta kiran number ki taki shiga" Nuri ta faɗa da farinciki. "An samu matsala Nuri, an daura min aure a Nigeria yau ɗin nan". "Aure kuma, sai kace wata yarinya, a garin yaya kuma da wa?" Nuri tayi tambayr a rikice. Azima ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce "Shi dai ɗan anacen mana wannan yaron, nifa wallahi ina ce wasa yake yi, kuma kin san halin Hajiya, ita fa a tunanin ta mijin Aure na rasa a nan Ingila, shine kawai daga zuwa tace a ɗaura aura fissabillahi sai kace wata budurwa". Nuri ta ce "Wai tsaya karki ce min wannan yaron da yake tasowa daga Nijeriya yazo har gurinki nan Ingila?" "Eh shi fa, jarabbabe ba". Nuri ta ce "This is serious fa, to yanzu yaya za'ayi da Tomas da yake ta shirin aure, kuma ya musulunta sabo da ke, har ma yayi faɗa da iyayensa? Kinga uban kayan da ya jido miki, shi kansa zoben ma mai tsadar ne, a yadda fa yace min gobe yake so a ɗaura idan kin yarda" Azima ta ce "Ke dai kin san ba zan fasa auran Tomas ba saboda auran wannan banzan da aka yi bada sanina ba wallahi, domin ko addini ya bani dama na zaɓi wanda nake so a matsayina na bazawara, ina da yanci". "Tofa, sabon salo, mai kike nufi, duk su biyun zaki aura a lokaci ɗaya kenan?" Ta ce "Kawai kizo gida ki same ni, I'm waiting for you please, wallahi ba zan fasa auran Tomas ba, sai dai asan uwar da za'ayi, a kwai abun da na ke son yi". Tana faɗa ta kashe wayar tana tunanin abun yi.
A gurin iyayenta auranta huɗu harda wannan da suka yi mata a tunanin su, sai dai ba haka lissafin yake ba a gurinta. Tun daga lokacin da ta fahimci cewa rayuwa kowa na tsaɓarwa kansa abun da ya fi dacewa da shi ne, kuma ta tabbatar da cewar ta tsaya da kafafunta, sai ta mayar da rayuwa sai abun da ta zaɓawa kanta. Kaman yadda maza suke da ikon auran mace ɗaya zuwa goma har a shirin a dalilin auri saki, haka itama ta zaɓarwa kanta, domin ta tabbatar da cewar ta gama kuka akan ɗa namiji, sannan ita tafi ƙarfin ta roki namiji alfarma ko ta mecece. Tsakanin ta da maza Aure ne shima sai wanda ya kai ya isa. Ba zata yi zaman banza ba, sannan ba zata taɓa yarda ɗa namiji ya juyata ba ko wanene shi, aure dai kam zatayi daga nan har lokacin da Allah zai haɗa ta da namijin da zai iya da ita. A cikin sharudan auran Azima a kwai rashin sanarwa iyayenta, aure ne take yi irin na turawa, idan ka shirya a ɗaura, sannan abu kaɗan ke sawa ta rabu da kai duk matsayinka duk dukiyar ka. Sannan ko kai waye idan ka aureta to sai dai ka biyota nan Ingila inda take aiki take da gidan kanta. (A kwai tsare-tsare masu yawa wanda duk zaku fahimta a cikin kabarin) Azima tana da kyau sosai, fara ce doguwa mara jiki sosai, ƙirar turawa, kyawunta da kuma iliminta yana daga cikin abun dake rudar maza a kanta. Ubangiji ya bata farin jini da kuma Sa'a na auran manyan mutane masu faɗa a ji a ƙasashe daban-daban ba iya Afrika ba. (Muje zuwa domin jin wannan kwamachalar ta Azima)
Lokacin da Nuri ta iso gidan ta sameta suna waya da Tomas ne. A saninta ko shi ma ba sonsa take ba, amma sai taga yau harda murmushi take sakar masa. Zuba mata ido tayi tana mamakin Azima. Sai kuma ta shiga tunanin mai take yiwa maza da suke rububinta, kuma gashi ba wai ita ce take binsu ba, abun ma da yafi bata mamaki yadda babu wani mai karimin ƙarfi a cikin mazajen da ta aura har ma da wanda suke sonta. Bata ma san ta gama wayar ba sai ji tayi tana mata magana. "Ta ce "Nuri wani mafarki nayi ɗazu, kuma cikin ikon Allah abun da ya faru a mafarkin ne yake shirin faruwa, sai yanzu na sake yarda da cewar Allah ya tsara mana rayuwa tun kafin muzo duniya, kenan hakan na cikin tawa rayuwar". Ta ƙarasa tana zama kusa da ita. "Wani irin mafarki ne?" Nan take ta faɗa mata abun da ta gani ɗin a mafarkin cewar an daura mata aure a gida, kuma gashi da ta tashi ya tabbata. "Hammm wai yanzu to meye abun yi dan Allah?" Shiru tayi tana son yin magana sai kawai ta ciji leɓenta na kasa tayi shiru.
Bayan tafiyar Nuri kamar da minti goma haka sai ga kiran angon nata. Wannan karan ta daga a dake. Ya ce "Amaryar Bello". Kamar ta gunduma masa zagi ta ce "Ban taɓa tunanin haka kake ba wallahi, ina ka taɓa jin anyi aure haka, ko a garin mahaukata ana irin wannan shirmen ne, kai ba zaka iya shawo kan mace har ta yarda da kai ba sai kawai ka bi mata ta bayan gida, a haka kake son kaji daɗin aure da ita, baka kawo cewar tana da wanda take so ba, ko kuma a kwai maganar wani kanta ba, hakan da kayi ka kyauta min kenan?" Ta jera masa maganar ba tare da ta ko haɗiye yawu ba. Ya ɗan yi murmushi mai sauti kaman yadda ya saba ya ce "Nima ba da nufin daurawa naje ba, kawunki ne ya ce a daura sannan nasan ba maganar kowa a kanki, kuma ni ina sonki, Kema nasan zaki soni zuwa gaba, yanzu dai ba wannan ba, a nan Ingila zan saya miki kayan aure ko nazo miki dasu daga nan Nigeria?" Ya faɗa yana kawar da waccer maganar, kuma har lokacin da wannan murmushin nasa. Ta sake jan tsaki wannan karan a fili ta ce "Ban sani ba stupid kawai". Ta kashe wayar gaba daya6. Ranta ne ya sake ɓaci. Taji har cikin ranta ba zata iya zaman aure da shi ba, kuma dole ne sai ta auri Tomas wallahi sai dai ayi duk uwar da za'ayi.
Kaman yadda kuwa suka tsara da shi. Washegari Lahadi, sai gashi tare da wani abokinsa. Suka jira har Nuri tazo. Suna kan hanyar su tana ganin kiran Bello amma ta sa wayar a silent. Ko kaɗan bata ji wani tsoro ko faduwar gaba ba har suka isa gurin da za'a daura auran nata da Tomas wanda ya musulunta saboda yana sonta. Kawai tasa a ranta cewar, ko dai ta auri Tomas sai ta kira gida tace musu tana da aure, ko kuma ta auri Tomas ɗin ta zauna dasu su biyun ba tare da kowa ya san da kowa ba, ko kuma dai tayi auran sai ta kira shi wawan ta sanar dashi tana da aure idan yaso ya faɗa musu da kansa, kinga kenan dole asa ya saketa da kansa. Wannan tunanin yasa ta sake jin ƙwarin guiwa sosai. Message taji ya shigo wayar ta daidai lokacin da suka zauna masu ɗaurin auran na Ingila suka fara musu tambaya kaman yadda yake a sharadin auransu. Kaman ba zata duba ba, sai kuma ta fito da wayar. Saƙon da ta gani ne yasa bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba tana zare ido tana sakin salati da karfi har wayar na suɓucewa daga hannun ta.
Labari
*Chapter 1*
Ko sallama babu ta banko har uwar ɗaka, tana yaye labule tana haɗewa da tambayar Ina Azima. Ta yi tambayar daidai lokacin suka haɗa ido da ita. Bata tsaya an amsa mata sallamar bama ta yo kanta sai ji kake tass ta ɗauke bakinta da marin da yasa ta dawo da doyar da ta tura a baki. Ta ɗora da faɗin "Wallahi sau goma kika ƙara taɓa Jidda sau goma ina rama mata, idan banda iskanci ma jidda sa'arki ce, ko kawai saboda mugunta da bakar zuciya Irin taki, to wallahi ina sake faɗa miki ki fita a sabgarta". Ta ƙara dungure mata kai tayi hanyar fita. Hajiya ta ce "Ai da kin fara tambayar abun da ya haɗa su, kinga daga nan zaki gane mai laifi, sai ki haɗa su duk ki yanke musu hukunci domin ai duk kin isa da su Maryam". Hajiya ta faɗa da sanyin murya. Maryam ta ce "Yaushe aka fara tambayar Azima idan tana faɗa da wani a gidan nan, yarinyar da baka shiga gonarta bama tana iya shiga taka, to ni dai a ja mata kunne sto". Ta na faɗa tayi waje da sauri. Hajiya ta juyo ga Azima zatayi magana sai gani tayi har ta miƙe tayi waje da sauri.
Babban gida ne na mutum ɗaya mai mata uku. Babbar itace mai yara goma sha ɗaya. Sai mai bi mata yara tara. Sai amarya mai yara shida Allah yayiwa biyu rasuwa ya zama saura guda huɗu. Itace mai suna Hajiya wanda da haka kowa ke kiranta da shi a cikin gidan. Babbar yarta mai suna Azima yar shekara sha biyar, sai kannenta guda uku duk Mata, Sadiya Ummi da Yusra. Su kaɗai ne a gurin Hajiya wacce itace karama a cikin gidan. Babu laifi mai gidan yana da rufin asiri wanda hakan yasa ya zama tsayayyen namiji a gidan sa, duk da wannan yawan da gidan yake da shi baya taɓa yin magana biyu akan yaran nasa ko kuma matan nasa. Idan har yayi tari akan abu to fa tabbas ya tabbata. Matan da yaran gaba ɗaya suna tsoron sa, ba irin tsoron da ɗa zai kasa magana ko wasa da ubansa ba. Duk taurin kanki tofa idan har Baba ya haɗa ido dake yanzu zakiyi laushi. Babbar matar gidan kowa na kiranta da Mama. Tana da yara mata da Maza wanda suka yi aure da kuma wanda suke tare yanzu haka. Sai ta Tsakiya Da kowa ke kiranta da Ammy. Mai yara tara. Maryam itace ƴa ta biyar a gurin Ammy, itace ta rage mata bata rufa ba, ana sa ran shekara mai zuwa, bayan ita a kwai ƙaninta Sani, shine sa'an Azima, bayan shi sai kuma jidda karamar cikinsu.
Sanin kanku ne irin wannan gidan dole a samu rabuwar kawuna kasancewar halin ƴan ubanci. Duk da wannan yawan yaran gidan bai hana Baba ya kwaso yaran Ƴan uwa ko kuma marayu ya ƙara rikewa ba. Hajiya Mahaifiyar su Azima ta kasance bakuwa daga cikinsu, wanda kaman yadda yake al'ada a gidan suna yin aure ne irin na dangi, lokacin kuma da Baba ya haɗu da Hajiya ita bama yar kowa bace a lokacin, kuma ba yar gari bace, amma Baba ya ce yaga Mata. Haka kowa ya ja baki har aka aurota. Wannan dalilin yasa basa raga mata. Tun aihuwar yaronta na biyu da ya koma ta samu ciwon hawan jini dalilin ciwon Diabitis da take dauke da shi. Sosai take shan wahala a cikin gidan har Allah ya bata cikin Azima wanda tun daga samuwar cikin ta fara haduwa da matsaloli, ga na abokan zama da yaran su, ga ciwonta. A wannan halin ta hafi Azima. Yarinyar da ta zamar mata kariya, sannan kuma ƙaruwar matsalolin da take ciki har kawo yau. Eh tabbas duk lalacewar mutum yana da amfani, kuma duk amfanin mutum a kwai lokacin da yake tafka shirme. Azima yarinya ce da taso a cikin wahala da rashin gata daga gurin yan uba, hakan yasa tun tana ƙarama zuciyarta ta ƙeƙashe, babu wanda bata addaba a gidan, wanda kuwa tafi karfi haka zata jibga idan wani naka ya taɓa ta. Bata barin bashi, haka duk girman mutum idan ya taɓa mata Hajiya tofa bata jin Please, Allah ya bata zuciya da fushi wanda kullum sai Hajiya ta roƙa mata Allah akan ya sassauta mata wannan fushin da ɓacin ran. Tun tana ƴar shekara tara take iya yin girkin gaba ɗaya gidan nasu. Kasancewar idan ciwon Hajiya ya tashi an dinga mata habaici kenan akan girki, kuma duk wacce tayi mata a matsayin bashi yake, idan ta warke sai ta biya, hakan yasa ta ɗauki nauyin ranar na Hajiya ita ce ta keyi....📝
Farawa da Bismillah kenan. Farko labarin Azima kenan, ina so ku natsu, mun fara labarin ne daga farkon rayuwar Azima har zuwa lokacin da wancen lamarin ya faru. Please yan amanar S-reza like and shire, shi zai sa na gane kuna son labarin