RAGAYAR DUTSE

PAGE 15

by @nanahaleema11

*RAGAYAR DUTSE.*


            ©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*

*Page 015.*



Muslim tunda Islaha ta shiga ɗakin ya kasa tsayawa, sai zagaye yake yi yana ji kamar ya zama iska ya shiga ɗakin ya ji abinda ake tattaunawa. 

Sai kallon ɗakin yake yi, yana ji zuciyarsa babu daɗi a kan hakan. 


Saleem da yake zaune ya bi sa da kallo ya ce, "ka zo ka zauna mana, sai zagaye ka ke yi kamar sabon soja." 


Ya ɗan kalle sa ya ce, "so nake ta fito kawai, ina ta addu'ar Allah ya sa ya amince." 


Saleem ya ce, "to ka zauna mana." Ya dawo ya zauna yana kallon ƙofar har lokacin bata fito ba. 


Wani iri yake ji a zuciyarsa, dan bai san me ake yi a ciki ba, ba haka yake so ba, so ya yi a buɗe iv card ɗin a gabansa, dan ya ji irin cin fuskar da za a yi mata.


Ya kalli Saleem ya ce, "kar fa mu je wani abun yake yiwa yarinyar nan."  


Saleem ya zaro ido ya ce, "me zai yi mata kuwa? Ka jira ka gani mana." 


"Ka san namiji ba abin yarda bane ba akan mace." Saleem ya ɗan yi murmushi bai ce komai ba. 


A lokacin Islaha ta fito duk suka miƙe suna kallon ta, ta ƙaraso wajansu ta ce, "mu je ko?." 


Saleem ya ce, "ba ki faɗa mana komai ba."


"Na yi tunanin sai mun je mota ai."


"Faɗa mana yanzu dai."


"Mun yi magana dashi, ya ce da kansa zai faɗawa baƙon na mu, kuma ya yi min alƙawarin ni ce ta farko da zan fara hira dashi." 


Saleem ya ce, "good, haka muke fata, Allah ya ba mu nasara." 


Ta ce, "Amin. Mu je ko?."


Saleem ya ce, "babu abinda ki ka manta?."


"Eh, ban bar komai ba" ta faɗa suna shiga elevetor ɗin. 


Suna sauka Reception suka ba da key ɗin ɗakin suka fita zuwa harabar hotel ɗin. 


Kamar an ce ta kalli gefenta, sai gaban ta ya faɗi, ta ɗan yi jim tana kallon wajan kafin ta juyo tana kallon su. 


Saleem ya ce, "mu je ko?." 


Ta ɗan girgiza kai ta ce, "ku je, zan biyo ku daga baya." 


Saleem ya ce, "kamar ya zaki biyo mu? Me za ki yi?."


"Akwai abinda zan yi, ku je kawai" ta faɗa tana komawa da sauri.


Mualim ya ce, "Anya ba shine ya ce ta koma ba?." Saleem ya ɗan yi shiru ya bita da kallo a lokacin har ta koma ciki.


Islaha tana shiga ta jawo mayafinta ta rufe fuska, ta saka faacemask ɗinta ta shiga eleavtor. 


A floor 7 ya buɗe waɗanda suke ciki suka fita itama sai ta fito. 


Ta yi hanyar dama su kuma suka yi haggu, kamar wacce ta manta hanya sai ta yi saurin dawowa da baya ta bi baya a lokacin suka buɗe room suka shiga. 


Ta ɗan zubawa ɗakin ido tana nazari, dan ko tantama bata yi wannan Hafsa ce, Hafsa ƙanwarta ta gidan marayu. Me ya kawo ta hotel har aka shiga da ita ɗaki?.


Dafe kai ta yi tunawa bata da inda zata zauna ta jira su, sai ta juya a inda take tsaye akwai camera, ta gyara nutuswarta ta ƙarasa bakin ƙofar ɗakin gabanta yana faɗuwa. Kamar zata yi knocking sai ta fasa, ta ja da baya ta koma ta sauka ta koma reception. 


A nan ta ga Saleem yana jiran ta, yana ganin ta ya ce, "me kika koma yi ne haka?." 


Ta ɗan yi jim ta ce, "wata na gani wacce na sani tuna baya, shine na koma muka gaisa. Mu je" 


Ta faɗa tana yin gaba ya bi bayanta suka shiga mota suka tafi zuciyarta cike da tsananin tunani akan abinda ta gani.  


         Rehaan bai farka ba sai gab da sallar la'asar, ya miƙe ya shiga wanka, bayan ya fito ya shirya a lokacin aka yi kiran sallah. Ya yi sallah a ɗakin ya tashi ya kunna kettel ya haɗa tea yana sha. 


A lokacin Jazy ya shogo ya bi sa da kallo ganin bashi da alamun shiryawa ya ce, "Malam ka tashi mu tafi. Na gaji wallahi." 


Ya ɗan lumshe ido ya buɗe ya ce, "baza mu bari sai dare ba?." 


Ya girgiza kai ya ce, "A'a, yanzu zamu tafi. Tashi" ya faɗa yana rufe masa box ɗinsa yana kallonsa.


Rehaan ya ajjiye mug ɗin ya ce, "ka kasa gane bana son komawa gida." 


Ya kalle sa ya ce, "wallahi dole ka koma, in ba haka ba zan yi tafiyata na ƙyale ka. Ya zaka dinga raina min hankali kamar wani yaronka, dan ka ga ina biye maka sai ka dinga yin abinda ka ga dama?."


Ya ɗan yi tsaki ya miƙe tsaye, ya ɗauki face cap ɗinsa ya saka, ya saka facemask ya ɗauki wayarsa ya ce, "mu je" ya faɗa yana yin gaba. 


Jazy ya riƙo hannunsa ya ce, "dakata malam, waye bawan ka da zai ɗaukar maka jaka? Ka san dai baka isa ba ko?."


Bai ce komai ba ga dawo da baya ya ɗauki box ɗin, har zai fita sai ya dawo ya cire charger sa ya fita daga ɗakin zuwa ƙofar ɗakin yana danna waya. 


Jafar yana fitowa ya ja ta sa box ɗin suka sauka ƙasa zuwa compound ɗin hotel ɗin. Suna ƙarasawa suka shiga mota suka ɗauki hanyar gida.


Tunda suka nufi gida yake jinsa babu daɗi ko kaɗan, sai kallon hanya yake yi yana ji kamar su koma. A haka suka ƙarasa aka buɗe musu gate suka shiga. 


Jazy zai buɗe ya fita ya riƙo hannunsa ya ce, "kar ka ce zaka wuce gida yanzu, ka zauna tare dani." 


Ya bisa da harara ya ce, "da yake ga bawan ka ko? Dallah cika min hannu, in na shiga muka gaisa da Abba da Mamy tafiyata zan yi, nima uwata tana son ganina ai" ya faɗa yana buɗe motar ya fita.


Jazy yana fita suka haɗa iso da Janan, ta saki ihu ta nufo sa a guje tana zuwa ta rungumesa tana welcoming ɗinsa. 


Jazy ya yi dariya ya ce, "Janan ya aiki?."


"Alhamdu lillah Hamma Jaafar. Ina Hammana?." 


Ya nuna mata side ɗin da Ray yake har lokacin bai fito ba. Ta buɗe ido ta ce, "da gaske tare ku ke?" ta faɗa tana zagyawa da sauri ta ƙarasa ta buɗe masa. 


Suka haɗa ido ta faɗa jikinsa a cikin motar, ya yi murmushi yana zare facsmask ɗin ya ce, "My little Jan." 


Ta ɗago daga jikinsa ta ce, "Hamma shine babu labari? Baka faɗawa kowa ka shigo ƙasar nan ba." 


Murmushi ya sake yi ya ja kunatunta kafin ya sakko daga motar. Janan ta kanƙame hannunsa ta ƙi saki, tana ta murnar ganinsa ta ce, "Kuma da yake ban ga security guard ɗinka ba, shiyasa ban yi tunanin kai bane." 


Ya kalle ta ya ce, "kina zuwa aiki?." 


Ta yi dariya har tana tsalle kamar yarinya ƙarama ta ce, "yanzu ma na dawo." 


Ya sake yin murmushi tana riƙe dashi cikin murnar ganin favorite brother ɗinta.


Ya kalli Jafar da ya yi nisa a hanyar apartment ɗin Mamy. Ya juya yana kallon Janan, kafin ya ce wani abu ma'aikatan gidan sun ƙaraso wajan ana ta gaishe sa ana yi masa barka da zuwa. 


Suka gaisa cikin sakin fuska, aka ɗauki box ɗinsa aka kai apartment ɗin Mamy. Janan dai tana riƙe da hannunsa suka nufi apartment ɗin Mamy, sai da zasu shiga sannan ta tuna ta bar abu akan gas ta sake shi ta tafi a guje.


A lokacin Riyya da Banisha suka fito a guje suka rungumesa a tare. Murmushin jin daɗin ganin ƙannen nasa ya yi, dukkansu kansu babu ɗankwali, gashinsu mai tsaho da santsi ya bayyana har gadon baya. 


Ya ce, "Riyya za ki yar da ni ba, baki san kina da girma bane?." 


Ta ɗago tana kallonsa ta ce, "Shine ko ka faɗa min."


"Saurayinki bai faɗa miki ba?." 


Cike da shagwaɓa ta ce, "bai faɗa min ba." 


Ya yi murmushi, ya shafa fuskarta suka shiga ciki har falon Mamy.


Da sallama ya shiga ya samu Mamy a zaune ita da Jazy gaisawa. Rehaan ya bita da kallon kewar mai yawa, fara'arsa ta ƙaru sosai. Ya ce "Mamy." 


Kafin ya ƙaraso ta miƙe ta cim masa, ta yi hugging ɗinsa ta ce, "sannu da zuwa My love." 


Ya ɗago daga jikinta, yana kallon fuskar ta, cikin harshen hindi ya ce, "na yi kewar ki Mamy." 


Itama cikin yaren ta ta ce, "nima na yi kewar ka Rehaan. Zauna." Bai musa ba ya zauna yana kallon kowa da yake zaune a falon. 


Riyya ta je ta kawo masa favorite drink ɗinsa, wanda ta san yana so indai ya zo gida, daman Jafar ya faɗa mata zai dawo, shiyasa ta yi masa da kanta. 


Ta ce, "kamar na san zaka dawo na yi cocunut drink, gashi ka sha” ta faɗa tana miƙa masa. 


Ya karba ya riƙe hannunsa, ta zauna a kusa dashi ya ce, "thank you. Ba ki ga saurayinki ba?."


Ta kalli Jafar da yake kallon ta, ta yi dariya tana kwanciya a kafaɗar Rehaan cike da kunya. 


Mamy ta yi dariya tana kallon Rehaan cikin murnar ganinsa ta ce, "tana murnar ganin ka, ko sannu da zuwa bata ce masa ba." 


Ta kalli Mamy ta ce, "Allah na ce masa sannu da zuwa.” Ta juya ta Jafar ta ce, "ban faɗa maka ba?." 


Shi dai murmushi kawai yake yi bai ce komai ba, yana jin daɗin ganin iyalan Mamy cikin farin ciki sosai, yana son zama a cikinsu dan kamar ba sirikin Mamy ba haka yake. Tun zamansu a Uk Mamy ta mayar dashi kamar Rehaan, komai tare suke yi, yadda take rarrashin Rehaan haka take yi masa. Zama da ita ya saka yake jin yaren ta kamar yadda Rehaan yake ji, komai in zata yiwa Rehaan zata haɗa dashi.


Ya yi tunanin da ya furta yana son Riyya, har maganar aure ta shiga tsakani zata ɗan canja saboda kunya, amma sai ya ga shine yake haukansa Mamy ko a jikinta. Yadda take yi masa ɗin nan dai bata canja ba, wani lokacin har tsokanarsa take yi. Shiyasa shima ya sake, ya daina jin kunyar ta gabaɗaya.


Jafar ya kalli Mamy ya ce, "Mamy Abba yana nan?."


"Ba ya nan Jafar, sai dai ka dawo in anjima."


"Shikenan, ni zan wuce Mamy."


"Amma zaka shiga ku gaisa da matan gidan ko?." 


Ya ɗan yi jim bai amsa ba, Mamy ta ce, "ka je Jafar, kar ka bar shaiɗan ya yi galaba a kanka." 


Ya girgiza kai ya ce, "To Mamy."


Mamy ta ce, "sai ganin ku kawai na yi, babu labari ko a waya." 


Ya yi dariya ya ce, "Rehaan ne wallahi, magiya ya dinga yi min akan kar na faɗa mu ku. Tun jiya muka dawo, a hotel muka kwana sai yanzu mu ka zo." 


Mamy ta ce, "na yi mamaki da ban ga Rehaan a gajiye ba, ashe kun jima da dawowa."


"Ai da yana nan yana faman furta ya gaji. Rago kawai." Mamy ta yi dariya kawai bata ce komai ba.


Jazy ya miƙe ya ce, "Mamy na tafi."



Mamt ta ce, "ka gaishe da Mummy, ka ce mata zan zo in sha Allah."


Ya ɗaga kai ya ce, "In sha Allah." 


Mamy ta kalli Riyya da take satar kallonsa tana murmushi ta ce, "baza ki raka sa ba?." 


Riyya ta miƙe tana ɗaukar hularta, ta saka ta bi bayan Jazy da sauri.


A lokacin Rehaan ya kalli Mamy da take kallonsa ta ce, "a kawo maka abincin?." 


Ya ɗan girgiza kai ya ce, "A'a Mamy, zan sha drink ɗin kawai, in anjima zan ci." 


"Me za a dafa maka?."


"Anything from my Mamy i like it." 


Ta yi murmushi tana cire hular kansa, gashinsa da ya ɓuya a ciki ya sauka har bayan wuyansa.