03
~~~
"Kuma Inna tsohon ne kaman yanda taji an fada din?"
Juwaira take tambayar Inna daga inda take zaune dai dai gaban durowar kayansu dake a wangale tana nade kaya.
Khausar na kwance kan gadon Inna dan tace kanta na ciwo yayinda Inna ke zaune cikin dayan biyun one sitters dinda ke dakinta tana shafa man zafi a kafarta wanda karfin warinsa ya cika dakin tareda na maganin sauron da Aisha ta kunna mai zagayen nan an dora sa saman wata kwalba dake cikin wani silver plate. Plate din yayi furi furi saboda tokar data manne a cikinsa na maganin sauron.
"Wannan kuma sai ki tambayeta dan nima ban sani ba". Inna ta baiwa Juwaira amsar tambayarta.
Aisha ta shafa addu'arta daga inda take zaune saman dardumar data gama sallar shafa'inta da witr. Ta mike daga dardumar tana nadiyewa ta ajiyeta kan wata karamar durowar gefen gadon Inna. Ta cire hijabin dake jikinta launin brown shima ta nadiyesa ta ajiye tana sanye cikin rigar bacci launin orange irin rigar baccin nan ta indiya. Hula ce a kanta baka. Ta zameta ta gaba kaman koh yaushe gashin gaban kanta yana nunawa.
"Tsohon ne kuma Aisha?"
Juwaira ta tambayeta ganin ta gama sallahr. Aisha ta karaso gefenta ta zauna kafin ta girgiza kanta, dan yanxu da Juwaira ke maganarsa sai fuskarsa kawai ta fado mata a idanuwa.
"A'a ba tsoho bane, kawai dai ya d'an haura talatin" Ta bata amsa.
Juwaira ta jinjina kai dan tun dazu aketa maida labarin na cewa mai kamfani ne ya mata interview dinda taje.
"Allah dai yasa ki samu aikin nan shine addu'ar mu, mai kamfani ai ba ruwanki dashi". Inna ke fada tana saka man zafin ta cikin wani d'an kwando dake ajiye saman window.
"Ameen, Allah ya karbi addu'arki Inna".
Wa'ennan kalmomin na Juwaira suka dawo wa da Aisha kalaman da El Yakoub ya fada mata bayan ta gama amsa mai duka tambayoyin daya mata.
"Toh let's hope Allah ya karbi addu'an Inna koh".
Wannan layin maganar tasa ta daki kwakwalwar Aisha a wannan lokacin da wani irin karfin da batasan sanda idanuwanta suka zare ba cikin dimbin mamakin da ya wanketa daga kai har kafa. Maganar tasa ta matukar girgiza ta. Wace Innar? Ta tambayi kanta? Dama yana jinta duk lokacinda take wayar nan?
Tana tuna yanda ya dago daga kallon iPad dinsa jin tayi shiru zuwa cikin idanuwanta dake a zare kafin ya daukesu d'an karamin murmushi yana hawa labbansa ganin yanda mamaki ya cikata. Murmushin daya bala'in karawa fuskarsa kyau. Kunya ta yiwa Aisha lullubi ta rasa ma me zatace. Shima bai sake maganar ba sai mata bayani yayi kan cewa idan ta samu aikin za'a tura mata email saita fara aiki gobe karfe takwas. Daga kamfanin asibiti ta wuce wurinsu Inna da uban yunwar data kwaso dan ba yanda Inna batayi da ita kan ta tsaya taci abinci lokacinda Juwaira ta kai musu amma tace ba lokaci bataso tayi latti. Gashi dama a kwanakin nan da Khausar ke rashin lafiya ba wani cin abincin take ba saboda tashin hankali.
Saida taci abincin tukunna taji ta dawo mutum, tana ci tana baiwa su Inna labarin yadda komai ya kasance, wannan abun da ya fada kadai ne bata iya samun damar fada musu ba. Data gama kuwa straight wajen Nurse Hadiza taje tace dan Allah ta ara mata wayarta ta saka email address dinta in yaso idan sun tura mata email din sai Nurse Hadizan ta kira ta fada mata.
Haka kuwa akayi, sai yamma suka dawo inda ta zayyanewa Mallam da Maman Nana yanda akayi cewan Interviewn din tayi kyau kuma sunce za'a tura mata email idan tasamu aikin koh a'a. Mallam yaji dadi sosai yanata mata addu'ar Allah yasa da rabonta a aikin nan.
Dama Inna keda girkin dare ranar toh saboda basu dawo da wuri ba Maman Nana tayi tuwo su kuma suna dawowa itada Juwaira suka hau yin miya. Sai bayan isha'i y'an nepa suka kawo musu wuta tana yin hour daya kuwa suka dauke Maman Nana nata dura musu zagi dan kankararta gabaki daya ta narke tass gashi zobonta zai iya lalacewa. Sukaci abinci ta baiwa Khausar maganinta ta kwanta, Juwaira ta tsiri nade kaya. Kayan da Inna ta ringa fadan su da zasuyi bacci yanxu wannan durowar tasu ta ina zata gama gyaranta ma.
Saida suka gyara durowar nan tsab itada Juwaira, sunayi suna sauraren labarin hausan da sukeji na tara da rabi a radion Inna. Sukayi wa Inna sai da safe kafin sukaje suka kwanta a dakinsu inda Nana ke zaune kan katifa tana waya. Koh kallon sasshenta basuyi ba suka kwanta dan dazun nan suka gama fada da Juwaira saboda ta dauki madarar sachet din Nanar ta Peak ta hadawa Khausar shayi aikwa ansha rigima dan saida Aisha ta dauki kudin madarar ta bata tukunna kuma fa ba kudin ne Nana batada shi ba fada ne kawai irin nata da bata rabo dashi.
~~~
EL YAKOUB
Karfe tara na dare dai dai message din Habeeb ya shigo wayarsa da d'an kara na alamar shigowar sako. Ya dago daga danne dannen da yakeyi a laptop dinsa dake saman dining inda yake zaune ya kalli screen din wayar. Kuma kasancewar wayar batada key ya saka kai tsaye layin rubutun da Habeeb ya turo masa ya nuna a fuskan wayar.
'An tura emails din, they start work tomorrow in sha Allah'.
Ya dauke idanuwansa daga kan wayar ya maida kan plate dinda ke gabansa na Jollof rice dinda ya siya bayan ya dawo daga sallahr Maghriba.
A ka'idarsa baya cin abinci mai nauyi da daddare dan sosai yake tsare abincinsa kuma yake kula da jikinsa wannan yana d'aya daga cikin abubuwan da yasaka kowani lokaci jikinsa baya nuna cewa ya manyanta. Baici abinci ba da rana dan bai bar office ba sai shida da rabi yana dawowa kuma wanka yayi kawai ya fita sallahr maghriba. Yana dawowa mota kawai ya dauka ya fita kai tsaye yana neman wajenda zai siya abinci dan jiya gabaki daya matar Habeeb ce ta ciyar dashi kuma da ya kirasa ya tambayesa ina zai samu restaurant sai bai samesa ba. Rabonsa da Bauchi kusan shekaru sha shida yanxu ko'ina ya chanja masa dan inda ma ya taba sani wajen siyar da abinci da yaje shagunan teloli yagani a wajen sunata harkokinsu.
Har wata ya gani ta saka Hijabi cream tsaye tana waya kuma kai tsaye sai kwakwalwarsa ta tuno masa da Aisha. Kokarinta da tunaninta sun burgesa matuka dan zai iya cewa ya jima bai ga mutum that is very smart ba kamarta. Kowace tambaya ya dauko ya watsa masa zata watso masa amsar da zata sakasa jinjina kai cikin gamsuwa. Shiyasa bayan ta tafi kai tsaye ya turawa Habeeb sunanta matsayin wadda yakeso as his secretary. Bai taba secretary mace ba dan a Abuja ma Mahmoud ne secretary dinsa shiyasa abun yaso ya baiwa Habeeb mamaki amma da ya yimasa bayanin kokarin yarinyar ya kuma sake tura masa Cv dinta yagani kawai sai shima ya gamsu da cewan babu wani matsayi da ya dace da ita sai wannan.Sai da ya d'anyi zagayensa tukunna har ya fara kokarin duba map yagan Habeeb din yana kiransa.
"Sallah nake da kake kirana, dana gama kuma ban duba wayar ba sai yanxu".
"Dama zan tambayeka inda zan samu abinci".
Kai tsaye kuma kaman yanda yayi tsammani Habeeb din ya kece da wata iriyar dariyar keta sai kawai ya danna trafficator ya paka motarsa gefen titin da yake kai.
"Dama ita rayuwar gauro haka take malam, in zaka zo kayi aure toh..".
Bai karasa ba El Yakoub ya katse sa
"Zaka fada mun ne koh na kashe wayata".
Habeeb ya sake wata dariyar yana taunar wani abu daya saka a bakinsa
"Gaskiyar ce bakason ji kenan".
"Habeeb"
Ya kiraye sunansa wanda ya saka ba shiri Habeeb ya ajiye dukkan wani wasa gefe ya fada masa inda zai samu abincin. Kuma da yaje ya siyo abincin ya fito tafiya kadan yayi yagan wani waje inda ake siyarda tsire ya tsaya kuwa ya siya. Saida ya tsaya masallaci yayi sallahr isha tukunna ya dawo gida. Yana shigowa ya tube bakar jalabiyyar jikinsa. Saida ya shiga kitchen dinsa ya dauko plate d'aya cikin jerin plates dinda ke cikin cupboard ya wankesa tukunna ya juye shinkafar. Ya duka ya dauki gorar ruwa daya daga cikin carton din da ke ajiye gefen fridge wanda ba komai a cikinsa dan har yanxu bai siya komai ba na kayan abinci. Toh ina ma yakeda wannan lokacin, ya sake tunawa kansa lissafin dayayi na siyan komai karshen satin nan kafin yaje dining ya zauna da laptop bude a gabansa yana cin abincin.
Sai da ya gama latsen latsen da yakeyi tukunna ya dauki wayar ya turawa Habeeb din reply ya sake ajiye wayar. Ya duba lokaci yagan karfe tara ne na dare, dare ya d'anyi da ya kira Hajiyarsa sun gaisa dan rabonsa da ita tun jiya da ya kira yace ya sauka ta mai addu'a. Sai wajen karfe goma da quarter ya kamalla abunda yakeyi, dukda ba wai yagama bane baccin da ya soma ji ne ya saka ya kashe laptop din ya rufe. Ya dauki plate dinnan yaje ya wankesa kafin ya dawo ya kwashi kayansa da sauran ragowar ruwan gorar nan ya nufi dakinsa.
Yana shiga ya sauke komai kan d'an karamin table dinda ke gefen dakin da aka yiwa kujerarsa a gabansa kafin ya karasa ya kunna A.C. Saida kuma ya cire vest dinda ke jikinsa fara kal ya ajiye ya rage daga shi sai wani dogon wandon bacci na flannel tukunna ya kashe wutar dakin ya kwanta. Ya kunna wayarsa ya shiga whatsapp inda yagan wasu notifications sun shigo masa dazu da bai duba ba. Contact dinsa mafi yawancinsu duka na aiki ne shiyasa babu wasu messages da bai bude ba sai wanda aka turo cikin Ningi Family group. Family group dinda Habeeb da kansa ya sakasa aciki.
Hotuna ne guda biyu wanda Umar kanin Habeeb din ya turo shi da matarsa sunje Eiffel tower dake kasar Paris. Dama bai dade da aure ba dan har Sokoto sukaje daurin aurensa saboda y'ar chan ya aura kafin suka wuce Abuja. Daga Abuja kuma suka wuce honeymoon dinsu. Yanda suke cikin tsantsan farin ciki ya riko hannunta sun hade kansu waje daya El Yakoub ya kalla wani abu mai kamada igiya yaji yana zagaye zuciyarsa kamar yana tamketa ne.
Ya kalli kasan hoton inda mutane wajen takwas dake group din sunyi reacting da hearts kafin yayi scrolling yana kallon reply din kannen Habeeb din. Sai kawai ya fice daga whatsapp dinma gabaki daya ya rufe wayar ya ajiye a gefensa.
Wannan abun da yake ji yaji ya sake yawa yana zagaye ilahirin kirjinsa gabaki daya saboda hoton Muneera tsohuwar matarsa da yake kaikawo a kwanyarsa. Ya sauke numfashi mai yawa kafin ya dafe kirjinsa da yaji yana mai azabar ciwo lokaci daya. Ya sake sauke numfashi da ya fito tare da wani sauti dake nuna alamar yana jin jiki. Lokaci daya zufa ta fara keto masa a goshi dukda sanyin da dakin ya fara dauka.
Da kyar ya iya mikewa zaune yana dafe da kirjinsa ya bude drawer dake gefen gadon cikin d'an karamin hasken fitilar da aka zagaye headboard din gadonsa dashi ya dakko maganinsa ya ballo daya yana dorasa karkashin harshensa batareda ya hadiye ba. Ya jingina bayansa gabaki daya jikin gadon yana sauke ajiyar zuciya ahankali.
~~~
Shekara ashirin da biyar da suka wuce.
Shigowarsa cikin gida kenan daga kiran gaggawar da Hajiya ta masa. Dama exams sukeyi yau bashida paper yana hostel yana karatu lokacinda ta kira wayarsa ta shaida masa tana son ganinsa. Wata biyu kenan da rasuwar mahaifinsa kuma koh a wannan lokacin kiransa tayi kan cewa mahaifinsa ba lafiya, kwana uku da zuwansa Allah ya masa cikawa shiyasa yanxu ma hankalinsa yake a mugun tashe da kyar yagan ya iso gidan.
Babban gida ne sosai dake nuna arzikin wanda ya gina sa. Ya taka kafarsa cikin parlon gidan da sallama idanuwansa na sauka kan Hajiya dake kai kawo a tsakiyar dakin. Hajiya Firdausi ta tsaya da kai da komon da takeyi ta juyo zuwa ga d'an ta kwalli daya tal da Allah ya azurta dashi wanda ya biyo mahaifinsa sak kama daga kamanni har ma da halayya dan ba abunda ya baro. Mijinta wanda ya rasu wata biyu da suka wuce kuma kaman jira akeyi ya mutu din dan daga cewa za'ayi binciken dukiyarsa a tattaro saboda a raba gado sai dukiyar tayi sama koh kasa. Saboda an gan cewa babu mai tsaya mata, batada wani d'an uwa namiji da zaizo ya tsaya mata akan hakkin d'anta.
A da tayi tinkaho sosai da dukiyar mijinta barinma lokacinda ta haifi d'a namiji. Sai take ganin ai duk yawan y'an uwan mijinta maza dole ne d'anta ya take su saboda shi zai gaji dukiyar mahaifinsa saidai ashe nasu shirin ya take nata, kallon ayaba suke mata tana musu kallon biri dan tun kafinma d'an nata ya gama makarantar dukiyar mahifinsa ta fara shiga hannunsa sukayi ajalinsa. Tana da tabbaci cewa da saka hannunsu mijinta ya rasu saidai hujjarce batada. Wannan shine abunda yafi komai yi mata ciwo a zuciya na yadda sukayi komai karkashin hancinta batareda ta gane ba yanxu kuma sun kwashe komai.
Lokacinda Yaya Habu babban yayansa yake mata bayanin yadda binciken da akayi na dukiyar mijin da yadda aka gano tarin bashikan dake kansa har ga Allah kasa cewa komai tayi tsabar yanda imani ya mata yawa. A yanda zuciyarta ke tafarfasa da ciwon mutuwar mijinta da kuma ciwon abunda yake fada a wannan lokacin da ta budi bakinta, zata gaya mai maganarda har ya mutu bazai manta ta bane. Koh daga yanda yake mata maganar tasan yasani. Yasan cewa tasan duka maganar da yake fada wani abu ne da sukaje suka kirkiro suka tunkude gaskiya suka dasa sa. Sun kwashe komai da komai ba abunda suka bar musu sai wannan gidan da take ciki.
Shiyasa bayan dogon tunani da nazari ta samo mafita kwalli daya tal da take ganin itace zata kaisu ga nasara, ita kadai ce hanya mai bullewar da zata dawo musu da abunda suka rasa. Bayan kuma ta kirasa ya zo ta zaunar dashi ta mai bayanin komai da yake faruwa kafin ta furta masa kalaman nan. Layi daya tal wanda shine asali, kuma mabudin duk wani abu dazai biyo baya a cikin rayuwarsu batareda ita kanta tasan da hakan ba.
"Ya zama dole ka auri Muneera Saraki".
~~~
YK Ventures
Aisha ta lankwasa siririn tsintsiyar hannunta na dama idanuwanta akan screen din katuwar na'urar dake gabanta. Koh awanni biyu cif batayi ba da fara aiki amma har hannunta ya fara kagewa dan tana zuwa El Yakoub wanda shine boss dinta kuma take aiki a karkashinsa ya tura mata uban files dinda yakeso tayi mai sorting dinsu by date da d'an karamin bayanin meye a cikin kowani file. Da farko batayi tunanin aikin zaiyi wahala ba sai yanxu data gan anyi kusa awa biyu tana abu daya batayi koh rabi ba gashi taga ya sake turo mata wani aikin da yakeso tayi. D'an kwarin gwiwar data fito dashi da safen nan ma duk taji yana bushewa.
Da sanyin asuba Nurse Hadiza ta kirata, ta sallame sallah kenan tana lazimi akan darduma Juwaira na gefenta tana rama raka'atanil fajr ta bata samu ba wayarta data kunna musu fitilarta ta nuna alamar kira. Dama ta sakata silent saboda Nana data rangada mata warning tun lokacin nan da karar shigowar kiran Mu'azzam ya tasheta daga bacci dama kuma sallahrta sai can tsakiyar rana takeyinta dan duk yanda zasu tasheta ba tashi take ba wani sa'in ma kurma musu zagi takeyi ayi fada tukunna. Maman Nana ce kadai idan ta tasheta take tashi da muzurai taje tayi sallahr, itama kanta wani sa'in ba tashi takeyi ba.
Zuciyarta ta buga a kirjinta da ganin kiran nan kafin ta dauka tana jawo sunan Allah a bakinta dan yanxun nan tagama rokon Allah alkhairi akan aikin nan dan haka kawai taji wani son aikin yana ratsa mata zuciya shiyasa ma tayi addu'a idan ba alkhairi bane Allah ya cire mata son aikin kar tazo ta dora wa kanta abunda ba shi ba. Aikwa tana dauka suka gaisa take bata hakuri kan cewa bata kirata jiya da daddare ba da aka turo email din service din MTN ne ya dauke gabaki daya taso shigowa kuma Abban Iman yace ai dare yayi ta kirata da asubahi kawai.
Ta shaida mata cewa sun turo email ta samu aikin zata fara yau karfe takwas na safe. Ai bata san sanda ta kai goshinta kasa ba tana godewa Allah. Ta fadawa Juwaira itama ta tayata murna. Bata san ma ta saki wayar ba sai da tagan Nurse Hadizan na sake kiranta ta dauka take ce mata zata shigo anjima idan ta shirya zuwa asibiti ta bata wayarta duba email din taga me aka turo sai Abban Iman ya saukesu. Aisha tayi mata godiya sosai kafin suka katse wayar. Baccin da basu koma ba kenan dan straight dakin Inna suka wuce wadda suka iske tana lazimi suka fada mata aiki fa ya samu. Inna tayi murna sosai Khausar na tayata. Suka zauna suka dasa sabuwar hira har Inna na cewa da yarda Allah anjima zata kira Uncle Murtala ta shaida masa ta samu aiki ta kuma ce mai ya turo kudi a dinka mata y'an sababbin dogayen rigunan da zata ringa zuwa aikin dasu.
Dama Khausar bazataje makaranta ba ranar saboda bata gama samun karfin jikinta ba tukunna. School din tasu ma sun san da excuse dinta na yawan rashin lafiya. Teacherta har kira tayi ta tambayi jikin Khausar lokacinda suna asibiti. Karfe shida da rabi Juwaira ta shiga kitchen ta dora musu karin kumallo yayinda Aisha ta dora ruwan zafin wanka. Ta taya Juwaira soya wainar rogon da zasuci kafin ruwan nata sukayi zafi ta diba ta shiga wankan.
Ta shirya abunta bayan ta fito suka zauna suna cin wainar rogon nan da kunun da Juwaira ta dama musu yayinda Inna ta fice dakin Mallam dan sanar dashi Aisha fa aiki ya samu yau zata fara zuwa. Yayi farin ciki sosai dan har dubu biyu ya bata yace ta baiwa Aishan tayi kudin mota. Ta tsaya dakin Maman Nana itama wacca bata fito da wuri ba tana shaida mata abun alkhairi wanda a gurin Maman Nanan baizo a abun alkhairi ba. Haka taji kamar Inna ta debi garwashi ne ta watsa mata a kirji dan da kyar ta iya yiwa Aisha addu'ar Allah ya bada nasara kai abun ma bai dada karuwa ba sai bayan Nurse Hadiza ta shigo ta baiwa Aisha wayarta dan ta duba email din. Ashe wai aikin sakatariya suka bata, sakatariyar ma ta mai kamfanin ga wasu makudan kudin da akace za'a ringa biyanta duk wata.
Ai bata san sanda ta dafe kirjij tace
"Kaii wannan uban kudin haka, wannan aikin na Allah da annabi ne kuwa".
Sai bayan ta fada tagan yadda dukkansu suka juyo suka kalleta tukunna ta kara da
"Kunsan fa yadda mutanen yanxu suke, ba karamin aikine zakayi ba a dauki wannan kudi mai yawa a baka. Bare matsayi karami na sakatare".
Nurse Hadiza ta mata bayanin ai babban aiki suka bata tunda sakatarin mai kamfanin zata yi. Wannan abun ya dada karfafa abunda yake ranta Taji taya za'ayi ace Aisha ta samu irin wannan aikin bayan kuma y'arta tana nan ita koh gama makarantar batayi ba. Ya za'ayi a ringa biyanta wa'ennan makudan kudaden duk wata su kuma suna nan zaune itada y'arta. Inna ke da yara maza a gidan ba ita ba, yaranta duka mata ne. Allah yayi daya tayi aure amma ba aiki takeyi ba, mijinta kuma ba wani abun azo a gani bane tunda ba kudi garesa ba a cewarta kenan. Sannan ga Nanan nan da ake fatan itace zata ci arzikin a wajenta ta kasa maida hankali tasan me ta saka a gaba. Mallam ba wata dukiya ya tara ba bare ace idan ya fadi ya mutu akwai gadon da zai isheta, sana'arta ba wata babbar sana'a bace sannan yanxu kuma ace wai Aisha tayi tsalle ta kame aiki inda za'a ringa biyanta kudaden da suka fi karfinsu dan ita a rayuwarta kapp bata tunanin wani abin arzikin ya taba samunta ba har ta rike irin wa'ennan kudaden a hannyenta tace nata ne. Dan koh auren Hindatu da kame kame da komai aka samu aka kammala mata kayan daki da kitchen batareda anji kunya ba.
Inaa bazata sabu ba, akace wai bindiga a ruwa.
Abban Iman yana sauketa ta musu godiya ta sauka. Ya dauki dubu uku ya mikawa Nurse Hadiza yace ta baiwa Aisha tayi kudin motar dawowa tayi masa godiya dan har taki karba da farko Nurse Hadiza ta chusa mata su cikin jakar ratayarta. Tana shiga receptionist dinnan ya ganeta suka gaisa ta sake fada mai sunanta yace mata office dinta yana floor na uku inda taje jiya. Ta haura saman kamar jiya suka sake haduwa da wannan matar wadda sai a yau take gaya mata sunanta Ayo. Ta sake nuna mata wannan kofar tace ta shiga nanne office dinta amma ta sake shiga wajen "sir" kamar yanda Ayo ta kirayesa ya mata briefing yanda aikin zai zama tukunna.
Sai bayan ta bude kofar ta shiga wannan open office din tukunna zuciyarta ta gasgasta mata cewa ta samu aikin dagaske. Dagaske itace a matsayin secretary din CEO a wannan kamfanin. Dan lokacinda ta gan layin rubutun a email dinnan a wayar Hadiza bata yarda ba, kudin ma ne suka sake saka ta jin kokwanton abun a ranta. Kawai zuciyarta bata yarda ba, ganin take kamar idan taje zasu bude baki su ce mata kuskure sukayi wani aikin daban ta samu ba wanda suka rubuta mata ba. Sai gashi receptionist dinnan bai ce komai ba, matar nan itama bata ce komai ba. Da tana takawa zuwa office din har jira tayi taji Ayo din ta kira sunanta ta tsayar da ita, koh ta shigo kawai taga wata zaune a kujerar ba ita ba.
Sai bayan ta shigo ta sake karewa wajen kallo da aka sake gyarawa har kyalli yakeyi tukunna ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah da wannan ni'imar da ya mata. Ya bata taimako a lokacin da take tsananin bukatarsa. Ta roke shi ya kareta da dukkan sharrin dake cikin aikin nan ya kuma hadata da dukkanin alkhairin dake cikinsa. Da bisimilla a bakinta kuwa ta kwankwasa kofar sa kafin ta turata tana taka kafarta ciki.
~~~
Ammi Malami🌸