LULLUƁIN BIRI

55

by @halimahz

A lokacin Zaytuna na waya da Bello.
"Ehh, haka ya ce ka tabbatar an samu report ɗin likitocin gaba ɗaya. Wai baya son wani kuskure. Komai yake so in lessthan 24hrs."

Kafin ta ƙarasa maganar, sai ta ji an zare wayar daga hannunta. Da sauri ta ɗago.
Hajiya Madina ce tsaye a gabanta, fuskarta ɗauke da ɗan ɓacin rai.

"Maama..."
Ta faɗi tana saurin miƙewa ta rungumeta. Irin rungumar da take jin tana buƙatar ta yiwa Hajiya Ramla, amma ba zata iya ba. Nan take kuka ya biyo baya.

"Yi shiru."

Hajiya Madina ta katse ta. Nan ta kama hannayenta suka nufa inda Hajiya Ramla ke tsaye tana kallon tahowarsu. Tana jin bugun zuciyarta na ƙara tsananta. Musamman da ta ga yadda Zaytuna take tafiya iri ɗaya sak da tata, da kuma yadda ta yi ƙasa da kanta tabbacin bata so ta zo gareta, ta taho ɗin ne a bisa dolen da Hajiya Madina ta yi mata. 

Sai ta ji ba zata iya haƙurin jiran ƙarasowarsu ba, don haka ta taka ƙafafunta da har yanzu zafin ciwo bai bar su ba, cikin sauri ta tafi garesu tana danne sautin kukan da take jin yana taso mata. 

Kuma zata iya cewa gaba ɗaya taku uku ta yi ta cimma su. Ba ta jira Hajiya Madina ta damƙa mata hannun ƴarta kamar yadda take shirin yi ba, kawai ta janyota da kanta zuwa jikinta tare da yi mata wata kyakykyawar runguma. Wadda tasa ƙasusuwan Zaytuna amsawa, lokaci guda sautin kukan Hajiya Ramla ya ƙwace. 

"Ki yi haƙuri... ki yafe min..."
Hajiya Ramla ta faɗa cikin muryar kuka.

Kuma nan take. Zaytuna ta ji wani abu da bata taɓa jin irinsa ba. Da farko ma bata gane mene ne ba. Domin a rayuwarta akwai rungumomi da yawa. Rungumar Hajiya Madina. Rungumar Mahaifinta. Rungumar Yayanta.

Amma wannan... Wannan daban take.
Wani irin natsuwa ne da take ji yana gangarowa daga saman kanta zuwa ƙafafunta. Wani irin ɗumi da ta kasa fassara shi. Wani irin yanayi da ya sa jikinta ya yi laushi ba tare da ta shirya ba.

Hannayen Hajiya Ramla suka ƙara matse ta. Kamar wadda take son mayar da ita cikin ƙirjinta. Kamar wadda take son rama dukkan shekarun da suka shuɗe cikin daƙiƙa guda.

Kuma a karon farko.
Zaytuna ta ji wani irin kuka yana tasowa daga wani lungu na zuciyarta da bata taɓa sanin yana nan ba. Sai dai da sauri ta daure ta haɗiye shi.
Domin har yanzu tana fushi. Har yanzu tana jin ciwo. Har yanzu tana son amsar tambayoyinta.

Amma abin mamakin...
Duk da fushin. Duk da zafin ciwon a zuciya. Duk da shekarun da suka shuɗe.
Bata samu kanta da tureta ba. Bata samu kanta da ƙwace jikinta daga rungumar ba.
Sai ta tsaya kawai, Yayin da kukan Hajiya Ramla ke dukan kunnuwanta.

Hawayenta suna zuba akan kafaɗarta. Ta kasa daina maimaitawa.
"Ki yafe min. Don Allah ki yafe min. Ban taɓa daina sonku ba.. Wallahi ban tafi na barku haka kawai ba, akwai dalilin da ni kaina ban san shi ba..."

Zaytuna ta lumshe idanunta. Domin ta tsinci kanta da jin wani abu mai matuƙar ban mamaki. Kamar zuciyarta na gajiya da riƙe fushin da ta shafe shekaru tana ɗauke da shi.

A daidai wannan lokacin. Turaki ne a hankali ya tura ƙofar ɗakin ya shiga. Tukunna ya tsaya, kafin ya mayar ya rufe ta bayansa. Shiru ne a ɗakin, shiru irin wanda sai sautin numfashin mutum ake iya ji, da numfashin na'urar sanyaya ɗakin da bugun monitor ɗin da ke gefe. 

Hannayensa duka biyu ya zuba cikin aljihun wandonsa. Ya jingina bayansa a jikin ƙofar. Ya tsaya cak kawai yana kallonta.

Dogon kallo! Irin kallon da ba na idanu kaɗai ba ne. Kallo ne da zuciya ke yi. Kallo ne da rai ke yi. Irin kallon da ake yi lokacin da baki ya kasa ɗaukar nauyin abin da ke cikin ƙirji. Kallon da dukkan kalmomi suke mutuwa.
Kallon da yake tattare da tambayoyi, da godiya, da tsoro, da ƙauna, da kuma wani irin farin ciki da ya fi ƙarfin bayani.

Yau ɗin ya yi abubuwa da yawa da zuciyarsa ba ta san zata ɗauka ba. Baccin take yi da gaske cikin salama, tamkar ba ita ce ta tayar da guguwar da ta sauya rayuwarsa gaba ɗaya ba. 
Wani irin murmushi mai rauni ya bayyana a gefen leɓensa. Yana daɗa cusa hannayensa cikin aljihu, domin yana jin idan ya sake su a waje, za su kai kansu gareta ba tare da izininsa ba. 

Kuma ba yanzu ne lokacin ba, ba yanzu ne ya ke so ta san da aurenta akansa ko waninta ba, don haka zai yi controlling kansa in sha Allahu, zai yi dukkan ƙoƙarinsa wajen ganin bai tattarota zuwa jikinsa ya kewayeta a faffaɗan ƙirjinsa ba, zai hana kansa wajen sunkuyo da fuskarsa zuwa tata, ya sumbaci kyawawa kuma tausasan laɓɓanta da yake jin tsananin sha'awar yi musu shan alawa.

Sai dai bai san ta yadda zai fahimtar da kowa cewa, bai son ya ɗora alhakin jinyarta akan kowa. Shi yake son yi. Shi yake son ya dinga ba ta magani. Shi yake so ya dinga lallashinta idan ta ƙi sha.
Shi yake so ya dinga jin ƙorafinta, ya dinga sauraron gunagunin da zata yi saboda magani. Ya dinga amsa mata kamar yadda ake yiwa yara.

Ba ya so ko kaɗan a takurata, yana so ta samu ƴancin zuba taɓararta son ranta a jikinsa. Ba irin waccan jinyar yake so ayi mata ba da idan bata sha magani ba za su yi mata faɗa. A yanzu so yake idan zata yi kukan shan maganin, ya zuba maganin a nasa bakin, tukunna ya haɗe bakinsu wuri guda, sannan ya kai hannunsa saman mararta ya danna, dole numfashinta ya ɗauke na wucin gadi, kuma dole idanun nata za su sakko da hawaye, a sannan dole ta buɗe baki don fashe masa da kuka, shi kuma sai ya zuba mata maganin a lokacin da yake yawo da hannunsa a saman mararta, dole zata gimtse bakinsa da ke cikin nata, wanda hakan zai yi sanadiyyyar da yawun bakinsa zai kora maganin kai tsaye zuwa cikinta.

Kuma a lokacin zai yi mata kyakykyawan matashi ne a jikinsa, ya dinga shafa gashinta a hankali yana sauraron shashsheƙar kukanta, ba zai ce mata komai ba, zai yi shiru ne, domin sau da dama shiru yafi magana.

A karon farko cikin shekaru masu yawa. Turaki ya ji cewa wataƙila zuciyarsa ta yi ƙanƙanta da ɗaukar dukkan farin cikin da yake ji a rana guda.

Ya haɗiye yawu a hankali. Fuskarta ta yi fayau saboda wahalar da ta sha. Bandage ɗin da aka naɗe mata a goshinta yana ƙara tunasar da shi irin bala'in haɗarin da ta tsallake. Amma duk da haka, a idanunsa bata taɓa yin kyau kamar yau ba. Ba wai kyawun fuska yake gani ba, kyawun rayuwa yake gani.

A yatsanta guda kuma akwai pulse oximeter da ba a cire ba har yanzu.
A karo na farko yana kallonta ne ba kawai da idanun mutumin da ya damu da lafiyarta ba. A'a. Kallonta yake da idanun mutumin da Allah ya yiwa wata ni'ima da ta fi ƙarfin tunaninsa. Murmushi ya suɓuce masa ba tare da izininsa ba. Murmushin da ya fito daga wani wuri mai zurfi a zuciyarsa.

Har yanzu yana jin kamar mafarki yake. Mafarkin da yake tsoron farkawa daga cikinsa. Domin idan har wannan mafarki ne, to baya son ya farka har abada. Idanunsa suka sake yawo akan fuskarta. Sannan suka tsaya a kanta. A gashinta da aka ɗan tura gefe. A laɓɓanta, a numfashin da ke fita ta ƙirjinta a hankali.

Sai ya ji zuciyarsa ta yi wani irin fayau. Fulani ta cike masa wani gurbi da ya kwashe rabin rayuwarsa yana rayuwa da ciwonsa. Kallon da yake yi mata ya canja, ya yi laushi, ya yi zurfi. Ya yi kamar na mutumin da ya daina neman wani abu a duniya, domin abin da yake nema ɗin, ga shi yana kwance a gabansa.

Wani sassanyan murmushi ya sauka akan leɓensa. Murmushin da bai san lokacin da ya zo ba. Ya sake lumshe idanunsa na ɗan lokaci tare da zuƙar numfashi.
Nan take hoton wasu mintuna da suka gabata ya haska masa. Yana zaune a gaban Dr. Anas. 
Ya je ne da niyyar yi masa bayanin dalilin da yasa suke son sallama. Ya je gaya masa cewa za su canja mata asibiti. Za su fita da ita ƙasar waje. Za su nemo mata duk wata kulawar da kuɗi za su biya buƙata.

Sai dai bai kai ƙarshen jimlarsa ba. 
Dr Anas ya katse shi da cewa,"Ai Alhamdulillah Patient ɗinku fa ta farka cikin ƙoshin lafiya..."

Har yanzu yana jin yadda kalmomin suka sauka a kunnensa. A lokacin ma ya tsaya yana kallon likitan ne kawai. Kamar bai fahimci abin da aka faɗa ba. Kamar ƙwaƙwalwarsa ta kasa sarrafa maganar.

Sai da Dr. Anas ya sake maimaitawa.
"Ta farka mintuna goma sha biyar da suka wuce, Alhamdu Lillah ba yadda muka yi zato ba... Yanzu tana bacci, Amma ba wani abin damuwa ba ne baccin nata. Ko da zata farka normal zata tashi in sha Allahu. Akwai tarin gajiya da baccin a tare da ita ne, Jikinta yana buƙatar hutawa sosai. But za ka iya shiga ka ganta idan kana so... Dr Yusuf ɗin wani uzuri ya riƙe shi."

Daga faɗar hakan. Komai ya disashe masa. Ba zai iya tuna yadda miƙe akan kujerar ba. Bai zai iya tuna yadda ya kai bakin ƙofa ba. Abin da kawai yake tunawa shi ne ya ji bakinsa yana faɗin,"Thank you Dr."

Daga hakan kuma kamar taku uku zai iya cewa ya yi ya kawo shi cikin wannan ɗakin.
So yake kawai ta farka, idan ta farka kuma ƙwayar idanunsu su sarƙe ana juna. Shi kaɗai ne abin ya rage masa don yanzu kam bai da sauran wata fargaba.

Idonsa da ke faman yawo akanta ƙur ya sauka akan yatsanta yana motsi mai ɗauke da pulse oximeter. Zuciyarsa ya ji ta bayar da wani fat! Fat! Fat! 
Kuma kafin ya gama wani tunani...
Sai ya tsinci muryarta a hankali tana ratsawa cikin kunnuwansa. Sai dai bai iya fahimtar abin da ta faɗa ba.

Nan take ya zare hannayensa a Aljihu. Cikin gaggawa ya yi takun da zai iya kiransa guda ɗaya. Sai ga shi a bakin gadon. Ya ranƙwafa akanta. Ya yi mata rumfa da dukkan jikinsa. Idanunsa ƙyam akan fuskarta. Yana kallon yadda gashin idanunta ke motsawa kaɗan-kaɗan, yana jiran ta buɗe idanunta.

Ba zai iya ba! Ya kasa jurewa! Don haka kawai ya kira sunanta da wani irin amo mai motsa zuciya.

"Fulani..."

Yatsunta suka sake motsi. Laɓɓanta suka ɗan motsa. Ya ƙara sunkuyawa kanta, har numfashinsa da nata na haɗewa. A tunaninsa ya fita daga dukkan wata fargaba, ashe da saura, don a yanzun da yake ta jiran ta buɗe ido kuma ta sake yin magana, sai ya ji sabuwar fargaba ta lulluɓe rayuwarsa.

"Fulani..."
A wannan karon muryarsa ta fita da wani irin rauni. Kuma kamar tana jiran ya sake kiran sunan nata ne kafin ta amsa. Sai ya ji ta a hankali. Da wata murya mai nauyi tana faɗin,"Mum! Mum please ki tafi, su Turaki na son ganinki a raye..."

Turaki ya daskare. Kunnuwansa suka daina jin komai sai maimaicin maganarta. Maganar da ta yi a wahalce.

"Kada ki tsaya Mum, ki tafi kina ta Hasbunallahu Allah zai tsare mana ke..."

Hannunsa ya kama zanen gadon ya damƙe da ƙarfi. Zuciyarsa na bugawa.
Hawayen da suke cikin idanunta suka zuba ta gefe. Sai kuma kalmar ta fito, Kalmar da ta karya duk abin da ya rage masa na daurewa.

"Mum Turaki na jiranki, don Allah ki tafi ko zai daina kukan rashinki, ki isa gare shi ko zai daina yiwa kansa rauni a duk sanda ya kasance a ɗakinki, yana jiwa kansa ciwo sosai Mum..."

A wannan lokacin, Kamar wani abu ne ya fashe a cikin ƙirjinsa. Dukkan abubuwan da ya ji yau. Komai ya haɗe lokaci guda.
Bai ma san lokacin da ya zira hannu ta ƙarƙashin bayanta ba, ya tattarota gaba ɗaya tare da zanin gadon.
Ya ɗagota yana haɗe jikinsu wuri guda. Da ƙyar ya iya saita kansa gudun kar ya yi mata rauni, ya samu daidaito ɗin da yayi mata Runguma mai ƙarfin gaske, Rungumar da ta fito da ƙarfin zuciya ba da ƙarfin jiki ba, runguma mai cike da godiya a gareta. Rungumar ban san ta yadda zan saka miki ba.

Har bai ji lokacin da ta yi wata ƙaramar ƙara ba.
"Ahhh..."
Ta faɗa da raunanniyar murya. Sai kuma ta sake motsawa kaɗan.
"Zafiii..."

Wannan karon ya ji ta. Sarai ya ji ta. Amma ba zai iya sakinta ba. Wallahi ba zai iya ba. Don kamar hannayensa sun manta yadda ake sakin abu. Kawai dai ya matsar da bakinsa kusa da kunnenta.

Iskar numfashinsa ta daki fatar wuyanta. Sannan ya furta cikin wata narkakkiyar murya.
"Sorry..."

Ya faɗa yana sake lumshe idanunsa tun bayan da ya rungumeta ɗin. Sannan ya sake cewa a hankali.
"So sorry Fulani..."

Kuma faɗar tasa ta haɗe da turo ƙofar ɗakin aka shigo...