GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 8

by @nusybee143

Page 8




Shiru ya yi na ɗan lokaci yana nazarin saƙon, kafin ya kaɗa kai kawai,ya tayar da mota ya cigaba da tafiya don wucewa wajen aiki 

Yana shiga office ya zauna akan kujerar da ya saba zama,ya ɗauki shayin da aka kawo masa babu daɗewa ya fara sipping a hankali yana nazari

Buɗe system ɗin sa ya yi ya lalubo ɗaya daga cikin hotunan Roxy da ta yi a ƙasashen waje,sanye take da sweater baƙa da dogon wando jeans,sai sketchers a ƙafarta,sai baƙin glasses da ta rufe ƙwayar idanunta,tana tsaye a cikin dusar ƙanƙara 

Ya kai mintuna biyu yana kurɓar tea ɗin yana nazartar hoton kamar mai son gano wani abu a hoton, kafin ya yi murmushi ya ce"smart girl!

I like you!!!"ya ture laptop ɗin gabanshi ya janyo wayarshi ya fara ƙoƙarin aika kira 

Bayan ƴan seconds kaɗan sai ya fara magana "Awwal ka same ni a office ɗina"yana faɗin haka ya kashe wayar 

Babu jumawa Awwal ya shigo,bayan ya sara masa ya ja gefe ya tsaya yana faɗin "morning Sir!"

"Awwal!

Ya batun aikin da na saka ka?"

Awwal ya sake sarawa Haisam Sannan ya ce"sir!

Mun kasa samun location ɗin"

Haisam bai yi mamakin jin hakan ba,don shima ya sani,a shirye take,abin da ya fi haka ma zai iya ji,a maimakon haka sai cewa ya yi "zauna mu yi magana Awwal"

Babu musu Awwal ya sake sara masa, sannan ya samu kujera ya zauna, Haisam ya buɗo messages na NOCCM ya nuna masa ɗaya bayan ɗaya 

Mamaki sosai ya kama Awwal,ya ɗago yana kallon Haisam da neman ƙarin bayani, Haisam ya gyara zama sosai ya ce"yarinyar nan a shirye take Awwal 

Babu wanda ya san cewa mu jami'an DSS muna bibiyarta,yaya aka yi ta sani?

Maybe akwai wani a cikinmu da yake kai mata rahoton komai,kuma zai iya zama ko ma wanene,amma ka san me na gano, kuma nake tunani a kai?"

Awwal ya girgiza kai yana faɗin "sai ka faɗa"

Haisam ya ce"tana da babban team da suke gudanar da aiki tare,waɗanda suke taimaka mata don cimma burinta,irinsu ne suka tare Amna da drivern ta suka ƙwace masa waya,a sigar gargaɗi"

Awwal ya sauke ajiyar zuciya,duk yadda suke tunanin yarinyar nan ta wuce haka,amma sai ya ce"to Sir ya kake ganin za'a yi?

Sannan kuma menene sabon shirinka?tunda abin ya fara haɗawa da ƴarinyar da bata san komai ba?"

Kai tsaye Haisam ya ce"babu gudu babu ja da baya,asalima yanzu nake jin na ɗaura ɗamarar kamo ta, yadda take jin cewa tana da wayon da yake jagorantar ta ta aikata laifi haka nake jin ina da wayon da zan daƙile kuma na kama mai laifi "ya miƙe tsaye ya ce "mu je zuwa! yanzu aka fara wasan!

I love the way you act!! smart girl!!!"







*MALIYA ESTATE*

Ringing ɗin wayarta ne ya tayar da ita daga baccin da ta kwanta bayan ta idar da sallar walha,ɗaga kanta ta yi tana duban wayar, kafin ta janyo ta a hankali ta ɗaga wayar ba tare da ta duba sunan ba

"Ummu Shaheeda!

Yau dai ga mu a Nigeria!"

Tuni ta wartsake,ta nemi baccin da take ji ta rasa jin muryar gudan jininta, wadda ta rage mata a duniyar nan da zata kalla ta ji daɗi,ta tabbatar da a ce tana ƙasar da ba ta kasance cikin kuka da ciwon da take ciki yanzu ba

"Yaya Saude!

Ke ce!ke ce a garin?

Allah sarki yaya Saude,ashe za ku dawo ƙasar "ta faɗa da muryar kuka

Murmushi Hajiya Saudat ta yi,itama ta yi kewar ƙanwar tata sosai,ta ce"muna ƙasar,jiya muka sauka, lafiya dai ko?"

Kamar wadda take jiran wannan tambayar sai ta fashe da kuka sosai, Hajiya Saudat ta yi murmushi tana lumshe idanu ta buɗe,ta ce"Zainab ba za ki girma ba dai da alamu

Menene dalilin kukan kuma? haba autar Hajiya"Ummeey ta goge hawayenta ta ce"zan zo yaya,zan zo yanzu,kina gida ko? babu inda za ki je ko?"

Hajiya Saudat ta ce"eh ina gida auta!

Ai ko zan fita in dai kika ce za ki zo zan tabbata na haƙura da fitar ko don faranta ran autar Hajiya,sai kin zo"Hajiya Ummeey bata sake magana ba ta kashe wayar 

Daga nan kai tsaye Alhaji Yusuf ta kira, ta sanar masa da fitar ta zuwa gidan Hajiya Saudat, Alhaji Yusuf ya ce"Masha Allah!

Ki ce ta dawo ƙasar kenan?"

Ummeey ta ce"eh,ta ce jiya suka dawo "Alhaji Yusuf ya ce"to babu matsala,a ce ina miƙa sakon gaisuwa,sai mun zo"Hajiya Ummeey ta yi murmushi sannan ta kashe wayar

A ƙasa da awa guda Hajiya Ummeey ta fito cikin shirinta na doguwar rigar lace,ta ɗora babban mayafinta yadda ya zama ɗabi'arta,ta faɗa mota,driver ya ja ta sai gidan Hajiya Saudat 

Hajiya Saudat ita ce ƴar'uwa ɗaya tilo ta Hajiya Zainab,wato Ummeey,su biyu kawai iyayensu suka haifa,sai da aka aurar da Hajiya Saudat sannan aka haifi Hajiya Zainab,tsakanin Hajiya Zainab da babban ɗan Hajiya Saudat wato Ishaq wata uku ne kawai,sai dai suna da shekaru biyu da haihuwa Allah ya yi masa rasuwa sakamakon ciwon ƙyanda 

Bayan shi Hajiya Saudat ta haifi yara uku amma duka ba su zo da rai ba,daga baya ma haihuwar ta tsaya gaba ɗaya 

Shekarar Zainab biyar Allah ya yi wa iyayen nasu rasuwa sakamakon haɗarin mota,a hanyar su ta dawowa daga tushensu,garin Duwala na ƙasar Kamaru,itama Zainab da suke tare a wannan lokaci ya ji ciwo sosai,amma da yake da sauran shan ruwanta a gaba sai ta samu lafiya 

Saude ta yi kuka sosai saboda rashin iyayenta,daga baya ta dangana, musamman da mijinta yake ba ta baki, ya nuna mata yanzu ba lokacin kuka bane, tunda Allah bai azurta su da nasu ɗan ba sai su rungumi Zainab,hakan kuwa aka yi

Duk wani gata da soyayya babu wanda Zainab bata gani a wajen iyayen riƙonta ba,har ta kai shekaru goma sha biyar,inda suka aurar da ita ga Yusuf Maliya 

Yusuf matashin saurayi ne da karatun allo ya kawo shi Kano, yaro ne mai sauƙin kai da girmama manya,mai zafin nema da dogaro da Kai

Ya kula da zainab sosai,sai dai itama shekaru sun ja har goma Allah bai ba suhaihuwa ba

Hakan ya sa ya auri matarsa ta biyu wato Atika,itama kamar Zainab babu wani batun haihuwa,hakan ya sa ya haƙura ya cigaba da kula da matansa

Duk da rikici da Atika ta so tayarwa bayan auren nasu sam bata samu fuska a wajen Yusuf ba, saboda mutum ne shi mai zafi,kuma baya taɓa ɗaukar raini 

Cikin hukuncin Allah lokaci ɗaya Zainab ta fara laulayi,sai ga ciki, Yusuf ya yi farin ciki irin wanda bai taɓa yi ba,hakan ya sa ya ƙara ba wa Zainab wata kulawa ta musamman 

Gashi kuma a lokacin harkokin kasuwanci suka buɗe masa sosai,kamar wanda ake jiran ɓullar ciki a jikin Zainab,haka ya yi ta kashe kuɗi wajen siyan kayan jarirai da sauran abubuwan buƙata kamar ba nemansu yake yi ba

Hakan ya sake rura wutar rikici a cikin gidan,sai dai kuma shi Yusuf tsayayye ne,ba ya ɗaukar raini sam, dalilin haka Atika ta saurara 

Bayan Allah ya sauki Zainab lafiya ta samu ƴa mace,ya je garinsu ya ɗauko mahaifiyarsa da ƙannensa,har da bazawara da auren ya mutu,wato Sa'adatu 

Ƙaton gida ya gina, don lokacin daidai gwargwado akwai wadata sosai,kowa ya yi masa nashi ɓangaren,har jaririya wadda ta ci sunan mahaifiyar Zainab wato FATIMA ake kiranta da SHAHEEDA sai da aka yi mata nata sashen 

A lokacin ƙannensa maza, Rufa'i, Habib da Aliyu kowa ya yi aure ya ajiye iyali,shi Aliyu ma bai juma da yin nashi auren ba

Zuwan innayyo, mahaifiyar Yusuf gidan ya sake tayar da sabon rikici,ba takaicin sunan da aka sakawa jikar tata ta wajen babban ɗanta,ba sunanta bane,don haka ta shiga tsakanin matan Yusuf don ta gwara kansu 

Sai dai ba ta samu damar hakan daga wajen Zainab ba,hakan ya sa ta koma suka haɗe da Atika, wadda ta fuskanci bayan kishin da take yi da Zainab har da hassada 

Cikin lokaci kaɗan arziƙi ya sake nunka na baya,an yi auren Salma autar innayyo,ta auri wani abokin Yusuf, itama Sa'adatu ta koma ɗakinta,inda Yusuf ya zama gatanta ya ba ta jari mai tsoka ya ba wa mijinta,a lokacin Shaheeda tana da shekaru biyu da haihuwa 

A lokacin ne Yusuf ya sake samun faraga ya buɗe kamfanoni har uku a kusan lokaci ɗaya, wadanda shahararsu a ɗan ƙaramin lokaci ya bayar da mamaki,hakan ya sa ya ƙara faɗaɗa kasuwancin sa,har ƙasashen waje yana fita don Kasuwancinsa

A lokacin ne ya ƙara auren matarshi ta uku, Ruƙayya,an yi tashin hankali sosai,don Ruƙayya ƙanwar ƙawar Sa'adatu ce,asalima ita ta haɗa auren,kuma kai tsaye innayyo ta goyi bayan hakan,a dalilin wannan auren har saki ɗaya sai da aka yi wa Atika, saboda kalamai na rashin ɗa'a da ta rinƙa jifan innayyo da su,ya taka mata birki ta ƙi ta ji 

Ita dai Zainab ta zama ƴar kallo,bata tankawa,ko wani abu aka yi mata wanda ya dame ta tana zuwa ta samu yayarta Saude ta bata ta shawara,ita kuma ta kan ba ta haƙuri ta bata shawara

A haka aka yi auren,tun sanda aka yi auren Ruƙayya ta so zuwa da fitina,sai dai laulayin da ya riske su kusan lokaci guda ne ya sa kowacce ta kama kanta 

Kusan lokaci ɗaya suka haihu da Atika,ita Atika ta haifi namiji,ita kuma Ruƙayya ta haifi mace

Hakan ya saka Atika alfahari ganin ita ce ta haifi ɗa na namiji,duk da farin cikin haihuwar da Ruƙayya ta yi amma tana jin zafin wannan fifikon,amma sai ta saka a ranta ai yanzu aka fara

Ranar suna namijin aka saka masa Safwan,macen kuma aka saka mata sunan Ummeey,wato Zainab 

Hakan ya sake tayar da bala'i na gaske,don Atika ta ce babu wata kishiya da ta isa ta haifa mata ya,har a saka sunanta,itama innayyo sai zuga ta take yi, saboda ta ga rashin dacewar saka sunanta

Wannan issue akan yarinyar nan har yaji sai da Ruƙayya ta yi ta bar yarinyar a gidan ta tafi gidansu,amma Alhaji Yusuf ya ɗauki yarinyar ya danƙawa Zainab,ya ce ita kuma kar ta dawo,babu inda zai je

Ko da ta dawo sai ta zo tare da yan'uwanta,babu kalar rashin mutunci da cin mutunci da ba su yiwa Zainab ba,amma bata ko kula su ba,sai dai ta ba su jaririyar 

Hakan ya sa Ruƙayya ta haƙura,aka cigaba da kiran ƴarinyar da Iman 

Wata sabuwa!duk da haihuwar da matan suka yi a kusan lokaci ɗaya hakan bai saka ya iya haɗa soyayyar Shaheeda da ta kowanne yaro ba,hakan ya tayar da rikici, musamman ma da matan gidan suka ƙara hayayyafa,amma ita Ummeey ko ɓatan wata bata sake yi ba tun bayan haihuwar Shaheeda 

Hakan yana damunta,amma ta miƙa lamarinta ga Allah,ta rungumi ƴarta tilo ta cigaba da kulawa da ita

Shaheeda tana da shekaru bakwai yaya Saude, wadda ake kira da Hajiya Saudat a yanzu ta koma Egypt da zama, saboda wani ɗan ƙanin mijinta da ta riƙe, ya yi mata komai,ya mayar da ita uwa, kasancewar ya rasa iyayensa tun yana ƙarami 

Ba su cika gaisawa ba sosai, saboda a can baya babu waya sosai,sai dai bayan wasu shekaru masu yawa sun dawo, inda suka samu mummunan labarin abin da ya faru da Shaheeda, yanzu haka ma ba'a san inda take ba,yaya Saude ta yi kuka sosai,ta ci burin ina ma ana dawo da hannun agogo baya?da ta dawo da baya ta dawo a ƙasar don ta ɗauki Shaheeda, wadda har zuwa yanzu kukan da ta fita tana yi ya kasa barin tunanin mahaifiyarta 

To daga lokacin da Hajiya Saudat ta sake komawa Egypt bata sake waiwayar Nigeria ba sai yanzu, wannan kenan




✨💫


A daidai katafaren gidan da Alhaji Abubakar, ɗan rikon Hajiya Saudat ya gina mata Hajiya Zainab ta yi parking, ba tare da ta iya jiran mai gadi ya buɗe gate ba,ta ƙwanƙwasa ƙofa,yana buɗewa bata tsaya amsa gaisuwarshi ba ta wuce cikin gidan 

A ƙaton luxury parlourn ta iske dattijuwar tana shan kayan marmarin da mai aikinta ta yi mata blending,tana shiga bata yi wata-wata ba ta faɗa jikinta ta fashe da kuka

Ɗan murmushi Hajiya Saudat ta yi,ta ɗago ta tana faɗin "za ki ƙarasa jikin tsufa autar Hajiya,zauna mu yi magana, wannan kukan ba shi da amfani,ya kamata ki san zuwa yanzu kin girmi kukan banza Zainab"





#Nusy_bee