NADAMAR DA NA YI

Nadama page 6

by @mrsomar

  NADAMAR DA NA YI🙆🏼

             

               

     

Fatima Isa

       

Edit......2026

Love story 2015🥰

  

         PAGE 6

Zuciyarshi ke mashi wani irin kuna kamar wuta, da za'a fasata da tabbas sai anyi mamaki.

A hankali ya ɗago jajayen idanunshi da suka koma kamar gauta, ya sauke su kan fuskar Fatima da take zaune a inda su Dad suka barta itama hawaye ne kawai ke kwaranya akan fuskarta.

A hankali Faruok ya taso daga inda yake zaune ya koma daidai inda Fatima take zaune yasa hannunshi a cikin nata ya haɗe waje ɗaya.

   Ta dawo kamar hoto ta ɗago kai ta kalleshi cikin sanyin murya ya fara bata baki.

“Haba! mace ɗaya tamkar a cikin dubu tauraruwar matan fulanin Yola.

Sudai fulanin ansansu da kunya kawaici da kauda ido ga duk wani abinda zaisa mutane suyi fushi dasu, kafin ma azo ga iyaye.

Haba! Fatima ina hankalinki da tunaninki yake? please don't forget that you're a real Fulani.”

Muryar shi ne tayi sanyi ita ko tunda yake magana idanuwanta na kallon ƙasa suna aikin zubar da hawaye.

Hannunsa yakai  daidai fuskarta hawayenta na sauka akan tafin hannunshi.

Ya ce

“Fatima yanzu bakisan wannan hawayen da kike fitawa a idanunki ba, jinsa nake kamar ana watsa min tafasashe ruwan zafi  a cikin zuciyata.

Wallahi Fatima duk wani motsi naki yana tafiya ne da bugun zuciyata, ke ce gatana please ki amincewa buƙatata da kuma umarnin iyayenmu.

Fatima ado Lara ko a wadinta danyobe amin do hani bo? No!! Fatima ya kamata ki duba wannan Lamar..”

Maganarshi ta tsaya ne dan ganin ta ɗago jajayen idanunta ta sauke su kan nashi .

Lips ɗinta ne ta cije masu kama da tana shafa masu pink din jan baki, ta girgiza kai ta zare hannunta dake cikin nashi sannan ta fara magana cikin fushi.

"Ya Faruok har kana da bakin magana kace wai na yiwa iyayenmu adalci.

Su adalci sukayi min da har suke shirin rabani da rayuwata. 

Anyone who tries to separate me from musaddiq, I will never forgive them, no matter who they are. That's my promise. Sai naga inda k'arfina ya kare.

Yaya Faruok tun lokacin daka faɗawa iyayenmu kana sona na ɗauki kin duniya na ɗaura maka, ada ina maka wata irin girmamawa ina tunanin duk abinda kake min kana min ne kawai dan ka ɗaukan tamkar kanwarka wadda kuke ciki ɗaya."

Ta yi shiru tana mai sakin murmushi takaici. ya yi ƙarfin halin cewa.

"Fatima ina sonki, ki ɗauke ni kamar yanda kika ɗauke ni a baya, ki dinga min kallon kima da mutumci."

Kai ta girgiza mashi tana cewa.

"Humm Farouk ai jotta a mara mangu a gite am tunda a yidi a senda am be yide bernde am walla"

Bata karasa ba Faruok cikin zafin rai ya fincikota da ƙarfi ta faɗa jikinshi.

Suna jin saukar lumfashin juna idonshi na kan nata da sauri ta lumshe ido.

“Fatima yanzu ni kike faɗawa baki ganin kimata da mutumci daga nace ina sonki?

Anyway idan har da gaske kike abinda kika fada open ur eyes, ki koma maimaita abinda kikace nayi maki alk'awarin ni nasan abinda zanyi."

Ƙara rumtse idonta ta yi dan ganin kamar yana son haɗa bakinshi da nata.

Murmushi ya yi ya saketa ya ce

"Marar kunyar karya.

Fatima har yanzu ina ganin kunyar fulani a idonki please! Fatima kada ki bari soyayya ta rufe maki ido. Kizo ki yi NADAMA nan gaba."

Saida ta sauke murmushin takaici kafin ta ce.

"NADAMA Yaya Faruok a kan auran Musaddik babu wannan ranar insha Allahu. Auren kane kawai zaisa nayi NADAMA amma banda auran Musaddik ai shi arziki nufin Allah ne."

"Au har yanzu kina nan kan bakanki baki canza ba kenan"

"In canza? Humm Faruok kenan ai bazan taɓa canza hali ba har saika janye maganar aurena a kanka ka barni na aure zaɓin ruhina."

”Fatima kenan ki dai yi tunani.”

Har ya juya zai fita ya dawo ya ce.

"Mi nani Fatima a volla pat ko a yidi.

But I want you to think very well and tell the truth.”

Yana magana yana nuna kanshi da ɗan yatsanshi. Sannan ya juya ya fita da sauri kamar zai tashi sama.

A hankali ta sulale ƙasa tana kuka.

»»»«««°°°°°=°°°°°°»»»»»»««««

Tsohowa ce mai kima nin shekara tamanin da wani abu, zaune take bakin murhu tana ta faman hura wuta, amma wutar sai hayaki take.

Gida ne dai ginin bilo da bilo amma dai babu filista a bango ƙasan gidan shafe yake da saminti, gidan ba wani babba bane ɗaki biyu ne sai wani daga bakin ƙofar shigowa ciki.

Tana cikin fama da wutar ne Musaddik da yaron dake tare dashi suka shigo tana jinsu ta ɗago kai da sauri tana kallonsu.

Daidai inda take Musaddik ya iso yace.

"Maman kakas me kike ta faman dafa mana haka?"

Fuska ta yatsina kafin ta ce

  "Anya Musaddik wannan rayuwar daka ɗaukarwa kanka mai ɓilliwa ce? A ce Kai ba ganni kake ba  baka iya zaman gida kullum yawo.

Anya musaddik ta be viya wodi ko memi hore mada fa.

Wallahi Musaddik a nasta hakkilo mada."

"O0!! Haba mama am jotta wodi ko a lari mi wadata vodai na?

Kinga mama mubar wannan magana ni kam wallahi yunwa nakeji."

"Au inda kaji yawon ba su baka abincin ba?"

Kai Musaddik ya girgiza sannan yasa hannu ya ya mutsa sumar kanshi yace.

"Ni kam am Mama kakas wai meyasa kullum idan zaki bani abinci sai kin min gori?"

"Saboda Musaddik yanzu baka da zuciyar nema tunda ka samu matsalar ido ka taro ka lalace nace maka ko ƙofar gida ka fara wata sana'ar amma ka kiya kullum sai faɗa min kake kuɗi sun kusan zuwa amma har yanzu banga alama ba."

Bakin ƙofar ɗakin Mama kaka ya zauna kafin ya fara magana cikin sanyin murya.

"Mama kaka ki ƙwantar da hankalinki in shaa Allahu komi yazo ƙarshe sanin kanki ne nafi kowa son na zama wani abu."

Baki Mama kaka ta taɓe kafin tace.

"Allah dai ya shiryeka."

Bai ƙara ce mata kalla ba, wayanshi yayi ƙara ya ɗaukota daga aljihu ko ba'a faɗa mashi ba yasan mai kiranshi.

Cikin isa ya ɗaga ya kanga a kunne sautin kukanta ya dake kunnansa da sauri ya dan janye wayar daga jikin kunnen nashi saida ya yatsina fuska kafin ya ce.

“Beb How fer?”

Kuka ta sake mashi tana mai ƙara dafe wayar dakyau ta sauke ajiyar zuciya ta ce.

"Musaddik maganar aurena da Ya Faruok tana shirin tabbata domin kuwa Dad yau ɗin nan ya nuna min iv ɗin aurenmu nan da sati mai zuw.."

"What? No!! Hubby ina karya ne wallahi, taya Dad ke shirin mana haka wai Fatima ban dace dake bane? Na tabbata dani mai lafiya ne ina gani kuma ina da tarin dukiya, tabbas Dad zai baki ni. Amma babu komi akwai lokaci har yanzu."

Ɗan shiru sukayi na wani lokaci shi kam babu abinda yake saurara sai sautin kukanta.

A hankali ta ce.

"Please Musaddik, listen to my heart. Wallahi, whenever I close my eyes, nakan ga fuskarka, sonka ya riga ya shiga cikin jikina banda burin da nake fata irin naga na aureka ."

A hankali Musaddik ya sauke ajiyar zuciya dan jin kalaman Fatima masu shiga zuciya.

Sai da ya rufe idonshi ya buɗesu a hankali ya kuma sauke wata ajiyar zuciyan kafin ya ce saboda ya tabbata Mama kaka zataji abinda yake cewa.

“OK Hubby please stop crying yanzu ina cikin mutane later zan kiraki musan abinyi..”

“Wallahi Musaddik kaji tsoron Allah.

Anya musaddiq a mari hakkilo bo? Wodi ko a taski kanjum wadi avi mo ado nder himbe ko?”

Tana fara magana Musaddik yayi saurin katsi wayar saboda ya tabbata Mama kaka zata iya faɗin duk abinda ya fito daga bakinta.

Haka Mama kaka ta ci gaba faɗanta har ta gaji Musaddik bai taka mata ba daga karshe ya laluba wayarshi har ya samu sa'ar kunna waƙa haka ya dinga bin wakar tamkar shi yayita.

  °°°°°°•••••••••••••°°°°°°°°°°°°

      OFFICE

Zaune yake a office ɗinshi mai ɗauke da sanyin AC kota ina.

Idanunshi a rufe suke yayinda kujerar da yake zaune a kai take juyawa.

Knocking ɗin da a ka yi ne ya sashi saurin buɗe manyan idonshi masu kama da madara. A hankali ya furta

“Yes come in”

Yanda ya yi maganar tamkar baya so yi yasa mai buga ƙofar turo ƙofar ya shigo.

Matashin saurayi ne ya shigo wanda bazai wuce sa'ansa ba fari marar jiki ga hanci babu laifi yana da kyau shima kayan jikinsa kaƙin soja ne da su ka yi masa gwanin ƙyau a hankali ya iso gaban Faruok yaja kujera ya zauna suna fuskantar juna Faruok ya yatsina fuska ya ce.

"Sai yanzu kaga damar zuwa?"

"Am sorry Col. Wallahi kasan garin nan yanda yake da cinkoso."

Wata irin harara Faruok ya yi mashi da sauri ya kauda kai, murmushi Faruok ya yi kafin ya ce.

"Major Bilal kenan kai dai kullum cikin uziri kake baka taɓa barin a kamaka da laifi. Anyway dama i just call u ne kawai dan muyi wata mahimmiyar magana u know bani da wani aboki sama dakai Bilal ina cikin damuwa."

A hankali Faruok ya tsaida kujerar da yake kanta yana fuskantar. Major Bilal sai da suka yi shiru na wasu yan mintina kafin Bilal ya ce

“Friend, what's the matter? Please tell me maybe idan wanda zamu iya warwarewa ne a nan musan abinyi tun kafin ya yi nisa.”

Saida Col Faruok ya girgiza kai ya cije lips ɗinshi na ƙasa ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce.

"Bilal, my problem is always about just one girl, kullum matsalata a kanta ne. Inama zata fahimci abinda ke zuciyata Bilal har yanzu Fatima taki amincewa da ni na rasa ina zansa kaina wallahi zuciyata na dab da bugawa."

Zama Major Bilal ya gyara kafin ya kama hannun Col Faruok ya ce.

“Abokina duk wannan matsalar mai sauki ce, me zai hana ka cire Fatima a zuciyarka ka barta ta auri wanda take so.”

“Bilal bazan iya ba a kullum idan nayi tunanin haka to wallahi Allah a ranar bazan samu damar yin barci ba. Bilal dole naso Fatima domin irin tarin alherin da iyayenta suka yi min i trust my heart wata rana Fatima zata so ni."

“Are u sure?”

“Am very sure”

Ajiyar zuciya Bilal ya sake sannan ya ce.

“Humm Col kenan har yanzu baka san meye so ba shi so wani abune dayake shiga zuciya a lokaci ɗaya fitar dashi kuwa zayi wahalar gaske shawara ɗaya da zan baka kabar yarinya ta aure wanda take so dan samin kwanciyar hankalinku baki day..”

“No!! Bilal bazan iya ba wallahi koda ban aure Fatima ba bazan taɓa barinta ta aure wannan ɗan iskan yaron ba."

"Why?"

“Au tambayata kake saboda me Anya Bilal kana so na?”

Murmushin takaici Major Bilal ya yi ya ce

"A kullum Col kana bani mamaki sanin kanka ne bani da wani masoyi sama da kai ko kana so na zama butulu ne mai manta alheri?"

Tsoki Faruok yaja ya ɗan lumshe ido ya buɗe a hankali haɗi da cewa:

  "Au kai baka so ka zama butulu amma ni kake so na zama ko ka manta wannan auran nawa da Fatima shine kadai abinda zanyi na sakawa wannan bayin Allah?"

Shiru Major Bilal yayi yana tunanin magana abokinshi kafin ya murmusa ya ce.

"Na yarda da maganarka Col problem ɗin shine kada ayi auran nan daga baya ayi dana sani."

"Insha Allahu baza ayi ba.

For a moment, ta fara wulakanci, but I decided to be patient. Na danne zuciyata har ta amince dani.”

"Alright Allah ya tabbatar mana da alheri."

"Amin."

Haka suka dinga fira suna jan junansu da wasa har Faruok ya fara mantawa da abinda ke damunshi..

  3days a go

Ana yinta fa...

Muje zuwa