Nadama page 7
by @mrsomar
NADAMAR DA NA YI🙆🏼
Fatima Isa
Edit....2026
Love story 2015🥰
Free book
PAGE 7
******
Yau saura kwana hudu bikin Col Faruok Ahmed Lamido da Fatima Bashir Lamido duk wani abu da ake na wajan ɓangaren ango da Amarya Dad ya gama komi hatta kayan lefe ya tura kuɗi Dubai aka haɗa komi hatta kayan ɗaki. Yayinda cikin manya-manyan gidajenshi yaba Faruok ƙyautar ɗaya duk da Faruok mahaifinshi ya bar mashi tarin dukiya amma baya komi da ita sai juya mai da Dad yasa anayi.
Gidan da Dad ya bashi a mafias quarter's gidan ya haɗu iya haɗuwa dan unguwar sai wane da wane.
Dad duk wani abu da zai yi dan ya shawo kan Fatima ya yi amma abin ya ci tura dan har ƙyautar sabuwar mota ya bata ƙirar Range Rover da ƙyautar kuɗi kimanin Naira million 5 duk dan tayi hidimar daya kamata.
Hmm amma abin haushin Fatima bata canza ra'ayi ba.
Rabon da Faruok yasa Fatima a idonshi tun ranar data suma wani irin wasan 'yar ɓuwa suke dashi bataso ta ganshi shi kuma yau ya yi alkawarin sai ya sakata a ido.
Misalin 5:pm na yamma ya shigo gidan babu inda ya nufa direct sai ɗakin Fatima knocking ya yi amma bata amsa ba ya tabbatar da tana cikin ɗakin a hankali ya murɗa ƙofar ɗakin ta buɗe zaune take a bakin gado tana wasa da wayarta,
Tana ɗaga kai sukayi ido biyu dashi ta kuma sauya fuska.
Why? why? why? I hate this guy in my life. I hate seeing him anywhere around me. I feel like killing myself because of him. Maye kawai”
Duk a tunanin ta a cikin zuciyarta ta yi maganar sai da taga yana murmushi yana faɗin.
"Why, fatima? I just love you. Why are you thinking of killing yourself because of me? Why? just because I said I love you? so ni maye ne, thank God ni mayenki ne kuma duk sonki ne ya jamin. Zaki iya kirana da duk sunan da kike so wannan ba damuwata ba ne.
But don't forget mun kusan zama inuwa ɗay.."
Da sauri tun kafin ya ida magana ta ce.
"Never"
"Why"
Wata irin harara Fatima ta watsa mashi mai firgitarwa da manyan idanunta, a hankali Faruok ya lumshe ido ya sauke ajiyar zuciya ya dafe hannunshi ɗaya a zuciyarshi ya ce.
“Oh my God sweetheart a kullum idan kina min irin wannan kallon na kanji ban san duniyar da nake ba. Please, dear, look at me again. I like the way you look at me.”
Murmushi takaici Fatima tayi take idonunta suka chanja colour zuwa red ta fara magana cikin gadara.
"Love, love! Every day you just talk about loving me. You don't even know anything about love.
Ya Faruok, shi so halinta ne dashi ke haihuwar mutum. Shi yasa aka halarci zuciya domin isar da sako. idan da zuciya kitse ce, ba jini bace tabbas da zata narke ba zata rike sirrin da ke cikinta ba, zuciya wata makulin sirri ce akan aika mata da sakon so ta amsa ta adana shi ba tare da barin kowa ya gani ba, wannan zuciyar tawa babu komi a cikinta sai son Musaddik.
Ya Faruok ya kake so ka zama mai son kai. Ko kana so ka raba soyayyar da aka share lokaci ana ginata ta hanya mai ƙyau.
To wallahi Ya Faruok koda ban aure Musaddik ba.
Kuma maza duniya sun kare, ace kai kaɗai ka yi saura bazan taɓa maka kallon mijina ba."
Wani abu Faruok yaji ya sokai a zuciya mai kama da kibiya.
Da sauri ya dafe zuciyarshi ya ce.
"Fatima kina tunanin har zan iya hakura da sonki?"
Baki ta taɓe ta ce
”That's your problem, it's not mine.“
“Alright na fahimce ki Fatima no problem duk ki yi abinda ki ka ga dama one day zan rama.”
Tsoki Fatima taja kamar zata cire halshenta ta wurga mashi pillown kusa da ita tayi hanyar waje da sauri.
A hankali Faruok ya lumshe ido ya ce.
“Oh ya Rabbi”
A parlour ya sameta zaune ta ɗan tada kai da hannun kujera ta takure babu kowa a parlour sai sautin ƙarar TV. Murmushi ya yi ya wuce ta dan yasan idan ya tsaya zata koma faɗa mashi duk wata magana data fito bakinta..
★★★★★★★
Ƙwance take kan gadon da yake ɗauke da lafiyayar shinfiɗa mai ƙyaun gaske daga ita sai wasu matsatson kaya da duk wani surar jikinta kana kallonta a waje sai juyi take a kai a hankali ya turo ƙofa sanye yake da jallabiya daka ganshi kasan daga masallaci ya fito.
Cak ya tsaya dan ganin Hafsat ƙwance a kan gadonshi.
Ga shigar da take jikinta take yaji wani sabon lamarin abu ya shiga zuciyarshi...
Da sauri Col Faruok ya rufe idanunshi babu abinda yake firtawa a bakin shi sai.
“Innalillahi wa'inna illaihi raji un lailaha illa anta subahanaka inni kuntu minaz zalimin.”
Abinda kawai bakinshi ke nanatawa kenan cikin karairaya Hafsat ta iso gaban Faruok tana wata rangwaɗa kamar zata karye.
Shi dai Farouk idanunshi a rufe suke ya kasa buɗesu.
A hankali tasa bakinta ta hura mashi iskan bakinta, take ya karajin jikinsa ya mutu, ya fara nai man rasa natsuwarsa.
Bakinta takai daidai kunnanshi ta ce.
"Please Ya Faruok help me. I can't control my emotions because I love you so much,l. Ya Faruok ya kamata ka gane ni ce mai sonka please, wallahi komi kake so yau a shirye nake zan bak.."
Hannunta ta kai daidai sumarshi cikin wani irin salo mai wuyar fasarawa da sauri Faruok cikin fushi ya fincikota ya haɗata da bango ya maida hannunta baya ya murɗe yana magana tamkar baya cikin hayyacinsa.
"Wa'iyazu billahi Hafsat tur da halinki lamarinki har yakai haka kina shirin bada kanki ga namijiin daba muharraminki ba? Tur!! Hafsat tur da halinki a haka har kike tunanin ni Faruok zan aureki bayan bansan yawan mazan da kika bawa kanki ba.
Lallai Hafsat a hilni am de har a numata mi wawai mi mbangu ma ɓawo a andi Nana a debbo mɓangugo am ba. Wallahi kinyi asara."
Da ƙarfi Col Faruok cikin ɓacin rai ya yi wulli da ita saman katifa.
Sai mai da lumfashi yake da sauri da sauri zuciyar yan maza ta ɓace dama Faruok tun yana yaro bai iya fushi ba.
Abinka da marar kunya irin Hafsat ta ƙara nufar Faruok yayinda idanunta suka canja launi.
"Ya farouk yide ma on wati mi wawai mi hokkuma ko dumejun on gam mi heɓa a mɓanga am.
Haba Ya Faruok ya kake so nayi da rayuwata wallahi tunda na tashi a gidan nan nake saka idona nake burin kazama mallakina please Ya Faruok listen to me.."
Hannu ta kuma kaiwa daidai bakinshi kafin ta rufe baki Faruok ya kai mata wani wawan mari cikin fushi.
"Never!! Hafsat, I will never listen to these stupid ideas of yours.
Hafsat dole naso Fatima saboda ita mai tarbiyya ce halinku ya bambanta duk namijin kirki yana so ya zaɓawa Ya'yanshi uwa ta gari, Hafsat wallahi ke ce kika dace da Musaddik ba Fatimata ba."
Magana Faruok ya ke kamar zai ɗaura hannun saman kai ya fasa ihu.
Wata irin tsawa ya daka mata ya ce.
”Get out of my room before I make your life miserable, Stupid girl, fool kawai!”
Shiru tayi tana kallonshi Faruok cikin zafin zuciya ya fincikota ya yi waje da ita da ƙarfi ya wulli da ita ya maida ƙofar ya rufe.
A hankali ya dawo bakin gado ya zauna yayin da ya lumshe idonsa yana faɗin.
"Why? Hafsat why? did u do this to me. Kinsan irin wahalar da nake idan naga tsirancin mace? Wayyo Allah Hafsat kin cuce ni.”
Da sauri ya rike cikin shi yana mirgina kan gado juyi kawai yake ya rasa inda zai saka kanshi.
*****
Yana tura Hafsat waje Aunty Zee ta fincikota suka nufa ɗakin Mom ɗinsu.
Suna shiga cikin fushi Aunty Zee tayi jifa da Hafsat kan kujerun parlour ɗakin zaka ɗauka Aunty Zee zatayiwa Hafsat hukunci ne akan abinda ta yi amma abin mamaki daga ita har uwar magana daban suke, cikin zafin rai Aunty Zee ta fara magana kamar zata kaiwa Hafsat duka.
"Hafsat u a very stupid girl, duk abinda muka faɗa maki yanzu ya tashi a banza kin kasa shawo kan Faruok kinsan ko idan kika bari Faruok ya aure Fatima munyi babbar asara? See u kamar zakiyi wayau amma a banza baki dashi, ni wallahi dan Faruok ba sa'an aure na bane amma wallahi da sai na baki mamaki."
Mom ɗinsu ce ta taɓe baki ta ce.
"Humm ai wallahi Hafsat lamarinki akwai gyara, me Fatima zata nuna maki da har kika kasa shawo kan Faruok duk abinda muka faɗa maki a banza.
Bamu ce maki ki bashi kanki ba.
Amma mun ce ki yi duk abinda zaki yi dan shawo kansa kin san ko irin dukiyar da Faruok ya mallaka yanzu? Kai! Wallahi Hafsat kada ki yarda Faruok ya auri Fatima."
Cikin muryar kuka Hafsat ta fara magana.
“Mom Aunty Zee u know Ya Faruok Duk abinda muke yana sane damu, wallahi na yi duk abinda zanyi dan ya amince dani amma abin haushi har da faɗi yake wai ni ba matar auransa ba ce saboda banda tarbiya."
“OK haka ya ce alright to idan yasan wata baisan wata ba.”
Cewar Aunty Zee kenan. Sun daɗe suna tattaunawa kafin daga baya dukansu ko wace ta kama gabanta.
★★
Kafin a ce maka me Faruok zafin zazzaɓi ya rufe shi sai juye yake.
Babu abinda yake bayana faɗi sai sunan Allah a bakinshi hannuwansa duka biyu na kan mararsa.
A hankali aka turo ƙofa. Idanunsa a rufe suke shiyasa bai shaida wanda ya turo ƙofar ba....
#Love
#yaudara
#Cin amana
#Kiyayya
#Fatima
#Farouq
#Musadiq
#Hafsat
#bilal
#Aunty zee