Chapter 26
Firdausi ta fito daga gida ko kallon gabanta bata yi
Tun daga lokacin da Zahra ta katse wayar, zuciyarta ta kasa samun nutsuwa
A bakin titi ta tsaya tana jiran abin hawa.
Motoci na wucewa, napep na wucewa, amma ko ɗaya yaki tsayawa
Lokaci zuwa lokaci tana sake danna number Zahra.
Wayar tana ringing, amma ba a ɗagawa
Hakan ya ƙara dagula mata lissafi.
"Ya Allah ka sa lafiya..." Ta faɗa a hankali
Da ƙyar dai wani napep ya tsaya, wata tsohuwa ce kawai a ciki, ta shiga haɗi da faɗa masa inda zai kaita
Tun daga nan ma wayar Zahra take ta kira, yana shiga amma kuma bata dauka
Firdausi ta rasa irin tunanin da zata yi.
A rayuwarta bata taɓa jin muryar Zahra kamar yadda ta ji ta yau ba.
A ɓangaren Zahra kuwa...
Bayan ta kashe wayar, ta zauna bakin gado tana kuka.
Kukan da ta yi har ta gaji, har hawayen ma kamar sun fara ƙafewa
Wayarta na gefe, amma bata da ƙarfin sake ɗaukarta
Hotunan da ta gani ne kawai ke yawo a fuskanta
Saudat... Kawarta Saudat... da Khalil.
Tana rintse idanunta sai ta kalli hotunan, sai ta bude su da sauri, ta dafe kanta
Wani irin ciwon maran kuma yana karuwa mata, a haka ta jingina da bango tana kuka a hankali, ko da wasa bata taɓa ɗauka akwai ranan da zata shiga kunci ko tayi kuka a rayuwarta ba
Farida ta fito daga ɗakinta tana tunanin aikin da aka saka ta anya zata iya?
Ta fara aikace-aikacenta kamar yadda ta saba, ta share parlorn, ta gyara dining, daga nan ta nufi kitchen.
Can aka fara bugun gate din gidan, da farko bugun a hankali ake yi, sai kuma aka fara da karfi
Farida ta ɗago kai
"Wayyo wa ya zo haka da sassafe?"
Ta faɗa tana cire apron ɗinta.
Ta fita da niyyar zuwa buɗewa, sai dai kafin ta isa, mai gadi ya fito da sauri daga toilet ya buɗe gate ɗin
Firdausi ce ta shigo da saurin ta
Kamar ma zata faɗi saboda hanzari
Farida ta ƙarasa gareta
"Ina kwana Anty Firdausi."
"Lafiya lau."
Ta amsa ba tare data tsaya ba, kuma ta ce
"Ina Anty Zahra?"
Farida ta ɗan yi mamaki.
"Tana ciki mana."
"Ta sauko?" Firdausi ta Kara tambaya
"A'a" Farida ta amsa
"Tun da safe bata sauko ba."
Firdausi ta ji gabanta ya sake faɗuwa.
"Okay." Kawai ta iya faɗa.
Daga nan ta kara sauri
Kai tsaye ta nufi sama, ko knocking bata yi ba, ta tura ƙofar ɗakin ta tsaya kallonta
Zahra na zaune kan gado.
Idanunta sun kumbura sosai, fuskarta tayi jaa
Da alama ma tun daga lokacin da suka yi waya bata daina kuka ba.
Zahra na ganin Firdausi... sai ta miƙe da sauri, ta ƙarasa gareta, ta rungume ta gam.
Nan take kuma ta sake fashewa da wani kukan. Kuka mai taba zuciya
Firdausi ta ruɗe
"Zahra!"
Ta riƙe ta
"Me ya faru?"
Zahra ta kasa cewa komai sai kukan da take yi ta cigaba
"Wallahi kina bani tsoro, gaba na sai faduwa yake" Firdausi ta ƙara faɗa
"Talk to me mana. Me ya faru?"
Da ƙyar ta samu ta zaunar da ita bakin gado. Ita ma ta zauna kusa da ita
Har yanzu Zahra kuka kawai take yi. Firdausi ta kamo hannunta.
"Zahra, ki kalle ni."
A hankali Zahra ta ɗago.
"Menene?"
Sai Zahra ta miƙa hannu, ta ɗauki wayarta, Gallery ta shiga, ba tare da ta ce komai ba ta miƙa mata wayar
Firdausi ta karɓa cikin rashin fahimta. Ta fara kallon hoton farko
A take ta zaro idanuntan kamar zasu fito fili
"Wai me...? Me nake gan..?"
Tayi sliding wani, nan take ta miƙe tsaye
Wayar ma kusan faɗuwa tayi daga hannunta
"What?!!!!" Ta faɗa da ƙarfi
Sai ta sake kallon hoton, sannan a jefar da wayar kan gadon saboda tsananin mamaki
"Saudat?!" Ta faɗa
"Saudat?!"
Zahra ta rufe fuskarta da tafin hannunta, sabon kuka ya sake ƙwace mata
Firdausi ta dafe kanta.
"Wannan yarinyar mahaukaciya ce wallahi." Ta faɗa cikin fushi.
"Saudat kuma?" Ta sake ɗaukar wayar
Ta sake kallon hotunan. Kowanne ya fi ɗan'uwansa ɗaga hankali.
"Wallahi sai tayi nadamar abin da ta aikata, idan har ni kawace ta gari, Duk halarcin da kika mata?"
Ta faɗa a fusace
"Na rantse sai tayi nadama."
Zahra bata ce komai ba.
Kanta kawai ta sunkuyar.
Firdausi ta sauke numfashi, ta zauna kusa da ita, ta janyo ta jikinta.
"Shhh..." Ta fara bubbuga bayanta a hankali
"Karki yi kuka Zahra, nasan abun da ciwo musamman yarda kika yarda da ita, Duk da ba sa'arki bace amma haka ko kyamanta bakya yi kika jawo ta jiki, yanzu please kiyi hakuri ki daina kuka musan abun yi"
Amma Zahra ƙara fashewa da kuka take yi, Firdausi ta lumshe idanunta
Ita kanta ta ji zafin abin, domin ba wata ba ce, ba yarinya daga waje ba ce balle ace bata san zahra ba, ace kawar Zahra.
Kawarta? Wacca tasan sirrinta
Wacce suke hira tare. Wacce Zahra ta amince da ita.
Ta ƙara rungume Zahra.
"Ki yi haƙuri." Ta faɗa a hankali.
"Wallahi komai zai wuce."
"Ki kwantar da hankalinki saboda cikin da ke jikinki Zahra"
"Ki bar ni da Saudat." Ta ƙara faɗa cikin fushi.
"Sai ta gane kuskuren da tayi."
A haka ta ci gaba da lallashin Zahra.
Tana bubbuga bayanta.
Firdausi ta daɗe tana lallashin Zahra kafin kukan nata ya ɗan lafa
Sai dai ko bayan ta yi shiru, idanunta basu daina zubar da hawaye lokaci zuwa lokaci ba
Firdausi na kallonta kawai tana jin tausayinta.
A hankali ta miƙe tsaye
"Ina zuwa" Ta faɗa
Zahra bata ce komai ba, kawai ta zauna a bakin gado tana kallon wani waje
Firdausi ta sauko ƙasa, ai tsaye kitchen ta nufa.
Farida ta samu tana gyara wajen breakfast, da alama ta gama komai
Tana ganin Firdausi ta yi murmushi
"Kin ga Anty Zahra?"
Kai Firdausi ta gyada.
"Na ganta."
Farida ta lura da yanayin fuskarta
"Lafiya dai?"
Firdausi ta yi murmushin dole
"Eh lafiya."
Sai ta kalli abincin da aka shirya
"Ta karya ne?"
Farida ta girgiza kai
"A'a, Kuma wallahi rabonta da cin shekaran tun jiya."
Firdausi ta sauke ajiyar zuciya, ta san halin Zahra Idan damuwa ta yi yawa, bata ma tuna da abinci
"Toh" Kawai ta faɗa.
Daga nan ta juya ta sake komawa sama.
Tana shiga ɗakin ta tarar da Zahra a yadda ta barta.
Har yanzu tana zaune, kai a sunkuye
Firdausi ta ƙarasa kusa da ita.
"Zahra." Ta kira a hankali
Zahra ta ɗaga kai tana kallonta
"Mu je ki karya"
Kai tsaye ta girgiza kai
"Ba na jin yunwa."
Firdausi ta ɗan haɗe gira
"Ba tambayarki ko kina jin yunwa nayi ba, cewa nayi mu je ki karya"
Shiru tayi ba tare data ce komai ba