CHAPTER 28
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️----28
Bai taba tunanin Iman zata Riga sa tashi ba haka ya koma dakin sa wanka yayi ya gabatar da tasa sallah a daki
Karfe goma na safe Abba ya kirasa kamar yadda suka tsara yau ne zasu je gidan Alhaji Ibrahim makama neman auren zeenah
Wanka yayi ya shirya kansa cikin wata sabuwar shadda blue black an masa dinkin captain daya daga cikin hulunan sa ya dauko ya saka ya fita
Iman ce tsaye tana jera breakfast kan dinning room duk da ta makara
Suhail ya fito Karin farko data gansa da kula a kansa kuma tayi Matukar yi masa kyau
Bata kula shi ba illa cigaba da tayi da abinda take
Duk a zaton sa zata mashi tayin breakfast kamar yadda ta Saba Amman da mamakin yaga ma ta cigaba da abinda take
Har ransa Yana damuwa da yadda Iman ta Daina kula dashi kamar da yanzu ko gaishe Bata yi idan magana yayi mata da ga eh sai a'a kawai shine amsar ta
Har yayi niyyar fita ba tare da ya karya ya kasa haka ya dawo kan dinning ya zauna Iman ta koma ciki ta barsa anan
Shi da kansa yayi serving kansa duk da ma abincin ba wani da yawa yaci ba
Key din Motar sa ya dauka ya fita
Abba ne zaune a dakin aunty fauziya Dan sai yau yake fada mata maganar auren Suhail
Damuwa ta bayyana karara a fuskar ta duka yaushe yayi aure har yake kokarin sake wa tausayin Iman kawai take ji Wanda yanzu take Jin tamkar yar data haifa
Kallon Abba tayi cikin yanayin damuwa ta ce"Alhaji kuma ka yarda ka barsa ya kara dauren duka nawa Suhail yake da zai Tara mata har biyu kuma nake ganin ma idan auren zaiyi ai ya bari a kwana biyu,a gani na ko iyayen yarinyar nan duka ji haka kamar ba'a masu adalci ba"
Murmushi Abba yayi ya ce"ai da amincewar ita matarsa ta sane zai Kara, Suhail yayi min biyyaya wajen zabar masa matar da ya aura yanzu ya kawo maganar matar da yake so zai aura babu ta yadda za 'ayi na tauye sa"
Shiru Aunty fauziya kawai tayi Dan ta ma rasa abin fada
Suna zaune Suhail ya shigo ya gaida Aunty fauziya ta amsa Amman gaba daya fuskar ta babu walwala koshi yaga chanji da ba haka ta zaba amsa gaisuwar Saba
Ba Bata lokaci suka kama hanyar gidan Alhaji Ibrahim makama tarba ta musamman yayi masu kamar yadda ya samu labarin zuwan su daga wajen mummy
Abinci na musamman yasa a girka musu duk da ma ba wani ci sukayi ba Bayan sun gama Abba ya fada masa abinda ke tafe dasu
Alhaji Ibrahim ya ce"naji dadin zuwan ka Alhaji kuma ai Suhail ɗa na ne koni mai shige masa gaba ne wajen neman aure sa bare kuma a gidana Dan haka sai a tsaya ranar Biki"
Abba ya ce"nagode sosai da karramawa kuma ai kaine ya kamata ka tsaida ranar Dan idan tamu a shirye muke ko gobe"
Alhaji Ibrahim ya ce"haka ne to a barshi Nan da sati shidda zanyi tafiya idan na dawo sai a fara shirye_shiryen bikin"
Alhaji ya ce"nagode Alhaji Ibrahim Allah ya dawo da kai lafiya"
Har bakin gate ya rako su suka kama hanyar gida
Suhail ya nufi part din Mami tana zaune a falon sama tana waya da likitan ta zama yayi har ta gama ya gaishe ta Mami ta amsa cike da sakin fuskar
"Suhail kun dawo kenan jiya alhaji yake fada min zakuje gidan su yarinyar da zaka aura"
"Eh mun dawo,an saka ranar Biki Nan da sati shidda masu zuwa"
Fara'ar dake kan fuskar ta ta karu "Masha Allah,Allah ya kaimu ai yanzu ne zakayi aure Amman ba gaira ba dalili mahaifinka ya kwakuba mata wata yar malamai Wanda ba abinda suka iya sai mallake mutane banda ma ina tsaye a kanka da da sun jima da raba ni da kai"
Maganganun Mami sun masa zafi a ransa tayi yayi zai fita ba tare da koyi Mata sallama ba har ya kai bakin kofa ta ce"akwai abinci idan zaka ci"
"I'm okay" ya fada yayi fitar sa
Mami ta ce"a banza dai duk fushin da zakayi kaje kayi tayi nidai bazan Daina zagin yar Malamai kuma duk haryar da zanbi Dan na raba ka da ita sai Dani dan Bata dace da kai ba"
Bayan kwana biyu
yau ne Yaya Mubarak ya dawo wani mai adaidaita sahu ya sauke shi a kofar gida malan na raƙo Alhaji Mahmud munnir kofar gida cike da girmamawa Mubarak ya bashi hannu suka gaisa ya shiga ciki ya tarrad da Ammi Bata Nan
Malan ya shigo ya kallesa"Mubarak an iso kenan ya hanya"
"Lafiya qalau malan"
Mubarak ya jima Yana kallon mahaifin nasa ganin kamar Yana cikin damuwa
Daurewa yayi ya ce"Malan lafiya kuwa miya kawo Alhaji munnir da safe Nan haka"
Ajiyar zuciya Malan ya sauke a hankali "mijin Iman zai Kara aure shine yazo ya fadamin "
Yaya Mubarak bai San lokacin daya sauke jakar dake goye a bayan sa ba ya ce"Aure kuma malan Kai kuma mi kace"
"Mubarak mi zance fa nayi masu fatan Alkairi"
Mubarak yayi shiru Yana tunani duk nawa Iman take da har zata iya zama da kishiya ba wani shekaru ne da ita ba kuma ma Iman ba wani fada ne da ita ba Amman Suhail ya bashi mamaki Shi da nake ganin sa mai hankali da tsoron Allah, ashe zai iya jefa Iman cikin irin wannan hali na yi mata kishiya
Malan ya katse masa tunani da cewa Mubarak ina so wannan maganar ta tsaya a tsaninmu bana so Maryama taji
Hankalin ta zai tashi fiye da a lokacin neman auren Iman kuma ita ma nasan bazata fada mata ba Dan har gidan Nan tazo Amman Bata fadi wa kowa ba"
Yaya Mubarak yasan indai Iman ce zatayi fiye haka tana da zurfin ciki fiye da misali
Kai ya jinjina ya ce"in sha Allah Malan ba Wanda zaiji wannan maganar"
"Allah yayi maka albarka,ka shiga ciki ka duba ko zaka samun abinda zakaci Maryama ta shiga makwabta wajen radin sunan"
kayan shi ya dauka zuwa dakin sa Abincin ƙasa ci yayi gaba daya hankalin na kan iman yanaso yaji Murya ta yasan halin take ciki
iman na zaune kan gado zaman ya zame mata al'ada kullum ta gama aikin haka take dawo tayi Zaune ita kadai
karar kiran wayar ya dawo da ita daga dogon tunanin data tafi ganin sunan yaya Mubarak yasa ta daga wayar da sauri "hello yaya Mubarak"
"Iman ya kike"
"Alhamdullilah yaya kwana biyu ya kano"
"na dawo gani a gida ma"
cike da farin ciki ta ce"yaya da gaske amman dai zaka zo yaya nayi kewar ka"
"Zan zo babu abinda ke damunki ko"
a yadda yayi maganar sai da zuciyar ta kare ta tuna lokacin da inda shiga damuwa take fada masa ji tayi kamar ta fashe da kuka ta mishi bayanin halin da take ciki amman ta ƙasa jin tayi shiru Mubarak ya ce"iman kin yi shiru"
murmushi yaƙe tayi ta ce"bakomai yaya yaushe zaka zo"
"zan samu lokacin nazo kafin na koma in sha Allah"
"Allah ya kawo ka lafiya agaida malan da Ammi"
ajiye wayar tayi ta jingina da allon gadon hawaye masu zafi na sauko mata
kuyi manage da wannan nayi busy yau