NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)

CHAPTER 41 ( Then.....)

by @deejasmah

Kamar yanda ya fad'i 4 days tsakani suka baro k'asa mai tsarki zuwa k'asar mu ta gado, wanda ya kama 4 days to sallah. Sab'anin zuwan yamma da suka yi wannan karon tashin asuba suka yi zuwa gida, hakan ya sa su isowa tsakar rana bayan Zuhr. Bayan sun kammala duk wasu shige da fice na checkout suka lallab'o kayansu zuwa waje, a bakin arrivals suka tarda Islaam a tsaye yana jiransu.


Yana ganinsu ya ware hannayenshi yana tararta, tsayawa tayi tana dubanshi da wani irin yanayi. Shi ko matsowa yayi ganin ta ja ta tsaya bai yi wata-wata ba ya rungumeta tsam a jikinshi, shigewa itama tayi ta lafe tana sauraran bugun zuciyarshi sai da ya d'auki lokaci mai tsayi tare da ita kafin ta janye jikinta cikeda kunya.


"Toh rasa kunya....." Sadeeq ya furta cike da tsokana yana mai mamakin halin Islaam, ji yanda ya k'wak'ufe Lele da azumin Allah a tsakiyar mutane kuma ko a jikinshi. Harararshi yayi yana cewa " ai da yake matata na rungume, ba ta wani ba me yasa ba zaka rungume taka ba?".


"Wannan kalmar ta mata dai tana jin jiki a wurinka, matata this matata that...."


"Kan ka kuma ake ji, zaka wuce mu tafi ne ko kuma zaka tsaya ne a wurin?" Ya tambaya yana sake rungume Sairah yayinda hannunshi d'aya rik'e da na Nadeefah kai ka ce za'a k'wace masa ita ne. 


"Dama ai ba mu kazo d'auka ba".


"Wa ya yaudareka dama, me zai sa in zo ɗaukar ku?".

"Mumu kawai".

"Ohon maka, Wife mu je kin ji" ya fad'i yana sakin hannunta ya ja babbar trollyn da ta k'aro, nata da ta tafi da ita ta janyo tana bin shi a baya har zuwa in da yayi parking. Jakar ya saka a booth kana ya bud'e mata baya yana kallon su, Sadeeq ya sanya kayan na su a booth wanda ya cika dam da kaya don ma Allah ya taimaka motar tana da babban booth kun san jeep da cin kaya.


Gaba Sadeeq ya shiga su Suleim da Baraka suka yi joining d'in Lele a baya, sai lokacin suka gaisa yana musu barka da zuwa. Kamar yanda ya kawo su a zuwa yana d'auke da Sairah yanzu ma haka yayi, tana cinyarshi ya sanya musu seat belt idanunshi a kafe kan Lele yana dubanta.

Suna tafe suna tafka tsiya da Sadeeq har yana cewa dama Farhaan ya kira ya zo ya d'auke shi, cewa yayi " yes da ka kira shi ma da ka huta". A haka suka k'arasa zuwa gidan direct k'ofar gidan Sadeeq yayi honk masu gadi suka bud'e gidan da gudu, ya danna hancin motar ciki har k'ofar compound d'in ya k'arasa yayi parking. Kafin ya gama parking ma'aikatan gidan sun lullub'e wurin motar suna musu barka da zuwa, fitowa suka yi har da Lele aka fitar da kayansu a huta gajiya suka musu kana ta koma gaba ya ja motar zuwa na shi gidan.



Honk d'aya yayi aka bud'e gate d'in ganin mai shigowa ya sanyasu washe baki suma suna rufe gidan su ka taho wurin motar, sauke glass ta yi tana amsa barka da dawowan da suke mata da murmushi mai yawa a fuskarta kamar kullum. Kafin ya ja motar suka wuce ciki a garage yayi parking yana duban Hamza da yake rik'e da hannun k'ofar motar, bud'e masa yayi ya fito ita ta bud'e nata ta fito. Hamza ne ya biyo su da kayan yayinda shi ya sanya key ya bud'e k'ofar shiga part d'in shi, a nan parlorn ya ajiye yana mata a huta lafiya. 


Parlorn ta bi da kallo a gyare yake tsaf sai tashin k'amshi mai sanyi yake yi, zama tayi a kan kujera tana mai cewa " ouch, nayi missing gida".


"Ba kiyi missing ɗina ba ko?" Ya tambaya yana dubanta cikeda k'orafi, murmushi tayi tace " faɗi ma ɓata baki ne". 


"Me too, sati ukun nan yacce kika san an jefa ni kurkuku. Na riga na gane ke ce hasken gidana, gidana da rayuwata fanko ne in babu ke welcome home wife".


Idanu tayi rolling tana murmushi mai kyau ta taso zuwa gabanshi tace " my Allah,ba zan kuma nisa da kai ba In shaa Allah Yaa".

"Ni ma ba zan kuma barinki ki yi tafiya ke d'aya ba".


Murmushinta ta fadada tana mai jin duk wani gajiyar da ta d'ebo ya tafi, mik'ewa tayi ya biyota a baya har zuwa d'akinta da tundaga parlor ta tabatar da an gyara shi don rug d'in da ke tsakiyar parlorn a wanke yake tas ga wooden floor d'in yayi smooth babu ko k'asa balle datti sai k'amshin humidifier da turaren wuta yana tashi a hankali. 


Dubanshi tayi tana cewa " wai Yaa, wa ya gyara room d'in nan?".

"Zulfaa ce ta zo da ƴar aikin ta, tare suka yi aikin i think".


"Allah sarki Lovieta, komai yayi kyau Yaa".


"Yes, sosai" ya amsa yana bud'e parlorn nata, shi ma tsaf yake sai kawai ta shige cikin bedroom wanda shigar yayi dai-dai da kiran sallahr asr, shigar mata da kayan yayi ya ajiye Sairah ya na mai shaida mata da ya tafi masallaci.


Wanka ta fara shiga ta yi kana ta yi wa Sairah ta shirya ta tada sallah, sai da ta rama zuhr da ta riske su a hanya kana tayi asr tana lazumi ya shigo d'akin. Zama yayi kan carpet yana mai duban Sairah da ke kwance kan carpet d'in tana cin biscuit d'in da Lelen  ta bata gudun ta yi mata kuka, tana ganinshi ta tashi zaune  tana washe baki tana magana cikin yaren yara sai kiran sunan PaaPaa take yi kamar tana gaya masa tayi missing ɗin shi. Shi ma d'aukarta yayi yana fad'i da baki " i've missed you dukan ku sweetheart" a haka ta idar ta same shi kan carpet d'in.


Duban yanda tayi da idanu yayi ya san shagwab'arta da sakalta cewa zata yi ta gaji, hakan ya sa shi cewa " me zamu yi order na Iftar? Ko fita zamu yi ne?".


"Zan iya fita kuwa Yaa? Lemme call Hajjah ta ba mu abun iftar".

"Kar dai ki wahal da ita, jiya ma gidan Ummu na yi iftar".

"Uhmm, yaushe ta zo?".

"Shekaran jiya, dukansu".

Kafin ta yi magana wayarta da ta riga ta yi roaming tun dawowarsu ta shiga ringing, wurin ta k'asa kusan a tare ita da Sairah don a Saudi haka take mata ana kira zata d'auko da gudu tana cewa PaaPaa. Ta rigata d'aga wayar in da sunan Zulfaa yake yawo kan screen d'in d'agawa tayi tana cewa " mai ciki".

"Fad'a ki k'ara 'yanmata kema ai kin kusa samu in dai shi ne, ya hanya?".


"Alhamdulillah Babe, ya jiki?".

"Mun gode Allah, Yawwa Babe kar kiyi komai da iftar na had'a mana a nan dukanmu da su Suleim".


"Zulfaa issa darling, amma a nan za'a yi ko?".


"Miye kuma nan?".

"I mean, gidana".

"An mayi an gama uwar son jiki, kar ki yarda in ban kawo nan ba".


"Kai Mom Nadeefah...!"

"Na fasa saka sunan ai ma, tun da abun tsiya ne".

"Allah ya baki hak'uri sweetheart, mun gode".


"Kar ma ki goden mana, ina babyta?".

"Gata nan wurin Yaa Islaam".


"Uhmm barin barki tohm see you by magrib".

"Bye" ta furta tana ajiye wayar duban Burhaan tayi tana cewa " an ma hutasshe da Hajjah, Zulfaa ta had'a mana Iftar".


"Allah ya saka mata da alkhairi".

Daga ba ta kuma cewa uffan ba sai ma mik'ewa da tayi tana d'auko milk daga bag d'in ta, Princess ta fara bawa a baki tana yi tana waya da Ummu tana shaida mata da dawowarsu. Waye-waye ta dinga yi suna d'an hira sama-sama sai after 5 ya fita wurin Fareesahr da dawowarta daga IT kenan don yau ta biya gida can ta samo k'osanta da kunu don ta gama lissafin yau ba zata yi girki ba tun da ko tayi ma ba ci zai ba ita kam sauk'i ne ya samu a gareta. Tana ajiye veil d'in ta ya shigo d'akin dubanshi tayi tana washe baki ta ce " ashe ka dawo Lifeline,i thought kana tafsir".

"Nope ina gida, Nadeefah ce ta dawo".

Ji tayi k'irjinta ya buga da mugun k'arfi, duk da ta san dole ta dawo amma har ga Allah ba ta san yau zata dawo ba ji tayi ranta ya b'aci sosai sai dai bisa darasin da aka d'aurata ya sa ta fuske tana cewa " masha Allah, Allah ya sa an yi ibada karb'ab'biya".


"Ameen" ya amsa yana kallon flask d'in da ta amso k'osai da kunu a kan center table bai ko damu ba bai d'aukeshi a bakin komai ba,duk da ko bai san abinda ta amso a ciki ba. Ba wai kuma don bai da kishin kai akan sabgar da ta shafi amshe-amshen abinci daga gida ba ne, sai dai daga kan Lele ya gane ba sai kana buƙatar wani abu ba ne kake amsowa daga gida ba Aa wani lokacin sai kaji abincin gida kake so ba komai ba a kan kanshi ma yanzu ya gani in da ya ce ba zai ci abincin gidan Umma ba toh da ba k'aramar wahaluwa zai yi ba.


Bai wani dad'e ba ya fita daga d'akin da idanu ta bi shi yayinda hawaye suke cika a cikinsu taf, ta san yau dai d'akin matarshi zai kwana ita da ganinshi kuma sai dai hange daga nesa. Baki ta cije tana zama rakwaf kan kujera tana yin tagumi duk komai ya kwance mata.


Su na sallahr magrib suka nufi gidan su Zulfaa, tana tsaye a bakin windonta ta ga fitarsu shi da ita. Lelen sanye da Abaya mai matuk'ar kyau da tsada kalar maroon wacce ta fito da haskenta duk da dare ne sai k'aramin Turkey veil kalar cream tana sanye da flat shoes sai wayarta d'aya a hannu, shi yake rik'e da hannunta yana kuma d'auke da princess a d'ayan hannun shi ma dai ya canja kaya zuwa soft tissue yard na maza bak'ak'e kan shi babu hula sai gashin da ya gyara da kyau had'iye abinda ya tokare mata a k'irji tayi tana mai sake bin su da ido sun mata kyau sosai wato dai Islaam da Nadeefah had'in Allah ne in dai suka fito waje duk k'iyayyarka sai ka yabawa hakan.


Lumshe ido tayi tana dubansu har suka bar gidan, sai kuma ta gyad'a kai tana cewa " rashin adalci k'arara, in yi magana a ce nayi toh wlh sai na yi maganar yau in ya so ran kowa ya b'aci ". (Nima ina bayanki Fareesah kar ki yarda da wannan rashin adalcin, haka nan ya tasa matarshi su fita bayan ke bai fita da ke? ).



Su ko ba ma su san tana yi ba don gidan Farhaan suka dosa kai tsaye suna hira, san da suka shiga ko har su ElSadeeq sun riga su. Halinsu na tsokanar juna suka fara musamman ma Farhaan da Lele da aka kwana biyu ba a had'u ba har tana ce masa wai tana raga masa ne saboda zai mata takwara shi kuma fad'i yake Allah ya kyauta ma ya sawa 'yar shi suna ta zo tana raina manya. Burhaan ne yace " albarka ce ma zaka samu in ka saka d'in malam, kuma bata roƙe ka ba".


"Toh sannu mijin 'yar albarka" ya furta yana harararshi.


Shi ko ko a jikinshi cewa ma yayi " ai ko baka fad'i ba, kuma ita ba mai raina mutane ba ce".

Tab'e baki yayi yana komawa wata maganar ita ma ba a yi nisa ba suka kuma jayayyya, Islaam ya sake shiga ciki sai da Farhaan d'in ya gaji yace.

"Ai kuma mun shiga uku, ko motsi k'wak'kwara ba mu da damar yi da 'yar uwarmu Islaam zai shiga tsakiya. Anya ba shiga tsakaninmu kake son yi ba?".

"Ba wani shiga tsakani a nan, na lura rainin da kuke mata ne yayi yawa musamman kai".



"Nadeefahr ce zan raina? Wlh Islaam sai in zage ka, yaushe Lelen ta zama yayata da zaka ce wai an rainata?".

"Ohon maka dai tsaya kana tambayata".


"Sai in kamata in zane in ga ta fad'i wlh".


"Da ko baka k'ara ba, ko tayi maka kalar duka ne ita d'in".


"Rama mata zaka yi ne?".

"Za dai kaga abinda zan iya yi kan ta".

Shiru yayi kasak'e da baki yayinda sauran suka saka dariya har da ita Lelen, harararta yayi yana cewa " ai kya yi dariya an sake baki license d'in raina mu".


"Ni ba ruwana, Abban Little".

"Ai in dai Islaam ne ya fi gaban nan, before da su twins ya fara but yanzu abun ya zo har kaina ni ma ban tsira ba" faɗin Sadeeq yana hararar shi.

"Ba ka ci ubanshi ba ne shiyasa, ka wanke k'anwar ka ba shi ne zai dinga maka rashin kunya?".


"Kai dai Farhaan ka lalace wlh, tun da aka sha ruwa kake zagi anya azumin nan naka ya karb'u kuwa?".


"Ban sani ba Islaam".

Zulfaa ce ta mik'e tana cewa " da alamu dai ba azumi kuka yi ba ko? In kun k'oshi ne ni bari in tashi in tallafi cikina" ta furta ganin tun d'azu ba wanda ya kalli gefen da abincin yake kusan a tare Lele da Suleim suka ce " acici".

"Na ji d'in" ta nufi dining su ma binta suka yi a baya kowa ya ja kujera ya zauna, matan ne kowa tayi serving mijinta abinda yake muradi kafin suka yi serving kansu suka zauna. A natse suka ci abincin babu magana mazan suna ci suna bawa yaran a baki cikeda kulawa, ko da suka gama Lele ce ta gyare wurin tsaf suka kai kayan kitchen ita da Suleim suka wanke-wanke fitowarsu ana kiran isha'i yau tare ma suka yi har taraweeh da suka idar ko suka dinga wa Zulfaa sannu don kuwa a zaune tayi sallahr.


Da suka idar ma wani hirar suka d'aura don sosai suka dad'e ba su yi irin wannan had'uwar da juna ba, dama Lele ce shugabar had'a iftar a familyn toh ba ta yi azumi a gida ba wannan shekarar ga shi Zulfaa ta fansheta. Ba su suka bar gidan ba sai after ten lokacin yaran sunyi barci dole sai a kafad'a aka d'aurasu kana suka nufi k'ofar waje bayan Lele ta ciko leda da fruits wai bata da na sahur, har gate suka rako su kafin suka juya zuwa ciki.


Da suka shiga gidan ita ta karb'i Princess ta wuce ciki shi kuma ya nufi d'akin Fareesah don mata sallama, a zaune ya tardata idonta rabi kan agogo rabi kan k'ofa barci take ji sosai amma saboda masifa ta k'i yi burinta ta ga time d'in da zai shigo gidan. Sai ga shi ya turo k'ofar tata ya shigo, d'ago kai tayi ta kalleshi shi ma ita yake kallo kamar mai mamakin zamanta har wannan lokacin ba kuma kallo take yi ko chat ba hasalima idonta k'uri yake kan k'ofa alamun jiranshi take yi wanda abu ne da bai tab'a gani ba a cikin gidan.


Da saura ya k'araso gabanta yana cewa " lafiya kuwa cherrie?".


Hawaye ne ya fara zubo mata a idanu ba ta tare ba sai ma shesshek'a da ta fara yi wanda ya d'aga mai hankali, zama yayi yana rik'eta lallashinta ya ke yi cikeda kulawa da bayyananniyar soyayya.


"Ohh sorry, ki yi shiru toh kar kanki yayi ciwo" ya fad'i a hankali ga kunnuwanta, d'an ajiyar zuciya ta saki sai kuma ta janye jikinta daga na shi tana share hawayen.

Sake janyota jikinshi yayi yana mai duban cikin idanunta yace " me aka miki? Me yake miki ciwo?".

"Ba abinda yake min ciwo".

"Toh me aka miki?".

"Mi ye ma ba a min ba Lifeline? In nayi magana kuma a ce ban da hak'uri na cika k'orafi bayan kuma ni ake zalunta a tsakar gidan nan ".


"Wa yake zalintarki a gidan nan Fareesah".

Dubanshi tayi da magana a bakinta kamar bakinta mara haila zai ce "kai" sai kuma wani irin kwarjinin da yake da shi mai girma ya mamaye idanun rashin kunyar nata, sai kawai ta duk'ar da kai k'asa tana fidgetting yatsunta.


Kai ya gyad'a ya gane me take nufi amma so yake mahaukacin bakin nata ya bud'e ta fad'i da kanta, ganin abinda take yi yasa shi cewa " me aka miki na zalunci".


Shi ma shiru sai d'ukar da idanunta da tayi kan yatsun nata da yanzu ta daina lank'wasu sai had'e su da tayi cikin juna, k'wafa yayi yana cewa " ashe ma ba zaluncin ake miki ba tunda har ba zaki iya magana ba".

"Ai ka san komai da ake mini".

"Ake miki ko nake miki? Ni dai na san a gidan nan babu mai shiga harkanshi sai ni da na ajiye ku. Na kuma san ni kad'ai nake miki laifin na kuma tambayeki kin gaza cewa komai mai kike son in miki tohm?".
Hawayen idanunta ta matso tana cewa " shi ke nan akwai Allah".

"Allah ya isa kike min Fareesah? Saboda me? Me na miki?" Ya fad'a a mugun gajiye da b'acin rai, cikin d'an rawar murya tace " ni ba Allah ya isa na yi ba, amma na tabbatar ko ban yi ba zai saka min saboda abun yayi yawa. Daga dawowar matarka ka tattara k'afafu ka kwashe zuwa can sashen, magrib na yi ka d'auketa kun fita sai yanzu kuke dawowa gidan nan ko taraweeh d'in da muke yi yau bamu yi ba. Yanzu kai tsakani da Allah a taka mahangar an mini adalci kenan?".


"Oh wow da gaske Fareesah? Oh so kike in k'yale matar da tayi good 3weeks bata gidana? Ko so kike in k'i kaita in da zata ci abinci bayan ke d'in ba kin girka kin bata bane, ba ma ki girka kin ci ba kin gwammaci ki amso a gida ko so kike ta yi girki a halin tafiya saboda in faranta miki rai? Huh tell me Fareesah!" Ya jero duka tambayoyin cikeda b'acin rai kamar wani namijin zaki da ke shirin had'iyeta d'anye.


Yawu ta had'iye tana cewa " in fitan ne ai sai dai mu fita gabad'aya shi ne adalci, ni tunda na zo gidan nan baka tab'a fita da ni wani joint or park ba kullum ina cikin gida har na zaci ko baka son fitan ne but i was wrong da ni ne baka son fitan ba komai ba".


"Eh dake ne ban son fitan sai aka yi ya ya? Uhmm na ce and so what?!".


Baki ta bud'e zata yi magana ya kad'a mata d'an yatsa cikeda masifa yace " shut it, Kar ki sake ki faɗi wata magana a nan ko kiyi nadama". Yana furta haka ya juya zai fita har ya kai k'ofa ya juyo yana dubanta.
"You know what? Na gaji da abubuwan nan. Ban saba da su ba ban son mita, naci da mayata ban son doguwar magana da yawa but ke shi kike so a kullum. Ba kuma zan gaya miki ki daina ba, ki cigaba ga ki ga saka ido da k'orafi nan Allah ya baki sa'a" yana fad'in haka ya juya ya fita ko sai da safe bai ce mata ba sai ma buga k'atuwar ƙofar katakon sashen nata yana wucewa.


Komawa tayi ta zauna cike da nadamar k'orafinta, da kuma rashin iya kissarta. Duka-duka fa d'azun nan yayarta ta gama mata karatun har ta yi kamar ta d'auka don d'azu ta kwata, amma yanzu gashi nan ta b'arar da komai da shegen bakinta. Sai kuma ta saki murmushi cikeda nasara don ko ba komai ta cusawa Lelen da yake rawar k'afar yaje ya samu, wanda ba lallai ma ta bashi had'in kai ba don haka duk rawar kan da yake yi dole ya tashi a banza dukansu su yi kwanar bak'inciki atleast zata samu sukunin cin zalinta da aka yi aka fita may be ma har da tsinannen kifin da take yawan ci har yake mata iyayi da " matata na siyawa" har da kwaikwayar yanda yake maganar tayi tana sakin tsaki mik'ewa tayi ta rufe k'ofar da ya bugo mata ta wuce ciki tana sakin dariyar mugunta.

Shi ko da ya shiga bai samu kowa a parlorn ba sai kawai ya wuce bedroom d'in shi, wanka ya wuce yayi kai tsaye ya saka pjs masu gajeran hannu da wando. Fitowa yayi zuwa part d'in ta hannunshi d'auke da wayarshi, sai da ya kashe komai kafin ya nufi bedroom d'in da ya san zai sameta.


Tana kwance tayi wanka ta shirya cikin kayan barci marasa nauyi, ta saki AC don yau akwai zafi ba laifi kasancewar ba a yi ruwan da hadari ya taru sosai ba sai 'yan yayyafi wanda ya tado zafin k'asa ya bazawa duniya. Dubanta yayi yana sakin ajiyar zuciya ita ko ba ma ta sani ba don barcinta take yi hani'an cikeda gajiya, wuta ya kashe yana hawa gadon rungumeta yayi cikin jikinshi cike yake da kewarta but kalaman Fareesah sun sa komai ya fice masa a kai ga shi ma bacci take yi wanda a bayyane yake tana buƙatar shi. Ba ma ta san da shigowarshin ba sai da asuba ne da ya tasheta suka yi sahur da hot milk and fruit, tana sallahr asubah ta koma ta kwanta.


Da safe ma ba ta iya bud'e idanu ba sai da Sairah ta isheta da tashi kafin ta tashi zaune tana d'aukarta shayar da ita ta fara iya gejin da zata iya gamsuwa kafin ta fito parlor grains ta had'a mata ta samu ta d'auka da kyau kafin suka koma ciki, wanka suka yi ta shiryata tana duban agogo yau fa saturday ina kuma ya je da safiyar nan haka?.


Goya yarinyar ta yi ta fara gyaran gidan ta kowani sak'o da lungu tana kan gyaran waiting room aka yi knocking lek'awa tayi Fareesah ce tsaye da waya a kunnenta tana magana, bud'e k'ofar tayi dai-dai da tana cewa " ina fa da k'yar ya tafi jiyan, kin san yace min bai so ta dawo ba ya tura ta umara ne saboda mu samu sakewa sosai ne. Ai ina gaya miki Lifeline ya susuce duk wani motsi cherrie...."


Kasak'e tayi tana ajiye wayar tace " sorry Mom princess ban san kin bud'e ba" ta furta kamar ba da gangan ɗin nan tayi duk abinda ta yi d'in bayan musamman ta taho part d'in da niyyar tada mata da hankali, don ta san jiyan ta ga dad'ewarshi wanda bata sani Lele ta riga ta yi barci sanda ya dawo ba. In ma bata yi barcin ba toh ko a jikinta kan dad'ewar ta shi don ta cire shigarshi d'akin Fareesah a abinda zai b'ata mata rai shiyasa bai damunta, kuma ko yanzu maganar nan da ta ji tana yi ko kusa bai d'ad'a ta k'asa balle ya kayar ba don ta gama sanin waye Islaam da kuma sabgarshi abun mamaki kuma ta gama fahimtar halayyar Fareesahn da ita d'in irin munafukan matan nan ne wainda in baki san halin mijinki ba zata shiga tsakankani in kuma ta had'a rabawa zai yi wuya, but abinda ta kuma lura da shi is ita kanta ba wai ta iya munafuncin da kyau ba ne hakan ne ma ya sa ta kan b'aro jirginta in ta kwaso kayan gulmar tata. Don haka murmushi tayi tana cewa " ki shigo" ta na fad'in haka ta juya ciki, hararar bayanta Fareesahr tayi tana mai jin mugun tsanarta wato ita dai bata tab'a nuna weakness d'inta a duk abinda zata yi, komai sai ta yakito rigar murmushi ta lullub'e fuskarta ta kuma kawar da duk abinda zai sa a iya karantar yanayin da take ciki.

A main parlor suka zauna da ita gaisawa suka yi kadaran-kadahan inda ta tambayeta ya hanya, Alhamdulillah ta amsa mata itama tana tambayarta gida, ibada da kuma ITn da Islaam ya shaida mata tana zuwa. Shiru ne ya biyo bayan zaman nata sai kuma bayan minutes Lelen ta mik'e tana ce mata bari ta zo, ciki ta shiga tana bud'e jakarta da ta dawo da ita wata doguwar silk riga mai tsada ta d'auko wanda musamman ta siya don bata tsaraba sai dabinon ajwaa da zam-zam da ma su bagaruwa tsarabar dai saudi da ake kawowa.


A babbar leda ta sanya tana fitowa daga d'akin mik'a mata tayi tana cewa " ga wannan babu yawa". Kamar kar ta amsa sai kuma zuciyarta ta raya mata ai gwara in amsa tunda da kud'in mijina aka siyo min, may be ma shi ya ce ta siyo min zata min iyayi in ma kud'inta ne ai ba rok'onta nayi ba balle ma ta ce.

Amsa tayi a gyatsine tace " nagode ai, mai yawan kenan" sai kuma ta mik'e tana cewa " na katse miki aiki bari in je".

"Haba kam babu komai na gode sosai".

Tare suka rankaya zuwa k'ofar fita ta bud'e tana fita Lelen ta saki murmushin halayyarta tace " kina ruwa yarinya, baki san da wa kike zancen ba wai har da wani kin san ya turata umrah saboda ni, mtsww mutumin da da k'yar ya bari na tafi babu shiita ga munafuka".

Ita ma tana fita ta ja tsaki tana cewa " munafuka kawai, komai aka miki ba za'a huce ba sai dai mutum ya k'arawa kan shi bak'inciki" ( tunda kin gane hakan da zaki hak'ura da yi da ya fi miki).


Kammala gyaran tayi ta saka turare mai sanyin k'amshi ta koma parlor tana zama, zamanta bai fi da mintuna ba sai ga Islaam ya yi knocking yana shigowa kamar yanda ya saba in ya kawo cefane a nan waiting room ya kan jera ko parlor sai ya gama shigar da kayan sai ya mik'a kitchen. 

Yau ma haka yayi sai da ya gama shigo da komai sannan ya fara d'aukar ledar farko ya nufi main parlor, da sallama a bakinshi tana daga zaunen ta taso tana dubanshi murmushi ya mata ta mi'ke tsaye tana cewa " sannu da dawowa" yawwa ya amsa yana wucewa kitchen itama waiting room d'in ta wuce ta d'auko ta bi bayanshi zuwa kitchen d'in.


 Kayan ta bubbud'e cefanen da ba su da shi ne ya kawo, tun daga nama, veggies da fruits har da kifinta da ma dried spices da duk da tana da wasu sai da ya k'aro mata da wasu
Saka komai a inda ya dace ta ta wanke hannayenta saboda k'arnin kifin da ta tab'a kana ta dube shi tana cewa " Allah ya k'ara bud'i Yaa, ya biya buk'ata" murmushi yayi yana rungumeta yace " Ameen ya rabb, yanzu yau me za'a mana for iftar".

"Abinda mijina ke so".

"Kin san komai kika yi ina so, but ina son kunun gyad'a".

"Duk yanda kace, your highness" ta fad'i tana jinjina masa irin na sarauta, murmushi yayi yana dungure mata kanta fita yayi don kai wa Fareesah nata ita kuma fiddo gyad'a soyawa ta fara yi ta murjeta da kyau ta fece ta jik'a ta d'ibi d'anyen shinkafa iya yanda zai isheta ta jik'a nan ta fara tunanin abun da zata had'a da shi. Murmushi tayi da ta tuno abinda zata yi wanda ta san shi ma zai so,kana ta fita ta koma parlorn.


Bai dad'e ba ya dawo d'akin nan suka zauna suna hira time-time suna amsar bak'i masu barka da zuwa kuma kamar kowani karo wannan karon ma sai da ta kawowa kowa tsaraba amma na Islaam da Sairah ya fi na kowa.



Yamma na yi ta koma kitchen shirin abincin iftar ta fara kamar yanda ta saba a kowani lokaci kai kace sabuwar amarya ce wacce take d'aukin gidan miji, Yam tofu ta had'a wacce ta wadatu da carrot da tarugu sai albasa da liver mai d'an yawa a cikin k'wai ta soya shi ta had'a chicken curry ta ajiye a gefe. Alkubus da garden egg sauce ta had'a da ya ji kifi busasshe ta zuba kowanne a inda ya dace kafin ta koma kan kunun gyad'ar da tayi masa wacce ta ji milk, coconut har ma da d'an apple extract a flask ta juye kana ta fito da su a kan dining ta jera.

D'aki ta koma tayi wanka ta shirya cikin gowns d'in ta gajeru sai dai ta yau ba free ba ce, dai-dai jiki take ta d'aure gashinta ta sanya hula ta fito. Lokacin har ya kuma wanka ya sanya short kaya shi ma a nan suka zauna suna kallon tafsirin Sheikh Murtadha Fadhlu, a haka har aka kira sallah.

Yau dai Islaam ba k'aramin abinci ya kwasa ba, ya ci ya k'ara don sosai yayi missing d'in girkinta kamar me. Yana ci yana yabawa har sai da ta saka masa waigi kunun ko cewa yayi a bar masa abunsa da asuba da shi zai yi sahur, ita dai dariya ta dinga yi cikeda jin dad'i tana mai jin kanta a sama.


Ai ko abincin da ya kwasa a kanta ya k'are don bai d'aga mata k'afa ba sai da ya tabbatar mata da cewa ba iya abincin Lele ya ke missing ba har da ita kanta, ta ko galabaitu ba laifi amma kuma bata damu ba don tana alfahari da abinda ke faruwa har ji take yi ta fi sauran mata zamowa mace abun alfahari ga mijinta. 

Washegari fita tayi office d'in ta ta fara zuwa sai da aka mata gyaran kai mai kyau ba ayi mata kitso ba da lalle, kana around 1 ta wuce Yerwa a can ta k'arashi yininta har dare ba ita ta baro gidan ba sai dare Islaam d'in ne ma ya ce ta bari ya zo ya d'auketa sai kawai ta bar motar a can.


Ranar jajibari da wuri tayi aikinta kamar wancan karon wannan shekarar ma Umma ta aiko musu da masu aiki, kowa da nata ita dai Lele tare suka yi aikin ita ko Hajiya Fareesah ta nad'e a kujera tana ta bada command saboda isa har waya ta kira gidansu sisternta ta zo tare suka yi aiki da maid d'in.


Kasancewar sun fara da wuri ya sanya wannan karon around 5 ta gama madara ta zafafa ta dafa couscous da taji kayan had'i ta ajiye ba tayi abu mai wahala ba saboda dai ba ita ke da Islaam ba yau so ba zata yi abunda zata ji a jikinta sosai ba.

Wanda shi kam ba haka ya so ba so yayi ya zamana ita ce da girki da sallah don ya san zai fi samun abinda yake so ta b'angaren abincin da sauran buk'atu amma ya ya iya da abinda ya fi k'arfin wuta wai in ji kishiyar k'onanna tunda shi ya kawo kayansa ai dole a bar masa abinsa ya d'aga sama. 

Tana samu tayi bud'e baki ta yi isha'i ta shige ciki ko sanda ya zo mata sai da safe ma tayi nisa a bacci dama key ya saka ya bud'e room d'in sai kawai ya d'uka yayi kissing lips d'in ta ya fita daga d'akin. Ko da ya koma can d'in ita da sistern nata ya tarda da zata kwana a nan saboda ba su gama aikin ba duk da ba wani abu da yawa take yi ba cincin ne sai cupcakes da tayi sai dubulan aikin naman ne tace a bari sai dare wai kar su yi a yi azumi talatin sai da ta tabbatar da an ga wata kafin ta yarda aka tafasa shi ko Islaam bai san wannan ba yana wucewa d'akinshi ta biyoshi a baya nan yace mata ta kawo masa naman da suka soya zai ci. 


"Ba mu soya ba ai".

Kallonta yayi a tsanake kana ya dubi wallclock yana cewa " wani irin baku soya ba".


"Ai ka san aikin da yawa wallahi, kuma na fi son in yi aikin nama da kaina".


Girgiza kai yayi a ranshi yana mai cewa " ai dole ki fi so kiyi da kanki kar wani ya ci" a fili ko cewa yayi " amma kun tafasa ko? Ku soya please".


"Ok Lifeline bari in je".

"Yawwa tohm cherrie" ta furta tana fita zuwa parlor, sawa tayi Adaman ( kanwarta) ta soya naman ta kai masa cikin room d'in shi har da chi exotic mai matsakaicin sanyi. Amsa yayi har da shi mata albarka ya fara cin naman cikeda k'walama kai kace shi ma bai cin naman ne ( ashe ba Fareesah bace kawai mayya).

3am ta tashi ta d'aura tukunyar tuwo da kaskon funkaso da shi zata yi wannan sallahr in da zuwa bayan asuba ta kammala komai tsaf ta jera a kulolin da ta saba, ta saka na nata gidan a wata flask d'in, gidanta ta gyara tsaf kana ta yi wanka ta ma Sairah itama. Agogo ta kalla to 8 shiryasu tayi cikin Abayar da ta siyo musu iri d'aya ita da Sairah daga saudi bak'ak'e ne sai hijabai cream na mercedes nata dogo har k'asa amma ba ta saka ba ajiyeshi tayi kan sofa da bag d'inta, ita kuma Sairah kids malaysian fashion hijab ta saka mata, tana cikin saka mata takalmi ya shigo d'akin sosai yayi kyau cikin milk d'in shaddah babbar riga da hula dara sai fitinannen k'amshin shi ne ke tashi dubanta yayi yana bud'e mata hannu da sauri ta taso tana shigewa jikinshi a k'asan mak'oshi ta furta " barka da safiyar sallah Alpha, Allah ya karb'i ibadunmu gabad'aya".


"Ameen wify, you too kun yi kyau dukanku".

"Kai ma kayi kyau, dama kai mai kyau ne Alpha".

Murmushi yayi still tana jikinshi sai da suka d'auki mintuna kafin ta zare jikin tana cewa " Alpha kamar ka san kayan da zamu saka yau?".

"Ban sani ba, amma na san kalolin da kike so ko dai  ki saka cream, milk or white hijab".


Murmushi tayi tana jan hancinshi jin wai saboda yayi anko da ita ya saka kayan, ita ma ta gama lissafin in da wani colorn kaya ya saka da tabbas itama sai ta canja colorn hijabin saboda su yi ankon, wristwatch d'in shi ya kalla yana cewa " wife kun gama komai mu tafi ko? 9:30 za a yi sallahr yau and it's already to 9".

Ok ta amsa tana nufar wajen jakarta shi kuma ya d'auki Sairah da tun d'azu take ta kiran PaaPaan nata amma hankalinshi na kan kiran Lunarshi sam bai ji ta ba, fita suka yi zuwa parlor in da sai yanzu idanunshi ya kai ga kayan da zata kai na sallah a bayyane ya furta kalmar Allah ya mata albarka ta amsa cikeda jin dad'i mai bayyana kan shi a fuskarta sosai. D'auka yayi bayan ya cire babbar rigar ya rataya a coat hanger da ke k'ofar shiga parlorn, waje ya nufa yana ajiyewa biyo shi tayi da wasu sai da suka gama jerawa a booth tsaf kafin ya kunna motar yana warming tare suka koma ciki hijabinta ta sanya ta rik'e jakarta a hannu shi kuma ya d'auki Sairah kamar ranar nan hannunta ya rik'e cikin na shi suka nufi wajen.


Tun sanda ya nufi gefen Lele suke tsaye a window har suka fito suka saka kayan a mota suna kallonsu, ko da suka wuce ciki ba su tashi ba sai Adaman ce ta tab'e baki tana cewa " yanzu Aunty Fareesah ina za'a kai wancan uban abincin?".


"Ohon mata, ko sadaka zasu yi ne wa ya sanin mata".

"Amma ba ita ta dafa duka ba?".


"Wa ya gaya miki? Duka ita tayi ai in kina nemar 'yar wahala da kin samu wancan tsinanniyar kin gama in tana aiki yanda kika san ba 'yar gidan masu hali ba cabd'in ina zan iya".


"Ni ma kam ban iyawa, ko a haka na in miji ba zai samo 'yar aiki ba toh ba komai zai iya samu ba".


"Ai haka nake masa, in ya gaji ya nemo mai aiki ni ban zo gidan nan don in sha wuya ba" dariya suka saka k'anwar na ce mata aikinki na kyau sai ga su can sun sake fitowa Adamar tace " ga su nan sun fito fa ki ce abun mai anko ce harda babynsu". Kallonsu tayi cikeda kishi tana cewa " ai haka suke yi in zasu fita anko suke sha, kamar wasu k'auyawa".

"But sun yi kyau fa Aunty".

"Sai su yi ta yi" ganin ya do shi d'akin ya sa su fita daga labulen da suke lab'en in da Allah ya taimake su tinted ne da sai an gansu. Dukan su kitchen suka wuce da sauri shi kuwa yana shigowa ya fara kiran sunanta " cherrie" fitowa tayi daga kitchen d'in tana cewa " dama ba ka wuce ba?".

"In wuce ina? Bayan i told you dake zamu tafi masallacin ga shi kuma ko shiryawa baki yi ba?".

"Ai babe bamu gama aikin ba ne, ku je kawai ban zuwa Ahh princess wannan gayu zo" ta k'arashe tana mik'awa yarinyar hannu, k'in zuwa tayi tana mannewa jikin baban tana kiran sunanshi harararta tayi a fakaice a fili kuma sai ta d'an yi yak'e tana cewa " wai har yanzu baki daina k'yuiya ba?".

"Baki d'aukanta sosai ne shiyasa yanzu dai kin ce baki zuwa ko?".

"Kalli fa time yaushe nayi wanka na shirya?".

"Ba son zuwa dai kika yi ba, Madam saura in na dawo ki ce ba a miki adalci ba".


Shiru tayi tana tunani kamar an tsikareta tace " gimme ten minutes to in shirya"

"Zan jira ki a mota in kika wuce ten minutes zamu wuce" yana fad'in haka ya fita, da sauri ta wuce bedroom d'in ta dan shiryawa tayi tunanin gara ta bi su da dai ta zauna tai musu gadi.


Ita ko Lele bayan shigarsu ta tuna bata d'auko na Fareesah ba gashi daga masallaci ba dawowa zata yi ba, key ta sanya ta bud'e part d'in ta d'auko package d'in da ta mata wanda fitowarta yayi dai-dai da dawowar Islaam d'in.  Kallonta yayi yana cewa " na waye wannan?".

"Fareesah" ta amsa cikin sanyin murya, cewa yayu '' barin mik'a ma ta " ya amsa yana komawa d'akin a bakin k'ofa ya tsaya yayi knocking Adama ta bud'e tana kallonshi mik'a mata yayi yana cewa " in ta fito ki ce mata in ji Nadeefah" ya furta yana juyawa, amsa tayi tana komawa ciki motar suka koma shi da ita zamansu bai fi da 5 minutes ba ta fito cikin Atamfa embellised mai matuk'ar kyau wacce ta hau da dogon farin hijabin da ta sanyo wanda ya ji guga ainun sai k'yalli yake yi shi ma mercedes ne. 

Baya ta bud'e ta zauna tana gaida Nadeefah amsawa tayi da faraa tana tambayarta aiki daga haka ba su kuma magana ba, Nadeefah ma hankalinta na kan titi da kuma Tasbihin tafiya masallaci ita da Islaam ita ko Fareesahr danna waya take tana yin streaks na tafiya masallaci kamar yanda mu kan yi dukda wasu su kan had'a biyu ne suna tasbih suna kuma yin streaks.


San da suka isa masjid d'in ma an fara haramar sallah sai ba su tsaya wata-wata ba suka jona layi a inda su Suleim suka ajiye mata, ita da Fareesah suka hau kan daddumar while shi ya wuce gefen maza. Da aka idar da sallahn suka samu sukunin gaisawa da mutane wanda ita Fareesah zama tayi 'yar kallo don daga gaisuwa ba sa kuma wata magana ita ko Lele tana cikinsu Suleim suna ta shak'iyancin da suka saba su Aunty Fadwaah suna mata tsiyan wai inda da Islaam aka je umrahn da sun ce tsarabar Mecca ko Medina ce aka samo, dariya tayi tana cewa '' ai yanzu ma sai ku fad'i hakan wa ya sanu ko jirgi ya hau ya tafi yi min cikin?''.


Ainah tayi k'asa da murya tana cewa " ga dai wacce ta samu cikin nan Amarya".

Kallon gefen da Fareesahr take suna gaisawa da Umma suna kwashewa da dariya suka had'a baki suna cewa " Ainah ke bala'i ce". Ba su wani jima a tsayen ba mazajen suka iso sai kawai kowa ya nufi motar shi kamar kuma yanda suka saba direct Yerwa suka nufa.


Yanda suka saba haka suka yi ma wannan karon ma haka suka yi sai da suka jera kowani gida suna yi suna ajiye kayan barka da sallah tun daga gidan Baba Tijjani har suka dangana gidan Umma. Ita dai Fareesah tana ta ganin abu yayinda duk rashin kunyarta ta ji wani kala don alamu ya nuna Lele tana da kyauta kuma ko kyautar riya take yi tana da mind wai ko da y'an uwanta ne ai ita ba zata iya bai wa natan haka ba, a familyn na su ma ba a haka kowa ta kanshi yake. Ta gefe guda kuma tana jin nauyin bata kawo komai ba,tana kallon sanda Safwaan ya kinkimi basket d'in da aka kawo da sunan Umman yana mai cewa " dama ke kad'ai nake jira K'amshi" harararshi Umman tayi taba cewa " ka ma ajiye shi don babu kai a wannan kwanon".

"Umma ashe za'a yi yak'i kenan, tab ai gwara a hanani na kowa da a hana ni na K'amshi".

"Ni dai ban kawo dominka ba ah toh" fad'in Lele tana murgud'a baki.



"Ashe za'a yi bala'i kenan?".


"A kanka" ta amsa kan ta tsaye, cewa yayi " haba K'amshi kar ki bari a mana dariya mana, yawwa barin miki renewing subscription d'inki na Showmax ma ".


"Cin hanci ko?".

"Barka da sallah dai" ya amsa yana karb'an Princess hannun Umma.

"Toh zo kayi yanzu kafin in nemeka in rasa, ni yama min kad'an as barka da sallah daga wurinka".

"Ya isheki ma malama, kud'ina na aure ne".


"Na dai 'yanmata" suka had'a baki ita da Najwaah da ke zaune gefen Ummahn dariya ya saki yana cewa " Lallai ma mutanen nan, ke Lele kar ki biyewa mutanen duniya kin san su da sa ido".


"Ka kira sunana kawai Safwaan".

"Ni dai ban ce ba, Malama kin ma ja barin sa miki wani abu Mom Princess ta mu Allah dai ya k'ara zak'in hannu " danne-danne yayi a wayarshi sai ga alert ya shigo mata tata wayar, d'agawa tayi tana cewa " hehehe Fave, gobe ka zo gida kana da special package".

"Shiyasa nake son ki uwargidan Yaa Islaam" ya amsa da mugun dariya yana wucewa wurin dining abincin data kawo ya zuba a plate yana dawowa nan ya zauna bai ko kalli Najwaah da ke cewa itama ya saka mata barka da sallahnta banza yayi da ita sai da ya ga zata dameshi kana ya tura mata yana cewa "yanzu sai ki bar ni in huta" ya amsa yana murgud'a mata baki. 


Dariya suka yi duka ba su sake magana ba mik'ewa suka yi suka fara haramar tafiya, gidan Hajjah ya kai su da gidan su YaMara da YaMadari ba su wani zauna ba ya wuce gidan Ummu da su a can ma sun samu tarba ta musamman har da Fareesahr shi ma dai ba wani zama yayi da ya d'auketa suka wuce gida aka bar Lele da Sairah.

Sai dare ya zo ya d'auketa suka koma gida in da bai sarara ba sai da ya amshi barka da sallahn shi yanda ya kamata har ma da k'ari, the next day ba su je koina ba sai su Adnan ne suka kawo mata ziyara wanda shi ne karon farkon da suka zo gidan tun bayan auren Islaam d'in san da suka zo ma Fareesahr ba ta nan sai gab da magrib ta dawo hakan ya sa Salmahn ce kawai Nadeefah ta raka ta ga d'akin amarya shigarta ne ma ta mik'o mata kwanonta na jiya tana godiya ba su dad'e ba suka koma sashen Lelen in da Salmah duk yanda ta so sai da ta kasa tana tseguntawa Lelen in da Islaam ya samo wannan matar.

Uku da sallah aka yi zaman meeting kamar yanda aka saba ana gamawa gidan Hajjah yau ta wuce don wancan ranar ba ta samu wannan damar ba, ita ko Fareesah sai tayi nata wucewar gidan Umma da d'an k'ullin da ta kawowa Ummahn na barka da sallah. Umman dai ta amsa tana kallon d'an abunda ta kawo ta kasa jurewa sai da ta raina don yayi kad'an ainun ko na Lele ita da ta yi rabo sosai ya fi nata yawa ita ko ko su YaBudu ba ta bawa ba balle 'yan familyn.


1 week after sallah aka yi launching sabon park d'in lele mai suna Yerwa Gardens and grills wanda wurin shak'atawa ne da kuma suya spot na zamani, wurin ya had'u iya had'uwa fiyeda tunanin mai tunani. Walima suka yi aka saka mata albarka washe gari aka fara normal sales, ko sati ba a rufa da yin walimar ba Zulfaa ta haifi kyakkyawar mace kamar ka saceta nan fa suka shiga zarya kullum suna gidan, in da tun ranar farko aka shaidawa Lele da cewa takwara ce fa aka yi matan da gaske nan fa ta k'ara k'aimi wurin had'a kayan takwara ranar suna ita da Islaam suka kai nasu kayan gwanin sha'awa abun sai hamdala.


Ana gama sunan da kwana biyu ta yaye Sairah bisa matsawar daddyn ta a cewarshi ko zasu samu a samu wani cikin, ba yanda ta iya haka ta yayeta da kan shi ya kinkimeta ya kai gidan Umma in da yana dawowa ya fara baza capacity da fatan ko za'a samu abinda yake burin...........


Ameen dai Islaam, mun k'osa a samu wasu 'yay'an muma😁.
Love y'all

Deejasmah🎭